Showing 18001 words to 19825 words out of 19825 words
mamy tayi mata bayanin hakan , taɗanji daɗi ,ta dawo itama ta shirya cikin leshi mai ruwan madara wanda yayi mata kyau ta sanaya warwaro da sarƙa bayan ta gama simple makeup ɗinta ,ta janyo wayarta suka gaisa dasu mamy da Humaira tace "sunanan lafiya .
After one week da biki , tun washe garin biki da Yasir ya kusanceta bai ƙara kulata ba ,a hakan ma yanacewa tsautsayi ne.
Yau ta kama Lahadi yana zaune a gida dama ba wani aiki yake ba iyakaci yaje office ya cike takardu ya shigar dasu ya dawo .
Da sassafe Anisa tayi wanka ta haɗe cikin english wear na riga iya cibiya da gajeren wando iya cinya ,ta sanya farar hula ,
Ta dawo palo ta sake kiɗa kamar gidan zai tashi sama , ta dinga tiƙa rawa .
Da sauri ya fito sbda baya son yawan hayaniya ya jingina da bango yana ƙarewa shigar da tayi kallo , beautiful baby amma kulata janyo raini " ya daɗe yana kallon kugunta inda yake karkaɗawa batasan yana gurin ba , kashewar da akayi ne ya sata juyow ...
[6/22, 8:50 AM] Zainab✍️: 75-76
Zatayi magana ya tako har inda take ,zai kamota ta ruga da gudu ta rufe ƙofa.
Satinsu biyu da aure mamy tazo , Anisa ko kaɗan bata sanar mata da halin da suke ciki ba ,haka kuma jikin Anisar bai nuna wata damuwaba .
Yasir dayaga mamy sai ya shiga nan nan da ita dan karta fahimci suna cikin wani irin zama ,mamy na tafiya aka koma gidan jiya .
Washe gari kuma Hajiyar Yasir tazo , Anisa tayi mata abinci mai rai da lafiya ,Hajiyar da Yasir duk suna palo a zaune ,Anisa ko sai kaiwa da komowa take gurin haɗa girki .
Cikin ikon Allah ta jerewa Hjya abinci iri-iri a gabanta da drinks wanda ta haɗa da kanta , wannan abu ba ƙaramin yiwa Yasir daɗi yayi ba ,sbda a rayuwarsa yana son mahaifiyarsa so mai tsanani ,abinda Anisa tayi sai yaji yana sonta sosai bazai ƙara wulaƙantata ba ,amma inda ta fara yi masa rashin mutunci bai san ya zaiyi ya gyarata ba .
Bayan Anisa ta kawo plet ta zubawa mamy jollof ɗin shinkafa wacce taji kayan lambu da yankakkiyar hanta da da soyayyen naman kaza a sama ,ta juya zata koma ɗaki Hjyar Yasir tace "yata zo ki zauna ki huta matso da abincin muci tare " tabbas Hajiyar ta burgeta dan tana ta nuna mata so sbda har tambayar Yasir take "yana ɓata mata rai ko ?"Yasir yace "a'a .
Langwaɓar da kai yayi a jikin hjya kafin yace "Hjyata ki tayani bawa Anee Haƙuri " Wow Anisa ta faɗa a cikin zuciyarta sbda ,inda ya kira sunan nata abin ya burgeta kamar a bakinsa aka samo Anee,
Hajiya tace "ƴata yana cin zalinki ko ?" Anisa tayi murmishi kafin tace "a'a momy " Yasir yace "hjya nidai ki tayani bata haƙuri " hjya tace " ƴata kiyi haƙuri inma wani abun yayi miki ,Yasir yanada saurin fushi haka yanada saurin sakkowa kiyi haƙuri " kukan dake ƙoƙarin taho mata ne yasata toshe baki ta miƙe da gudu tabar gurin .
Koda taje ɗakinta kuka tayi mai isarta ,ɗago mata kai taji anyi ,cikin lallausar muryarsa yace "Anee ina mai neman yafiyarki duk wanda ya kula da mahaifiyata ko tsanarsa nayi takan koma soyayya ,hjya ce tace kizo "
Muryar Anisa ƙasa ƙasa tace "ina zuwa ,
Sai da ya fice itama ta fito tare da zubewa gaban Hjya tace "momy gani " hjya tace "kai Yasir kaine mai lefi ,Anisa kiyi haƙuri ki yiwa mijinki biyayya ku gina rayuwarku cikin so da ƙaunar juna "
Anisa ta gyaɗa kai Yasir yana ta sakar mata murmishi sbda kyautatawa mahaifiyarsa da tayi yama mance da auran dole akayi musu .
Bayan sati ɗaya ,yau da bikinsu sati uku cif ,
Zaune take a palo ,hannunta na hagu riƙe da remote ,hannun damanta kuwa ta riƙe glass cup mai ɗauke da kunun aya ,wanda mamy tace ta yawaita sha ,
A yanayi na son kasancewa da mijinta take ,sbda tsigar jikinta har wani tashi take , tana sanye da yaloluwar riga mai shara-shara ,wacce da ita da babu duk ɗaya , gajeren sikel ne a jikinta wanda ya baiyanar da kyawawan mazaunanta sikel ɗin iya guiwa yake gashi pink rigar far tayi mata kyau , kanta ko babu komai sai ƙananun ƙitso da suka zubo mata gadon baya ,
Cikin Sauri Yasir ya fara saukewa daga bene ,
Ɗaga kanda zaiyi ya hango Anisa zaune hannunta riƙe da cup tayi masifar yi masa kyau , yana son yaga mace tayi shigar ƙananun kaya ,
Cikin nishaɗi ya ƙarasa saukowa yana takowa a zuciyarsa ko cewa yake "ai hjya ta sasantamu mun shirya "ya isa gurinta yana cewa "my Anee "da gudu tabar gurin har wani karkaɗamasa ɗuwawu take ,ta koma bedroom ɗinta ta danna key .
Mararta data murɗa lokaci ɗaya ne ya sata ƙwala ƴar ƙara kaɗan tare da riƙe marar tana ambaton sunan Allah , a fili tace "kodai inje gurinsa ne ? sai kuma naji tace "kai ina sai na ƙwatarwa kaina ƴanci " haka ta wuni ,shigo ransa ya ɓaci kuma a nasa ɓangaren ma neman kasancewa da ita yakeyi .
Haka ya haƙura ya fice , yana fita masu tsaronsa suka fara kwasar gaisuwa ,
Yau kam sunga sauyi rai a ɓace yake amsa musu saɓanin da ,da yake amsa musu cikin sakin fuska amma inya amsa sau ɗaya shikenan .
Kwanci tashi asarar mai rai yau sunkai kusan wata uku da aure ,Anisa ko ɗai ɗai ranar da bazatasha lemon tsami ba , gashi kullum sai tayi wannan shigar tunda taga yana so ,
Washe gari Yasir ya ɗau alwashin ,kasancewa da ita da kuma zama su fuskanci juna inhar shi yayi mata laifi ya bata haƙuri.
Yauma kamar kullum ta fito ƙarfe 12:11pm na rana ,ta kunna kiɗanta tana rawa , sbda yau kam a cikin farinciki take Humaira da mama Ruqaiyyya sunce zasu zo "
A raɓe yake kamar koda yaushe tana ganinsa ta gudu ,yau kam cikin sanɗa yaje ya ɗagata cak tana faman ihu ya wuce da ita bedroom ɗinsa tare da sanyawa ƙofar key ya zare ya cire na toilet ya dawo kusa da ita tare da ɗaukarta ya ɗora a kan cinyarsa kafin yace " my Anee haukatani zakiyi ? tun yaushe nace miki na tuba amma kinƙi fahimta , hjyata bata baki haƙuri ba ? ko kinaso inje ince mata guduna kike ?
Anisa tai saurin ɗago kanta kafin tace "nifa ba gudunka nake ba ,kaine kace baka sona tom meye na rawar kai a kanka ?" Yasir ya ɗan rausayar da kai kafin ya haɗe hannayensa biyu yace "dan darajar fiyayyen halitta ki yafemin ,mu gina rayuwarmu mai tsafta "
Anisa na kuka ta rungumeshi daga nan yahau raɗa mata kalmomin soyayya waɗanda sukayi tasiri a zuciyarta.
Sai da ya tabbatar soyayyarsa ta sami gurbi a zuciyarta sannan yazo zai fita tace masa "ƙanwar mamy da ƙanwata zasuzo " Yasir yace "akwai kuɗi a loka duk abinda kika ya dace ki basu .
Anisa tace "Allah ya kareka daga dukkan sharri,Allah ya dawo dakai lafiya " Yasir yace "amin"
Yana fita Anisa tace "wai dama yana magana ?shegiya soyayya .
Yasir na cikin mota yana ta tuno adu'ar da Anisa tayi masa ,
[6/22, 9:56 AM] Zainab✍️: 77-78
2:33 Humaira da mama Ruqaiya sukazo , bayan Anisa da Humaira sun shiga kitchen sunyi girki mai rai da lafiya ,suka baje kan kafet sukaci suka ƙoshi anata hirar zumunci ,mama Ruqaiyya tace "Anisa kinga inda fatarki ta kuma gogewa kuwa ? Anisa tayi dariya.
Mama Ruqaiyya tace " ansa bikin Humaira fa nanda sati uku inga ba'a sanar miki ba ?"
Anisa ta fara tsokanar humaira , bayan sunyi azhar anyi la'asar sannan suka fara shirin tafiya ,ta ɗibo musu bandir ɗin yan ɗari biyu kowa biyu ta miƙa musu tare da rakasu gurin mota .
Kwanci tashi asarar mai rai yayinda abubuwa suka zo suka wuce ,ciki harda bikin Humaira aka kaita anguwar rimi ,ta auri wani shahararren ɗan kasuwa , gidanta ma gunin burgewa amma bai kama ƙafar na Anisa ba .
After 1yr Anisa na hango tay ƙiba tayi haske sosai ,duk wanda ya santa a da zauyi wuya ya ganeta sbda yanda jikinta ya sauya , tafe suke a mota tana rungume a jikin Yasir da titsesten ciki a gabanta wanda da gani naƙuda take .
Babu wanda bai kira ya sanarwa ba ,suna kaiwa asibitin aka wuce da ita labor room ,
Yana tsaye ya ga mamy da hajyarsa can kuma sai ga mama ruqiyya ,zuwa anjima hjya kakarsu da umma sukazo ,asibiti ya cika da ƴan uwa , sunzo ƙarfe 9 na safe ,sai wajen azahar ta aihu ,inda ta haifo twins mace da namiji macen tana kama da Yasir namijin kuma sak Humaira ,har ƙibar.
Fainciki ya karaɗe family da wannan kyauta da Allah yayi musu.
Ranar suna namijin yaci sunan baban Anisa Muntari suna kiransa da dady ,macen kuma taci sunan mahaifiyar Yasir wato Khadija ,suna kiranta da momy
Alhmdulilh akayi taron suna lafiya aka kammala lafiya ,bayan suna hjya ta buƙaci a wuce da ita can ayi mata wanka , abin yayiwa Yasir daɗi sosai.
Kwanci tashi babu wuya ,Anisa tayi arba'in bayan ta gama ziyartar ƴan uwa aka maido da ita ɗakinta , soyayya suke gwadawa junansu ,ko wanne burinsa ya farantawa ɗan uwansa , dole aka samar mata mai rainon yara , Alhj mahaifin Yasir yayiwa dadyn Anisa kyautar 5 millions naira a matsayin tukuaici aihuwar ƴan biyunnan sun faranta masa ga buɗi ta ko ina da suka dinga samu .
Dady a ranar ya kasa bacci tsabar farinciki
Humaira ce dai har yau Allah bai bata aihuwa ba , hospital sun tabbatar da dukkansu ita da mijin lafiyarsu ƙalau lokaci ne baiyi ba.
Bayan shekaru huɗu ...
Gidan Sadiq , kyawawan yara na hango su biyu duk mata , babbar itace mai suna Bahijja ita kuma ɗaya Nana Faɗima , alhmdulilh shima yana zaune da ƴar uwarsa kuma matarsa cikin ƙoshin lafiya ,
Kowanne ɓangare suna cikin kwanciyar hankali da ƙoshin lafiya , Anisa tun daga ƴan biyu bata sake aihuwa ba , sai ƙibarta take tayi ,suma yaran gunin sha'awa anfara shirye-shiryen sanyasu a makaranta.
😘Kuyi haƙuri dajin ƙarewarsa yanzu , kinsani nasani idan dambu yayi yawa sam bayajin mai , kuzo ku daina mararinsa nima ya ficemin a kai , tabbas nagode masoyana akan soyayyar da kuka nunamin ta hanyar siyan littafina , ina fatan zaku gafarceni a kura kuran da kuka gani akasi ne kunsan ance ɗan adam ajizi 👏soyayyarku tasa bazan iya mancewa daku ba nagode nagode nagode , sai kuma Allah ya sake haɗamu a cikin littafina mai suna *ABU-RAHEED*
Ina roƙon wanda na ɓatawa da wanda yaga kuskure akan ya yafemin👏.
Littafin da zanyi shi shine *ABU-RASHEED*
bansan ya zan kwatanta muku inda littafin yake ba ,amma wallhi duk wacce ta mallakesa babu dana sani a tafiyar , zani iya bakin ƙoƙarina gurin farantawa masoyana .
Nagode Allah yabar zumunci sai mun haɗu a ABU-RASHEED littafi mai dogon zango nagode 🥰.
Taku har kullum Mom Islam