Showing 3001 words to 6000 words out of 27791 words
yaga wanka tun da ban fita ba kaga ko ai su Ummi suka yi asarar wankan su". Ta faɗa cike da shaƙiyanci.
Shikam tuni ya ji kamar ta duka ma sa wani abun mai nauyin gaske cikin jarumta ya ce "to ashe yaran Umma sun girma har samari ne da ku kuna ƙananin nan". ya faɗa cikin nauyin murya.
Ummi ta ce "Yaya wallahi ƙarya ta keyi Bama da samari".
Idan ma suna da samarin mai za ka yi ne ehhe, maganar Umma suka ji aiko saurin ɗago kansa ya yi ya ce "Umma ina wuni"?.
Umma ta ce "ban san in da ya ke ba tashi kabar ɗakin nan tunkan ranka ya ɓaci kazo ka takurawa yara".
Laaaa Umma waye ya ce ya takura mana ne Umma. cewar Fatima.
Fatima karɓi wannan zagin naki ne idan nasake magana kika ce ba haka bane sai na ɓataranki.
Hakuri suka bata sannan suka kama hanyar zuwa part ɗin Mama.
Mama ta ce "kai ma tashi kabani wuri ko ba za ka je masalaci bane ana kiran sallah ka wani kafe ni da idanuwa"?.
Yi hakuri ban ji ba ne wallah bara nayi Alwala idan na je sallah kawai zanyi.
A ina za ka yi Alwalar?.
Umma a toilet ɗinki idan naje sallah kawai zanyi.
Umma ta ce " wallahi ba ka isa ba ka je can ai akwai kayan alwala sai ka yi Alwalar a can".
Ya ce "toh shi ke nan Umma sai anjima".
Yana fita ya ci karo da su Rashid amma bai tsaya ba kawai ya yi tafiyar shi abin shi, tare suka isa masallacin dake ƙofar gidan su.
Magarib suka idar amma ba su su ka ta shi ba sai da aka idar da isha'i Sannan su ka shiga gidan amma har lokacin Ma'aruf bai kula Rashid ɗin ba.
A falo suka tarar da mutanen gidan saboda su ma sun idar da ta su sallar.
Shaga falon su ka yi bakin su ɗauke da sallama "Assalamualaikum".
Mutanen falon su ka amsa da ko "waalaikumussalam".
Gai da iyayen nasu suka yi sannan su ka zauna.
Ashe mutumen kan hankalin shi ya kar ka ta a wajen Ummi saboda shigarta ba ƙaramin kyau ta yi ba, riga da wando ne na Pakistan a jikinta.
Ita ko jikinta ya ba ta cewa ana kallon ta ai ko ido huɗu suka yi haɗe fuska ya yi kamar ba shine ke kallon ta ba ya dallah ma ta harara, ka sa da kai kawai ta yi jikinta har rawa yake yi.
Umma ta ce "Rashid ku tashi mu je dainnin kafin Ummi ta fara yiwa mutane ehun abinci ta ke so".
Hahaha dariya su ka sa ka ma ta tako har da kukan ta wai su dai na ma ta da dariya.
Mama ta ce " Rufa'i ko dai na ma ta da dariya ha ka ta isa".
Ta shi suka yi su ka nufi dainnin zama kowa ya yi ku da masoyin shi amma ban da Ummi da Rashid.
Wajen Umma taje ta zauna Umma tace ta sakawa kowa abinci aiko ha ka aka yi ta sa ka wa kowa tazo zuba ma sa ya ce "shi team za ta haɗa ma sa jikin ta na rawa ta haɗa ma sa team ɗin garin ta bashi kofin ya faɗi sai a jikinsa.
Maruka masu kyau da tsada ya saukar ma ta a fuskarta, ha de fuska ya yi kamar bai taɓa dariya a duniya, kuka ta ke yi sosai saboda ba ƙaramin shigar ta marukan suka yi ba.
Mama ta tashi dan ramawa Ummi sai Umma ta dafe ta Mama ta ce "sakar ni Maryam kina ganin wannan mari da ya saukar ma ta ba kice komai sannan yanzun za ki wani da fe ni"?.
Haba Amina ki yi hakuri na ga ita ta zuba ma sa ruwan zafi a jiki meyasa idanuwan ki basu ga abin da ta yi ma sa ba sai na shi za ki gani kuma a gaban ƙannan sa za ki da ke shi ha ba Amina.
Ma'aruf ya ce "wai kai kam Rashid meyasa bakada hankali ne jakin banza kawai mara hankali, toh wallahi duk ranar da ka sake dukan ta sai na rama ma ta saboda ba wani girma na kayi ba shekara 2 ne kawai kuma bazan ji ƙunyar ka ba wallahi.
Umma ta ce "toh sannu uban shi ai kai ne jakin bashi ba saboda ko ba komai Rashid Yayanka ne kuma wallahi ko da wasa na ji an ce ka yiwa Rashid rashin kunya sai na saɓa ma ka".
Ta shi Ma'aruf ya yi ya bar wajen saboda yaji haushin maganar Umma sosai .
Haba Maryam menene ha ka ne yanzun ga shi kin sa ke ɓatawa wani rai akan mutum ɗaya ta shi Mama ta yi ta ji hanun Ummi su ka bar dainnin ɗin su ka yi shigewar su part ɗin Mama.
Ka yi hakuri ka ji Rashid kar abin da ya fa ru ya ɓa ta ma ka rai ka ji ni Ko, "eh Umma" ya faɗa.
Kwanciya kuwa ya yi saboda gobe ne mazan su za su dawo.
Amma Ma'aruf ba a ɗakin su ya kwana ba a part ɗin Umma ya kwana cikin uwar ɗaka ya kwanta kar Umma ta ganshi dan yasan ba za ta ba ri ya kwanta ma ta a ɗaki ba.
Rashid ba ya son fushin Ma'aruf ko ka ɗan saboda ko ba komai Ummar su na son shi kuma ba za ta ta ba su Ma'aruf gaskiya ba sai dai shi, ha ka ya kwanta ranshi cike da tambayoyin da ba mai amsa ma sa su.
Rufa'i ma bai yiwa Rashid magana ba saboda haushin shi yake ji sosai saboda Ummi ƙanwar sa ce.
Asuba ta gari.
London
Wa ta matashiyar mata ce sanye da baƙaƙen ka ya ta na waya da alama da wa ta ƙawarta ce ta ke waya ta can ɓangaren aka ce, "wai Balkisu ke shegiya ki na can ki na can ki na jin daɗi kin manta da abin da Boka ya ce kuma na ji ya ce za ki dawo Nigeria gobe ba shiri dan ha ka sai kin ba da bakar akuya a yanka saboda zafi-zafi ake dukan ƙarfe".
Balkisu ta ce "kamar nawa ne zan bada saboda wallahi natsani Maryam da yaranta sannan kuma inason arabamin Rufa'i da shegen yaronnan na ta yanzun dai zan ba da dubu ɗari biyu na san dai za su yi ko"?.
Hajara ta ce "toh sai dai an ji wajen boka shi zai faɗa idan sunyi kin san aikin ba ɗaya ba ne".
Eh Hajara zan kira ki anjima yanzun tsohon banzan nan ya shigo zan kashe waya,ɗim ta yanke kiran.
Balkisu ta ce "ka ce gobe za mu koma gida amma banga tikiti ba kuma ban ga tsaraban yarana ba mai ka ke nu fi ne toh"?.
Abban Ma'aruf ɗin ya ce "ai na yi tunanin kin yiwa yarannaki tsaraba ne yanzun toh ki shirya mu je siyayyar ko".
Balkisu ta ce "toh shi ke nan ni ma akwai abin da na ke son siyawa Maryam da Amina ni ma na kai mu su".
Toh shi ke nan ga tikitin na siyo jirgin safe za mu bi. Toh kawai ta ce.
Shiryawa ta yi amma kayan ne a jikinta fita suka yi, siyayyar mai yawan gaske su ka yi sannan su ka koma gida, ko wanka bata yi ba ta yi kwanciyar ta abin ta.
Nigeria
Kiraye kirayen sallah ne ya tashi ƴan gidan mazan su ka wuce masallaci matan ma sallah su ka yi, sannan yaran su ka koma bacci Umma ɓangaren ma su aiki ta je ta ce su gyara gidan da kyau saboda za su yi baƙi sannan ta ce ita za ta yi abinci da kan ta.
Aiko Mama ita da Mama suka yi abincin farfesun naman kaza, dambu naman rago, Farfesun kayan cikin rago, da sauran su kai komai ma sha Allah.
Bangaren ma su aikin ta sa ke komawa ta ce su je su bangaren Balkisu su gyara ma ta shi sosai ha ka kuwa akayi an gyara shi sosai da sosai.
Bangaren Mama kuwa ha ka ne ita ma an gyara ɗakin ma sha Allah.
Bangaren su Balkisu su ma sun shirya tsab za su airport jirgi safe su ka shiga sai gida Nigeria.
Mama ta ce "Maryam yanzun sai yaushe yarannan za su yi hankali dan Allah kinji sunce idan su ka dawo ba su fitar da matar aure ba toh za su yi sadakar su ne amma gashi shiru".
Uhmm wallahi yaranan ba sa ji ko kaɗan ai idan aka yi sadakar su za su huta ne ai.. ba ta ƙara sa maganar ba sakamakon wayar ta mai neman agaji.
Ta ce "Assalamualaikum"
Ta can ɓangaren aka amsa "waalaikimussalam"
Barka da safiya Abban yara ko kun iso ne.
Eh gamu a airport kicewa Ma'aruf yazo ya ɗauke mu har da Daddyn su gashi a airport ɗin mu ka tarar dashi.
Laaaa har da Yaya kenan amma ko bai faɗawa Amina zai dawo ba saboda ga mu tare amma banji ta na maganar dawo War sa ba.
Toh mu ma anan muka tarar da shi sai kicewa yaran suzo su ɗauke mu.
Toh Abban yara zan kira Rashid ɗin.
Ma'aruf ɗin fa.
Am toh ai duk ɗaya ne ni dai sai ka gansu.
Amina kinji wai har da Yaya ya na airport ɗin.
Wane Yaya ɗin cewar Mama.
Wane Yaya ne a gidan nan in ba mijinki ba.
Uhmm kawai Mama ta ce.
Rashid Umma takira tace suje su ɗauko Mahaifan su a airport su na jiranku. toh Umma kawai ya ce ya kashe wayar.
Kiran Ma'aruf ya yi amma har wayar ta katse bai ɗauka ba sa ke kira ya yi nan ma shiru ba amsa.
Bangaren Ma'aruf kuwa ya na ganin kiran amma yaƙi ɗagawa saboda haushen sa da ya ke ji.
Kiran Rufa'i ya yi sannan ya faɗawa Rufa'i cewa su Daddy na airport ya zo su je ɗauko su.
Shiryawa suka yi su ka nufi hanyar airport su ka ɗauko su sai gida.
A hanyar ta zuwa gida Rashid ya ma su barka da fita jirgi lafiya.
Shima Rufa'i barka da fita jirgi lafiya ya yi ma su.
Sannan Rufa'i ya ce "Daddy munyi kewarku fa sosai wallahi".
Abbah ya ce "au Daddyn ku kawai ku ka yi kewa ban da mu kenan?.
Rufa'i ya ce "ai Abba har da kai da momy duk munyi kewarku sosai".
Daddy ya ce "toh za ka haɗa kan ka da mahaifin su ne .
Rashid ya ce "Daddy yaranka sun gagara su ganku fa saboda kullum tambayar ku suke yi.
Momy ta ce "ayya ni ce kawai ba wanda yadamu da ni saboda ga shi Rufa'i ko kallo na bai ba.
Wace irin magana ce wannan Balkisu ba sunyi mana barka da fita jirgi lafiya ba, ba yanshi mai ki ke son su yi ma ki ehhe.
Allah yabaka hakuri Abban Ma'aruf.
RASHIDA
By
Sha'awanatu faruk diggi✍️✍️
Wtspp 08084277827☎️📱
Saƙon miƙa gaisuwa ga sister's
Ina miƙa gaisuwa ga aunty Saratu
Ina miƙa gaisuwa ga sister Shamsiyya
Ina miƙa gaisuwa ga bro Abubakar
Ina miƙa gaisuwa ga ƙawata Firdausi
Ina miƙa gaisuwa ga ƙawata Rashida
Ina miƙa gaisuwa ga sister Yasira
Ina miƙa gaisuwa ga ƴata Salma
Ina miƙa gaisuwa ga my son hafeez
Ina miƙa gaisuwa ga duk kannin musulmi Allah ya barmu tare da masoyan mu ameen ya Allah.
3
📝
Da haka dai har su ka isa gida, su na shiga gidan su ka tarar da mutanen gidan har da Kaka, ran da Ummi ta ga sun sa ka hancin motar cikin gida ta sheƙo a guje ta budewa Daddy ƙofa, ya na fitowa ta ɗale shi ta na ehun ganin su shima rungume ta ya yi sosai ya sakar ma ta kiss a goshi ya ce "innan Daddy har yanzun ba ki girma ba ko"?.
Hahaha dariya ta yi sannan ta ce "ai Daddy ni yarinya ce ga su aunty A'ishah da aunty Fatima can gefe da ya ke su sun girma", ta na maganar ne cikin shagwaɓa da ita ma ba ta san da ta na da ita ba .
Rashid ga ba ki ɗaya hankalin shi ya koma kan Ummi dan shagwaɓar ba ƙaramin kyau ta ƙara ma ta ba, ya na nan ya na tunani ji kawai ya yi an mangare ma sa kai da sauri ya dawo hayyacin shi, Kaka ya gani ba kowa har su Rufa'i sun tafi su ka barshi.
Kaka ta ce "ashe Bokan turai ka na nan amma ba mai laiƙani saboda Allah daga kai har su Ma'arufa ba mai laiƙani". (Ma'aruf ta ke nu fi).
Ya ce "kai Kaka surutun ki ya yi yawa kin cika min kunne da surutu toh yanzun dai yaranki su zo ai sai kije Ku zanta ko".
Tafiyar shi ya yi ya barta a nan sa ke da baki.
Falon ya shiga ya ƙara gaida iyayen nasu sannan ya zauna a kasan ƙafafun Abba.
Abba ya ce "inna ina wuni mun sa me ki lafiya"?.
Inna ta ce "lafiya ƙalau Iro barkanku da fita jirgi lafiya".
Yauwa barka dai Inna cewar Daddy.
Ummi ta ce Abba mu je dainnin ko dan ni kam yunwa nake ji.
Umma ta ce "ba in da zashi sai sun yi wanka tukunna sannan ai maganar cin abinci", sannan Balkisu ki je ki yi wanka ke ma ki zo mu ci abinci.
Balkisu ta ce "uhmm ni ai sai na gyara ɗaki na dan nasan ba gyara min aka yi ba".
Mama ta ce "haba Balkisu ya za'ayi ace kuna ta fe mu ƙi gyara maki ɗakin dan Allah kiriƙa tauna magana kamin ki fitar da ita ".
Balkisu ta ce "atoh ni kam nasani dan naga ba a murnar dawo wa ta".
Abba ya ce "wai Balkisu mai yasa ke kullum fitina ce kawai ke ma ki daɗi yanzun yaushe rabon da mu yi zama da yaran mu da sauran ƴan uwanki yanzun gashi mun samu dama kina shirin warga za ta haba dan Allah ".
Abban yara ki yi hakuri dan Allah mu je ka yi wanka sai ku ci abinci, Ummi ku je ra mana abincin a dainnin ɗin.
Ƙin tashi ya yi hanu ta sa ta kama hannun shi kamar yaro su ka shiga ciki .
Ummi ta ce "Umma mu na nan fa ko kin manta ne"?.
Mama ta ce "kai Ummi kin cika sa ido", fa ta na maganar ta na dariya saboda ita abin ya ba ta dariya.
Mama ta ce "Daddyn yara ta shi mu je ka yi wankan kai ma ko sai na goya ka ne".
Hahaha su Ma'aruf su ka sa ka dariya.
Rufa'i ya ce "kai Mama mu ma Allah yabamu matan da za su yi mana ha ka dan naga ko ƙunyar mu Umma ba ta ji ba kema Mama ha ka".
Abba ya ce "ku na nufin ba ko tsaida matan aure ba shi ke nan zan ba da ku sadaka ga mai bukata ".
Ma'aruf ya ce "haba Daddy ka san mu yara ne har yanzun ba mu san dai-dai ba da ba dai-dai ba saboda yara ne mu dan Allah ku yi hakuri Daddy har mu girma Please".
Mama ta ce "ai ba ku isa auran ba amma ku ka san Allah ya ba ku matan aure irin mu".
Dariya su Ummi ke yi sosai .
Fatima ta ce " Mama jiya fa Yaya Ma'aruf cewa ya yi shi kam aure ya ke so dan Allah na bashi ƙawata Ihsan".
Ma'aruf ya ce "wallahi Mama ba gaskiya bane ina ma naga ƙawar ta da zance inaso".
Dariya su ka sa ka sosai har da Rashid sai da ya dara.
Mama ta ce "Daddyn yara ta shi muje tun kan su fito".
Ta shi ya yi su ka yi shigewar su ɗakin Mama.
Ma'aruf ya ce 'ke Fatima ni za ki wa sharri a gun Daddy saboda ki na son a yi sadaka na ko".
Fatima ta ce "haba Yaya ai wasa ce na ke yi ai ni nafi da son ka sama mana aunty Mai kyau da hankali".
Rufa'i ya ce "ka san mai za ka yi ka rama abokina"?.
Ma'aruf ya ce "a a sai ka faɗa".
Rufa'i ya ce "ka cewa Daddy ai Fatima ta ce ta na sonka kuma kai za ta aura idan babu kai ba za ta iya rayuwa ba", nan ta ke Daddy zai yi amanna da ha ka shi ke nan ka rama abin da ta yi ma ka.
Yaya dan Allah ka yi hakuri wallahi ba zan sa ke ba yau idan ka faɗi maganar nan ai nasan ba zanyi sati a gidan nan ba dan Allah ka yi hakuri na rantse da Allah ba zan sa ke ba. Cewar Fatima kamar za ta yi kuka.
Dariya su Ummi su ka sa ka ma ta Ummi kam kan dariya har hawaye ta ke yi.
Ma'aruf da Rufa'i ma dariya su ke ma ta sosai shima Rashid ɗin ya na murmusawa sakamakon dariyar da Ummi ke yi.
Balkisu ta na shiga ɗakin ta tarar da shi fes-fes-fes kiran Hajara ta yi a waya ta ce ma ta "sun iso a Nigeria yanzun ha ka ta na gida ".
Hajara ta ce "toh shi ke nan sai na zo zan faɗa ma ki abin da Boka ya ce".
Toh ta ce "sai kin zo ɗin ina jiran ki fa Hajara " yanke wayar ta yi.
Wanka ta yi ta canza kaya sannan ta fito falo ta tarar da su Ummi sai dariya su ke yi.
Ummi ta ce "kai ma Yaya Rufa'i sai mu ce kai ka ce ka na son A'ishah shi ke nan mu kam musha shagali a gidan nan wallahi".
Rufa'i ya ce "ai da A'ishah za ta kashe ni wallahi wannan ƴar Bala'in zan aura.
Su ka suka dariya har da Rashid.
Momy ta ce "yau nishaɗi kawai ku ke yi toh na ji kamai kai Ma'aruf zance kai ka ce ka na son Fatima, kai ma Rufa'i ka ce ka na son A'ishah, kai ma Rashid ka ce ka na son Ummi duk ku bari Abban ku yazo sai na