Showing 12001 words to 15000 words out of 27791 words

Chapter 5 - Rashida Part 1 Complete Hausa Novel

Shaawatu   

07 Aug 2026

112

ce na kwana ba fa."

"Toh kace ma sa ni nace sai ka kwana."

Shi dai Ibrahim dariya kawai ya ke wa Inna.

WASHEGARI

Ya tashi tun da safe ya ce "Koma wa zai yi", wannan karun Inna ba ta hana shi ba dan ta san aikin shi .

A'ishah ta ce "Yanzun Yaya sai yaushe za ka dawo"? .

Ya ce "Zan dawo ba da jimawa ba zan kawo ma ki auntyn ki."

Ehu ta saka da murna .

Haka dai rayuwa ta ci gaba da gudana, ciki har da auran Muhammad da Amina da taimakon Amina ya sa mu aikin yi gidan ma da taimakon Amina ya gina shi.

Shiryawa su ka yi shi da Amina zasu ƙauye In da Inna.

Muhammad Ya ce "Amina dan Allah idan mu ka je ki saka baki ko Inna za ta dawo nan da zama."

Ta ce "Toh shi ke nan zanyi maganar in sha Allah."

Kama hanya suka yi sai ƙarfe 2 suka isa zo kaga murna wajen Inna saboda ganin sirikarta ma sha Allah.

A'ishah ta ce "aunty bara na kawo maki abinci saboda na san kin sha hanya."

Hutawa suka yi Sannan aka zo fira da dare Amina ta ce "Inna Dan Allah dan darajar Annabi Muhammad s a w, Inna ki bimu mu tafi tare wallahi gidan ba daɗi dayake ba kowa acikin shi amma idan ki ka je zan samu mahaifiya a cikin gidan dan Allah kar kice a a Inna."

Inna ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un yanzun ƙara ta ka kai mata ne shine ka wani kawo min ita ashe dan ku cuceni ne kura ba ni da gari na, kuma kurasa da wa zaku haɗa ni sai da wan da ya fi ni haba dan Allah."

Muhammad ya ce "Haba Inna ni ban San da za ta yi wannan maganar ba ai da ba zan zo da ita ba dan Allah ki yi hakuri, kuma yanzun Inna ya za ki yi."

"Kai ɗan nan ka ji tsoron Allah sai ka ce ba da kai aka haɗa baki ba."

Amina ta ce "Inna yanzun ba zan samu wannan alfarma ba, shi ke nan amma gaskiya ban ji daɗi ba wallahi Inna."

Ke yar nan ai ba yanda na iya saboda kin haɗa ni da Allah har da Annabi Muhammad s a w, ai dole zan biku.

Saura ƙiris Muhammad ya rungume Amina a ga ban Inna akan daɗi.

Ya ce "Inna gobe zamu tafi ko?."

Ta ce "A a ni kam ba zan je gobe ba sai dai ku ta fi da Ibrahim da A'ishah."

Amina ta ce "Haba Inna ba yan kin ce min za ki je kuma yanzun ki ce a a dan Allah ki yi hakuri Inna", Amina yi tayi kamar za ta yi kuka ganin haka ya sa.

Inna ta ce "toh shi ke nan na yarda amma ai sai na shirya kaya na ko."

Amina ta ce "a a Inna akwai komai a can."

Toh shi ke nan zan je ban kwana saboda tafiyar tazo min a bazata.

Toh shi ke nan Inna na gode sosai da ki ka yarda.

Maƙota Inna ta je ta yi ma su sai wata rana.

WASHEGARI

Tun da safe su Inna suka kama hanyar Kano, A'ishah kam sai surutu ta ke bu gawa idan mota ta ga ni mai kyau sai ta yi magana da haka dai har suka isa gidan su.

Inna ta ce "Yanzun yaron nan kai ne mai gidan Allah Mustapha da kana raye da yanzun muna tare cikin gidan yaron ka", hawaye ne suka shiga anbaliya a fuskar ta.

Ibrahim ya ce "Haba Inna Dan Allah ki yi hakuri ki dai na wannan kukan ai farin ciki za ki yi saboda Allah ya nuna ma ki ranar da yaronki ya gina gida kuma gaki cikin shi sai ki godewa Allah."

Inna dan Allah ki yi hakuri wallahi mutuwa bata da daɗi ko ta tsofa bale yanzun da Allah ya nuna maki cewa yaranki sun girma har gaki a cikin gidan shi dan Allah ki dai na kukan nan kin ji Inna. Cewar Amina.

Muhammad ya ce "Inna mu shiga da ga ciki kinga A'ishah kuka za ta yi, ganin kina kuka dan Allah ki bar haka nan Inna idan ba so kike muma mu yi kukan ba."

Hannun ta Ibrahim ya ja sai cikin gida, cikin gidan ma sha Allah.

Part ɗin ta da ban da nasu gidan dai ga baki ɗaya part 6, part ɗin Amina, part ɗin Ibrahim idan ya tashi nashi auran, sannan part ɗin Inna, part ɗin yaran su na mata da ban na maza da ban, toh ɗayan ban san na meye ba.

Part ɗin Inna Amina ta nuna mata sannan ta haɗa mata ruwan wanka ta ce "Inna ga ruwan wanka can kije ki yi wankan."

Toh kawai Inna ta ce ta na jin wani sabon al'amari a jikin ta.

Amina in da mijinta ta je ta haɗa ma sa ruwan wanka sannan ta ce "Mijina ka je ka yi wanka sai warin dauɗa ka ke yi ta faɗi maganar ta na dariya."

Ya ce "Amina ban san da wane baki zan gode maki ba saboda wannan abin da ki ka min na gode sosai mata ta Allah ya sa ka da alkairi."

Hmm kar ka manta nima mahaifiya ta ce fa dan na yi wannan abin ai ba komai ba ne, ni dai ka je ka yi wanka dan Allah.

Rungume ta ya yi ya fa ra shafata ni dai na ce nayi nan na rufe ƙofa na yi tafiya ta .

Inna ce ta fito da ga wanka ta tarar da kayan ta a waje ta ce "A'ishah me yasa kika ɗauko min kaya eyye."

Kai Inna bani bace aunty ce tace nace idan ki ka zo ki sa ka su .

Humm kawai ta ce.

WASHEGARI


By
Sha'awa marubuciya✍️✍️
WhatsApp number08084277827☎️


RASHIDA PART 6

📝
Amina ta ce "A a Maryam ba du ka suke ɗaya ba sannan me su ka yi da kike faɗar wannan maganar akan su?."

Maryam ta ce "Amina Ibrahim ya ci amana ta, Ibrahim ya yaudaran, Ibrahim bai yarda da Allah ba, ku ma wallahi a gidan mu zan kwana dan ba zan kwana ta re da shi."

Muhammad ya ce "Ibrahim me kayiwa yarinyar mutane ne da har ta ke faɗan wannan maganar akan ka?."

Ibrahim ya ce "Wallahi yaya na ga ji da rashin haihuwar nan ina bukatar na sa mi ƴan yarana nima."

Muhammad ya ce "Anya Ibrahim kai ne wai saboda Ibrahim ɗin da na sa ni ba irin wannan na yanzun ba ne, ok idan na fahimta so ka ke ka ƙara aure ko?."

Ibrahim ya ce "Eh.

Maryam ta shi ki je ɗakin ki zan je da shi wajen Inna.

Maryam ta ce "Dan Allah Yaya kar ka kai ƙarar shi wallahi bana son na ji ana ma sa faɗa saboda ina son shi."

Muhammad ya ce "Maryam wacce irin mata ce ke mutum na son rabaki biyu ina son nagyara abin kina son lalata shi?."

"Dan Allah ka yi hakuri Yaya cewar Maryam.

Rashid ya ga Umman shi na kuka ya zo ku sa da ita ya ce "Umma waye ya dakeki na rama ma ki?." Duk cikin gwalancin shi ya ke yin maganar.

Rungume shi sosai Maryam ta yi ta na kuka abin tausayi.

Ganin haka shima yafara kukan.

Muhammad ya je ya kira Inna tazo ta tarar da Maryam na kuka ita da Rashid.

Inna ta ce "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, me zan gani ne amma kai Ibrahim wallahi sai hakkin yarinyar nan ya bi ka, saboda Allah wannan abin ita ke bawa kan ta ne ka san lokacin da na ke yarinya kamar ta?."

Kamin shiru kabani amsa mana.

Ibrahim ya ce "A a Inna."

Ta ce "toh lokacin da nake yarinya kamar ta na shekara 5 ban Haihu ba sai da ga baya Allah ya ba ni Ku, sannan yanzun akan rashin haihuwa wai za ka Rusawa yarinya rayuwa."

Maryam ta ce "Dan Allah Inna ki barshi kawai ya yi auran idan dai zai samu abin da ya ke so kawai ki barshi ba komai, nima ina son na ga yaran shi Allah ya ba ka mace ta gari Allah ya sa auran ne alkairi a gare mu."

Amina ta ce "Amma Ibrahim wallahi ka ban mamaki yanzun duk yadda Maryam ke son ka kai ma kake son ta amma wai za ka yi ma ta kishiya haba Ibrahim."

Maryam ta ce "Amina dan Allah ki dai na faɗar haka ni ina mai farin ciki da auran nan kawai matar da zai auran ce ban san halin ta ba, wallahi Amina kishiya idan ba mai rabaka da mijinka ba ne, ko mai rabaka da lafiyar ka ba ne, ko mai rusamaka rayuwa ba, ai abar su ce ke dai kawai Allah ya sa mai zuciya ɗaya ce."

Inna ta ce "shi ke nan Maryam tun da haka kika ce ba damuwa Allah ya sa shine mafi alkairi sannan Allah ya sa ba ƴar biyan bokaye ba ce."

Su Amina Ameen ya Allah kawai su ka ce.

Muhammad ya ce "Ibrahim yanzun idan ka je ka auro yariyar da kake ganin za ta haifa ma ka yaran a ka zo bata haihuwa me za ka yi?."

Amina ta ce "Ni ba komai na ke dubawa ba na ga shi likita ne makin ya binciki kan shi ya bincike ta ai zai gane mai matsalar amma babu sai kishiya, toh yanzun ka je ka yi aure ka tarar da ita da ciki me za ka yi?."

Muhammad ya ce "Ciki kuma?."

Amina ta ce "Eh."

Muhammad ya ce "Ai da ya ji kunya wallahi."

Amina ta ce "Wallahi duk alamomi sun nuna cewa Maryam na ɗauke da ciki, ka dubi fuskar ta, sannan ga ƙirjinta ya yi yawa sosai, sannan idan mu ka shiga kitchen toh wallahi abu za ta ne ma dan rufin hancin ta idan na tambaye ta sai ta ce min wai ba da lafiya."

Ibrahim ya ce "Aunty wallahi ba wa ni cikin da ta ke da amma ba ku san ko auran nan alkairi ba ne."

Maryam ta ce "Ibrahim ni ma na san ba na da cikin kawai ka je ka yi auran ka ba damuwa."

Inna ta ce "Toh yanzun me ake ciki ga me da auran".

Ibrahim ya ce "Inna cewa su ka yi na tura iyayena da kuɗin an ga ni a na so da kuɗin sadaki."

Muhammad ya ce "Ƴar wa ne gida ce?."

Ibrahim ya ce "Yar gidan Alhaji Murtala ne."

Amina ta ce "Wane Alhaji Murtala ɗin ka ke nufi?."

Ibrahim ya ce "Ɗan kasuwa."

Amina ta ce "Murtala ɗan kasuwa kuma yanzun ka rasa wa za ka haɗa kishi da Maryam ƴar masu kuɗi kuma ƴan dangi wulakanta mutane?."

Muhammad ya ce "Kin san su ne?."

Amina ta ce "sosai ma."

Muhammad ya ce "budurwa ce ko bazawara?."

Ibrahim ya ce "budurwa ce sunan ta Balkisu."

Amina ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, amma lallai Ibrahim ka cika butulu wallahi, yanzun wannan ƴar iskar ka ɗaukar wa kan ka."

Maryam ta ce "Yaya, Inna, Amina, dan Allah ku bar shi ya yi auran shi wallahi ni dai idan ba ƴar bokaye ba ce ba zai daman ba."

Muhammad ya ce"Toh shi ke nan zan je dan kai kuɗin auran, amma ka sa ni duk abin da kayiwa amarya toh sai kayiwa Maryam ka ji ni ba."

Maryam ta ce "Yaya dan Allah ka dai na wannan maganar kawai barshi ya yi abin da ya fiye ma sa."

Inna ta ce "Nima ina bayan ka yaron nan dan dole sai ya yiwa ƴata sabin kaya."

Da haka dai su ka watse .

Da dare aka je kai kuɗin auran.

Aka sa ka ranar aure nan da sati ɗaya.

Suka dawo gida su ka sanar da ƴan gidan.

Su ka ce Allah ya kaimu.

Maryam ta ce "Dan Allah Yaya gida na ke son zuwa kuma na tambaye shi ya ce ba zan je ba sai an ɗaura auren kuma ina da wata matsala ta zuwa gida."

Muhammad ya ce "A kan mi za ka hana ta zuwa gidan su?."

Ibrahim ya ce "Yaya saboda ba na son wani abun ya faru da auran ne."

Maryam ta ce "Ibrahim yanzun ni kake zargi da lallata ma ka aure saboda mi zan lallata ma auran naka, halam duk namiji dan mace ɗaya a ka yi shi duk namiji zai iya auran mace huɗu toh ni a kam mi zan hana ka raya sunnar Annabi."

Muhammad ya ce "Maryam ki yi hakuri ki je gidan idan kika ga ma abin da kike sai ki kirani zan ɗauko ki kin ji."

Maryam ta ce "A a Yaya na fasa wallahi tun da har yafaɗi wannan maganar ba zan je gida ba sai ya ban hanya da kan sa."

Tafiya part ɗin ta ta yi wayar ta ɗauka ta faɗawa mahaifiyar ta abin da ke faruwa.

Mahaifiyarta ta ce "Maryam ki yi hakuri ko wacce irin mata ce zai ɗauko da talaka da Mai kuɗi duk suna a hanun Allah, dan Allah haka ki kwantar da hankalinki ki yi kamar abin bai miki zafi ba, sannan ki da ge da addu'a saboda ita ce katangar zarfe tsakanin ki da ita, Maryam ban san ki da fitina ba kar na ji kar na gani kishi ba akan ki aka fara ba kuma baza a gama akan ki ba ki yi hakuri ki bi mijin ki sauda ƙafa idan wuta ya ce ki faɗa toh ki faɗa, amma abu ɗaya zance karki aikata shine bin hanyar da Allah ya haramta kin ji."

Maryam ta ce "Toh shi ke nan Mama nago de sosai kuma zan sa ke fuska ta ayi komai da ni in sha Allah Mama kuma ba zanyi sake da addu'a ba da ga ni har yaran da zan haifa ba zan bari ko ɗaya ya yi wasa da ibada ba."

Mamarta ta ce "Allah ya yi maki albarka autana."

Maryam ta ce "Ameen Mamana."

Sai anjima su ka yi rayuwar kowa ba daɗi.

Amma Maryam rayuwarta ta yi sanyi akan ɗazun.

BAYAN SATI ƊAYA

Maryam ce zaune da Amina da amaryar wato Balkisu.

Maryam ta ce "Wai Amina ina yaro na ne ko har yanzun bai dawo daga school ba ne?."

Amina ta ce "Ai na huta ni kam saboda yaron nan wallahi akwai shi da baƙin rai ko dariya fa ba ya yi tun yana jariri."

Balkisu ta ce "Ba wani nan kawai sharri kike ma sa."

Maryam ta ce "Ke dai Balkisu kya faɗa mata."

Amina ta ce "Wallahi ku yi sauri ku bani yarona ko yarinyata idan ba ha ka ba ko humm basai na ida ba."

Maryam ta ce "ki ka sa ni ko Balkisu ta ɗauka maki yaronki ko yarinyar ki."

Balkisu ta ce "A a Maryam rufamin asiri ai ni kam tun da ba kaza nake ba sai na jima ban Haihu ba sai dai ke."

Amina ta kalli Maryam su ka haɗa ido.

Maryam ta ce "Ban gane ba saboda mi za ki mana wannan fatar toh bata saɓu ba gaskiya."

Balkisu ta ce "akan mi wallahi ni kam ban ki na shekara 5 ban Haihu ba saboda ai saurin haihu na tsufar da mutum."

Amina ta ce "Toh a bar maganar kawai."

Rashid ne ya dawo da ga school tare da Ibrahim Rashid ya ruga aguje ya yi in da Maryam ya ce "Umma na dawo."

Maryam ta ce "Toh yaron albarka sannu da dawo wa ya hanya?."

Ya ce "Lafiya ƙalau Umma ina abinci na?."

Balkisu ta ce "ga shi can a dainnin na haɗa ma."

Ya ce "Ni ba na son naki na Umma na ke so."

Ran Balkisu ya ɓaci sosai kenan har yaron ya fi son ta akan ta.

Maryam ta ce "haba yarona Momyn ka ce fa ka je ta ba ka abincin."

Rashid ya ce"Ni kam Umma na ki na ke so yafi daɗi."

Balkisu cikin zafin rai ta ce "Kana nufin ban iya abinci ba ne ko meye ehe?."

Maryam ta ce "Haba Balkisu mene ne na biyewa shiriritar yaro toh ko mahaifiyarshi ya ce wa ba ta iya abinci ba bale ke da ba ma sabo kukayi ba."

Balkisu ta ce "Ai dole za ki faɗa haka tun da kowa ke yake so ni ba mai su na kowa ya tsanan."

Maryam ta ce "Meki ke nufi ne Balkisu kamar ya kowa yatsaneki?."

Amina ta ce "Ya ko za ayi yaro ya saba da ke bayan ita ya tashi da ita ba ke ba ai dole zai fi sannan ta."

Maryam ta ce "Dan Allah Amina ki bar faɗar wannan maganar ba daɗi fa."

Balkisu ta ce "Ai dole za ta nuna miki cewa yaron ta ne banaki ba ne dan haka ki je zuwa haifar naki."

Maryam ta ce "Dan Allah ku dai kubar maganar."

Maryam ta ce "Rashid ka je kaci abincin da Momyn ka ta dafa maka ka ji yaron albarka."

Ya ce "toh Umma."

Ta shi ya yi ya ce "Momy mu je ki bani abincin."

Ibrahim ya ce " haba dai Balkisu ai sai ke yi hakuri saboda yaro ne duka duka yaushe kika zo kinga ko ai bakwa ɗaya".

Balkisu ta ce "Ai dole ne za ka ce haka amma ba komai da sunnu zai san Ni."

Maryam ta ce "Yi hakuri Balkisu kin san yaro ne sai an bi shi a hankali."

Da haka dai har su ka watse Rashid bai ci abinci ba.

Ya na ɗakin Amina ya ce "Mama wai sai yaushe Umma za ta haihu a samamin kane?."

Amina ta ce "Kai dai duk wanda ya ga girman ka toh ya shiga uku tun yanzun sai tambayar masifa."

Maryam ciki har ya fara fitowa saboda ya fara girma, sai kwaɗayi ya ke sa ka ta.

Sai yanzun hankalin Ibrahim ya bashi lallai fa ciki ne da Maryam, aiko murna ba a Magana wajen Ibrahim.

Ya ce "Yanzun Maryam ciki ne da ke amma ba ki faɗa min ba kuma akan mine kika ƙifaɗamin?."

Maryam ta ce "Saboda yanzun ba na burge ka ko kaɗan, kuma bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login