Showing 18001 words to 21000 words out of 27791 words
lemo ta ce "Mama wai ina so Yaya Rashid ne?."
Umma.
"Su Rashid na can lambo."
Mama.
"Ba ki iya gaisuwa ba ne?."
"Na manta ne ina wuni Umma."
Umma.
"Ba damuwa yi tafiyar ki ƴar albarka."
Mama.
"Wallahi aunty na rasa laifin me na yi
wa Allah da ya bani wannan yarinyar, bata dubin kowa da idon rahama, aunty wallahi har mahaifin ta bata bari ba, ya yi dukanta har ya gaji ya daina."
Umma.
"A'ishah ki yi hakuri kici gaba da yi mata addu'a in sha Allah za ta nutsu da yarda Allah, ki yi addu'a ki riƙa yawan yin sadaka, shi ma ya riƙa fitar da Zakka in sha Allah,Allah zai cire mata wannan abin."
"Toh shi ke nan aunty na gode sosai, shi ya sa nake son faɗa maki damuwa ta saboda kina bani shawara mai amfani."
"Hahaha toh ai nima yarinya tace saboda ai dole zan baki shawara, saboda nima ban san wace irin yarinya zai ban ba ko yaro."
"Na gode sosai Allah ya saka da alkairi Allah ya mayar maki hankalin Yaya."
"Ameen".
Inna su ka ji a bayan su ta na faɗin toh mata da miji ai sai ku tashi kuje dubin Balkisu, ta haihu amma bakwa wajen.
Umma ta ce.
"Inna me ta haifa ne?".
Inna.
"Yarinya ce".
"Toh ma sha Allah."
Tashi sukayi dan zuwa in da Balkisu.
"Assalamualaikum".
"Waalaikumussalam".
"Balkisu a she kin haihu bamu sa ni ba, muna can muna shan fira."
Balkisu.
"Ai dole zaku barni ni ɗaya tunda ni ba sona ake yi ba daga ke har su Innar."
A'ishah.
"Dakata Balkisu karki sa ke ki zagi mahaifiyata a gabana, dan wallahi na fiki rashin mutunci, idan kika sa ke zagin ta wallahi sai naje har gidan tsofinki naci mutuncin su."
Balkisu kuka ta saka ta ce.
Yanzun A'ishah ni kike zagi saboda nace Maryam ta kawo min ruwa."
Ibrahim.
Ya kwashe A'ishah da mari sai da ta yi tingil tingil za ta faɗi.
Umma ta ce.
"Haba Abban yara mene ne haka daga faɗan gaskiya sai duka, Inna ce fa take ciwa mutunci, kuma kake sa ran A'ishah ta barta."
Ibrahim.
"Wallahi kema zan ɗauke ki da mari idan ba ki bar wajen nan ba."
Umma.
"Ai da ka bala'i wallahi dan ba zan kwanta ka dakeni akan kishiya ba, ko kishiyar wacce bata san darajar mahaifan ta ba bale ta san na mahaifan wani."
Ɗago hannu ya yi ta niyar sharara mata mari sai ya ji saukan mari a kumatunsa.
Inna.
"Yanzun kana nufin za ka daketa akan Balki?, lallai yau ka nuna min kai ba Ibrahim ɗina bane, saboda Ibrahim ɗina ba ragoh bane."
Balkisu.
"Yanzun kana nufin kyale ta za ka yi marin ka fa ta yi."
Ibrahim.
"Inna yanzun ni kika mara saboda wannan bagi dajiyar ƴar talaka?."
Umma.
"Ibrahim yau kaine ke kirana da ƴar talaka?, na gode sosai Allah ya saka da alkairi."
Fita ta yi daga ɗakin, ɗakinta taje ta ɗauki mayafin ta tana fita A'ishah da Amina na kawowa.
Amina.
"Umman yara ina zuwa haka, ba dai tafiya za ki yi ba?."
Umma.
"Wallahi tafiya zan yi kuma ba zan dawo ba sai ya ne meni da kansa sannan zan dawo."
A'ishah.
"Haba aunty dama haka ne take so fa kenan kina nufin taci galaba akan ki."
Umma.
"A'ishah Amina ba galaba ta yi akaina ba kawai ina son in ni santa kaina da shi ne ."
Amina.
"Humm haka kika ga yafi maki."
"Eh"
"Toh shi ke nan ki tafi kawai".
Tafiya ta yi A'ishah da Amina sai kuka suke yi.
Amma Maryam Ma'aruf fa idan ya dawo me zamu ce ma sa.
Maryam.
"Dan Allah karki tura min shi, ya yi zaman shi in da kike, ga su Rashid da Rufa'i nan."
RASHIDA
BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number08084277827☎️
14
📝
Ga su Rashid da Rufa'i nan sai ya zauna in da suke.
Cikin kuka ta ja hanun Maryam tana cewa
"Yanzun da gaske tafiya za ki yi, ki barni bayan kin san cewa kece ƙawata a gidan nan, amma duk da haka za ki tafi?."
Cikin kuka ta janye hanunta tana cewa
"Haba Amina ai ba mutuwa zan yi ba kuma zan dawo in sha Allah".
"Haba aunty ya za kice za ki dawo ai tafiyar ce bama so, yanzun idan Ma'aruf ya nemi mahaifiyar shi me kike son a ce ma sa?."
"A'ishah karki damu ai baiyi rashin uwa ba saboda ga mahaifiyar shi nan."
Bata sa ke magana ba ta yi waje abinta.
Fita tayi daga cikin gidan cikin sanɗa dan kar ƴan gidan su san fitar ta.
Tana fita ta tare mai machin ta mai kwatancen gidan sai ƙofar gida, kuɗi ta biya mai machin ɗin ya yi tafiyar shi.
"Assalamualaikum"
"Waalaikimussalam"
Oyoyo oyoyo Gwaggo sannu da zuwa, wasu ƴan yara ne su ke gaida ta.
"Yauwa sannu ƴan albarka ina kabar ne?".
"Gwaggo yana can yana bacci."
"Ok toh ma sha Allah."
"A a a ƴata sannu da zuwa, amma yana ganki da kaya niƙi niƙi haka ina zuwa?."
"Mama ba komai kawai na kawo maki ziyara ne fah."
"Toh shiga daga ciki dai ina zuwa."
Kayan ta je ta ajiye sannan ta dawo tana cewa
"Mama wai su Yaya nan kuwa?."
"Eh lafiya dai."
"Ba komai kawai na tambaya ne saboda na yi missing ɗin su ne sosai?."
"Toh Allah yashirya min ke." ta faɗa cikin dariya.
"Ina Ma'aruf ne?."
"Yana can na barshi idan yazo baya barina na sa ke sosai."
"Toh shi ke nan."
Faɗa min meke faruwa ne Maryam na san zuwan nan naki ba a banza yake ba.
Mama wallahi na gaji da wulaƙancin da Ibrahim yake min saboda gaba ki ɗaya baya sona baya ƙauna ta.
Haba Maryam kin san ba a cikin hankalin shi yake ba sai kici gaba da hakuri har Allah ya yi ma sa sauƙin walahar nan.
Ni kam yanzun sai dai na yi ma sa addu'ar shi a nan amma ba zan da wai ba sai yazo biko na da kan shi.
Toh wannan cikin fa idan kika tashi haihuwa fa.
Haihuwa ba yanzun ba sai nan da wata uku in sha Allah.
Toh shi ke nan.
Cikin sanyin jiki ta ce .
"Mama meke damunki ne naga duk kin rame haka kamar ba ke ba wallahi?."
"Ba komai lafiya ƙalau nake."
"Haba Mama ki faɗa min dan Allah."
"Maryam ina son ki riƙe mijinki tsakanin ki da Allah idan kika cuce ɗan mutune wallahi ban yafe ba ko bayan raina ne, kuma ki riƙe addu'a ban da wasa da ita yanzun ke ba ƙaramar yarinya bace, ki riƙe ibada ki riƙe karatun azkar safe da yamma kar ki bari maƙiya suyi nasara akan ki, ki riƙe Allah shine gatan ki shine mahaifiyar ki shine Mahaifin ki, sannan ki riƙa roƙon Allah ya shirya mana zuri'ar mu, ki kula da yaran ki sosai ki ɗaura su akan hanyar daidai kar kuɗi su ja ki ki bar yaranki su lallace."
Cikin sanyin jiki take cewa
"Mama in sha Allah zan yi duk abin da kika ce in sha Allahu ba zan ba ki kunya ba."
"Maryam bana da lafiya sosai olsa ce ke damuna kuma taci ƙarfi na ban so, faɗa maki ba amma ba yanda na iya dole sai na faɗa maki."
"Olsa Kuma mama me ya sa ba ki faɗa min ba bane, yanzun Mama idan kika mutu wallahi sai nafi kowa damuwa...." Bata ƙarasa ba saka makon kukan da ya ci ƙarfin ta.
Ke kukan mi kike ne haka ce maki na yi ance mutuwa zan yi ne ehhe.
A a amma ..
Yi min shiru bana son Wata magana.
Kiran sallah magarib aka yi hakan ya sa suka tashi zuwa yin sallar.
BAYAN WATA UKU
Maryam ce zaune a cikin daƙi Mama na a waje zaune ita ma .
Cikin ta ne ya murɗa mata sosai wani danshi danshi taji aiko tana dubawa taga jini na bin kasan ƙafarta.
Cije baki ta shiga yi saboda a zabar da take ji cikin ikon Allah ta haihu lafiya.
Mama jin kukan jariri ya sa ta tasowa ɗakin ta shiga jariri tagani cikin murna ta furta cewa
"Ma sha Allah Allah na gode ma."
Dubawa ta yi sai taga ƴa mace ce aka haifa murna ba ƙadan ba ta ji .
Gyarata Mama ta yi sosai da sosai sannan ta gyara Umma .
"Kira ƴan gidan can ki faɗa masu haihuwar."
Bangaren Ibrahim kuwa komai yake yi sai yaga Maryam idan bacci yake yi ita yake gani abin ya dame shi ba kaɗan ba ya je wajen Amina yana sanne kai ya ce
"Aunty dan Allah ki taimaka min ki dawo min da matata wallahi ina son ta kamar raina amma wani lokacin sai naji na tsane ta ba kaɗan ba."
RASHIDA
BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number08084277827☎️
15
📝
Shiryawa su Amina suka yi sai ga Ma'aruf, Rashid, Rufa'i sun dawo daga school.
"Ma'aruf Mama ina zuwa naga kin shirya haka?, kuma ni Umma nake son na gani Mama".
"Gidan Ummarku zamu je ita ta haihu dan haka je ka shirya mu tafi Rufa'i je ka shirya kai ma."
Toh suka ce sannan suka je shiryawa .
Rashid ya ji daɗi sosai da a kace Ummarshi ta haihu sai ji ya matsu baiga yarinyar ba.
Fitowa suka yi sai gidan su Maryam Rashid yariga kowa shiga gidan sallama kawai ya yi sai cikin daɗi da yake ta saba zuwa dashi .
Yana shiga ya tarar da yarinya kwance sai bacci take hankali ƙwance kafe ta da idanu ya yi haka kawai ya ji yana son yarinyar fiye da su A'ishah.
"Umma yarinyar nan akwai kyau ji bakinta jawur kamar janbaki a ka saka mata, kuma ga ta fara ga ta kyakkyawa, kai ma sha Allah."
"Hahaha kai Rashid wannan yabawan haka, ko kana son ta ne a baka ita har sai ka tashi aure."
Hahaha kai shirme ke kam ko neman mu bazaki yi ba.
"Ayya yi hakuri Maman yara wallahi ban kula da ku bane."
"Wai ina kishiyar tawa ne naji shiru?." Cewar Inna
"Da yake ba kya da ido ba ai ba za ki ga in da take ba ya cilla mata harara."
"Kai ɗan baƙin rai wallahi ka kiyaye ni in ba haka ba sai na saɓule Yanzun ka ji min mai ƙatun kai."
"Mtsww sai ki saɓule ni ɗin mai warin goro kawai."
Kai Rashid ya isa haka .
Toh ai saika bamu yarinyar ko, Inna ta faɗa tana shararar shi.
"Ba zan bada ba sai ki yi ta ƙarfi ni wallahi kin saka min ciwon kai saboda wannan surutun naki mai bakin aku kawai."
"Ga mai bakin aku nan zaune ba ni ba."
Banza ya yi da ita saboda gaske kanshi ciwo yake ma sa ɗan wannan maganar da ya yi.
Maryam ta kalli in da Inna ta nuna wa Rashid kawai sai taga Ibrahim yana kallon ta.
"Umma nayi kewarki sosai dan Allah ki dawai gida."
Yi ta yi kamar bata ji shiba.
Ibrahim Maryam dan Allah ina son magana da ke idan babu damuwa.
Bana da lokacin magana da wanda ba ya sona kuma baya ƙaunata.
"Haba Maryam cikin yara muke fa, kuma yanzun sun mallaki hankalin kansu, ba yara bane. Cewar Amina
Yi hakuri Maryam yanzun ya fara jin sauƙi, saboda addu'ar mu ta taimakon Allah dan Allah ki saurare shi.
"Toh" kawai ta ce dan ko ba komai ta ɗauki Inna a matsayin Uwa.
Tashi suka yi dan basu waje su gana.
"Dan Allah Maryam ki yi hakuri wallahi bana cikin hankalin kaina, kema kin sani dan Allah ki yi hakuri wallahi idan ina tare da ita, duk abin da take so shine zan yi, ko Inna bata isa ta hanani abin da ta ce ba, nima ban san meye dalili ba."
Ba komai amma ba zan koma sai anyi suna .
Kamar ya sai anyi suna gaskiya a gidan Ubanta za'ayi mata taro.
Toh shi ke nan ba damuwa.
Anjima nake son ki koma ni zanzo na ɗauke ki.
Toh sai nayi shawara da Mama.
"Assalamualaikum wai har yanzun baku gama maganar ba, tafiya muke son yi amma kazo ka yi zaune".
Mun gama mutafi kawai sai anjima Umman yara.
"Toh".
"Umma karki bari kowa ya ɗauke sai ni." Cewar Rashid.
Umma "Toh Rashid ba wanda zai ɗaukar maka matarka ."
Dariya kowa yasa ka har da Mamar Maryam.
Dare nayi aka zo ɗaukar Maryam sai gidan su Ibrahim murna wajen Rashid, Ma'aruf, Rufa'i, ba a magana
Ita ma Maryam ta ji daɗi saboda ko ba komai mijinta ya yo bikonta Kuma taji daɗi sosai.
Rashid ya ɗauke jaririyar wai ba mai ɗaukar ta sai shi Ma'aruf da Rufa'i har sun ga ji da magana sunyi shiru.
"Kai ɗan rainin hankali ba ni ita na riƙa dan Uwarka, zoka riƙe yarinya kace ba mai amsar ta sai kai, dan iskanci da samun waje". cewar Amina
"Haba dan Allah Maman yara ki barshi har ya gana da matarshi mana, kin taƙurawa yaro ke akwai mai rabaki da Yaya ne, da za ki raba shi da tashi."
"Wallahi bana ciki da bakin ki, Allah ya tsere ta da auran wannan, ɗan baƙin rain."
"Ai kam dai dan baza ta aura min miji ba, salon ya ganta yarinya ni tsohowa ya ce ita yake so ba ni ba, toh ba zai yiwu ba tam."
"Mtsww wai ke kam mai zan yi da ke ne kina warin goro ji bakin ki."
Kai ya isheka haka idan nasake jin maganar nan sai ranka ya ɓaci, wanda bai san wasa ba."
BAYAN SATI ƊAYA
Anyi suna yarinya ta ci sunan Inna wato Rashida su na kiranta da Ummi.
Su A'ishah kam har sun saba da rashin ɗaukar da Rashid baya yi amma kullum yana riƙe da Ummi sun yi kuka har sun daina.
Idan fita ya yi sai ya siyowa Ummi chocolate da Sweet sai su Mama sunyi da gaske sannan su samarwa su Fatima.
Ummi ta saba da Rashid sosai.
"Idan mutum baya sona toh dole yaso takwarata kuma sai najawa mutum aji sannan zan ba shi auranta ehhee." cewar Inna
"Wai ni kam ba Kya da zuciya ne ki kyale ni mana karki sakamin ciwon kai Please."
Aiko kan shiya daɗe bai cire ba dan rainin hankalin kawai."
"Haba Kaka me ya sa kullum sai kin ɓatawa Abokina rai ne." Ma'aruf ya faɗa
Kaci gidan ku mai kai kamar na mangoro.
Hahaha dama mangoro na da kai ne .
Haka suka sa ka Inna a gaba su na dariyar ta.
"Kai Rashid bana son rashin kunya ya zaku saka mana Inna a gaba kuna dariya, saboda rashin kunya ai ga Uwayenku nan baku saka su a ga ba kuna dariya ba, sai Inna da ku ka raina." cewar Muhammad mai shigowa ya ji abin da suke wa Inna
Sai cewa ta yi
"Ai kai ne sukewa ba ni ba saboda ni nafi ƙarfin su har mahaifan nasu."
Harara Ma'aruf da Rashid suka aika mata lokaci goda.
Ai sai dai idon mutum ya ya tsiyaye ehhe na faɗa maku.
Rufa'i "Haba Inna wai ke kullum sai kin zagemu hankalin ki zai kwanta, mai warin goro kawai ji bakin ki duk ya yi jan goro."
Ga mai warin goro nan zaune kai jama'a wai ba zakuwa yaranku magana ba kun min shiru haka kuna kallona .
"Yi hakuri Inna Rashid, Rufa'i kaima ku yi wa mutane shiru yanzun ko sai na mutuncin ku."
BAYAN SHEKARA BIYU
Haka rayuwa ta ci gaba har tafiya zuwa London ta kama Abba da Daddy dan ƙarfafa officer ɗin su.
Abba ya ce "Rashid idan muka je zan kira akai mana kai, saboda da Umman ku zan je sai ka zauna a nan."
"No ba zai yiwu ba kawai ka bar shi idan ya isa zuwa sai yaje da kan shi, idan suma su na da ra'ayin zuwa can sai suje tare."cewar Daddy
"Toh shi ke nan ba damuwa Yaya ki shirya dake zan je."
"A a ni kam gaskiya ina nan ba in da zan je, kawai ka ɗau matar ka ku tafi wallahi na yafe ina tare da Maman yara."
"Amma dan Allah ka ce kar taje da Fatima ta ta barta a nan kawai."
"Eh gaskiya ne tun da yanzun ba Nono suke shaba."cewar Mama
"Toh shi ke nan."
Ummi tana ta jagol jagolo abin ta sai daɗi take sha a hannun Rashid.
Su Fatima Ma'aruf sun fara jan su a jiki idan suka fita sai son siyo masu abu ko bai kai na Ummi yawa ba.
Yarinyar tasha gata da musamman dau su A'ishah basu samu gatar ta ba Ummi.
Masu tafiya sun shirya komai yau ne ranar tafiyar su.
Rashid, Ma'aruf, Rufa'i, duk kujini da idon rahama, kamin mu dawo ku tabbatar da kun fitar da matar aure, dan yanzun ba zamu dawo ba sai nan da shekara goma ,ku kam kun kai ashirin da hayi sama.
Rufa'i ya sakawa Daddy dariya, "Daddy duka duka yaushe muka tashi da har ake mana zancen aure."
"Idan na dawo baku fitar da matar aure ba, duk wacce nasa ma ita zan haɗa ku da ita tam, a sannan ne zaku tabbatar da cewa kun isa aure."
Rashid "Daddy Yi hakuri amma karatun mu fa?, ni gaskiya bana son karatu a Nigeria nafi son India ko London, saboda ga baki ɗaya na gaji da wannan makarantar wallahi, kuma maganar aure gaskiya Daddy ba Yanzun ba."
Abba "Ok toh shi ke nan ba damuwa sai ka tashi kamin magana."
"Amma Ibrahim kana da hankali ya zan kai shi India karatu ina laifin London ɗin, amma India basa da tarbiyya ko kaɗan."
Da India, da London, da Nigeria, duk kabar wa Allah zaɓi shi zai shirya mana su ba dibarar mu ba dan haka kabar shi ya yi karatun shi a in da yake so."
RASHIDA
SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number08084277827 ☎️
19
"Assalamualaikum"
"Waalaikumussalam"
"Kaka Barka da safiya kintashi lpy."
"Lafiya lau masu ƙantan kanu yau