Showing 15001 words to 18000 words out of 27791 words

Chapter 6 - Rashida Part 1 Complete Hausa Novel

Shaawatu   

07 Aug 2026

114

a ranka ba ka sona ba ka ƙaunata ka gaji da zama da ni kawai ina zaune ne alfarmar Inna da Yaya ne."

Ibrahim ya ce "Bangane ba Maryam meki ke nufi da waɗan nan maganganun nan naki?."

Maryam ta ce "Wallahi ko da na rantse ba zanyi nadama ba yanzun ba ka sona."

Ibrahim ya ce "Wallahi Maryam ina son ki ina ƙaunar ki meki ka min da har zai sa nace ba na son ki dan Allah ki dai na wannan maganar Please my love."

Maryam ta ce "Toh shi ke nan tun da kace na bar maganar toh na dai na in sha Allah, amma ka sa ni cikin nan cikin wata na 6 ya ke dan haka kasan yadda za ka yi kuma dan Allah kar ka bari matar ka ta sa ni dan Allah."

RASHIDA

Sha'awanatu Faruk diggi✍️
Sha'awa marubuciya✍️✍️

WhatsApp number 08084277827☎️

8

📝
Fita ɗakin Balkisu ta yi part ɗin ta shiga ta tarar da Ibrahim.

Ibrahim ya ce "Balkisu a ina ki ka fito ne haka?."

Balkisu ta ce "Haba dai mijina muna tare da Maryam ne fa, ina kwance ta zo ta ce min mu fita mu je fira."

Ibrahim ya ce "Toh shi ke nan dan Allah hakkina nake son ki bani Please Balkisu."

Balkisu ta ce "Gaskiya ba zan iya ba sai dai ka yi hakuri saboda ko jiya fa ni ka saukar wa gajiyar ka, toh yau kam ba za ta saɓu ba gaskiya."

Ibrahim ya ce "Yanzun idan ke baki bani hakkina ba waye zai ba ni, Maryam ce kuma yanzun jego take yi ya zan je in ce ta bani hakkina."

Balkisu ta ce "Au kana nufin gorin haihuwa ka ke min?."

Ibrahim ya ce "Allah ya baki hakuri ni ban maki gori ba."

Balkisu ta ce "ga abincin ka can idan zaka iya ci."

Tashi ya yi yaje ya ɗauko abincin ya dawo ya fara cin abincin, ya manta bai yi bismillah ba kawai ya fara cin abincin.

Jin kanshi ya yi kamar an buga ma sa wani abun mai nauyin gaske ga baki ɗaya fita ya yi a hayyacin shi.

Ibrahim ya ce "Mata ta abincin nan ya yi daɗi sosai."

Balkisu ta ce "Ai na sani."

Tashi ya yi dan zuwa part ɗin Maryam amma sai ta ce "Ibrahim ina zuwa ne haka?."

ya ce "Ba in da na yi kawai falo zan je."

Ta ce "Kar na ji an ce wai kaje in da Maryam, wallahi idan ba ni na baka hanya ba kaje sai na ɗau mummunan mataki akan ka."

ya ce "Bama zan je ba wallahi."

ta ce "Toh ta shi ka je."

Ibrahim da sauri ya fita a ɗakin sai ɗakin Maryam ya tarar da ita ta na shayar da Rashid.

Ganin shi kawai ta yi ba sallama ba komai .

Maryam ta ce "Yaya meke damunka naga ka shigo ba ko sallama?."

Ibrahim ya ce "Idan na yi maki sallama cinta za ki yi ne?."

ta ce "A a ka yi hakuri."

Zama ya yi yana son yin magana amma ba maganar taƙi fitowa.

Maryam ta ce "Dan Allah Yaya ka faɗa min meke damunka na ga kana cikin damuwa."

RASHIDA


By
Sha'awanatu Faruk diggi ✍️ ✍️
Wtspp 08080304152☎️

10

📝
Su Ma'aruf ne zaune a falo rike da littafan school suna rubutu .

Maryam ta ce "Rashid kai da ƙanen ka Rufa'i ku zo ku ci abinci kubar rubutun haka nan."

Rashid ya ce "Umma aboki na Ma'aruf fah."

Ta ce "Abokinka ko ƙanen ka?."

Ya ce "Umma ai Abokina ne kuma ƙanena ne."

Ta ce "Toh ku tashi mu je ku ci abincin."

"Toh" su ka ce

Amina ce zaune da ƙaton cikin ta a kan dainnin tebur.

Balkisu ma da cikin ta, na Maryam ne ƙarami bai girma ba.

Amina ta ce "Wai Maryam ba za ki bar wannan yaron ba, wallahi baƙin ranshi ya yi yawa ji dan Allah ko dariya ba ya yi."

Ta ce "Eh ba komai yana dai jin maganar mahaifan shi ko."

Amina ta ce "Wallahi ba gaskiya bane ba, saboda Ma'aruf akwai shi da jin maganar mahaifan shi, amma wannan ɗan baƙin rai ba mutunci."

Balkisu ta ce "Ai Amina baki san mai mutunci ba wallahi, saboda ga bakiɗaya Ma'aruf bai da mutunci, kina ganin shi haka kin san ba ɗan mutunci ba ne."

Amina ta ce "Kamar ya ba ɗan mutunci ba ne, meki ke nufi da wannan kalmar."

Maryam ta ce "Ai gaskiya Balkisu ne, saboda ga baki ɗaya ɗan ki ba ya jin magana ko kaɗan."

Ta ce "Wallahi wannan maganar ba gaskiya ba ne ba ehhe."

Rashid ya ce "Umma sai yaushe za ki haifa min ƙanwa ne?."

Ta ce "A a Rashid ƙanwa ka ke so ne?."

Ya ce "Eh Umma."

Ta ce "Toh kwantar da hankalin ka ta kusa zuwa in sha Allah."

Ya ce "Toh Umma."

Amina ta ja tsaki mtss aikin banza kawai.

Dariya Maryam ta yi ta ce "Toh su kishi har ya bayyana Amina ai da kin ɓoye shi."

Ta ce "Ni ce zanji baƙin cikin wannan abin."

Ta ce "Eh mana."

Ibrahim ne da Muhammad su ka shigo bakin su ɗauke da sallama su ka ce
"Assalamualaikum"

"Waalaikumussalam" su ka amsa ma su.

Su Rashid da gudu su ka tarbi mahaifan su amma abin mamaki Ibrahim Rufa'i kawai ya amsa wa sannu da su ke ma sa shida Ma'aruf.

Ma'aruf ya ce "Abba sannu da zuwa."

Nan ma shiru Ibrahim ya yi ma sa.

Muhammad ya ce "Wai Ibrahim mene ne haka, baka ji sannu da Ma'aruf ke ma ka bane?."

Ya ce "Yaya ban ji ba ne ba."

Ma'aruf yi ya yi kamar zaiyi kuka sai Muhammad ya ce "ma sa yazo."

Maryam ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba amma haka ta share shi.

Ya ce "Balkisu sa ka min abinci na."

Ta ce "Gaskiya ba na iyawah saboda cikina ciwo ya ke min ka ce wa Maryam ta haɗa ma."

Ya ce "Maryam haɗa min abincin."

Tashi ta yi ta yi tafiyar ta ta bar su nan a dainnin ɗin.

Sakin baki su ka yi ga baki ɗayan su .

Rashid sauka ya yi daga jikin Muhammad ya ce "Abokina mu je in da Umma."

Shima Ma'aruf sauka ya yi su ka yi tafiyar su in da Umman su.

Muhammad ya ce " Wai Ibrahim me ya sa har yanzun kai yaro ne, yanzun dan Allah wulakanta yaron nan na ta da ka yi a gabanta daidai ne ehhe?."

"Nifa Yaya ban kula da shi ba ne"

Amina ta ce "Wallahi Ibrahim ban taɓa ce ma ka ƙarya ka ke ba, amma yau kam zan faɗa wallahi ƙarya ne, ka ce wai baka ganshi ba."

Ya ce "Wai dan Allah a kan wannan yaron ne kowa zai zo ya na gaya min Magana."

Muhammad ya ce "Toh fa ko ramawa za ka yi?."

Balkisu ta ce "Ibrahim ka min shiru dan Allah duk kunci ka min kunne da surutu."

Shiru Ibrahim ya yi bai sake magana ba.

Amina ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un Maryam kin banu, tashi ta yi ita ma."

RASHIDA


By
Sha'awanatu Faruk diggi ✍️ ✍️
Wtspp 08084277827☎️

11

📝
Muhammad ji jiga kan sa kawai ya yi shima ya bi bayan Amina.

Sallama ya yi. "Assalamualaikum"

"Waalaikamussalam." Amina ta amsa.

Ya ce. "Maman yara mai ya sa ki ka tawo ba a gama cin abincin ba?."

Ta ce. "Wallahi Maryam na cikin matsala sosai, shi ne ke wayan sa ka ta ciwo kenan amma ba ta faɗa min ba."

Ya ce. "Ban fahimci zancenki ba."

Ta ce. "Abin da na ke wa Ibrahim gudu kenan ga shi ya faru."

Ya ce. "Amina ki faɗa min yan da zan fahimci maganar ki."

Ta ce. "Ta asirce Ibrahim sai yan da ta yi da shi dan Allah ku ta ya shi da addu'a, ni dai zan ta ya Maryam in sha Allah."

Ya ce. "Ai ba yau ba na ke ganin Maryam cikin wani hali, kawai saboda ta na jin nauyi na ne ya sa ban yi mata magana ba."

Rashid ne ya zo da gudu ya ce. " Mama Mama Umma ba ta da lafiya sai kuka take yi."

Barin ɗakin Amina ta yi, da sauri Muhammad ya riƙe hannunta ya ce. "Ki bi a hankali kar ki ji ciwo kema."

Ta ce. "Toh".

Sakin ta ya yi amma duk da haka sai da ta haɗa da gudun.

Ɗakin Maryam ta je ta tarar da Maryam a kasa sai kuka take gata riƙe da kanta .

Ta ce. "Maryam mene ne haka, idan ki ka hallaka kanki fa, kuma gaki da ciki, haba dan Allah ki yi hakuri ki barwa Allah komai shine zai saka maki, ba wani ba ke dai addu'a ne ta ki."

Ta ce. "Amina na shiga uku tun auren nan na Ibrahim ban da kwanciyar hankali, kullum da abin da zai min wallahi na ga ji gidan mu zan ta fi."

Ta ce. "Haba Maryam kenan ta yi galaba a kan ki?, ki yi aiki da hankalin ki ba zuciyar ki ba."

Ta ce. "Amina Ibrahim ba ya sona kuma ba ya son yaron ki, ai idan bai soni ba toh ya so yaronki amma mu duka bama samun hakan."

Ta ce. "Maryam ki yi hakuri zan ta ya ki da addu'a in sha Allah, na san Mama tana can tana ta ya ki da addu'ar in sha Allah zai dawo dai dai kamar yadda ki ka san shi."

"Toh" kawai Maryam ta ce.

Jikin ta Amina ta taɓa zafi ta ji sosai ta ce. "Maryam ba ki da lafiya ne har haka?."

Ba ta tanka mata ba kawai kai ta ɗaga mata.

Ta ce. "Rashid ya je ya kira Abban su yazo ya duba Umman ku."

Da gudu su ka fita a ɗakin sai part ɗin Balkisu.

"Assalamualaikum."

"Waalaikumussalam."

"Momy wai Mama ta ce Abba yazo ya duba Umma."

Ta ce "Baya nan sai ya dawo."

"Toh" su ka ce

Fita su ka yi sai ɗakin Umman su.

Mama ta ce "Mai ya ce ne?."

Su ka ce.
"Wai cewa ta yi baya nan sai ya dawo, kuma Mama mun gan shi a zaune."

Mama ta ce "Zaune fa ku ka ce?."

"Eh" Mama

Ta shi ta yi ta je ta kira Muhammad ta faɗa ma sa halin da a ke ciki.

Ran Muhammad ya ɓaci sosai ɗakin ya nufa, ya na zuwa ya wankawa Ibrahim mari har sau biyu ya ce.

"Ibrahim ka na da hankali kuwa ehe, maike damunka ne da za ka hallaka ƴar mutane?."

Amina ta ce. "Na shiga uku Daddyn yara dan Allah ka yi hakuri, wallahi da na san abin zai kai ku haka da ban faɗa ma ka ba."

Muhammad ya ce "Za ka bani amsa ko sai na ci uban ka a nan ne?."

Ya ce. "Yaya ka yi hakuri ni wallahi ba na son ta ne."

"Baka son ta fa kace Ibrahim?."

"Eh" Ibrahim ya faɗa .

Amina ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Ibrahim kai ne wai kuwa gaskiya ba kai ba ne, Ibrahim da na sa ni mai son Maryam sosai."

Maryam da ke ba kin ƙofa ta ce. "Ai na sa ni Ibrahim ba sai ka faɗa masu ba, kuma na gode sosai da sakayyar da kai min."

Cikin kuka ta ke maganar abin tausayi.

Muhammad fita ya yi ya kira Inna ya faɗa mata duk abin da ke faruwa.

Inna ta zo ta ɗauke shi da mari ta ce "Sha-sha-shan banza mutumin banza, toh yadda ka yi mata nima na san za ka iya yi min shi."

Balkisu ta ce "Wai wane irin wulaƙanci ne wannan, a ga ba na a zo a na ciwa mijina mutunci toh wallahi ba zan yarda ba."

Mari ta ji a kuncenta da sauri ta dafe kuncin na ta .

Muhammad ne ya ce "Duk wulaƙancin ki ya tsaya a kan shi, idan ki ka ce za ki wulakanta, mahaifiya ta a ga ba na, toh wallahi komai zai iya faruwa."

Amina ta yi saurin riƙe shi ta ce. "Haba Daddyn yara bafa muharramar ka ba ce ba fa, kuma har ka iya ɗaga hannu ka dake ta?."

Wayar Maryam ce riƙe a hannun Rashid kiranta a ka yi sai kawai Rashid ya ɗaga kuma bai yi magana ba.

Maryam ta ce. "Dan Allah Yaya ka yi hakuri in dai a kai na ne wannan abin ke faruwa, wallahi na warware sosai jiki na ya ji sauƙi dan Allah mu ta fi."

Ya ce. "Maryam mu je part ɗin Inna zan yi magana da ke."

"Toh" kawai ta ce.

Fita ya yi itama Maryam bayan shi ta bi.

Inna ta ce "Ka sa me ni a ɗakina ina jiran ka."

Sannan su ka fito ita da Amina.

RASHIDA

PAGE NA 12

BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️
WhatsApp number08084277827 ☎️

12

📝
Tashi ya yi da niyyar fita ta ce "Ina za ka je ne?."

Ya ce "Zan je wajen kiran Inna ne."

Ta ce "Ba za ka je ba."

Ya ce "Toh shi ke nan."

Zama ya yi sai bacci.

Kiran hajara ta yi ta ce "Hajara wallahi bokan aikin shi na kyau, ga shi sai juya dan iskan nan na ke yi, yanzun kuɗin sa na ke son na fara ɗibawa."

Ɗaya bangaren ta ce "Ai Balkisu gara ki juya ɗan iska, ai shi ma ya san ruwa ba sa'ar kwando ba ne."

Ta ce "Ke dai bari yanzun haka ana kan wata dirama a gidan nan, kuma ba zan ba shi hanyar zuwa can ba."

"Hahaha kai ƙawata shegiya ce ke wallahi."

Ta ce "Balkisu wai ya maganar ƴar iskar kishiyar nan taki ce, har yanzun ta na nan da addu'ar tan ne."

Ta ce "Ai ki barta wallahi ba zan kya le ta ba, kuma ba zan kyale yaranta ba, saboda suma ina jin kamar kishiyoyina ne."

Hajara ta ce "Gaskiya ne kinsan da zafi zafi a kan duke ƙarfe."

"Gaskiya ne kam" cewar Balkisu

Sallama su ka yi.

Amina ji ta yi cikin ta na mata ciwo amma ba ta yi magana ba.

Maryam ta ce "Amina meke damunki ki ne naga kamar ba Kya jin daɗi?."

Ta ce "Maryam cikina ne na ke jin yana min ciwo sosai."

Inna ta ce "Ayya ko naƙodan ce?."

Muhammad ya ce "Naƙoda kuma Inna cikin wannan halin."

Amina ta ce "Maryam dan Allah ka ma min na tashi zan je ɗakina."

Ta taimakon Maryam Amina ta isa ɗakinta.

Tana shiga ɗakin cikin ikon Allah ta haihu lafiya.

Maryam da gudu ta yi part ɗin Inna ta ce "Inna Amina ta haihu."

Inna ta ce "Yanzun idan kika ji ciwo fa wannan gudun haka."

"Inna wallahi ina murna ne ban san yadda zan yi ba, saboda farin ciki ƴa mace fa ta haifa."

Muhammad ya ce "Kai Maryam ki rage wannan abin, yanzun idan kika hallaka min ƴarinya ko yaro fa?."

Cikin jin kunya ta ce "Yaya yi hakuri wallahi ina son ƴa mace ne sosai da sosai."

"Ya ce "Toh Allah ya baki mai albarka."

Ta ce "Ameen Yaya na gode sosai."

Tashi su ka yi zuwa in da Amina ita da Balkisu su ka tarar zaune.

Balkisu ta ce "Maryam ko baki faɗa min ba toh na ji sai hakuri."

"Amma Balkisu yanzun nake da niyar kiranki, kawai dai na kira su Inna ne."

Ta ce "Amma ai na ga kamin ki kai ga resu sai kin wuce ni."

Maryam ta ce "Amina meki ke bukata yanzun?, dan Allah ki yi hakuri kwanciya nake son na yi."

Ibrahim ne ya shigo Inna ta lallai Muhammad ya ce

"Ibrahim Ina ki ran da Inna ta yi ma ne, ko kafi ƙarfin zuwa ne?."

Ya ce "Ni fa wallahi na gaji da wannan abin, kullum ana takurawa mutum."

Inna ta ce "Ai sai ka koma in da ba'a takura ma."

Su Ma'aruf ne su ka shigo ɗakin su ka ga jariri, sai Ma'aruf ya ce "Laa Mama waye ya haihu?."

Balkisu ta ce "Ai Mamarka ce ta haihu."

Rufa'i ya ce "Laaa wallahi Mama ta na da kyau sosai."

Rashid ya ce "Umma sai yaushe za ki haifa min ƙanwa ne?."

Umman ta shi ta ce "Yarona sai lokacin fitowar shi ya yi."

Ya ce "Shi ke nan."

BAYAN SATI ƊAYA

Anyi suna yarinya ta ce sunan Goggonta A'ishah ma sha Allah.

Har da A'ishah ta zo sunan dan sun dawo da tafiyar ta su ka yi .

A'ishah ta ce "Aunty Maryam wai Aunty Balkisu nan na da hankali?."

Ta ce "A'ishah saboda mii za ki kirata da maras hankali, kin ganki idan Yayanki ya ji ki, toh wallahi sai kunyi faɗa tam."

Ta ce "Yanzun aunty Saboda na ce mata maras hankali shine za mu samu matsalar?."

Ta ce "Eh sosai ma."

"Allah ya kyauta" kawai A'ishah ta ce

Amina ce ta kira Maryam ta ce "Ta zo ta karɓi A'ishah."

A'ishah ta ce "Wallahi aunty ni zan karɓe ta, saboda yanzun ba zama na ke ba tafiya zan yi na barki da ita."

RASHIDA

SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number0808427727 ☎️

13

📝
"Toh shi ke nan ɗauke ta ɗin ba damuwa."

"Yauwa aunty na."

Wata yarin ce tafi toh rike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login