Showing 6001 words to 9000 words out of 27791 words

Chapter 3 - Rashida Part 1 Complete Hausa Novel

Shaawatu   

07 Aug 2026

105

faɗa ma su".

Rashid ya ji gaban shi ya ba da tim, sai da ya dan rufe idanunshi kaɗan kamin ya biɗe a kan Ummi.

Ummi ta ji kamar Momy ta zuba ma ta ruwan zafi ta ce "Momy dan Allah ki yi hakuri wallahi ba ha ka ba ne kawai mu na faɗa ne amma ba gaskiya ba ne dan Allah". ta na maganar ta na hawaye.

Momy ta ce a zuciyar ta dole tun da ta ga Ummi ba ta son ana haɗa ta da Rashid dole ne ita za ta yi shiga da fice sai an ɗaura auren Ummi da Rashid duk a zuciyar ta ke zan cen nan.

A fili ta ce "mai ya sa ki ke kuka ne Ƴarinyata ai basai kinyi min a sarar hawayen nan na ki ma su daraja ba kawai faɗa na ke yi amma bazan faɗawa Abban ku ba kinji ƴata hankalin ya kwanta, Fatima kawo min ruwan sanyi ta sha ko ranta zai yi sanyi.

Fatima ruwa ta kawowa Ummi tasha sannan hankalin ta ya dawo kan ta.

Su Umma su ka fito, ba su jima ba su Mama su ka fito Umma ta ce "su je dainnin Ummi wajen tsakanin Abba da Daddy ta kai kujeran ta ta zauna.

Umma ta ce "Ummi sa ka wa kowa abincin", Abba ya ce "ba za ta sakawa kowa ba sai dai kar su ci", haka Umma ta tashi zuwa sakawa kowa abinci.

FARKON LABARIN

Wani dan karamin ƙauye ne mai suna gada a jahar sokoto.

Wata mata ce mai kimanin shekaru 24 ta na aiki a tsakar gida.

Wata mata ce mai kimanin shekaru 55 tana aikin masifa ta ce "ke Rashida wai wannan abin aikine ki ke yi haka a bu kamar ba ki da jini a jiki tun da ki ka ki haihuwa toh wallahi aiki yanzun ki ka fara".

Iya dan Allah ki yi hakuri bana son musu da ke saboda ke mahaifiyata ce amma kin san da rai da mutuwa da haihuwa duk suna ga Allah

Yee-yee kuka Iya ta saka tana cewa Rashida yau ni ki ke zagi lallai yau kin tabbatar min cewa ke ba tagari bace saboda ko uwar ki ba ki bari bale ni uwar miji tana maganar ne tana kuka sosai har da fece majina.

Rashida ta ce "haba Iya yaushe na zageki wallahi ban zage ki ba dan Allah ki yi hakuri ". tana maganar ne tana kuka ita ma.

Wani matashi ne ya shigo ɗauke da sallama a bakin sa "Assalamualaikum" Iya Mai yasamai ki ne ehhe, Rashida Mai yasami Iya ne naga tana kuka"?.

Ai dole za ka tambayi uwarka tun da ni kam banza ce ba ni na haife ka ba kuma ka sa ni wallahi na gaji zama da wannan juyar dole ka zaɓa ko ni ko ita.

Ita dai Rashida kuka kawai take yi saboda da mutum ba shi ba kan shi cikin da sai ta bawa kanta.

Ya ce "Iya dan Allah ki yi hakuri ki bani ɗan lokaci in sha Allahu za ki ga jikan ki amma dan Allah ki yi hakuri yanzun wallahi bazan iyawa Rashida kishiya ba saboda ina son ta sosai".

Toh ni za ka faɗawa cewa kana sonta lallai Mustapha dole za ka yi min yan da ta ke so.

Ita dai Rashida kuka kawai take yi da taga abin yaƙici yaƙican yewa ya sa ta bar wajen da gudu ta na kuka.

Mustapha dai gabaki ɗaya hankalin shi ya tashi saboda ya na son Rashida sosai.

Bin Rashida ya yi ɗaki ya na ba ta hakuri ya ce "Rashida dan Allah ki yi hakuri wallahi Ni ma na gaji da wannan abin da Iya ke yi ma ki kuma nasan bakya jin daɗi amma ha ka za ki yi hakuri dan Allah".

RASHIDA


By
Sha'awanatu faruk diggi✍️
Sha'awa marubuciya✍️

Wtspp 08084277827☎️📱

PART 4

📝
Amma fa cewa ta yi dole cikin mu ka zaɓi ɗaya ko ita ko ni yanzun dan Allah saboda ban sa mu haihuwa da wuri ba ne za ta tsane ni har ha ka, ai ba ni ke ba wa kai na kuma shirun da haihuwa ta yi min ba shi zai sa Allah ya manta da ni ba Kum.... Kuka ya ci ƙarfin ta ya sa ba ta ƙarasa maganar ba.

Nisawa Mustapha ya yi ya ce "ni dai ba zan gaji wajen ba ki hakuri kuma da ki ke maganar cewa wai na zaɓa wallahi bazan sake ki ba saboda ina son ki sosai dan Allah Rashida ki dai na sa ka damuwa a ranki.

Toh shi ke nan ba na son yin musu da kai mijina ka yi hakuri na dai na amma dan Allah idan ta buƙaci ka sake ni dan Allah kar ka yi ya yayya da ita saboda ba na son fushin iyayye akan mijina.

Hahaha toh shi ke nan amma fa ba na fata ki ka san ko na yi ajiya a cikin cikin nan na ki.

Hahaha dariya ta yi sosai sannan ta ce "toh Allah ya sa da gaske ne mijina, mijina ina son ka ina ƙaunar ka."

Matata ina son ki ina kaunar ki ina ma ki son da idan Iya ta matsa rabuwa na ta ke toh wallahi za ta yi biyu babu bu.

Rufe ma sa baki ta yi sannan ta ce " haba mijina mai ya sa ka ke faɗan wannan maganar dan Allah ka dai na in sha Allah a tare zamu yi rayuwa har lokacin da Allah zai bamu yara".

Rungume ta ya yi sosai a jikin shi ya ce "ina son ki matata" ai da ga nan na fito na bar ma su dakin saboda um a bar shi kawai.

A kwana a tashi a sarar mai rai yau Rashida ta shi da matsanancin ciwon ciki abu kaɗan ta ci sai amai, Mustapha ya ga ciwon ya yi yawa ya ɗauke ta zuwa ɗan ƙaramin asibiti likita ya yi yawan da ya ke yi ya ce idan za ta iya tashi ta je ta yo fitsari ya bata ƴar ruba ya ce ciki zata yi fitsarin ta je tayo ta ba shi ya yi awon da ya ke yi ya ce "ta na da aure ne"?.

Mustapha ya ce " eh".

Likitan ya ce "ina mijinta"?.

Mustapha ya ce "likita ga ni ko wa ni abun ne ke damun ta saboda wallahi ta ji jiki sosai dan Allah kar ka ce min ta na da matsala ne likita".

Likitan ya ce "kwantar da hankalin ka abokina ba abin da ke damun matar ka ta na nan lafiya, congratulations abokina matar ka na dauke da cikin wata biyu.

Mustapha ya ce "mai ka ce likita ban ji da kyau ba dan Allah ka sa ke faɗa min wallahi kunne na wani abun ya ji da ban"?.

Hahaha dariya likitan ya yi ya ce "abokina na ce matar ka na ɗauke da juna biyu na wata biyu".

Mustapha sujada ya yi ya na wa Allah godiya, sannan ya ce "likita da mai zan saka maka wallahi da mai kuɗi na ke ta yau zaka sha kyauta ta musamman saboda wannan albishir ɗin da kai min".

Likitan ya ce "akwai abin da za ka bani amatsayin tukuici".

Mustapha ya ce "likita kafaɗa min menene shi har in baifi ƙarfi na ba zan ba ka shi in sha Allah".

Likitan ya ce "abota kawai nake son mu yi idan ka amince saboda wallahi kabirge ni sosai ina son namiji mai irin halayyar ka".

Mustapha ya ce "yau kam tazo min a Sa'a Allah na gode maka da wannan alkairin da ka ke nuna min, na amince in sha Allah ba zanci amanar ka ba sai dai idan kai kaci tawa amanar".

Likitan ya ce "abokina na gode sosai nima saboda wannan abin da kace min yasa na ƙara jinka a rai na, Allah yabawa matar ka lafiya Allah ya sauke ta lafiya abokina".

Tashi ya yi likitan ya ce mu je na raka ka saboda bana son iska ya ta ɓaka, hahaha dariya su ka gabaki ɗaya.

Barin asibitin su ka yi sai gida su na shiga Iya ta tasu su da bala'i sunje sunyi zamansu a can.

Rashida ta je wucewa ɗaki sai Iya ta riƙe ma ta hijab ta ce "ai daga nan gidan ubanki za ki koma dan nagaji da wahalar min yaro da ki ke yi ".

Mustapha ya ce "Iya ba dai haihuwa ce matsalar ba toh shi ke nan tazo ƙarshe in sha Allah, yanzun daga asibiti muke kuma sunce ta na ɗauke da cikin wata biyu".

Ciki fa kace Mustapha Rashidar ce mai ɗauke da cikin ko aure ka yi ban sa ni ba?.

Iya Rashidar dai ce mai ɗauke da cikin yanzun kam ai sai ki nuna ma ta soyayyar da ba ta samu ba tun da.

Allah sarki Rashida ƴar albarka Allah ya maki albarka Allah ya rabaki lafiya dan darajar Annabi Muhammad s a w ameen ya Allah.

Ameen ya Allahu Iya cewar Mustapha.

Iya ta ce "ƴata sannu kin ji mai zan dafa maki yanzun eh dan nasan ki na buƙatar wani abun ta ɓawa"?

Iya ba komai Na gode sosai yanzun ba na jin yunwa bacci daina ke ji.

Toh shi ke nan ƴata ki je ki kwanta ai nasan kina bukatar hutawa.

Iya toh yanzun ya maganar ƙara auren kisama min mata kawai .

Iya ta ce "Mustapha ai yanzun kam ba zancen ƙara auren dama jikokina na ke son ga ni shi ya sa wallahi nace sai ka yi aure amma yanzun kam ba wannan zancen".

Toh shi ke nan bara na shiga ciki sai na fito.

Ɗakin ya shiga ya tarar da Rashida na riƙe da cikin ta tana kuka.

Ya ce "Rashida lafiya daina ga ki na kuka ko wani abun ya faru dan Allah ki faɗa min"?

Cikin kukan ta ce "ba komai mijina kawai ina tunanin maganar Iya ne kenan idan ba wannan cikin ba yau rabamu za ta yi".

Haba Rashida kawai Iya na faɗa ne ba gaskiya bane ki dai na wannan tunanin ba mai rabamu in sha Allah mu na ta re da ke har abada.

"Allah ya nufa".

A kwana a tashi sai yaro ya za ma babba .

Rashida na ga ni da ƙatan cikin ta sai wa ni ni shi take yi da alama na ƙuda ce tazo ma ta ta ce "Iya Iya ki na ina cikina zai zube".

Iya taji ehun ya yi yawa taje ta leƙa sai taga Rashida a yashe a kasa.

Ta ce "Rashida Meya same ki ne ha ka ko naƙudan ce"? tazo aiko ta taimakon Iya ta haihu ɗanta namiji murna wajen Iya ba a magana.

Ruwan wankan mai jego Iya ta haɗawa Rashida taje ta yi wanka sannan ta zauna, Iya ta ce "ƙarfe shi ki bashi madarar shi yasha".

Rashida ta ce "Iya kibari har Mustapha ya zo sai na bashi madarar dan Allah Iya".

Iya ta ce "yau ni naga ta kaina toh idan yazo shine zai bawa jaririn mamarshi ne".

Haka ba dan tasu ba tabawa yaron madarar shi, tana cikin bashi madarar sai ga Mustapha ya ce "Rashida kice kuwa nake gani da jariri a hanu?.

Iya ta ce "eh itace ko da wani abun ne"?.

A a kawai na tambaya ne ya ce "Iya dan Allah ruwa nakeso zan bawa yaron wani abun ne".

Toh shi ke nan bara na ibu ruwan ta na fita ya zauna a kusa da Rashida ya ce "wai yanzun ni ne na zama uba amma kamar a mafarki".

Ruwa Iya ta kawo ya ce ai ya gama abin da zai yi .

SATI ƊAYA
Yau ne ranar suna yaro yaci sunan Muhammad.

Haka dai rayuwa ta ci ga ba da gudana .

Rashida na gani da wani ƙatun cikin ta ta na zaune baƙin murhu ta na hura wuta.

Wani yaro ne ɗan kimanin shekaru 4 ya ce "Inna banga jaka ta ba kuma a makaranta dukan litti a ke yi"?.

Rashida ta ce "toh ni kam ina nasan in da ka yada jakar ka yaron nan kawai ka duba a cikin jakar mahaifin ka".

Dubawa ya yi sai ko ya ganta ya ɗauka sai makaranta.

Ya na fita ita ko Rashida naƙudar ta tashi da kyar ta samu ta shiga ɗaki ta na shiga ta na haihu ɗanta namiji, Iya ta kira ko da Iya ke shaga ɗaki ta tarar da jariri, aiko daɗi har kunne.

Waje taje ta ce akira ma ta Mustapha yana shigowa Iya ta ce bani abin da za ka bani na faɗin haihuwa dan matar ka ta haihu ɗa namiji..

Kamin Iya ta rufe baki har ya shige ɗaki.

BAYAN SATI

Ɗa yaci sunan Ibrahim an sha shagali sosai Mustapha ya faɗawa likita haihuwar matar shi dan ha ka likita yazo suna .

BAYAN SHEKARU 5

Bayan shekara 5 wasu yara ne nagani sun dawo daga school ɗayan ba zai wuce shekara 9 ba, ɗayan ma bazai wuce shekara 5 da rabi ba mai shekaru 9 ne riƙe da mai shekaru 5 su na tafiya hankali ƙwance gwanin birgewa.

Wa ni ƙaramin gida na ga sun shiga wata mata ce tsugunne ta na fama da wuta su ka "Assalamualaikum" Inna sannu da gida su ka cewa matar ɗago kan da zata yi sai naga Rashida na ce toh su Rashida manya .

Ta ce "a a ƴan makaranta har kun dawo"?.

Su ka "ce mata eh Inna".

Rashida ta ce "Ibrahim nawa ya hanya Allah ya sa dai malaman ku ba su dake ka ba"?.

"Eh Inna" ya ce

Rashida ta ce "kai yaron nan ku je ku cire kayan sai ku zo ga abincin ku".

Toh wai ina Iya ne.

Mustapha ya shigo bakin sa ɗauke da sallama "Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" ta amsa ma sa ta ce "sannu da zuwa malam" saboda yanzun karantas suwa ya ke yi.

Yauwa barka da gida kawai ya ce ya yi tafiyar shi.

Bin shi ta yi a ɗakin ta ce "malam lafiya na ganka ha ka dan Allah ka yi hakuri Allah yabamu ita kuma shi ya amshi abarsa".

Ni sawa ya yi ya ce "wallahi Rashida ba ki san yadda mutuwar Iya ta tsaya min a rai ba saboda itace kawai na ke kalla na ji daɗi".

Ayya Allah sarki Iya Allah ya gafarta mata ni daina ce.

BAYAN SHEKARU 7

wa ta ƴar tsohowa na gani kwance da alama ba tada lafiya wata yarinya na a kusa da ita yarinyar ta ce "Inna wai ina su Yaya suka yi ne har yanzun basu dawo ba kuma yunwa nake ji"?.

Wacce aka kira da Inna ta ce "A'ishah ki yi hakuri zasu dawo in sha Allah kuma za su sama ma ku abincin da zaku ci kinji".

"Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" ƴar tsohowar ta faɗa

Babban cikin ƴan samarin ya ce "Inna ya jikin"?.

Sannan ƙaramin ya ce "Inna kin ji sauƙi"?.

Ta ce "eh naji sauƙi sosai sai dai abin da ba a rasa ba".

Inna dan Allah ki fitar da mutuwar nan ta Baba a ranki yau fa shekara 2 amma kullum sai ki yi kuka ga shi ke ba lafiya ba. Cewar babban.

Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba.

A a Inna mun samu abinci ga shi kwano ɗaya ne dai ba yawa.

Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi ma ku albarka Allah yabaku sana'a mai albarka".

Muhammad ya ce "Inna mai zai ha na ki bari naje Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah".

Humm me yasa ka ce kar na hana ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne.

Ƙaramin saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen waharmu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi yatafi ai Inna ina tare da ke".

Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne.
Eh to Inna duk ranar da ki ka ce tayi maki ni Ashirye nake.

Toh shi ke nan sai na gani sai na faɗa maka kuma Kanada kuɗin tafiya ne.

Mustapha ya ce "a a Inna amma ai ba zasu yi wuya ba saboda akwai wata ƴar wahala wai sona take sai nace ma ta tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuɗin mota".

A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi nasan kuɗin zasu yi ma ka .

Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci .

Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a .

Ameen ya rabbin alamina.

BAYAN SHEKARA 2

Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe zamu koma birni dan naji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can zamu koma da zama"?.

A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko bakya son ya yi aure.

Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shine ya ce min wai can zamu koma da zama?.

A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali.

"Assalamualaikum" a a Inna kina nan da ƴar ki ko?.

"Waalaikamussalam" Toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni".

A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuɗin maganar ya yi ne kuma kin san ƙurota zasu yi.

Haka ne kam toh Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login