Showing 51001 words to 54000 words out of 56336 words

Chapter 18 - NANA KHADIJA COMPLETE

13 Jul 2025

17317

A kan kujera ko kallonta baiyi ba domin tsigar jikinshi yaji tana tashi kadan kadan fa'iza ya mikawa hannu wacce ke kwance a kasa tana jiran dukan Dija kamma hannu tayi ta tashi zaune yace ke kam kinji kunya duk wannan girmab jikin naki kibari wannan ta kayar dake harda " hayawa kanki kin tsaya kina kallonta wacce kina nai mata duka daya zata fadi """ dariya falon ya dauka, harda ummin Asabe ma ba,abarta a baya ba ita kam Na'ima kamar tafado daga kan kujera dan dariya harararta Aliyu yayi yace meye ,Abinda dariya Anan dan ubanki shiru tayi tana mai da dariyar ciki ummi tace har damu zaka zaga tunda muma munyi dariya ba,abin dariya Akai ba kuka fa,iza ta fashe dashi domin ita hawa kanta da Dija tayi bai mata ciwo ba illa dariyar da suke mata wanda harda ita Dijan




Yaya Aliyu kaganta tana yimin Dariya ko tafada tana nuna Dija kyaleta zan nuna miki yadda zaki dinga yi mata kema, in ta kuma hawa kanki da kokawa "kice mata yar kauye mai hawasan jakai' kinjiko tunda ita kunne kashi gareta'' shuru Dija tayi bata ce ko mai ba Amma ranta ya 6aci kallonta Aliyu yayi yace "malama ina dankwalinki ban hanaki zama babu dan kwaliba iyi? Dago kai Dija tayi tana kokarin kallon inda ta zaauna hijab din skull din ta hango can kusa da kafar ummi sabida haka bata ce komai ba ta tashi taje ta dauko ta zira ta kama han yar dakinsu




Cikin magana kasa kasa take cewa "ko ina ruwansa da dankwalina oho kawai sabida a dinga ta kura mutane " bata yadda yaji Abinda take cewa sabida tana jin tsoron dukan da zai mata in yaji dakin tashige ta kwa6e unipom din tasamu zaninta ta daura iya kirji tashiga toliet wanka dan ita ma gwanar wanka ce a rana tayi sau uku zuwa hudu wanka tayi tafito daure da zanin taje ta dauko wasu riga da wando na fakistan'' tasa mai kawai ta safa a jikinta bata yi tunanin yin wata kwaliyya ba kayan sunyi masifar yima ta kyau sun fito mata da Ai nihin qirar jikinta '' bom,bom din ta ya fito a cikin wando duk da wando bayi da 'shaf' Amma yafito ya zauna das das sabida rigar me shaf ce ga tsaga da ta ke dashi a gefe da gefenta cikinta kuwa A shafe kamar wacce bata cin Abinci """ kirjinta kuwa sun fito sunyi cir cir kamar goroba Alama ce da bata jima da fara irgar dangi ba tunda wani lokacin ma ba'a gani in dai ba kurawa gurun ido kayi ba Alamun bayyanar fara girmanta sunfi ga mazaunanta dan karamin hijab dinta take nema gaba daya tafito da duk kayan sif' din har na fa,iza ma basu' tsira ba ranta a 6ace tace to ina hijab dina tun ranar da suka zo bata ne meshi ba sai yau dashi tazo garin kuma haka takaraci ne mansa bata ganshi ba ran ta a 6ace ta fita daga dakin




Still dai kanta babu dan kwali domin ta manta ma dama hijab din take so tasa, kan fa'iza ta tsaya tace ke fa'iza baki ga hijab dina ba ? Da kallo suka bita har Aliyu shima yana falon har yanzu suna hira da ummi kallonta fa,iza tayi tace' ni zaki tambaya banganshiba to ba dole na tambaye ki ba kije ki duba min cikin kayanki ko yana ciki' bazan jeba fa,iza n tafada tana tashi daga gurin da nufin zuwa ta cire unipom dinta ''' ya Na'ima kiyi mata magana ta dauko min hijab dina Dijan tafada' idonta a kanta kamar zata yi kuka ummi ce tace "ban da Abunki Dija" hijab din daya ne da ke kije kisa wani mana mybe, shi wanda kike ne ma yana gurin wanki ko kallonta Dija tayi tace shi daya ne dani ' ummi Ai '' ok yi hakuri ke Na'ima dauko mata A ran naki tasa kafin gobe sai ku shiga kasuwa" ayimata siyyaya A binda bata da shi kin ji ko '' to Na'ima tafada ta mike tana kallon Dija tace "ko meye Abin kuka Anan oho kwai sabida bakiga hijab sai kidinga 6are wa mutane baki" sabida shagwa6a tafada tana dariya'' "ke kam kin cika zubar da girma ummi tafada tace' yanzu kuma in tarama kice zaki dake ta sai kace wadda kuka samu jaka' tana tafiya tace "ke dai ummi bakya son laifin Dija' tace "e ba naso din" ummi n tafada





Shi kam Aliyu tunda yayi wa dija kallo daya yayi saurin dauke kansa fuska ya dinga ya mutsewa bai ce komai ba cikin ransa kuwa yana mamakin yarinyar gaskiya duk Namiji' da ya san mace yasan menene mace to ya kalli "Dija yasan tana cikin jerin mata masu Amsa sunansu babban Abin bada mamaki ma yarinyar bata gama cika mace ba Amma ko mai ya fito masha Allah"" sabida haka hannusa ya zira cikin Aljihun jins din daya ke jikinshi yana laluben glass dinshi fuska babu walwala ya dauko ya zira sannan ya dago kai yana kare mata kallo tunda ga kafafunta har zuwa tsakiyar kanta lokaci guda sai ya dinga jin wani matsanancin kishinta yana damunsa fuska A mutukar murtuke yace " wuce daga kan mutane yarinya mara tarbiya kawai kinzo kinyi wa mutane kerere Aka wallahi wataran sai na raunata ki na ji miki ciwo shasha " vileger" kawai " sai zuba ruwan bala,i yake wanda shi kanshi bai san dalili ba' Amma baya rasa nasaba da jin wani irin bala'in kishinta yana kamashi


Cikin kujera taje ta zauna tana zumbura baki bata ce ko mai ummi kam cewa tai "kai kam kana da ta kurawa me tayima ne ' shiru yayi bace komai domin sai yaji zaman a gurin ya gundureshi wayarsa ya dauko yana daddadannawa bai kuma kallon in da take ba




Ummi tace "da yamma Na'ima sai ta kaiki salon ko Dija ? A wan ke miki gashin nan naki ko baya damunki ne"? Sakin fuska Dija tayi tace 'yana damu mana ummi' Ammafa bana son kitso Abar min haka" ummi tace "da har ina cewa Ayi miki kitso zaifi miki kuma zaki ji dadi kan" "A,a ummi ni dai " Dija' tafada kallonta Aliyu' yayi yace "to wallahi kitso za,ana yimiki bazaki dinga yi mana yawo da gashi a gida ba kina hana mala'iku rahama su shigo mana gida in ba haka ba sai dai ki wayi gari kiga nayi miki kwal kwabo sosai zan Aske miki kan tunda bakyajin magana'' ya hakikance sai faman bala'i yake zuba masa ido ummi tayi tace " wai kai ina ruwanka da yarinyar nan ne iyi? Kabi kadamu da lamarinta' don Allah karabu da ita ta sake mana''





Saurin gyara fuska yayi yana kallon ummi' yace "rayuwar da tayi abaya baza tayi ta ba yanzu lokacin da tana gaban Nene sai Abinda ta gada ma take' Anan kuwa wallahi ummi bazatayi ba" sabuwar tar biya za ayi mata can daban nan daban" duk yanayin wanan fadan ne sabida yaji ummi tayi maganar zuwa gurin saloon so yake ya soke fitar kallon ummi yayi yace Akwai wata mata data ke zuwa tana yiwa Nafisan faruk kitso ita Na'ima n tasan yarinyar kice tayima 'Nafisa waya ta turo yarinyar sai ta dinga zuwa tana yi mu su kitson gaba daya Amma daga yau na soke zuwa gurin saloon kitso ko wankin kai





Hararsa ummun tayi tace "to sannu ubansu ka hakikance sai faman fada kake kamar wani wanda Akai wani Abun " zo nan " Dija ummi tafada tana dauke idonta daga kan" Aliyu' zuwa Dijan tayi gun ummi n ta zauna A kasa kusa da kafafunta kama kan ummi tayi tace "wannan gashin naki dole sai An wanke shi sosai kafin Ayi kitson " kiyi hakuri ana minki kitso kin ji ko " to Ummi Dija n tafada"
Tsaki Aliyu ya dan ja kasa kasa shi kadai yasan Abinda yake da munshi'' mikewa yayi yana kallon ummi yace "zanje in kwanta zuwa biyar na yamma" kallonsa ummi n tayi tace '' to Abinci fa? "Ok kibarshi kawai ummina inna tashi naci yanzu ban jinyunwa'' "shikkenan Ai " ummi n tafada tana cigaba da warwarewa Dija tufkar da take kanta gashinnata kallo daya yayi musu ya sa kai ya fice daga falon






To Siyama kam lokacin da taje gida momy n ta tana zaune A falo ita da babbar Kawarta hajiya ladidi suna ta hira cikin farin ciki hajiya ladidi tana bata labari sabon malamin da tayi A can da garin nasu cikin zumudi momy tace haba dai yaushe zaki rakani " kin tabbatar ya iya Aiki in ce ko? rike baki hjy ladidi tayi tace "Ai shi wannan akin shi kamar yankan wuka ne karki damu sabida haka duk sanda kika shirya sai kizo in rakaki " Amma Asubanci zamuyi " domin Akwai layi A gurin " jiki na rawa momy tace "ni kam ko yanzu ma A shirye nake wallahi "kallonta hjy ladidi tayi tace " me kike ci na baka na zuba mubarwa gobe mana sai mutaki sa'a" "to Allah ya kaimu momy tace" tana Allah Allah gobe tayi suje' domin ita kam duk inda taji sabon malami ko boka "yan tsubbu da sauransu jikinta har 6ari yake" shiyasa dadyn Siyama gashin Asusuce kamar wani shashassha kullum ka ganshi tsabar ta wanke ta bashi ya shanye


To suna tsaka da wannan hirar ne Siyama tayi sallama kai tsaye cikin kujera taje ta zauna tana ya mutse fuska Wallahi na gaji momy tafada ko sallama batayi ba washe baki momy n nata tayi tace "dama yau zaki dawo doughter ko waya Ai kyayi min ko insa delu mai Aiki tai miki girki na mussaman tafada tana faman washe baki ya tsine fuska tayi tace yanzu Aikin me take ki kirata mana tayi min Ai kam yanzu kuwa kuwa momy tafada tana kwalawa delu kira hjy ladidi ce ta kalli Siyama cikin washe baki tace babu " magana ne yar gidana '' kallonta Siyaman tayi tace "o momyn Samha yakike"? "Lafiya lao nake " tafada tana wangame katon bakinta ko kunya bataji ba *nikam nace kunyi Asara wallahi kudinga yiwa "yayan cikinku biyyaya* "baki tambayi mutuniyar taki bah " in ji hyj ladidi " Ayya yaushe ne mukai waya da,ita ne ki gaishe ta bani da numbar ta yanzu Ai " jiki narawa hjy ladidi ta zaro wayarta daga cikin jaka tace "kawo in sa maki numbar tata " Ai tana can tana korafin kin daina mu,amala da ita ko Ayawa ne" "laa habadai numbar ta ce in nakira bata shiga" "e Ai tacanja ne mi kamata wayar tayi tasa mata numbar sannan ta tashi ta nufi dakinta'' momy , kam sauke numfashi tayi tace "Ai koda zan rasa zanin daurawa Sai Siyama ta Auri yaron nan dubi yadda yarinya ta kyakyawa tabi ta susuce sabida son data kewa yaronan"




"Wane yaro ne wai ta kwallafa rai A kanshi iyi" hjy ladidi take tambayar momy "hummm!! dan gidan Alh bashir craman mana danshi na fari Aliyu gashinan yana Aikin soja' ko kwanaki rigimar da taki ci taki cinyewa A can jahar taraba da taimokosa Aka kawo karshenta bakya kallon tv ne Ai har hira,Anyi dashi da sauron ,sojojin da " yan ta adda da ya kama jiya, dady' Siyama yake cemin har karin girma Akayi masa'' sai zuba momy take' ita kuwa hjy ladidi bata sauraronta tun lokacin da ta fahimci' wa take nufi ''' ta tsunduma cikin tunani tana girgiza kai cikin zuciyarta tace ta6 dijam lallai za ,ayita yaron da "yarta take mutuwar so take nufi" Ai kam itama yadda taci Al,washin ,"yarta Samha sai ta Aureshi itama sai ta cikama ta burinta kamar yadda ta daukar mata Alkawari

Yaqe kawai hjy ladidi take wanda hausawa sukance yafi kuka ciwo tace "ina bayanki hajiyata gobe karkisa wasa zan fito da wuri sai mu dau hanya Allah ysa muje mutaki sa'a Amin " momy tace cikin farin ciki ta samu wani malamin tana da tabbacin ya'iya Aiki tunda taji hjy ladidi tana wasashi




Gab da magarb Aliyu yata shi daga wani nannauyan bacci da ya dauke shi tun bayan da ya sha maganinshi na fama ya kwanta A gajiye yana ta faman sake sake cikin ransa har bacci ya sidado yayi A wun gaba dashi jiki a mace ya tashi yafiti minti goma A zaune kafin ya mike cikin mutuwar jiki' A gurguje " yashiga toliet ya hada ruwa mai dan zafi ,ya watsawa jikinshi sannan yayi brush ya daura ,Alola yafito daure da guntun tawol jalabiyya me yan kakken hannu ya zura sa gaje wando" sannan ya feshe jikinshi da turaranshi wanda ya riga yaga kama jikinshi sabida yawan Amfani da yake dashi komai na dakin kamshin turaran yake mussaman tufafinshi "carbin shine A maqale A dan ya tsanshi sannan ya zira wani silifas na zallar fata' mai uban taushi kafafun nan kuwa sunyi kyau Acikin ta kalmin' kamar ka matsa jini ya 6illo tas dasu




Kai tsaye ma sallaci yanufa jin An fara kiraye kirayen sallah bakin shi dauke da tasbihi ga *Allah jallah wa Azza* baba mai gadi ne ya tashi yana kokarin bude masa A karamar kofa Aliyu ya da katar dashi yace haba baba Kofar ma sai ka bude min Alola fa kake to ko ba Alolo kake ba kawuce ina tsaye ka bude min kofa ni Aiki me nake iyi " bude get da kake wannan Akan Aikin ka kake, hannu baba me gadi ya ya daga yana dan rankwafawa yace "godiya nake, uban gidana "Ai girmanka ne yafada yana dariya shima Aliyu, dariyar yayi kadan yace "ka gode wa Allah domin shine Abin godiya'' yafada yana kokarin bude kofar ...........................................


Yana fita motar Abbah tana sawo kai layin "haruna drever" yana jansa dan tsayawa yayi sai da ta karaso sannan ya dan rankwafa yana wa "Abbah barka da zuwa "" sannan haruna, yaja motar bayan ya gaida oga Aliyu" dan haka suke kiranshi





Sai da ya jirayi isha'i sannan yafito daga masjid" din yana fitowa suka hadu da Abbah sabida haka tare suka jera zuwa gida suna hira kamar wasu Abokai




Tare suka shiga falon wanda kowa ya hallara Aciki har jameel yana nan bayan ya gama yawon boll dinshi Dija tana zaune kusa dashi wayarsa na hannuta tana ta faman gem da ita saurin dauke idonshi yayi daga kansu yana jin wani matsanincin bacin rai kan kace kwabo ya hade fuska tamau ! tamkar wanda bai ta6a dariya ba tunda Allah ya halliceshi can dannig ya nufa jameel kam cikin sakin fuska yace "broth barka da yamma" yana tafiya yake Amsawa " "yawwa barka kadai ya yau kashigo da wuri ko babu , kwallo ne"? Yafada yana kokarin danne Abinda yake taso masa yanzu nan A game da jameel din' wanda shi kanshi bai san me nene ba"" cikin dariya jameel din yace, "yau kam babu Amma gobe muna da me,zafi " "to Allah yabada sa'a" Aliyu yafada ya na kokarin zama cikin kujerar cin abincin """



Dukkansu suka hada baki gurin yiwa Abbah barka da shigowa duk da lokacin da yashigo sunyi masa to A gurguje ya Amsa,Sabida yana saurin wucewa massalaci kada jam'i ya shigeshi can kan kujera ya zauna yan fito da wayarsa ya mikawa ' Na,ima wayar yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login