Showing 6001 words to 9000 words out of 56336 words
tace "nifa nene badake nake ba"
"To dawa kike iyi ? shiru tai nene tace Alin sa'anki ne wai wai."?
"Ba gaskiya ya fada miki ba na hana ki yiwa nagaba dake rashin kunya kinki ji to babu ruwa na ai gaki nan gashi"tafada tana kukarin kunna redio nta.
Ali kam bai ce komai ba cigaba da cin abincinsa yai amma sarai yaji irin maganganun da dija take fada ,,shi abin ma yanzu mamaki yake bashi gannin yarinyar kamar wacce ake kara zugawa tai mai rashin kunya,,
Gashi shi bashi ga sabgarta yake ba ballantana ace kawai dai halinta ne da kuma rainon da nene tayi mata wanda hausawa suke cewa rokon kaka
Tsaki ya ja aransa hade da girgiza kai yace tabbas sai ya tsawatar wa da yarinyar nan kafin ta dai daita hankalinta
Dija kam bayan ta wanko bakin zama tai tafara cin abincin tace "nene baki samin man shanu ba" kallonta nene tayi tace gashinan ai kusa dake ki tsiyaya mana"
Man shanun ta ta zuba cikin niyar ta cigaba da cin abincin ta kar bata yi laifi ba da sawa kamar batai wani laifi ba
Shiru gurin yai in banda sautin ridio nene dake tashi babu wanda ya kuma cewa kala a gun
Yana gamawa ya mike daga gun yaje ya daureye sannuwansa domin cin towa dai dole sai da hannu bai ce komai ba ya fuce daga gidan ransa a mutukar bace yana tunanin irin hukunci da zaiyiwa wan yarinyar .
Nene ce tace. "Ina zaka naga kana kokarin fita Cigaba da tafiya yai yace "zan dan fita ne insha iska" domin dai ita kanta nene haushi take bashi ganin duk da sa hannuta yarinyar tazama abinda tazama
Ficewarsa yai ko kallonta taba baiyi ba yayin da take cewa kai da ba kowa ka sani ba a garin."
Shikam Ali a zahiri zama ne bayasan yayi inda dija na gurin dan ji yake zai,iya karyata ya zubar a yanda zuciyarsa take mai zafi Sabuda ya tsani raini rainin ma daga yarinya karama shi abin ma mamaki yake bashi ,,ganin yadda su Na'ima da jamil suke bala,in jin tsoransa ko acikin abokai ne shi nada ban ne sam ba,a kawo masa raini amma abin mamaki wanan kazamar yarinyar bata shakkar ta zage shi a gaban kowa.
Lallai kam bazai dauki wanann ba wallahi sai yayi mugun saba mata in dai shi ne a haka take so taje cikin jama,a tayi musu rashin arziki tana zubar musu da kima wannan bazai yiwu ba dole sai ya saita mata tunani
Haka ya gama zancan zucinsa da irin tanade tanaden a zabar da zai ganawa dija mudun tace zataje abuja da wannan haleyen nata
To nene kam daki tashige bayan Ali ya fita
Kokarin sauko da akwati take daka kan siff so take ta zuba musu "yan kayan da zasuyi amfani dashi ,,tunda yace gobe da wuri zasu kama hanya ,,
Ace warta bazata dibi wasu kaya dayawa ba tunda bawani dadewa zasuyi ba itakam tabazata wuce sati biyu zata dawu
Dija ta kwalawa kira dake tsakar gida gama cin abincinta kenan amsawa tayi tace "Nene menene?
Nene tace "zo ki tayani zuba kayannan acikin jakar nan gobe in sha,Allahu da wuri zamu tafi amma ki nikkesu akafin kisa domin sufi zama
Dija tace to fara zuba kayan tayi tace nene kala nawa kika ibar min nawa kayan, kuma yaushe zamu dawo?
Ai bawani dadewa zamuyi ba baza mu huce sati biyu ba" turbune fuska dija tayi tace "gaskiya nene in munje kar mu dawo da wuri mu bari sai andan kwana biyu kinji ta fada cikin shagwaba nene tace ",inbanda abinki dija makarantar wa zaije miki ita"
Dija tai sauri tace basai aje a fada ba,,
Shiru Nene tayi taci gaba da ninke kayansu tana zubawa cikin Akwati
D'ija ta marai rai ce tace"kin ji Nene. Dan Allah aje a fada"
Nene tace"waye zai je ya fada bayan lokaci ya kure"
Marairai ce fuska D'ija tayi tace "ba sai Haruna Na gidan baba malam yaje yafada ba"
Nene tace"to Allah ya kaimu
Ai ba wani dadewa zamuyi ba sati biyu zamuyi mudawo"
D'ija ta bata Fuska,tace"gaskiya kar mu dawo da wuri Nene Naji an ce garin yana da dadi"
Nene tace"sai kiyi kuma ni bazan je wata Abuja in share guri in zauna ba bayan ga dakina Na bari"
.zumbura baki D'ija tayi tana gyara kwanciya,sabida tasan halin Nene duk Abinda tafada ya sauna.
Ali ko yana shiga dakinshi Wanka yayi ,
Yayi shirin bacci ,sai ya zauna gefan katifarshi ya kunna loptp din shi yana duba sakkonin.
Duk yawanci sakkonin daga Abokan Aikinshi ne,mussaman ogansu,sai sakon Aminin shi Faruk yana kara jaddada masa dole gobe ya dawo domin Akwai wasu takkadu da zasu cike.
Sai sakon mutuniyarshi Siyama
Yafara dubawa Fuskarshi a sake lokacin da ya duba wani sakon ta inda take fadin ,ya taimaka ya karbi soyyayar ta zuciyarta ta makance a kansa,Zara iya hakura da Aure har abada mutukar bai Aure ta.
Yarinyar ta bashi tausayi ,sabida yadda ta damu dashi da rayuwarshi shi kuma kwata kwata bata gabanshi domin bata da tsarin da yake son Matar da zai Aura,yana son Mace doguwa mai Addini wacce tasan meye rayuwa ,bayan haka yana son Mace mai sharp da tsarin jiki mai kyau. Gami da gashi bayan haka shi duk wani kyalekyalen matan Zamani baya rudashi ,a cewarsa duk qazamai ne a waje zaka gansu tsaf tsaf Amma daga anyi Aure ,sai qazanta ,da rashin iya kula da miji
Shiyasa matan da suke burgeshi ,
Mai hafin Siyama Abokin Abbah ne tare suke harkar kasuwancinsu sun shaqo sosai har ta kai suna son su hada zuri'arsu Aure ,wato Siyama da Ali
Siyama sa'ar Na'ima ce kanwar Ali shiyasa tasu tazo daya,siyama Na yawan zuwa Hutu gidansu ,Amma sabida Ali take zuwa ,Wanda bai San tanayi ba
Ashe ta cewa babanta soyyaya suke da Ali har sunyi Alkwarin Aure ,da ta kammala karatu zasuyi Aure ,Dady nta cikin farin ciki yasamu Abbah ya sanar dashi,sukaita farin ciki har dai suka saka lokacin daurin Aure duk ba tare da sanin Ali
WANAN KENAN
WACECE D'IJA?
Lawan Dai Kani ga Alh Bashir Mahaifin Aliyu Shine Mahaifin ta, Yayi Aure in da Ya Auri Wata yarinya mai suna Khadija nan bayan gidansu, babu yadda Alh Bashir bai yi ba a kan Lawan ya je Abuja,Zai Samar masa Abin yi,yace yafi son zama kusa da Nene,Dan ko da yayi Auran ma Ciklin gidan suka tare da matarshi Khadija,mai kirki kamar mijinta,Nene tana jin dadin Zama da ita Sosai Shiyasa duk wani Abu da tasamu Na ta ne
Cikin ikon Allah ,Allah ya azirta ta da ciki ,Nene ta riqa Murna,ta dauki son duniya ta dorawa cikin,
Cikin Khadija Na da wata takwas tafara wani irin ciwon Kai! Mai zafi,sukaje Asibiti likita ya Dora ta a kan Magani,
Yace ta rage Aikace Aikace yin hakan yana iya barazana da lafiyarta da ta jaririn.
To haka Nene ta hanata duk wasu Ai kace Ai kace Na gida ,ita take yi,
ranar wata laraba Khadija ta tashi da wani irin ciwon mara maitsanani lawan ya fita ,cikin daren yaje ya kira Nene,
Kallao daya tayi mata ta fahimci haihuwa ce,ta karasa cikin dakin sosai ta rirriqe ta ,tana mata sannu.
Ta kalli lawan tace"maza yaje gidan baba malam ya karbo rubutun nakuda(haihuwa)
Lawan ya fita da sauri yana addu'a Allah ya sauki Khadija lafiya,tabbas duk wanda bai bi iyayensa ba ya shiga uku,ganin yadda matarshi take shan wahala.
Ko minti goma bai yi ba ya dawo gidan hannunshi ruqe da rubutu a daure a farar leda yayi sallama ,gami da mika wa Nene rubutu,sannan ya ja ya tsaya bakinshi dauke da addu'o i na fatan Allah yasa ta haihu lafiya
Cikin ikon Allah Khadija na shanye rubutun ta haihu ,Nene tai yiwa Alkah godiya ,sannan ta dauke jaririyar ta nan nade a zani,sai ta dawo kan Khadija,tana yi mata dabaru domin a samu nahaifar ta fado,
Khadija sai nishi take na wahala tsawon awa daya da haihuwar ta mahaifa taqi fadowa,
Nene hankalin ta ya tashi ,ta kira Lawan ,wanda yake waje a tsaye,
Ya daga labule,kafin tace wani abu,yace"ta haihu ne"?
Nene tace "e ta haihu"
Cikin farin ciki yace"Nene mai a kasamu"?
Cikin tausayi Nene ta kalli Khadija dake durqushe tana nishi! ga jini ya tsinke yana zuba mahaifa bata fado ba.
Tace"macace maza kaje ka samo mana mota mutafi asibiti mahaifa taqi fadowa"
Nene ta fadi maganar
Cikin qarfin hali,domin ta gama sarewa da lamarin ganin yadda khadijan take ta salati tana rirriqeta
Lawan hankalinshi ya tashi,ganin yadda hankalin mahaifiyarshi ya tashi ya fita da sauri,
Nene tayi iya kokarin ta amma abinda Allah ya hukunta babu makawa sai ya faru, ana kiran sallar farko Khadija ta amsa kiran Ubangiji rai yayi halinshi.
*innaliliahi wa'ina ilaihi rajinun*
Shine abinda Nene tariqa maimatawa ta gyara gawar gami da lullube ta da zani, ta fito daga dakin tana wa Allah tasbihi gami da nemawa Khadija rahamarsa.
Tun a hanya jikinshi yayi sanyi zuciyarshi tana tayi masa saq-saq hakadai suka karaso kofar gidan dashi da mai motar.
Zai shiga gidan keken yaga Yayar Khadija da wasu daga cikin danginsu sun tawo suna kuka, daya daga cikinsu tace"Lawan ya mukaji da hakuri ,Allah ya jikan khadija
Bai ce mata komai ba ya sakai ya shiga gidan gabanshi yana faduwa
Ko da ya shiga gidan Nene na tsaye tsakar gidan ita da wasu mata duk sunyi jigum jigum yace" Nene ga mai motar nan"
Nene tace"ai ta samu sauki ma ,Allah ya amshi abinsa Lawan kayi hakuri kaji ko Allah ya jikan Khadija"
Lawan ya rika salati jikinshi sai karkarwa yakeyi ya bude dakin da Matartashi take kwance,ya ganta a lullube da zani,sai ya tsuguna kusa da ita ya bude fuskar yana kallo tamkar mai bacci haka ya gani innallilahi wa'ina ilayi raji'un kawai yake fada a zuciyara yace"yanzu Khadija kin tafi kin barni,Allahu akabar,zama yayi ya rika yi mata adduoi har a kayi kiran sallah,asubah ya fito ya daura alwala ta nufi masallaci,
Duniya kenan ,haka a kaiwa Khadija suttura a ka kaita gidanta na gaskiya, sai bayan sarakar bakwai ne sannan Alh Bashir yafara shirin tafiya shida iyalinshi a lokacin Ali na Engila karatu,sai waya a kayi masa,gaskiya yaji mutuwar auntyshi sabida yadda jininsu ya hadu da ita in yaje gurin Nene tayi ta hidima dashi ,yana son mace mai hankali da fahinta da tsafta shiyasa suke shiri da ita sosai,nan dai yayi mata adduoi na Neman rahamar Allah
Alh Bashir yayi yayi da Nene tabashi baby su tafi tare da ita ,Ummi ta hadasu tare da yarinyar ta da take goyo a lokacin Fa'iza ta shayar dasu Nene tace Sam a kyale mata ita zata iya kula da ita,babu yadda ya iya haka sukaje asibiti a ka Dora baby kan madarar da ta dace da ita ,sai da ya tabbatar ya ajiye musu komai na bukata sannan suka wuce abuja tare da iyalinshi,
Nene ta dau son duniya ta dorashi kan D'ija bata so ko kuda ya sauka a kanta sabida yadda take rattalinta,lokacin da ta isa shiga makaranta Alh Bashir yazo ya yiwa Nene maganar ya kamata tafara zuwa makaranta ko Ka wai ta bashi yarinyar ya tafi da ita ya hadata da sa'arta Fa'iza ya sakasu a tare,Nene tace Sam bata yadda ba ,ita ya kyale ta,alokacin shi kanshi Lawan yaso Nene ta hakura ta bada D'ijan a tafi da ita abujan amma ganin yadda ta rika fada yasa ,yayi shiru da bakinshi domin dama in Nene tana rigimarta akan "yar tasa yasa yaja bakinshi yayi shiru kawai ya zuba musu ido
Haka Alh Bashir ya kammalawa D'ija komai na makaranta sannan ya wuce ya tafi bayan ya tab star da ya ajiye musu komai Wanda zasu bukata
D'ija ta taso da rigima gami da kwarafniya yarinya mai wayo sosai gata Sam bata barin takwana shiyasa ko a makaranta yara sa'ointa suke shakkarta ,tana da bala'in son girma kamar gyambo shiyasa Sam basa shiri da kawarta Indo sabida itama indo bata son rai ni ko kadan,kullum sai ankawo kararta Nene tayi ta fada tana cewa sun takurawa marainiya kwata kwata D'ija taqi karatu ko taje makarantar ma babu abinda takeyi sai naiman fada ,malamai duk sun San halinta,Lawan in yana mata fada Nene sai tasa kuka tace"yana nuna mata iko dan yaga "yarsa ce"haka yake hakura kawai amma abinda "yartasa takeyi yana bata masa rai
Allah sarki rayuwa,D'ija na da shekara shida a duniya Allah ya karbi ran Lawan sakamakon ciwon ciki farat daya,mutuwar ta girgiza zukatan al'umma mussaman dan uwansa Alh Bashir Nene tayi kuka sosai da sosai ta fawwala wa Allah ikonshi bayan sadakar bakwai nanma Alh Bashir ya rika tausar Nene kan ta bishi abuja ganin yanzu tazama ita daya kadaici zai dameta,Tace Sam bata amunce ba ita dai ya barta a dakinta ai a kwai "yan uwa da abokan arziqi,haka alh Bashir ya tafi badan yaso ba sai Dan gudun bacin ran mahaifiyar tasa
Haka rayuwa tai ta tafiya D'ija Sam taqi karatu yau in taje makaranta gobe baza taje ba ,wannan ne dalilin da yasa makarantar boka suka sallame ta gaba daya Nene tace ta nemi guri ta zauna ai ba dole bane a karatun bokon ,sai na addini,ko isilamiyar ma a makare take zuwa ,shiyasa Sam bata gane karatu sosai.
To a cikin wannan lokacin Ali ya sauka garin bayan ya kammala karatunsa na aikin Soja a kasar Engila
Misalin karfe shida da wani abun ya fito yana sanye da jallabiya ruwan toka tsakar gidan ya rika bi da kallo ganin ko ina a share babu datti ,tsaf iska sai kadawa takeyi gwanin sha'awa ,girgiza kai yayi ,kawai sabida dama tuntuni yasan Nene macace mai bala'in tsafta,kai tsaye kchin ya nufa ,domin bazai iya Wanka da ruwan sanyi ba kasancewar an kwana ana ruwan sama ,duk da yake mutum ne shi Wanda baya kaunar zafi ko kadan hakan bazai sa yasawa jikinshi ruwan sanyi da safiyar nan ba ,Nene na zaune kan kujera "yar tsuguno a kchin din tana joye ruwan zafi cikin fulas ,ya shiga kchin din
Ta dago kai tana kallonshi , yana tsaye jikin kofa sai faman ya mutse fuska yakeyi kamar yadda ya saba
Tace"ka tashi ashe ,ka ganni nan nima sauri nakeyi in kammala hada kayan karin kummalo ,sai muyi wanka domin bana son muyi tafiyar rana"
Gyaran murya yayi kadan ,yace"Nene kin tashi Lafiya"?
Ya share maganar da take masa
"Lafiya kalau na tashi ni kam"
Nene tafada tana juye sauran man kulin da tayi suya da shi cikin wani kwano
Ya mutse fuska yayi yace"kina da ruwan zafi ko"?
"Me zakayi dashi"?
Nene ta tambayeshi kai tsaye
Sabida tasan ba ya wanka da ruwan zafi
"Wanka zanyi dashi naji garin a kwai sanyi"
Cikin mamaki Nene tace"Yau kuma kai ne zaka yi wanka da ruwan zafi,?ashe dai karya ce kawai mutum yace ,shi baya jin sanyi da ko wane lokaci
Babu abinda yace mata ,ya sunkuya yana kokarin daukar fulas din da ta juye ruwan zafin a ciki sabida yaga lokacin da take juyewa
Nene tace"ai ka tsaya na miko maka ko"
Shi dai bai ce mata komai ba ya dauki fulas din zai fita,tace "Muskili kafi mahaukaci ban haushi
Dai-dai bakin kofa suka kusa yin karo da D'ija ta shigo kchin din ,yayi saurin ja da baya yana ai ka mata da banzan kallo fuskarshi a murtuke
D'ija ma tsorata tayi ganinshi ne tsaye a gabanta ,sai jikinta yafara rawa,
Saurin dauke kansa yayi daga kanta ganin kayan da suke jikinta ,riga ce iya gwiwa gashi ta kama mata jiki ,gashin kanta duk a barbaje fatarta luwai luwai , gabanshi ya rika faduwa ,sabida Allah da ya halliceshi yana bala'in son mace mai gashi mai sharp sosai fatar ta tazama kalar coffee ya lura wannan yarinyar duk ta tara abubuwan da yake muradi ga "ya mace duk da take yarinya bata gama cika mace ba amma duk ga alamu nan sun nuna
Ficewa yayi yana jan tsaki ko da wasa bai kara kallon ta ba
D'ija ta sauke ajiyar zuciya tana tabi bayanshi da harara ta zumbura baki , kawai ta wuce ciki gurin Nene
Nene tace "kin tashi ko dube ki don Allah,kai yayi duguzun babu gyara gaki Allah ya baki gashi,amma Sam sai kice baza'a miki kitso ba"
Da zaki daure sai kije gidan Delu tayi miki ko manya ne kafin mu tafi"
D'ija ta karasa kusa da Nene tace"Nifa Nene bana son kitso wallahi kawai ki taje min kamar yadda kike min"
Tabe baki Nene tayi tace"ai shikkenan kanki ne ,ke zai dama, ai
Zumbura baki tayi gami da cewa "Ni dai ki kyale min kai na haka"
Nene tace",to mai kika ji nace dake ne "yannan"?
"Allah ya shiryeki
Tashi tayi daga kan kujerar da take zaune ganin sabon ruwan data daura yana nai man tafasa bandaki tashiga tare da dauko baban bahon dasuke wanka tajuye wa Dija ruwan tace " kimaza kije kiyi kifito kin tsaya surutu da fadi ba,atambayeka ba kinsan in yariga fito zai zo ne ya azzalamana ko"
Fita tayi daga kchin din ta nufi ban daki tana zumbure zumbure na shagwaba
Ita ko Nene kayan Karin nasu ta hau dauka tana shiga dashi daki tana kimtsa gurin da zasu zauna
Ali ne ya fito tsaf dashi cikin wata shadda wacce tai bala,in yi masa kyau ga sumarsa da tayi luf ta kwanta a kansa sai sheki take da ,alama ana kula da ita
Idanunsa sanye da glass yayin da hannunsa yake daure da a gogo as'usuel fuskarsa kamar ko da yaushe ya shigo dakin yana bin ko i na da kallo
Fuska Nene ta hau gyarawa tace " AF ashe kagama kintsawa kaga muma mungama ai ga kayan kari ai yauma mutumin naka nai ma" tafada tana gyara zama itanan lallabashi take karya botsare al halin basugama kintsawaba, bayan hakama tana so tashiga makotan nasu ta yi musu sallama ganin cewar ansaba babu dadi kayi tafiya irin wannan baka sanar da abokan zamanka ba
Ya mutsa fuska yayi yana duba a gogo yace "duba time fa Nene yanzu karfe Tara har da "yan mintoci ummm"! yafada yana kallonta tare da fadin sai yaushe kike so mu kama hanya ne"?
Cikin sauri Nene tace "yanzu nan ai babu abinda zanyi kuma in ba wanka ba Dija nake jira ta gama nashiga naje nai"
Bai CE komai ba ya shige dakin kan kujera ya zauna yana Dada gyara link din hannun rigarsa
Nene kam kunun ta hau zubamasa da zafinsa gashi sai kamshi yake yaji kayan kamshi sannan ta