Showing 18001 words to 21000 words out of 56336 words

Chapter 7 - NANA KHADIJA COMPLETE

13 Jul 2025

17319

black book tun da dan adawa ne kai ma"



Kallon dija tayi wacce take zaune kamar ta shige jikin jameel din


Tace "ummi kunyi ba kuwane "?


"Dija ce fa ta nene baki gane taba?


"La,a wallahi bangane ta ba kinsan bantaba ganinta a fili ba sai hotonta na sani

Haba shiyasa na ga kamar tana yanayi d ya Ali"



Kallonta dija tayi aranta tace amman wannan kin cucuni ni ce ma nake kama da wacan mutumin tab dijam Allah ya isa wallahi

Fada ranta tanayi tana murmuda baki


Fa,iza dake zaune itama hankalinta nakan tv wani series ake yi a mbc tana bala,in son kallo itakam shiyasa suke yawan fada da ya Ali


Kallon gefen da siyaman take tace "aunt Siyama ina wuni "

Cikin washe baki siyama nta amsa "lafiya lau Fa',iza ya karatu"?

"Alhmdulilh "Fa'iza tafada ta juya ta ciga ba da kallonta domin dai ita gaisuwa ce kawai take hadata da siyaman



Abbah ne tare da Aliyu suka shigo

Cikin sallama kai tsaye Ali teble yanufa bayan ya gama karewa musu kallo fuska a dage

Shikam abbah Kai tsaye gurin Nene ya nufa ya zauna kujerar dake kusa da ita


Kusa dashi Fa'iza tadawo ta zauna kamar zata shige jikinshi shima abban jawo ta jikinshi yayi

Idon shi yana kan Nene yace ' naga kamar akwai magana a bakin ki " yafada bayan ya kuma gai da ita

Kallonsa tayi tace "kwarai kuwa kafin ta rufe bakinta Siyama ce ta sakko daga kan kujera tace "abbah ina yini"


Kallon gun abban yayi yace "a,a Siyama kece yaushe kika zo gidan?"

Yafada bayan ya amsa mata gaisuwar da fuska a sake


"Wallahi ban jima da zuwa ba Abbah"


"Hakane bakajin tsoron fitar dare ko
Dady n naki yanan kika fito yanzu"?

"A,a abba momy CE tace nazo kawai"

Abbah bai CE komai ba sabida ya Riga yagama fahimtar irin son da Siyaman takewa Ali wannan fitowar ma domin shi tayi mybe tasamu labarin ya dawo garin


Ummi kam mikewa tayi ta nu fi dinnnig din dan tasan zaman da Ali yai abinci yake son abashi kamar wani yaro maganar ma bazai ba


Yana zaune fuskarshi babu yabo ba fallasa


Ummin takaraso gun
Sakin fuska yayi yace "my ummi me kika girka ne "? yafada yana gyara zamansa sosai


"Zaka gani yanzu ai"

Wayarshi dake hannushi ya ,ajiye kan teble din yace "ok "

"Ummu Allah ya jamin da ranki ya karamiki lafia Ameen"


"Ameen " ummin tace tana kokarin zuba mishi abinci wata lafiyar yiyar jolof ce ta macoroni wacce akai mata mis da dankalin turawa taji bushanshan kifi hade da kayan lambu sai kamshi ne ya ke tashi


"Wow my ummi wannan wane irin abinci ne "? ya fada yana da murmushi a fuskarshi ummi CE kawai take ganin murmushin sa sai ko abokanshi shima ba sosai ba sai Nene shi itakam ai in ta tabka wani abin har dariya yake sosai


"Bakin ka zai gayama ko wane irin abinci ne " ummin tafada tana kokarin tura mai plete din bayan ta hada mai lemonshi na fama da take masa ko wane kwanan duniya,,


"Yawwa son dan haka take kiranshi sabida alkunya tace "akwai maganar da za muyi"


Kafin ta rufe bakinta Siiyama ce ta karaso gun cikin kwarkwasa da iyayi ta ce " laa ummi dakin bari na zo na hada mai abinci bana so ki wahala " tafada cike da kissa

Gabanta sai faman faduwa yake tana tunanin.irin kalan dizgin da Alin zai mata

Ummi n itama cikin wayewar kai tace "ai laifin ki ne kina ganin zamanshi a gun baki taso kin bashi abincin ba ko'


Sabida tagama fahimtar yariyanyar makirar yarinyar ce me halin uwarta sabida azahiri za a nuna a nasanka a badini kaman abin bahaka abin yake bah irin su sunanan da yawa a duniyar nan Allah karabamu da masu fuska biyu ameen


"Aikam dai " siyaman tafada tana dan murmushi yayin da take kokarin zama kan daya daga kujerun zaman cin abincin


Barin gun ummi tayi a zuciyarta tace "ai Ali ne a gabanki yarinya dai dake ne in banda rashin zuciya irn nawasu mutane mutumin da akewa wannan abin bazai gane kora da hali ake masa ba amman sabida tsabar naci anki ganewa

Ita dama ba wani son abin take ba sabida tasan halin mahaifiyar yarinyar "yar bin malamai CE da bokaye "yan tsubbu ita tsoronta kar aje a sabauta mata danta


Dan ma Alin a tsaye yake gurin tsare jikinsa to amman sihiri waye bazai Ciba tunda yaci fiyayyan halinta Allah dai ya tsare ya kare tafada a ranta yayin da take barin gun



Ali kam abincinshi yake ci kamar bai san da wata hallita a zaune a gun ba


Cikin rawar baki siyama tace " ya Ali anyini lafiya "

Shiru yayi bai amsaba sai data kuma mai mai tawa sannan ya dago kai yana dan ya mutse fuska as,useul yace "lafiya kalau ya cigaba da cin abin cinshi

"Andawo lafiya ya hanya"?


Bai ce komai ba sai kallonta da yayi akaro na Biyu


Fuskarshi shade yace "wannan wace irin Shiga ce a jinki " ?yafada yana nuna sai tin kirjinta da suka bultso ta saman rigar ta da cokalin da yake hannusa

Dadi ne Yakama Siyama sabida haka sai ta kuma gan tsaro kirjin cikin fari da ido tace " laa ! ya Ali me shigata tayi domin kai fa nayi"


Kallonta yake yana balla mata harara fuska a mutukar murtuke

Yace" tashi daga nan stupid haka zan aurekin kina fito da sasan jikinki don rashin mutumchi da sunan kwalliya usseles kawai "


Cikin tsawa yace " ba dake na ke ba dan uwarki , wuce kibani guri ni zaki zo kina nuwa wannan abin naki" yafada yana kara kallon kirjin nata a karo na uku


Cikin rawar jiki Siyaman ta mike daga gun har tana yin tuntube da kujerar bayanta


A ranta kuwa tana kam ba ba irin rashin mutunci Ali

Wai wannan abin yana nufi kirjin ta bai birge shiba yanda take ji da abinta amma Allah ya isa wallahi tafada lokacin da take Barin gun



Da kallo suka bi Siyama
jameel sai kunshe dariya yake a zuciyar sa yana cewa Allah shi kara


Samun guri tayi gefen Na'ima ta zauna tana cika tana batsewa


Da kallo Na'ima ta bita ganin yanayin Siyama murmushi tayi cikin magana kasa kasa tace "ya akai ne mutuniyar "tafada cike da zolayar ta domin dai sun dan ji irin dizgi da Ali nya tabka mata


Basawar wa siyaman tayi tace "normal "

To itama Na'ima ba tace komai ba ta cigaba da danne danne nen ta a waya aranta tace in tayi wari maji



Dija ta koma inda Fa'iza take zaune itama ta zauna kusa da ita


Cikin magana kasa kasa tace "wai wannan wacece ne"?

Tafada tana kallon gefen da siyaman take zaune


Kallon gurin Fa'iza tayi itama tace " aunt Siyama kike nufi"?


"Eh mana" Dija ta fada tana ta be bakinta


"Budurwa ya Ali CE ita. Zai aura karatu zata karasa sai ayi bikin"


Kallon inda Siyaman take zaune dijan tayi

Tab dijam ta hadu da jaraba ita tarasa wazata aura sai shi cab


To ai shima ba wani sonta yake ba ita ce ke son sa Abbanmu kuma yace ita zaura sabida "yar gidan amininsa ce fa,izan tafada tana hararar dijan


Tabe baki dijan tayi tace aikuwa dai naga tana sonsa yana mata wulakanci watakila in ya auretan ya dinga dukanta tafada cike d yarinta



Ai y Ali baya duka shi ko laifi kayimishi

Karkarinshi rankwashi ko yasaka daga hannu ko tsallen kwado


Tabe baki dijan tayi idanta akan siyaman tana mamakin wai son ya Ali take ita tausayima take bata



Nene ce da abba suke magana cikin fahimta da kauna irin ta da uwa hira suke dangane da dangin maihaifinsu Abbah dake can dan batta wasu su suna cikin halin rashi da talauci


Sabida haka Nene tace " yakama ta yaje can garin ya fitar da zakka acan

Sannan yatai makawa wa "yanda basu da sana,a da jari mai karfi


Abban yace "insha Allahu yanda kikace haka za'ayi Nene


Kallonsa tayi tace "yawwa sai magana tabiyu "


To Abban yace yana kara mayar da hankalinsa kan ta


In da Ali yake zaune ta kalla sannan tadawo da kallon ta gurin Abbah


Tace" maganar Aliyu ce da siyama wai me,aka tsaye ne yakamata ayi a gama inace ai ya gama karatun kuma yasamu Aiki yana da gurin zama ya cika cikakken namiji tunda yanzu inace she karunsa in banyi karya ba talatin da biyu ko"?




"Kwarai kuwa nene hakane"

Abbah yafada ya ce


"Wai ana jiran yarinyar kammala karatun n nata sai ayi"

"To meye laifi in anyi ai sai ta kammala a dakinta bana son ganin Ali babu iyali ganin duk abokanshi kowa da aure dai dai kune babu a cikinsu


Numfashi abban ya sauke yace "duk yadda kikace haka za,ayi zan samu dady Siyaman zamu tautauna akan maganar


"Yawwa ko da najii"

Nene tafada fuskarta cike da murmurshi


Shima Abban murmushi yace "ni nata 6a ganin me so kishiya ma Nene in bake ba" yafada yana kokarin tashi daga gurin da nufin zuwa gurin cin abinci


"Yo ai ta dole ce amma in tazo dole tazama gora ehee"!!


Dariya jameel yayi wanda yake zaune a gefen ta tundazu yana fama da waya

Yace" kewa zai iya kishi dake "?


Kallonsa tayi tace "kai ashe kana nan " tafada tare da kama ha6a

Dariya jameel yayi yace" ai kin soma makan cewa ne shiyasa kikasa ganin inan ko banan ,,


Filon kujera ta dauka taje famasa tace "sai dai in kai ne ka makance shakiyyi
Kasan masifar rashin ganin kuwa tafada tana hararasa"

Tashi jamel din yayi yana dariya yace" to ke wai ke me kike jira ne
Kikwantar d hankalin da idannunku zaki zaki mutu munanan munayi yimiki a du,a "


Harararsa tayi tace "dallah wuce kaban guri samo dari kawai baka da aiki sai na kwallo n kafa da faman latse latsa a waya"


Dariya jameel din yayi
Yanufi dannig din shima


Ummi kam tun lokacin da Abban ya tashi itama ta mike taje tahada mai abincinshi


To duk wannan abin Siyama da Na'ima suna zaune dan kasa kunne Siyaman tayi babu abinda bata jiba

Dadi kamar yakasheta tana ta shiwa Nene albarka ai in abin nan ya tabbata bazata taba mancewa da Nene ba a ta rihin rayuwara taba


Cikin kan kanin lokaci ta saki fuskarta tana ta jan Na'ima da zance


Girgiza kai kawai Na'ima tayi tana tausayawa Siyaman ganin irin wahalar da kanta datake a inda ba ,asan tanayi ba

Yin aure da wanda bai sonka akwai babban kalubale aciki amman ta lura Siyaman tayi nisa a halin da ake ciki yanzu duk wanda yace zai mata maganar tarabu da Ali sai sunyi kaca kace sabida bata ji bata gani


Ita dai fatanta Allah yahada kansu duk yadda take so Syama bakamar Ali ba tunda wata kusan tafi wata



Mikewa sukayi dukkaninsu suka nufi gurin cin abincin suka banda Nene sabida bakasafai take cin abinci a sama ba sakamkon ciwon kafa datake fama dashi


kujera suka hau gyara wa kuwa yana kokakarin zama

wani kallo ALi yabisu dashi yana ya mutsaya fuska as,usuel ya dauke kansa yama yar da han kalinsa kan abba wanda suke tattaunawa game da yanayin aikin shi


wayoyinshi da mukulin motorshi dake kan dannig din ya dauka yana kallon ummi wacce take kokarin sawa kuwa nashi abincin bayan ta kammala hadawa abbah nashi


cikin tsawa yakalli Na'ima yace "aikin me kikeyi ke da baza ki hadawa kowa nashi ba "



cikin sauri Na'ima ta ajiye wayar datake hannuta kan cin yar Siyama wacce take gefe sai faman kallon sa take kamar wata mayya


tana kokarin karbar ummi
ummin tace "jeki zamanki
nagama ai bakwasan aiki ko kadan sai san jiki da fama da waya ai kun kusa fara shiga khicin din da kan ku ato muga karyar san jiki " ummin tafada bayan tagama hadawa kuwa nashin



tsaki Ali yayi ya bar gurin aranshi yace shashashan yara kawai waye ma zaci abincinsu.


shi kam abba murmushi yayi bai ce komai ba yana mamakin Alin yadda yake da tsamtsami abin a jinshi yake tunda jininka ma baka barshi ba


ummi ma Nene ta hadawa nata takai mata har inda take

Nene kam sai sa mata albarka take



kai tsaye inda motorsa take yanu fa yana kokarin kiran faruk a waya


wayar na makale a kafadarsa yana kokarin bude motar


"hello" Ali yafada bayan yaji an dau wayar


"kana gida ne " yafada a karo na biyu

daga bangaran faruk din cikin shakiyanci yace " ya akai ne kai gwawro"?


banza Ali yayi mishi batare da ya saurari maganarshi ta farko ba


cikin dan bacin rai yace "kana gida ne" a karo na biyu


"ehman ina zani a irin wannan lokacin wannan yawon ai sai irin ku marasa mafadi " faruk din yafada yana sakin dariya kasa kasa sabida yasan halin yan kayansa


cikin bacin rai Ali yace " kai dai ka san abinda katsaya yi dan iska jarabbabe wallahi kabi musu da yarinya a hankali dan nafisa baza ta iya da jarabar ka ba " yafada yana faman huci


dariya faruk din yake yace " to meye ruwanka da iyalina matanka ko tawa
to wai ma da kake tambayar ina gida me zakayimin a wannan lokaci "?


"Ubanka zanzo in maka" Ali yafada yana kokarin kashe wayar sabida ya fuska ci rashin mutumcin furuk din ne motsa


yasan yana gida bazai fadama masa bane sai yai mai iskanci


sabida haka kai tsaye gidan faruk din yanufa

wajan tara da rabi ya isa gidan faruk din

motar shi ya kule ya fito yana kokarin kiran faruk din awaya


mai gadin gidan ne ya tashi.da sauri kunneshi makaleda redio yana sauraron tashar friedom redio cikin shirinsu na inda ranka


ya budewa AIi karamar kofar tunda ya fuskanci ba motar zai shiga da ita ba


sai faman washe baki yake

yace " oga Ali kaine a wannan daren"? kalonsa
Ali yayai yaga sai faman rawar jiki yake shi yana mamakin mutane da kwadayi da zubar da mutunci sabida ya saba yana bashi kudi shiyasa duk sanda yazo gidan faruk din kamar yai mai sujjada sabida tsabar rawar jiki


A nutse Ali yakalleshi yace "meye haka malam isiyaku kake ?
wannan bai dace ba ALLAH kadai shi muke bautawa mu dukanmu bawani dan ADAM ba sabida haka duk daya muke a gurin ubangiji daga yau kar ka kuma yimin irin wannan abin da kake min bana so ko kana so dani dakai mufada cikin fushin ubangiji ne"?


cikin sanyin jiki malam isiyaku yatashi daga gurfanan dayayi, gaban ALI kamar wani mai neman gafara yace "tuba nake ranka yadade insha ALLAHU baza a kuma ba"


Ali bai ce komai ba ya zira hannushi cikin aljihun jins din dake jikinshi ya fito da kudin ya bashi kamar yadda ya saba duk sanda yazo gidan faruk din hannun narawa malam isiyaku ya karba yana ta godiya "ALLAH ya biyama bukatunka na ALkairi Allah yabaka mace ta gari ALLAH ya azurtaka.da "yaya masu Albarka"

"Ameen Ameen " AIi yafada yana kokarin shiga gidan hannushi rike da wayarshi yana kokarin kiran faruk din a karo na biyu



ba zai iya shiga kai tsaye gidan ba duk da cewar gidan ba bakonshi bane ba to amma yasan halin Faruk bai da mutumchi zai iya takar Nafisa a ko ina ne ba damuwarshi bane



"kafito ina cikin gidan ka " Ali yafada bayan ya tabbatar da faruk din yadau wayar bai bari faruk din yace komai ba yakashe wayar



faruk di ne yafito yana kallon Ali cikin dan baciran rai yace "wannan wani sabon salo ne kuma "?


banza Ali yayi dashi kai tsaye cikin gidan ya nufa


bin bayansa faruk din yayi yace " bafa ka isa ba kazo har gidana kana cimin magani ba sai faman wani muzurai kake wa mutane da girma na da iyali na " faruk din yafada yana tarar gaban sa


wata dariya ce ta kama Ali amma sai ya share azuciyar sa yace wai da girmana da iyalina shi abinma dariya yabashi kamar ba yau yabar yawo clob clob ba dan yanzun ma abin yayi sanyi darajar aure
hararar faruk din yayi ya bige kafadarsa ya wuce yana dariya ciki ciki



sakin baki faruk din yayi yana bin shi da kallo yana mamakin karfin halinshi shi kowa sai ya gwada mai iko da mulki girgiza kai yayi yana dariya a ransa yace kaje can akwai inda zaka yi wannan mulki naka amma bani ba yafada yana bin bayan sa


tsayawa yayi dai dai kofar falon yana sosa kunnesa da mukulin motorsa idanunshi tsaye akan faruk da yake ta wo wa da murmushi akan fuskarshi yakalli faruk din yace "to mai iyali fara shiga kai min iso gurin uwarginnaka " yafada yana kanne masa ido daya dan yasan yagama kunna shi


bazan faruk din yayi mishi yana kokarin bude falon sannan yace "in kaga dama kar ka shigo dani nake maka iso cikin gidan "


dariya Ali yake yace "wallahi kabi ni ahankali in bahakaba in fasa kwai dan kasan zan iya wallahi"


da sauri faruk din ya tsaya yana gyara fuska yace " wai meye haka kai fa baka da mutumci kar ka rusamin bajat dina na yau mana wai ma meya kawo ka ne yanzu" faruk din yafada sai faman gyara tsayuwa yake dan yasan halin Ali


dariya Ali yake sosai ganin yadda faruk din yashiga taitayinsa kamar ba yanzu ya gama cika baki ba shi mai iyali.shi yana mamakin yadda wasu mazan suke rawar jiki akan mata shikam duk irin son daya kewa mace bazai iya wannan shirman ba



shiga falon .yayi bakin shi da sallama



Nafisa na cikin kujera a kwance jikinta sanye da kayan bacci masu kauri da hula a kanta da alama bata jin dadi


cikin sauri tata shi fuskarta dauke da murmushi tace "ya AIi kaine ashe sannu da zuwa" ta fada tana kokarin gyara zamanta sosai


murmushi Ali yake sabida yarinyar tana birgeshe tana da hankali sosai yace " Nine nafisa wannan mijinnaki bai da kirki ya hanani shigowa da kyar ya barni na shigo sabida kawai nace kar yayi miki kishiya shine yake jin haushina " ALI yafada yana kallon faruk din wanda tun shigowarsa yaje ya makale jikin Nafisan yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login