Showing 15001 words to 18000 words out of 56336 words

Chapter 6 - NANA KHADIJA COMPLETE

13 Jul 2025

17315

yace "wai ina wannan "yar kauyan yarinyar ne ko bada ita kikazo ba "?


Harararsa nene tayi tace "e"


Dariya yai ya fita dan yasan fada tai kawai yasan nene bazata iya tafiya mai nisa irin wannan batare da dijanta ba



Kallon su Na'ima tayi wa "yanda sukai tsorutsoru a gaban Ali ko motsin kirki bau wacce take


Shikam Ali hankalinsa baya kansu kallon sa yake bayan ya canja tashar da Fa'izaa ta kama


Labarai yake saurara a tashar aljazeera,,


"Ku kuma meye haka , sai kace wasu masu nai man gafara " tafada tana rike ha6a



Shirou sukai babu wacce tayi maganan acikinsu,,


Kallon Alin nene tayi tace "miskili kafi mahaukaci ban shaushi kenan,,

"Wai me suka yima ne" ?



Banza yai mata haushinta yakeji yasan tunda tace zata gayawa abba maganar siyama sai tafada yasan halinta da tada zaune tsaye kawai zatazo ta dama mai lisssafi,,


Sai da ta kuma mai maitawa sannan yace
"Meye ruwanki to " yafada still idansa na kan tv



"Da ruwa na wannan cinzali ne ai , ya zaka zaunar da yara guri guda ka hana su motsi sabida mugunta, ai ba sojojin ne su ba ko masu laifi ballanta kai musu irin wannan horan"



Kallon Fa'iza nene tayi tace "ina dija n take ?


"Tana dakinmu " " tashi kije ki ki ra wu min ita


Kallon Alin tayi yana kallonsu ta gefen idon sa bai ce ko mai ba




A darare ta tashi ta nufi dakin nasu











tare suka shigo ita da dijan kai tsaye inda nene take ta nufa ta zauna kan hannun kujerar da take kai



Fai'za ma kusa da nenen ta zauna dija tace "baki baccin ba nene "?


"Yau she zan iya bacci yanzu ai yamma tayi "


Kafin ta rufe bakinta ummi ce ta sakko daga sama tana kwala a sabe mai aikinsu kira ,,


Kallon Alin Ummin tayi tace "au kananan ashe ba ka fita ba?


"Eh nadan tsaya sauraron labarai ne"


Bata ce komai ba tane mi guri ta zauna tana kara gaida Nene



Asabe ta shigo cikin sauri tace "gani hajiya"


Ummi ta kalli Nene tace "meza,a da fa miki ne?


"Da ni kuke tambaya iyi"?

Nene tafada tana kallon ummi


"A,a nene wai ko kina sha,awar cin wani abin "


"A,a duk abinda aka dafa zanci bana son tsurfa daga zuwa za,tsiri tambayata "


Dariya ummi tayi tace" Nene kenan"

Kallon asaben tayi tace "kije ki shirya abincin yadda ya kamata"


"To" asabe tace ta bar gun


Canja tasha ummi tayi zuwa mbc,maxx

Wani shiri suke nunawa na kiwon lafiya ,,


Na'ima tace "don Allah ummi mayar mana arewa mukalli dadin kowa duk da cewa sun kusa gamawa"


"Ba maimaici suke ba yau"?


"Eh ummi ai bamu kalla ba duka ba"


Ba tace komai ba ta mayar musu da shi arewa


Tsaki Ali yayi kasa kasa ya mike yace " ummi nafasa fita sai anyi magariba zanje in dan kwanta" yafada yana kokarin barin gun



"Aikam dai da yafi tunda faruk din yazo gwara ka huta zuwa an jima "tafada tana kallonsa,


Yace "ai haka za,ai sai yanzu gajiyar take damuna wallahi ,,


"To ai dama dole "


Kallonsa nene tayi yayin dayake kokarin barin falon


"Ai gwara daka tashi daga gun kazo ka kankane kamar wani kai ne mai gidan sai faman mulkin mallaka kakewa mutane,,


Dariya yayi kadan "yace kanki akeji "


Ya fita daga falon shashesa ya nufa yattada key din jikin kofar budewa yai yasan. Faruk ne ya barshi yana ganin asarar mayar mai dashi



Zama yai gefen katuwar katifar dake dakin yana kokarin balle botoran rigar dake jikinsa ,,


Kwanciya yai rigingine ya daura hannayenshi saman goshinsa



Tunanin. Maganar dazu yake dasukai da faruk gaskiya shi kwata,kwata siyama ba taima sa ba bayajin sonta ko daya a ransa sai irin na addini isilama


To amma maganar faruk abin duba wace tunda hakikanin gaskiya siyama da iyayenta sun saki jiki zai aureta dasu kansu Su Abbanshi da ummin


To amma babban abinda suka kasa ganewa game da shi baya ra,ayinta tunda shida bakinsa baita6a gaya musu yana sonta ba ita take haukanta har suka fuskanci hakan ta bangaranta



To shikam mutum ne da yake girmama mai kaunarshi baya ga hakama bashi da ra,ayin wulakanta mutum ballanta me kaunarsa shine abinda yake dubawa yakasa furta wa da bakinsa baya ra,ayinta ,,


Shiru da yayi shiya basu karfin gwiwar kamar shima yayi na,am da abun


Gaskiyar lamari babu wannan a ransa ,,shifa har yanzu bai ga macan da tai mai ba wacce tatara abubuwan da yake so ba



Duk da cewa akwai tarin "yan matan dasuke karakaina akansa to amma su dun ma akwai matsala dan duk macen da tayi ma tallan kanta to tabbata bata da kamun kai



Shiyasa yake musu kallon dai-dai



Shikam bashi da mafita a wannan lamari zai iya auran siyama sabida irin kaunar da take nunawa a gareshi to amma kam. Zai yi aure in yasamu dai dai dashi,,


Wannan shine hukunchin da ya yanke ,,



To a can falo kuwa yaran samun sakewa sukai sabida dodon su ya bar gun ,,kallon su suke cikin raha suna dariya ,,nene ma takan sa mu su baki cikin surutun nasu



Abbah ne yai sallama
Hannu shi rike da wa yoyinsa bayanshi kuwa salmanu ne rike da jakar abban da sauran ta muhiman takaddunsa ,,



Cikin ihu Fa'iza ta tashi taje ta dane shi "abbana sannu da dawowa "shima cikin dariya ya rike ta yace Fa'iza n abbah ya gida?


"Lafiya kalau abbanmu" Rike hannusa tayi suka jera har inda nene take



Zama yai a kujerar da take fuskantar nene


"Sannu da zuwa nene kunsha hanya ko"?


"Yawwa sannu aikam dai mun same ku lafiya?"


"Lafiya kalau nene yaya su baba malam da sauran "yan uwa?"


Nene tace " kowa lafiya lau suna gaisheku da kyau,,


Yace " ai inata saurin in fito daga officee da wuri sai ga baki nayi wallahi naso in dawo da wuri ,,



"Ai gwara daka yi zamka ka tawo a nitse tunda ba tafiya zamuyi ba "


"Hakane" Ya fada yana kallon dija yace "zo nan doghter "



Kanta a sun kuye taje tace "abba inayini munsame ku lafi,a?


"Lafiya lau dija ya karatunki " ? Yafada yana sata a jikin shi yana bala,in tausauyin yarinyar kasan cewarta marainiya batasan iyayenta ba. Shikam dan dai nene tafi karfi shine amma da babu dalilin da dija zata zauna babu cikakkiyar makaranta wallahi ya kewa yaran wasu ma ballantana wannan daya ke jin kamar shine ya haife ta



Itama dijan kwanciya tai a jikinshi ,tace " abba karutu alhmdulilah"



Na'ima dake gefe tace "abbah ni an manta dani ko?


Tafada da yanayin shagawaba. Murmushi abbah yayi yace "nina,isa zo nan mai babban suna nimatullah ya fada yana mika mata hannu shi


Cikin dariya taje itama tace "abbah an dawo lafiya ya fama da jama,a?



"Alhmdulilah mun gode Allah "



Nene kam baki tasaki tace "o ni "yasu "!


"Haka ka ke wa yaran nan bashir iyi "? dariya abban yai yace "menayi musu nene "?


"Yo ai duk abinka mata ne ko wacce aure zakai mata ato in banda abu irin na zamani ai mu bama kallon "yan yanmu mussaman nafari"



Murmushi abbah yayi sabida yasan za,a rina yasan halin nene duk da itama fada kawai take domin itama tana da bala,in son yayanta dan dai tana da kawaici ne kawai



Yace "shine dalilin dayasa nake jansu a jiki ai nene ganin basu da wani sai ni gashi ko wacce miji ya na zuwa aure zan yimata "


Dole in tausaya musu,,



Yafada yana kokarin tashi daga gun yace "nene zanje inwa watsa ruwa magariba ta na neman yi "



"To a sauko lafiya" nene tafada hankalinta na kan tv da suke kallon



Ummi ce ta fito daga khicin tace " naji kamar abban yara ya shigo ko?



"Eh yanzu ya hau sama "


Itama saman tabi shi cikin sauri ,,


Yana shiga dakin itama tashiga


"Sannu da dawowa abbah"


Juyowa yayi yace " yawwa dama kina kasa ashe "?

Tace "shiga ta khicin kenan naji shigowar ka"

An dawu lafiya?

"Lafiya lau "ya fama da hidimar mu" yafada yana mata murmushi


"Alhmdulilah Abbah ai akin lada ne" tafada tana kokarin Shiga toliet tasan wanka yake son yi



Ruwa ta hada masa tafi to mai da duk abinda zai bukata



Sannan ta fito yana zaune gefen gado yana cire a gogon dake daure a hannusa tace "abbah an hada ruwa wanka jikin sef din dake manne a bangon dakin ta nufa ta ciro mai jallabiya mai yankaken hannu ta a jiye a gefe.



Yace "sannu uwar gida uwar Aliyu haidar zakin fama,


Yafada da murmushi a fuskarsa ,itama murmushin take tace" abbah kenan"



Yace "akwai magana ne " "ehe ai gaskiya na fada dariya tayi tace" to wa yace ma kayi karya"



"Yawwa akwai maganar dana keso mu tattauna zuwa anjima game d Aliyu ne"



Kallonta abba yayi yace "wani abin ne??


"A,a akan maganar siyama ne?"


Tafada tana kokarin barin dakin sabida ta daura musu Abinci shida Alin tunda bata yadda yaci na asabe wannan tsarinta ne



Bai ce komai ba shima ya mike yashege toliet din







Sakkowa ummi ta taddasu suna zaune har yanzu tace "Na'ima bakuji Kiran sallah bane yakamata kutashi haka "


"Eh ummi yanzu zamu tashi ai"


"Ba ruwana wallahi Ali ya fito yattada ku anan kar wacce ta nemeni" Ummin tafada tana kokarin shiga khicin



Cikin sauri Fa,iza ta tashi. Tace "ai kam dai dan dazu nene ce ta cece mu. Daba dan itaba da sai munsha rankwashi ko ya murmurde musu hannaye haka yake musu in suka yi wani abin



Tace "Dija muje muyi sallah ko"


Tashi dijan tayi tace "muje dakin nene muyi a can"


Kai tsaye dakin da nene take suka nufa


Ita kam Nai,ma tanan zaune to bata sallah prieod take sabida haka zama ta gyara wayarta ce a hannuta nema layin siyama take sai ace busy


Tsaki tayi a karo na biyu ta kara gwada kiran wayar



"Hello Siyama"

Daga bangar siyaman itama tace "ya akai ne kanwata " tafada tana dariya dan tasan Na'ima n ta tsani ta ce mata kwanwarta


Cikin bacin rai Na'ima tace "wai ke dawa kuke waya ne tun dazu nake kira busy"


Dariya siyama tayi tace "Wata friend dina ce wallahi iyabo damu kayi skull tare "



"Ok. Ya Ali fah yadawo dazu"


Ihu !! siyama tayi tace "da gaske kike?


"Ba yace sati biyu zai yi ba" ?


"Eh wani aiki ne yata so musu ya zama dole sai dashi shine dole yadawo tare ma suka tawo da nene"



"Kai sistar naji dadin labarin nan naki wane tukwici zan baki?"


Dariya Na'ima tayi tace "kedai kin shiga uku akan namiji kike haka wanda bai san ma kinayi ba"


"To ya zan yi Na'ima Allah jarrabeni da son yayanki shikam naga kamar baya ra'ayina"



To itama Na'ima tasan gaskiya siyama tafada ya Ali baya ta tata sabida haka cikin rarrrashi tace "ki kara hakuri komai zai yi daidai kinsa ya Ali al'amarinshi sai shi wani baudandan mutum ne sabida haka ko yana son ki baza nuna ba"


"To ya zanyi don Allah kidinga shigar dani a gunshi kinji sistar na " siyaman tafada cikin kwantar da murya


Dariya Na'ima take tace "rufan asiri in mutu maza su kaini"

"Wai ance wargi ma guri shika samu ke dai din da kikaga zaki iya bissimillah mu dai. "Yan addu'a ne"



Daga daya bangaran siyama tace "haka zamuyi dake ko?"


"Ai anyi angama ma wallahi bazaki sani a jarfar ya Ali ba a yanxu ma ya , aka kare
Kizo kici gaba da kafa gwamnatinki ko Allah zaisa a dace"


Ka she wayar Siyama tayi tace "mara mutunci nasan ta inda zan bullo muku da ku da ya Ali"



Kai tsaya dakin Momyn ta ta nufa ta tadda ita a zaune gefan gado tana waya da kawarta hajiya ladidi, ta zube kan bed din tana sauke nuffashi,Momy tayi saurin kashe wayar tana kallon "yar tata tace"ya aka yi ne naga kin shi go kina bacin rai ,nifa na tsani in ganki cikin damuwa my daughter"

Siyama ta mike zaune tana ya mutse fuska ta ce "Momy kinji ya Ali ya dawo ko ,yanzu wane shiri za muyi"?


Momy ta aje wayar kan mudubi tana kallon "yar tata tace"ai tashi zakiyi ki shirya ki cancada kwalliya ta ban mamaki ki dira a gidan domin naga yaron nan in ba haka mukai masa ba a kwai Matsala na lura yana da taurin kai"

"Humm! Wallahi momy har narasa yadda zan bullo masa duk wani dabaru na a kanshi sun kare"Siyama tafada tana tausayawa kanta


"Ai baza mu yi kasa a gwiwa ba ki ci gaba da kokarin a kanshi ,in yaqi zamu bullo masa ta bayan gida kawai,tunda shi yace dan taurin kai ne"


"Yawwa momy dama haka kukayi masa wallahi domin zuciyata tana azabtuwa da so da kaunarsa ,shi ko nunawa yakeyi kamar bai damu da ni ba"


"Ai yanzu nan muka gama magana da Hajiya ladidi a waya tace min tana kan hanya ,zuwa nan, zamu shirya yadda komai zai zo mana cikin sauki"


Farin ciki ya lullube Siyama ta rungume Momy nata tana fadin "shiyasa nake sonki momcy na wallahi sabida kina son abinda nakeso"

Dariya Momy tayi tana farin ciki ganin diyar ta tana farin ciki tace"ai duk inda zan shiga in fita zan shiga ,domin in ga kin auri yaron nan ko da zanyi yawo tsirara sai burinki ya cika ,kuma da ke kadai zai zauna babu kishiya ,kamar yadda nake zaune ni babu kishiya"


Siyama ta riqa murna tana ganin burinta ya kusa cika zata auri gwarzon maza Aliyu zaki mazan fama ,mutukar ta aureshi tasan ta gama dacewa,kuma tasan halin momynta inda tace zatayi abu za tayi


Sabida haka mikewa tayi cikin qwarin gwiwa tace"Momy bari naje na shirya kawai na tafi"

"Yawwa dota kiyi sauri kinji ko kiyi wanka sosai yadda zaki dauki hankalinshi"

Dariya Siyama tayi lokacin da take kokarin fita saga dakin momyn nata,tace"sai momyna wallahi Allah ya bar minke"

Momy ma dariya tasa tamkar wata ma haukaciya


Cikin wata atamfa ta fito da gani a tamfar mai tsada ce sosai, amma dan iskanci anyi mata wani mutsiyacin dinki ,wanda ya fito da sassan jikinta ko ina gashi nan mussaman kirjinta duk sun bullu tso ta saman rigar ,da ta daga hannu hammatar ta a waje sket din ya da meta sosai ,kanta ya sha karin gashi kafarta sanye da wani takalmi mai tsayi ,ta fito hannunta ruqe da key din motarta sai karamar jakarta pose sai taunar cingam take klas!kas!las!


Cikin farin ciki Momynta tace"gaskiya kinyi kyau my douhter ,kin ga yanzu ko shi waliyi ne dole in ya kalleki ya kwadaitu dake ,dama nasan yarinya ta bata wasa ba ce"

Siyama sai dariya takeyi cike da farin ciki yadda momynta take kwarzanta kyawunta


Har har waje nomyn ta rako ta sai daga taga motarta ta fita daga gidan sannan ta koma ciki tana tafiya tana magana ita kadai tamkar wata shashasha


lokacin da siyama tashiga gidan ana tafaman kiran sallahr isha'i bayan baba mai gadi yabude mata get din kai tsaye danna hancin motar tayi cikin far fajiyar gidan



Tana kokarin gyara faking shi kuma Ali fitowarsa kenan da nufin zuwa massalaci
Hannu makale da carbi irin mai dannawa nan kallo daya yayiwa gun ya fahimci motar siyama ce


Tsaki yaja ya wuce aransa yace wannan yarinyar bata da hankali meya kawuta da wannan daran oho


Mikawa baba mai gadi hannu yayi suka gaisa ya ce " Abba yafito ne?


"Eh ai bai shigo ba yana jiran ya sallaci isha ne kasan cewar tun fitarsa sallar magariba bai shigo "


Bai ce komai ba shima ya nufi ma sallacin


Ita kam siyama ta ga lokacin da ya fito sai taji wani bala,in tsoro da fargaba ya kamata kasan cewar taga ko kallo bata ishe shiba


Cikin sanyi jiki damutuwar jiki fito da ga motar jikinta a sanyaye ta nufi cikin gidan,,



Duk suna zaune. A falon har jameel ana ta hira sai dariya ake


Dija tana zaune kan hannun kujerar da jameel yake zaune sai faman nuna mata hotona yake a wayarsa a cewarsa "yan matansa ne ita kam dija so take ya bata wayar yaki ya bata tana bala'in son babbar waya kasan cewar ta nene karama ce ,, bata da game masu yawa shiyasa duk inda taga waya sai tace abata tayi game



Sallama siyama tayi bayan tashiga falon


Ummin ce ta, amsa tace "Aa
Siyama kece da wannan daran " ? "eh wallahi ummi " siyama tafada yayin da ta ke kokarin zama a kusa da Na'ima



Dariya Nene tayi tace "au biyo sawo kikayi sabida kinga yaki zuwa ko"?


"To duk abinki nice dai ta karfen sai na ga damar barinsa yaje ehe"!


Dariya siyama tayi cikin kissa tace " dama wace ce ni inja da uwar gidan Aliyu ai nima sai yadda kikayi dani"


Nene tace" eh "yar nema abaki ba ai nasan zuciyarki tananan tana zafi na hana shi zuwa"


Dariya Na'ima tayi tace "me ya Ali zai yi da ke da kai duk fur fura ai shi sai yarinya sabon jini"


Cikin kissa siyama tace "ai fur fura bai wace wani yayi mana"


Hararar Na'ma Nene tayi tace " ke kuma waya sa dake"?


"Sai ansa dani " Na'ima tafada tana dariya



Dariya Siyama tayi tace" babu ruwanki sistar wannan abinda ya shafi kishiya d kishiya ne ",


Ita kam umma tana zaune tana mamakin siyama da,ita da budewar idon ta gata a zaune ko kunya bata ji ta ke wannan abin lailai zamani wasu yaran basu d kunya,,



Siyama takali ummi tana sinqe kai wai ita nan kunya tace " bamu gaisaba bama Ummi ina yini"?



"Lafiya kalau siyama ya momy n taki "?

"Wallahi tanan nan kalau tace ma a gaisheki wai kwana biyu ba ko haduba"


"Ai kam dai ai momy taki ce bata da kirki ba ta ziyara"


Dariya siyaman tayi idanonta akan jameel
Tace" kai na karfe abun ma babu magana"


Kallon ta jameel yayi
Ya tabe baki yace "ni dake waye zai gaisar da wani iyi"?


"Kai ne" Siyaman tafada tana murmushi domin dai tasan tun tuni jameel baya kaunar ya ga tazo gidan ya dinga harararta kenan in ba,ita ce ta kulashi ko za,a shekara bazai mata magana ba



Yace "zaki dade a gun kenan in dai ni kike jira na gaisheki"


Itama bata ce komai ba a fili acikin zuciyarta kuwa tace zakaci ubanka kai ma
Nayi lis dinka a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login