Showing 3001 words to 6000 words out of 56336 words
lafiya cikin Dakin ta in da tasamu da Namiji ,farin ciki gurin Malam Ibrahim babu kama hannun yaro "yan Uwa da Abokan Arziqi suka riqa tayashi murna ,shiko ya din ga fitar da hatsi yana rabawa talakawa,ranar suna yaro yaci sunan Bashir.
Haka Bashir ya ta so gaban iyayenshi cikin kulawa domin Nene macace mai kula da yara gami da tsabta,
Sai da Basir ya shiga pramary 4 sannan Nene ta samu wani cikin lokacin yana shekara goma sha biyu ,wannan karon ma Malam Ibrahim yayi farin ciki haka yayi ta hidima da Nene da cikinta.
Lokacin da Bashir ya fahimci Mahaifiyarshi Na da ciki sai yayi ta murna zai samu qani,domin yana da bala'in son yara
****
Wannan karon ma Allah ya sauki Nene Lafiya a dakinta in da raqara samun da Namiji ,malam Ibarqhim yayi farin ciki sosai da sosai ,ranar suna a ka sawa yaro suna Lawan,
Nene taci gaba da rainon yaranta cikin kulawa,Bashir yana kaunar Dan uwansa sosai ,in babu makaranta shi yakewe Nene raino Dan har makarqntar Allo ya kan tafi da Lawan
Allah sarki mai yadda yaso ,shekarar Lawan Uku a duniya Allah ya karbi ran Malama Ibarahim mutuwar da ta gigita Zukatan Al'uma sosai,Nene tasha kuka daga karshe sai ta danga ga Allah taci gaba da rainon yaranta.
*****
Bashir mutum ne Na jama'a baya zama ,sosai tunda ya kammala scondry skull yafara harkar Siyasa,
A daddafe ,ya tafi ,bayaro univasity dake kano ya samu difoloma ,sai ya watsar da karatun ya shiga siyasa gadan gadan
Tun Nene bata so ,daga baya sai ta dawo tana masa Addu'a.
Dan Uwanshi kuwa Lawan babu ruwanshi domin magana ma bata dameshi ba,
Shima a yanzu yana makarantar gaba da primary
Duk Abinda Bashir ya samu Na jama'a ne ,shayasa a kasa ka masa Bashir Mai jama'a
Ganin girma yazo masa ya
Sa Nene tayi masa maganar yayi Aure domin shine cikar mutum
Nan ya nuna mata shifa yanzu bashi da wata budurwa harkar Siyasar sa kawai yake
Nene tace to yaje yaga Zainab "yar gidan kawun shi wato Kanin Malam ibarahin tace taga yarinyar tana da hankali da nutsuwa
.yace to shikkenan zai je ya ganta
Ko da Bashir ya ga Zainab sai yaji ta kwanta masa,sabida haka ba'a dauki wani dogon lokaci ba a kasha shagali Amarya ta tare nan gidan kusa da Nene dake gida ne girman gaske ,haka Bashir ya yanki guri yayi ginin zamani sosai.
Yawan kyautarsa da tausayin talakawa yasa matasa da tsaffin yankin Nash suka tsayar dashi takarar Craman ,Aikuwa Abin ikon Allah lokacin zabe yana zuwa Bashir ya lashe yazabe.
Zoka ga murna gurin jama'ar gari ,da "yan Uwa da Abokan Arziqi jama'a sun ji dadi domin suna ganin Bashir zai kawo ci gaba a yankin nasu
Lokacin Zainab matarshi tana da tsohon ciki ,Haka tai ta taya mijinta murna,
Nena ma tayi farin ciki sosai tai tayi masa fatan Alkairi gami da Addu'a Allah ya tayashi riqo,ya sauke nauyi da ya dauko
Lawan ko dashi a kai ta fadi tashi ,bakinshi yaqi rufuwa ,Sai murna yake.
A taike dai Alh Bashir yariqe mukamai da dama ta fannin Siyasa in da daga baya yasaki harkar Siyasa yafada kasuwanci ,shida wani Abokinshi Alh Auwalu ,sosai suke shi go da motoci Iri daban daban Na zamani Cikin farashi mai sauqi
i ta iya da halinshi.
Tun yana yaro yake da mugun kyankyami Abu qalilan zai sashi yai ta kwara A mai
Nene tayi kewarsa sosai sabida sun shaqu da juna
Basu jima da komawa Abuja ba Hajiya Zainab tasamu ciki Alh Bashir yayi ta murna
Lokacin haihuwa yazo Allah ya sauke ta lafiya an samu da Namiji
Nene tace A sama jamelu
To haka rayuwa ta tafi Alh Bashir Arziqi yana kara bunkasa sosai da sosai
Yaranshi hudu biyu maza biyu mata
*wanene Aliyu*
yana da bakar zuciya da miskalnci sai kai mai mgn goma bai kula kaba sai yaga dama zai amsa daya yana da bala,in tsafta dan haka ba abincin kuwa yake ciba in kacire nenensa da ummi bai yadda ko ruwa masu aiki subashi ba indai bai daga hannu ummi ya fito ba duk da cewar ruwan roba ne
Yana mutukar san ya ga yazama soja tun yana yaro shiya sa yadage sai da yatafi yai karatu sosai akan aikin yanxu haka ya kammala aiki kawai yake jira ya fara,,,
To lawan ma akwai wata daya so anan bayan gidansu yarinyace mai sanyi hali kamar sa sunanta khadija ,,
Da nene ta fuskanta tace to baza ai jinkiri ba taje ta sami yayan mahaifinsu tace to aje a ne mar mai auranta ,,
Aikam ba,awani dau lokaci ba aka sha shagali bayan duk 6angare biyu sun amince amarya ta tare anan gidan kusa da nene tunda gida ne mai girman gaske bangare bangarene ,,
Idan baku mantaba dama mlm ibarahim mai arzikine a wannan yankin nasu a wancan lokacin gidansa ma abin kallo ne
Nene tana mutukar jin dadin zama da khadija sabida irin matan nan ne masu kirki da saukin kai babu ruwan ta da hayaniya haka shima lawan din yana jin dadin zama da ita ,,
Alh bashir kam yakanzo lokaci zuwa lokaci dashi da iyalinsa yakan dan jima kan yakuma abuja shiyasa yaran sukasa saba sosai musamman Ali mutumin nene tana bala,in sansa ,,shikam Ali bai san tanayi bah
Sai tahana kowa abu tace Ali zata bawa sai yazo tabashi yace bayaci ko ya kar6a ya bayar a gabanta ba yadda zata,yi takari mitarta ta gama yai mata banza ,,
To haka rayuwa taita tafiya lawan Allah bai bashi haihuwa da wuriba sai da sukai shekara sha uku da aure sannan Allah ya a zurta khadija da samun ciki,,
Nene taita murna dan a zuciyarta take cewa shine yagaji irn haihuwata dan har tana ganin ma ko bazai haihu bashi huumm ,,,,,nace nene ai abin na Allah
Tunda khadija tasamu ciki take faman shan wahala yau da lafiya gobe babu irin cikin nan ne mai bala,in laulayi ta ke dashi dan haka nene bata barinta tai komai a gidan. gashi nene ta d'au son duniya ta daurawa cikin abu kadan khadija zatai zatahau yi mata fada wai bata kula da kanta itadai sadai tai dariya kawai.
To da haka watan haihuwa ya kama ciwo matsawa khadija musamman ciwon kai da mara nene tace suta fi asibiti aikam da sukaje likitoci suka dubata sukace haihuwa da sauran kwanaki amma akan hanya take suka ce ta kula da daukar abu mai nauyi da yin aiki n wahala kuma tadaina cin gishiri dayawa idan da wata damuwa d tasa ranta ta cire,, nene tace ai dama bb wani aiki da take kawai larura ce irin ta masu ciki haka suka dawu gida bayan an bata magani kuma sukace yaron lafiyar sa lau
Kwana biyu da zuwansu cikin dare khadija ta tashi da ciwo haka lawan ya fito ya sanarwa nene
A gigice nene ta shiga bangarannasu ta tarar da khadija sai faman zubda jini ta ke gashi sai nishi take haihuwa taki zuwa da sauri nene taka mata ta rike tana tofa mata adu,oi sannan ta kalli lawan tace yai maza yaje yakarbo rubutun nakuda a gun malam yahaya wani makocinsun ne anan mai "yan makaran ta
Cikin a zama yatafi yana tafiya yana ado,a acikin ran,sa ganin irin wahalar d khadija take sha yana girmama irin wahalar da mata suke sha yayin haihuwa tunda duk a gabansa khadijan tafara nakudar,, a xuciyar sa yake fadin duk wanda bai bi iyayen sa ba yayi asara,,
To cikin hunkuncin ubangiji kan yadawu ma Allah ya sauki ta lafiya inda ta haifi diya mace ya dawu wa yai ya tarar nene sai hidmar gyara baby take baki ya washe yana nene me,akasamu ne?
Nene jikinta a sanyaye tace mace ce lawan bani rubutun daka kar6o ka kuma waje tukkun kafin a gyara gun,,mikamata yai shima jikin sa da dan sanyi ganin yanayin nene,,
Nene kam khadija ta dago tana bata rubutun ganin har yanzu mabiya bata fado ba gashi jini sai zuba yake sosai,,
Tayi duk dabarun irin na gida abin ya faskara ,,lawan takira tace maza yatafi ya samu mota suzu sutafi asibiti ,,da sauri yatafi gashi har an soma kirayekirayen sallar asubah ,,
Allahu Akabar kafin yadawu rai yayi halinsa kadija ta amsa kiran ubangiji
Wayyo duniya abar tsoro,,
Innalilahi wa ina,illahi raji,u shine abinda nene take ta fada
Wannan yarinya Allah yakar6i shadarki Allah yasa annabi yasan da zuwanki Allah ya kafartamiki shine abinda nene take ta maimaitawa,,
Tun a hanya lawan yaji gabansa yanata faduwa yacigaba da nana ta innalilahi a ransa sai yaji kamar anace masa ta mutu ay ,,,gabansa ya yanke y fadi da sauri ya shiga gida ,,sai yatarar da nene a tsaye da wasu mata biyu ,,
Yace nene ga mai motar nan ansamu ina khadijan ta ke yafada ya na kokarin shiga dakin nene ce ta rike hannunsa tace jeka sallami mai motar ai tasamu sauki ma ,,to yace jikinsa a sanyaye ya fita yana fita yaci karo da yayar khadija da maihaifiyarta da wasu daga cikin danginta ,,wasunsu nata hawaye ,,
Tsayawa yai kawai yana kalloansu sai yaji wata acikin su tana lawan ya hakurinmu ido ya bita dashi kawai ya sallami mai motar yajuya shiga gidan ,,
Kai tsaye dakin da khadijanta ke ya sa kai yana so ya tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiye mai,,
.
Bb wanda ya hanashi shiga har nene ,,yana shiga yadaga zanin da nene ta rufe khadija da shi yatsaya y na kallonta ,,a ransa yana ta nanata innalilahi wa innalahi raju,u ,,sai yaji wata dauriya tazo masa ya tsuguna a gefe daya ya fara yimata karatu yana ta nai man mata gafara a gun buwayi gagara misali,,
Ya ji ma a gun a zaune babu wanda yashiga dakin ,,dakansa yatashi ya fito ganin gari ya soma washewa yaje ya dauro al wala yai sallah,,
To haka rayuwa take dama haka akaima khadija suttura a kaita gidanta na gaskiya,,,,,
Haka lawan yaci gaba da karbar gaisuwa gurin "yan uwa da abokan ar ziki""
Alh, bashir shida iyalinsa sun jima kan sukoma abuja ,,,,ganin yadda hankalin nene ya tashi a wancan lokaci ya zauna yadinga rarrashin kanin nasa da ita kanta nene n,,,
To yarinya dai nene tace amayar mata da sunan maihaifiyarta ,,wanda nene tadauki son duniya ta daura mata bata san ko tsinke ya sauka a kanta,, ita tasama ta dije wai tunda sunan maihaifiyarta ne da ita ,,Alh bashir ba yadda vaiyi da nene tabashi baby sutafi da,ita tunda a lokacin hjy zainab tana da karamin goyo ta hada ta shayar dasu tare ,,amma nene ta ke kashe tace bata yadda ba a kyaleta a gunta ita zata kula da ita ,,haka suka je asibiti a ka daura baby n da irin madarar da yakamata a bata,,
Sai da ya tabbatar komai ya kammala sannan suka tafi bayan yadada kwantarwa da kanin nasa hankali ganin yadda kanin nasa ya koma lokaci qan kani,,,,,
Duk wnn abin da yafaru Ali bayanan yanaca london karatu sai dai waya yaji komai shima yaji mutuwar auntynsa ,,sabida yana mutukar kaunarta ,,
Haka kawai Allah y hada jininsa da ita ,,a rayuwarsa yana san yaga mutum mai tsabata wanda yasan meye rayuwa ya san abinda yake,,,
To khadija duk tana da wnn halin
Haka yai mata adu,a acan ,amma yaji mutuwar sosai
To nene haka taciga da rainan dije tana bata kulawa yadda ya kamata ,,tai bala,in shagwabata batasan Bacin ranta ,,duk abinda tayi daidai ne a gunta gashi zataje tai tsokana amma in aka doke ta tace anci zalin mairaniya ko makaranta dije batasan zuwa saitace wai dukan ta,ake ita ko nene sai tace tai zamanta,,,
Lawan har yagaji ya zuba musu ido dan baya iyawa da bala,in nene in dai akan dije ne,,,
Allah sarki rayuwa shekarar dije hudu Allah ya karbi ran lawan ,,ranar wata juma,a da dadddare ciwon ciki farat daya,,
Wannan mutuwa ta lawan ta gigita Alh bashir da nene ,,to ya za,ai haka duniya take dama,,
Dije tazama marainiya gaba da baya bbu maihaifa ,,
Nene kuwa tace ,,yan nan bazakiyi maraici ba indai ina raye,,
To ko da Alh bashir yazo bayan an share makoki bayyada bayi da nene ba akan tazo su tafi can abuja n amma nene tace bata zuwa haka yahukara ya kyale ta suka tafi sai dai duk wani abu na more rayuwa yana siyar mata ya a ajiemata kan yatafi shiyasa bata da matsalar komai na rayuwa ,,sai dai lokaci zuwa lokaci yan kazo ya ganta ko yaran su zu hutu ,,
Acikin wanan lokacin Ali ya dira a gidan bayan ya kammala karatun sa yadawo gida,
baya na ciki ba yaushe ya fita"? nene tafada cikin mamaki
Tace" yanxu mana naganshi zai fita bayan nadawo daga gidansu sa,a
Nene. Tace" to ai ni banga fitarshi ba inanan ina fama da aiki"
Zumbura baki dija tayi tace" wallahi nene bakiji yadda hannuna yake zogi ba Wallahi Allah ya isana bazan taba yafewa hakafa dazu dayaje makaranta yasa aka zane ni wai ni mai nai mai ya tsaneni tafada cikin kuka
Kallonta nene tayi tace" bai tsaneki ba dija ai dan uwanki ne kawai halinki ne baya so wanda nima fada nake miki akansa"
Sake turo baki tayi tace "to ai ni ba kulashi nake ba haka kawai sai yadinga cemin kazama "
Dariya nene tayi tace "ai sai kiyi Halin Ali ai sai shi kowa haka yake kiranshin bake ba"
Wucewa tayi tasa mu guri tazauna idonta sunyi ja sabida kukan da ta ci acikin ranta kuwa tayiwa Ali Allah ya isa yafi dubu
To Ali daya fita ma bai samu serve's din dayake nema ba kasancewar garin akwai hadari shiyasa zafin yai yawa
Zamansa yayi sai da yaji amfara kiran sannan ya mik'e tare da barin gurin.
Gidan ya shiga kai tsaye inda botocin Alwala suke ya nufa daya ya dauko ya soma daura alwala
Nene ce dake cikin kichin ta kai kallonta inda yake tace "wai inakaje ai nadauka kana daki ai danaji kace ka gaji "
Shiru yai sai data kuma maimaitawa sannan yace" ina waje ina dan shan iska yafada ya kokarin barin gidan gannin har wasu massallatai sun so ma tayar da sallah shikam ai baya bari jam,i ya shigeshi Ali a kwai riko da addini,,
Dija ce itama ta tashi ta yazo ta dau bota taje takama ruwa tazo tai tata alwalar
Domin rai nan Nene ce
Nene kam akwai riko da addini
Bai dawo gidan ba gidan ba sai da ya tsaya
Ya jira isha tayi ya gabatar da ita sannan .
Wata katuwar tabarma Nene ta shinfida kamar dai jiya a tsakar gidan tana zaune itama tana Jan carbi gefenta dija CE a kwance bacci yana son kamata
Neman guri yayi kusa da nene ya zauna hade da ciro wayarsa daga aljihu ya hau latse,latsensa da,ita
Nene kam ganin dija tana son yin bacci gashi bata ci abinci ba ,sai ta hau yin gyaran murya!! a nufinta tanayiwa dija a lama da ta tashi ta ci abinci
So take ta karasa jan carbin ta bata so ta katse tunda ta kusa kammalawa
Dija kam ai batasn tanayi ba bacci har ya kwasheta,,
Ali ta kalla tai mai alama!!da hannuta cewar ya tashe ta ,,
Sarai ya fahimchi mai take nufi sai ya nuna kamar bai fahimta ba ya share kawai yana dan ya mutsa fuskarsa ya cigaba da abinda yake
Haka nene ta hakura har saida ta idar sannan tace "kana ganin ta tai bacci mai makon ka tashe ta "
Kallonta yayi da fuska a ya mutse ya ce "kina nufin wai in tashe ta ta zageni yarinyar da bata da kunya ta Riga ta raina mutane"
Nene tace "kai kam ai halinka sai kai haka kawai sai tahau zaginka akan katasheta daga bacci?
Don Allah kacanja hali Ali" tafada tana mikewa
Kichin ta nufa ta fara debo kulolin abinci.
Tana fadin ai "yau mutumin ka nai towan Alkama ne da miyar kubewa" tafada tana murmushi domin tasan yana son towan mussaman in nata ne
Ai kam sakin murmushi yayi ya ce "amma kin birgeni uwargida yau inayi dake" yafa da da murmushi akan fuskarsa
Dariya nene tayi tace "d'an nema ai ko ka ki ko kaso nice dai takarfen duk wacce za tazo sai dai ta biyo bayana" tafada tana kokarin zu ba masa abincin.
Wani iri kamshine yake tashi tunda tafara zubamai abincin, wata miya ce ta daji nama sosai da man shanu sai kamshi yake towan ko a mulmuleshi a leda abin gwanin sha,awa,,
Shima Ali gyara zama yai dan tunda tafa ra zuba mai miyansa yake faman tsinkewa jawo flet din da ta zuba mai yayi yai bissimillah y faraci. Hummm nene badai iya girki ba yafada a cikin ransa
Nene kam dija tau tashi domin taji abincin itama,, tashi tayi zaune nene tace kinsan banasan ki kwanta baki ci abinci ba gaki da shegen magagi kan ki wartsakema aiki ne tafa da tana tura mata flet din abincin bayan ta zubamata,,
Ali kam kallon ikon Allah ya tsaya yana yi ganin dija tana kokarin jawu plate din ta fara ci batare da taje ta wanke bakinta a ganinsa ya kama ta ta wanke bakin ta in ba kazanta ba
Tana kokarin tura towan bakinta yaji zuciyarshi tana faman tashi dan shi kam abu kadan sai ya sashi jin tashin zuciya.
Cikin wata irin tsawa yace "ke! dan ubanki tashi kije ki wanke baki wawuyar yarinya kawai inbanda kazanta kiyi bacci kitashi kidau abu kisa abakinki sabuda rashin hankali" yafada yana ya mutse fuskarsa
Itakam Nene bata lura bama sai da yayi magana sannan takai dubanta inda dijan take zaune
tace "ai shiyasa banasan tafara bacci sabida tana da magagi yanzu da a haka zaki ci abinci"? ta fada tana rike baki!
Ita kam dija zumbura baki tayi tace "nifa banyi bacci ba duk abinda kuke ina jinku"
nene tace "tashi dallah kije ki daurayo bakinki waye yake miki karya anan kin kwanta kinayin magari ba ko isha bakiyi ba kice ba bacci kike ba,,
Tashi tai tana faman kunkuni a ranta itafa an ta kura mata ko ina ruwan mutum da,ita oho ita har ga Allah bata ji wani canji abakinta ba ganin ba wani baccin kirki tayi ba ,,daza,ace ta wani wanke baki ta to bakin wa ye ai nata ne tafada cikin kunkuni
Nene tace "au!! surutai kike dan anfada miki gaskiya in banda ke dija ai ke kanki sai kinfin jin dadin cin abinci in kika kuskure bakinki"
Cikin sauri dija