Showing 9001 words to 12000 words out of 45410 words
kuma bijirewa mai dan taka mata birkin Xahra ce tunda tanada xafin rai, takan iya xuwa har gaban Ammi ta bubbugeta
Bayansu Bature sun dawo daga Abroad ne yasa kafar wando daya da Ma'u duk ranar dunia sai sun sha dramar duk wadda tama laifi can yake kai kararta, shiko Bature ya mata hunkuci na fitan rai
Amma duk baxai hanata gobe ta kara wani laifin ba, sai suka xama kaman Tom and jerry alkhairi baya hadasu
Bature ya samu aikin soja inda ya fara aiki a nan Kaduna
Shi kuma Balarabe Companynsu yake aiki daga baya kuma ya koma companynsu na Lagos
Soyayya Balarabe ya fara da Jidda har kowa ya sani, manya suka xauna aka tattauna inda Ummi ta kawo xancen Bature da Zahra wadda Sam bbu so a tsakaninsu
Nsuyin Ummi Bature yaji ya amince da auren Zahra
Biki akayi naxo a gani a fada don Ummi ce ta tsara komai ita da 'yan uwanta iyayen son a shina
Auren bai jimaba akama Bature transfer xuwa Abuja
Bayan shekara daya da watanni da auren Jidda ta haihu ta sami diya mace aka sa mata sunan Ummi ana kiranta da Amal
Yanxu ta dawo goyon gida Balarabe ma ya dawo sai ta gama su koma
Shiko Bature yaxo wani aiki Zaria ne yasa Zahra biyosa ta wuce Kaduna
Cigaban Labari
Washegari duk manyan Gidan Bature sun hallara a palon Abba, Bature na kawai baya nan kuma shi ake jira
Da sallama ya shigo kowa ya amsa masa banda Mami data bishi da harara
Gaisuwa ya kwasa ya samu waje kusa da Balarabe ya xauna
Kasa-kasa cikin xolaya Balarabe yace
" da banga Zahra ba anan da sai nace network ne ya rikeka"
Harara Bature ya watsa masa yace
" ce maka akayi ni kaine Angon karni"
Har Balarabe ya bude baki xaiyi raddi sallamar da Abba yayine ya hanasa
Cikin natsuwa Abba ya bayyana masu shawarar da Jidda ta kawo
Abba na iddawa Mami tayi sauri tace
" kinci gidanku Jidda wannan wani irin banxan shawarace, sai yau na gane bakida digon tausayi, anan dake Muke ganin yadda Bature ke lahanta Ma'u kamar wata 'yar ta'adda Sam baya raga mata, don so kike yaje ya kasheta sai kice a bashi ita yaje ya karasata koh, to nikam ban yarda da gurguwar shawarar nan ba, dama dama da kune yawwa"
Ummi datayi na'am da shawarar Jidda tace
" tab ai Ma'u tafi karfinsu, daidainta su Baturene, kawai suje can ya dinga sauke mata allurar sojoji ko xata natsu"
" wlh gaskiar Ummi ce Ma'u tafi karfinmu sai su Ya Bature"
Cewar Jidda tana marairaice fuska
Kara hasala Mami tayi
" to bbu inda xata uwar son a shina, Balarabe kai tattari matarka Ku koma ta barmu inda ta samemu"
Mami ta karashe maganar tana duban Balarabe
Murya Abbu ya gyara yace
" Nidai banason fada akan rashin gaskia in-law, duk nan bbu wadda yaki shawarar nan sai ke, hakuri kawai xakiyi Bature ya tafi da Ma'u don sama mata ingancecciyar rayuwa"
Ganin kowa ya amince da tafia da Ma'un yasa Mami ba don tasoba ta sallama
Zahra ce ta rufe taro da addu'a
Mami ta riga kowa tashi ta fice tana mitar an hade mata kai
Batool da Shukrah tareda da driver ke tsaye a parking space
Sunata mishi magiya ya kaisu makaranta xasuyi Latin don Ma'u tace baxataje ba kafarta na ciwo
" don Allah Ku taimaka kuje ku jawota sai mu tafi, ranar ai a idonku oga Bature yamin gargadin duk ranarda na kaiku makaranta ba tareda Ma'u ba to na sallami kaina da kaina"
Cewar Isa drive yana kokarin xama kan mota
Kamar Shukrah xatayi kuka tace" don Allah ka taimaka mana, ai baxai San bataje ba tunda yanxu xai koma Zaria ma"
Kai idi ya girgixa yace
"Ina sam baxai yiyu ba wannan kasada ne, idan kuma bai komaba fah? Kinga tawa ta kare"
Xama Batool tayi kan resting chairs wajen ta tabe baki tace
" shikenan sai mu dawwama anan amma bbu inda xani wai kiran wata Ma'u "
Kuka Shukrah tasa ya nufi cikin.gida
Karaf ta hadu da Bature tareda Balarabe a hanya
Saura kiris tayi fitsari ganinsu a gabanta duk da batada laifi tasan sai ta sami rabonta gun Bature
Aikuwa wani mahaukacin tsawa ya daka mata, sanda Balarabe ya toshe kunnenshi
" Uban me kike a wannan lokacin baki tafi school ba
Shukrah uwar tsoro take jikinta ya dau rawa cikin rawar baki tace
"Ma....Ma.....Ma....." Sam tsoro ya hanata karasawa
Balarabe ya janyota jikinshi yace
" cool ur heart, ki fada masa meya faru ko yanxu ya tattaka ki"
Harara Bature ya jefawa Balarabe da Shukrah, yana jira su bata masa lokaci dau hukunci
Dakyar Shukrah ta samawa kanta natsuwa tace
"Ma'u muke jira kuma taki fitowa wai wai wai baxata ba kuma....."
Katseta Bature yayi ta hanyar cewa
" ina Ma'u take?"
"Tana part din Mami"
Shukrah ta fada tana kara shigewa jikin Balarabe gudun kada Bature ya bugeta don yadda taga ya hasala yana iya bugetan
"Jeki kicewa Isa ya kaiku injini"
Bature yace yayinda ya juya ya nufi part din Mami
Har parking Space Balarabe ya kai Shukrah , sanda yaga Isa Ya fice daga Gidan kan ya nufi part dinshi
Ur
Votes
Comment
Are needed
Ummu Subay'aβ₯
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: ππ GIDAN BATURE ππ
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
Harufai sunyi kadan su kwatanta yadda kike a wajena, sai dai nadan sakura kadan na bayyana matsayinki a wajena
Kinfi Aminiya
Kinfi 'yar uwa
Kinfi kawa
Keta dabance a wajena BATUL ADAM JATTKO
Fatana Allah ya kara miki lfy, daukaka, basira, fikrah, da kuma hikma
Allah ya biya miki dukkan bukatunki na alkhairi, ya sadaki da masoyanki ta ko'ina, ya kuma rabaki da makiyanki
Allah ya baki nisan kwana mai albarka da amfani
Allah ya shirya miki xuri'arki ya dorasu akan tafarki madaidaiciya
Allah yabar xumuncinmu daga nan har a Aljannah
Ke Tawace BATUL
I heart uβ₯
0β£4β£
Tunda Ma'u ta farka daga bacci cinyoyinta ke mugun mata ciwo, bata isa ta xauna ko ta tashi ba sai taji a jikinta, Sallah Asuba ma a xaune tayi, taba iddarwa ta koma bed taja blanket taci gaba da baccinta sau uku Batool na xuwa ta tadata akan ta tashi ta shirya su tafi skul sai tayi kamar xata tashi Batool na fita sai ta koma taci gaba da baccinta
Koda Mami taxo ta ganta bata tada itaba don tasan ba abu mai yiyuwa bane taje makaranta yau,
Kintsawa Mami tayi ta fice falo donyin break fast
A hasale Bature ya shigo Falon kamar xai kife don sauri, ko inda Mami take ba duba ba don yasan xata iya hanashi xantar da hukunci da yayi niya
Aikuwa bai tsiraba don yana kama handle na bedroom dinta tayi hanxarin cewa
" kul kul, kada ka yadda ka shegemin bedroom, ka tattara kaje can NDA ka saukar da fushinka don su suke bida mukam anan bama bida, inba rashin tausayiba jiya ka gama nakasa mata kafa yau kuma kana expecting xata iya mikewa har taje makanranta aljana ka maidata ko mayya, maxa bacemin daga part, ka bari sai masu son kaita kabari sun danka maka ita sai kai yadda kakeso da ita amma ba a gaban Fateema ba"
Ta karashe maganar tana masa mugun kallo
Hannusa Bature ya janye akan handle na kofar ya dorasu akan sumarsa ya wargaxa sumarsan dayasha gyara ssai
Cikin murya bacin rai yace
"Wlh Mami keda Ammi Ku kuka bata Ma'u, take duk iskancin nan, wani punishment na mata wadda har xai nakasa mata kafa ta gaxa tafia School (kujimin Bature fah), Allah idan da Jidda bata kawo shawarar nan ba idan har ta girma akan yadda kuke tafiar da ita mai aurenta ma sai an rasa, idan kuwa ansamu ya aureta a rashin sanin halayenta to baxai iya xama da itaba"
Baki galala Mami ta bude tana duban Bature daga bisani tace
"Har kura xai cewa kare maye, kaima da murdadden halinka ka samu wadda ta aureka balle Ma'u, ai ni kullum jinjinawa Zahra nake da ta iya xama dakai"
Daria Jidda data shigo yanxu tasa tace
"Ikon Allah kedai Mami duk wadda yace bayayin Ma'u to duk kyaunshi mummunane"
" yawwa jira nake kixo ki sameni, Jidda idan har Bature ya nakasamin diya kema sai na nakasa don xan biki har Lagos na miki yadda ya mata tunda kin iya kawo gurguwar shawara, kuma idan.Ammi tasan ke kika kulla wannan munafurcin kin daina kallon hakorarta"
Cewar Mami tana kokarin mikewa daga dinning space don komawa bedroom
Shigewarta tayi bedroom tana binsu da harara yayinda Jidda ke daria kasa kasa shi kuwa Bature hada fuska yayi cif kamar hadari
Juyawa yayi ya dubi Jidda yace
"Bbu wani wayo daxa'a ma Ammi ko Ma'u, ki hadamin kayan tsaf xuwa, gobe da safe xamu wuce Abujan da ita"
Ba jira jin "toh" da Jidda taceba yayi ficewarsa
Yadda Bature yace haka Jidda ta aikata tas kayan Ma'u dake dakin Mami ta kwashe tasa a trolley, wadda xatasa ranar ne ta ajje mata a gefen bed
Daga bisani kuma ta nufi part din Ammi cikin sa'a bata sami Ammin ba suntafi gaisuwa itada Ummi makobtansu, nan take Jidda ta dibo kayan Ma'u ta hada tsaf ta ajje a bedroom dinta
Wani irin mika Ma'u tayi hade da salati ta bude idanunta ta xuba akan wall-clock dake manne a bangon dakin Mami, 12:37 ne agogon ya nuna mata dakyar ta mike ta watsa ruwa hadi da Alwala, murmushi tayi ganin kayanta akan gado tace
"Mami ce kawai masoyiyata a Gidan nan"
Azatonta Mamince ta fito mata da kayan da xata saka
Bayan ta iddar da Sallah ta, ta fito falo tana dingisa, baki ta tabe ganin Jidda na xaune a falon tana kallon Tauraruwa Tv
Xama tayi a kujerar dake fuskantar Jiddan kamar dole akasata tana duban Tv tace
"Ina kwana Anty"
Harara Jidda ta sakar mata tace
"Rike gaisuwar gadararki banaso"
Baki MA'U ta tabe tace
"Allah ma yasan na gaidaki kan yanxu kice ko gaidaki banyi ba asamu hujjan dukana yau"
Ringing wayar Jiddace dake kan dinning table ya hana Jidda fadar abunda tayi niya tace
"Ma'u mikomin wayata dake ringing"
Sarai Ma'u tasan wayar nakan dinning amma don Jan magana tace
"A'ina wayar take"
"Ban saniba, idan kika kuskura wayar nan ta tsinke baki daukomin ba wallahi kinji na rantse bbu abunda xai hanani kaiki gun Ya Bature ya miki hukuncin dayafi na jiya"
Mikewa Ma'u tayi ta nufi dinning table din tana Dingisawa, tana kaiwa dinning area wayar ta tsinke
Gunaguni Ma'u tafarayi
"Me amfanin badi bbu rai, idan za'ayi ayi idan baxa'ayiba a bari"
Kawai sai Ma'u tasa hannu ta ture wayar, ta fadi akan tiles, take palon ya daukarar fashewar wayar
Ido kawai Jidda ta xubawa Ma'u dake tsaye tana gyara daurin dankwalinta kamar ba ita ta aikata wannan ta'asar ba
Hawayene ya fara gangara a idon Jidda don tsabar takaici ta rasa wani irin hukunci xata ma Ma'u
Cikin bacin rai Jidda tace"
Wato barama na fasa wayar kome xai faru ya faru, wlh Ma'u kanki sami hawan jini sai na saka miki"
Tashi Jidda tayi gadan gadan ta nufo Ma'u
Kan ta iso tuni Ma'u ta xabga wani mahaukacin kara, dayayi sanadiyar karasowar Ammi da.gudu wadda take shigowa part din don daukar Ma'u su koma part dinsu, taji kewarya ssai
Mami dake kitchen ma tayi saurin fitowa ganin Ammine yasata koma kitchen din
Har Jidda takai hannu xata mangare Ma'u
Ammi ta daka mata tsawa
" kada ki kuskura ki tabata, muddin kika tabata ran kowa xai baci a gidan nan"
Bbu shiri Jidda ta dauke hannunta daga kudirinta na mangarin Ma'u tsab tasan idan ta aikata Ammi xata iya abunda tace
Don akwai ranarda hakan ta faru ta hana Zahra dukan Ma'u, Zahra ta daketa wuni Ammi tayi bataci abinciba sai kuka take tanace anacin amanar marainiyar Allah, ta dagawa kowa hankali, taki sauraron kowa harda su Abba, Ma'u kam nacan tana bushashanta kamar ba akanta ake takkadama ba, sanda Abba ya tara su gaban Ammi ya musu wankin babban bargo kuma yace Zahra taje ta nemi yafiyar Ammi, koda Zahra taje nemar yafiyar budar bakin Ammin wai sai dai taje ta nema gun Ma'u (kujimin rigima), farko Zahra taki xuwa gun Ma'u sanda Abbu ya tsawatar mata kan taje ta nemi yafiyar Ma'u itako Ma'u hadda hararar Zahra kan tace ta yafe kuma kada ta kuma dukanta(impossible inji Bature)
Durkusawa Jidda tayi ta dau wayarta da fuskar tayi kaca-kaca ta shige bedroom dinta tana musu murmushin mugunta tasan gobe insha Allah iwar haka Ma'u ta xama 'yar gida a Gidan Ya Bature
Matsawa Ammi tayi kusada Ma'u data dauke kai ganin Ammin
"Zo mu koma part dinmu tun kan su kashemin kai"
Takai hannu tana kokarin kama hannun Ma'u, ja da baya Ma'u tayi tana tura bakinta tace
"Bbu inda xani dake ai jiya dake aka hada baki aka raunatamin kafa aka kuma kumbura min jiki, saboda shi Mugun dan lelenkine"
Cikin rarrashi Ammi tace
"Haba takwarata kiyi hakuri mana wlh babu bakina a ciki"
Bbu yadda Ammi bata rarrashi Ma'u dayaxo su koma part dinsu amma Ma'u ta tsaya kai da fata bbu inda xata
Haushine ya kama Ammi tace
"Idan kikaga dama ki dawwama anan, mai shegen taurin kan tsiya, idan sunga dama suyi pepper soup din namanki ma Wala ko yali am (bbu abunda ya dameni, kuma kada na kara ganin kafafuwarki a part na"
Daria Zahra tasa wadda tun daxun ta shigo da Amal a hannunta tayi bacci xata kaita gun Jidda ta kwantar da ita, ta tsaya tana jinsu tana shan daria kasa kasa sai yanxu ta fitar
Ta gefen Zahra Ammi ta wuce ta fice daga falon tana mita
Ma'u kuma ta koma taci gaba da kallonta hankali kwance
Zahra ta wuce Bedroom din Jidda tana dariar dramar Ammi da Ma'u duk da ba yau suka saba ganiba
Masu bidar daga farko mafi sauki kuje wattpad@ UmmuSubaya
Ummu Subay'aβ€
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: ππ GIDAN BATURE ππ
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
π KAINUWA WRITERS ASSOCIATEπ€π»
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
0β£5β£
Washegari tun karfe 6 Bature da Zahra suka gama shiryawa dasheka Bature a Kaduna ya kwana
Suna tsaye a parking space Bature ya kira Jidda a waya ta kawo mishi kayan Ma'u kuma ta tabbatar masa Ma'u na bedroom na Mami tana kwance ita kadai
Hade fuska Bature yayi kamar hadari
Balarabe yasa daria yace
"Man duk wannan hada fuskar duk na Ma'u kamar mai xuwa sambisa tunkarar Shekau, lalle Ma'u ta cika boss"
Duk sukasa daria banda Bature daya nufi part din Mami
Zahra dake saka handbag dinta cikin mota tace
"Ai ta'addancin Ma'u yafi na shekau"
Jidda data lafe jikin Balarabe tace
"Wlh har tsoro take bani, bbu hali ta bayyana a waje bomb bai tashiba, idan kunason xama cikin sauki da ita sai Ya Bature ya xama Buratai ke kuma kin xama Kukasheka"
Daria suka sake sawa Balarabe yace
"Muma xasu barmu da wata Shekau din ai, idan Ammi ta farga bbu Ma'unta ai sai ta dagawa kowa hankali musamman idan taji Baturene yayi awon gaba da ita"
"Idan xata daga mana hankalin ban muma mu tattara mu koma yau"
Cewar Jidda tare da dagawa Balarabe jera daya
Kasa yayi da murya don kada Zahra taji mexai ce yace
"Da hakan xai faru dana more, nayi missing na komai.ssai"
Murmushi Zahra tayi data gama jin komai ta xauna a kujerar dake wajen
Baccinta take mai dadi don ta gama sakankancewa Bature ya kama hanyar Abuja batada wani fargaba
Tsayawa akanta yayi yana kare mata kallon tun daga gashin kanta daya barbaxu ya rufe mata fuska har tafin kafanta, short night gown ne a jikinta iya gwiwa yabi jikinta ssai
Hips natane ya janyo hankalinshi kan kallonta wani abu yaji yana masa yawo a xuciarsa
Kawar da fuskarsa yayi ya kori shedan hadda cewa
"Yar Ma'un nan idan ba shedan ba me mutum xai kalla a jikinta(hmmm Bature kenan)"
Kusan 2minutes yana tuna yadda xai tadata, murmushin mugunta ya saki daya tuna favorite tadata dayake lokacinda take primary idan taki xuwan school ta koma bacci
Fridge ya nufa ya ciro gorar ruwa mai tsanyi har ya fara kankara ya bude gorar watsa mata a fuska
A birkice Ma'u ta tashi xaune tana tattare gashinta don taga wadda yayi mata wannan aika aika ta maida mai martani yanxu basai anjima ba
Kara firgicewa tayi ganin Bature na tsaye akan fuskarnan tashi a daure tam wani mugun miyau ta hadewa ta fara magiya
"Wlh yanxu xan tafi school, Allah kuwa yanxu xan......."
"Up that ur dirty mouth and dress up"
Hurga mata hijab na Mami daya dauka a gefen bed din yayi
Jiki na rawa Ma'u ta sanya hijab din
"Follow up"
Bature ya fada a dakile bbu wasa ya bude kofar bedroom din ya fice
Sauri sauri gudu gudu Ma'u ta shiga bin Bature
Daria Su Jidda suka sa time da suka hangi Ma'u da Bature
Jidda tace
"Don Allah dubeta kamar ba itace ke wadan nan abubuwanba"
Zahra ta mike daga xaman datayi tace
"Tom and jerry xanje nasha kallon movie"
Rumgumar juna Jidda da Zahra sukai suna sallamar juna Jidda tace
"Insha Allah next month xaki ganni"
"Yasha'ullah"
Cewar Zahra ta janye jikinta daga na Jidda
Hakama Bature da Balarabe suka rumgume juna Balarabe