Showing 18001 words to 21000 words out of 45410 words

Chapter 7 - GIDAN BATURE Complete

13 Jul 2025

3481

Bayan Hisham Abdallah yayi yace

"Nidai nagani inaso wlh kuma duk yadda take xan xauna da ita macece ai lankwasata bbu wuya"

Wani dariar Zahra tasa tace

"Badai Ma'u da shegen taurin kantan nan ba, kai dai xakaji jiki mukam namu sannu ne"

"Kinga Zahra banason renin sense, nan gaba kadan Antynki ce Ma'u"

Abdallah yayi maganar yana dan hade rai

Baki Zahra ta kama tace

"Ikon God sai looking, Ma'u ce Antyn nawa"




Harara Jidda ta watsawa Ma'u data shigo dakin

"Sai yanxu kikaga damar xuwa jin kiran nawa?"

"Ni bbu abunda naji sai yanxu"

Cewar Ma'u tana tuttura bakinta daya xama mata jiki

Handle na kofar toilet Jidda ta rike tace

" dauki Amal kije da ita ki riketa"

Tana fada tayi shigewarta Toilet yayinda Ma'u taje ta dau Amal ta mata rikon ko in kula

Kuka Amal tasa don kanta na rinto

Daga cikin toilet Jidda tace

"Wlh Ma'u idan kika yarmin da diyata xan sassaba miki"

Xarewa Amal ido Ma'u tayi

"Kimin shiru ko na yaddake a kasa don uwarki, anajin kukanki hadda min kashedi, gaki diyar gold shegiya mai kama da ubanta"


Gyara rikon da ta mata tayi ta fice falo

Kai tsaye cinyar Zahra ta dire Amal

"Gashi inji Anty Jidda wai ki riketa kan ta fito"

Xama tayi kusa da Zahra, ganin wani irin kallon da Abdallah ke matane yasata shagwabe fuska tace


"Ya Abdallah kallon nan yayi yawa kona maka kama da budurwarkace"


"Ai ba kama bane kece Budurwar tawa"

Baki Ma'u ta tabe taci gaba da kallon datake

Hisham ya mikawa Zahra ledojin da suka shigo dasu yace


"Zahra ga tsaraba"

Karbar Ledojin Zahra tayi ta musu godia

9 dai dai suka watse a falon har Ma'u tayi bacci, Jidda ta tasheta ta shiga bedroom

A gigin bacci Ma'u ta haura bedroom din Bature tayi kwanciyarta

Sai 10 Bature suka dawo, Balarabe ya shige bedroom dinsu da Jidda yayinda Bature ya shige Bedroom dinsa

Murmushi yayi dayaga mutum kwance kan bed dinsa, duk xatonsa Zahra ce don bayason ya dinga binta bedroom dinta, itako ragwanci ne ke sata kwanciya a Bedroom dinta

Sanda ya shirya tsaf ya kashe wutar dakin ya hau kan bed din


Tun kan kamshi yaji akwai banbanci don ita Zahra bata amfani da Humra, Ma'u ko wanka da Humra Falmata ta mata

Bai damu da banbancin daya keji ba don yasan bbu wadda xata xo dakinsa sai Zahrarsa

Ssai yakai kaimi wajen aikawa Ma'u sakonni masu rikitarwa

Cikin bacci Ma'u ta dinga jin wani bakon yanayi, ssai ta bude tana karbar sakonnin don duk xatonta mafarkine sai nishi take tana sauke numfashi a hankali

Bature kam ya rikirkice don bai taba jin irin haka daga Zahra ba



Tsaki Zahra taja don mugun felling takeji sanadiyar Fura da Nonon datasha daxun, kuma tun daxun taji shigowar Bature amma yaki yaxo gareta


Saukowa daga bed tayi tana mita

" jarabar Sweety ya rabe nima"

Kai tsaye bedroom din Bature ta nufa

Ummu Subay'a❀
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: πŸ›πŸ› GIDAN BATURE πŸ›πŸ›
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🀝🏻

Kuna Raina
Batool Adam Jattko
Ummi ontop
Maryam Paki
Mrs Adam
Maman Rufaida
Anty Fauxy
Zainab Goni
Mrs Mansoor

Da duk writer's na KAINUWA
Da fatan anyi Sallah lfy


Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE

1⃣0⃣

Mtssssssssssw

Bature yaja dogon tsakin jin ana bugun kofar dakinsa, gashi saura kadan ya fada Duniar Ma'aurata wakeson kawo mishi cikas

Jin bugun na kara tsananta yasashi mikewa akan Ma'u ya dau jallabiyarsa ya nufi bakin kofar a harxuke

Ma'u ko tanata sharar baccinta kojin bugun ma batayiba don tanada nauyin bacci

"Wayene?"
Bature ya tambaya cikin baccin rai

Shan jinin jikinta Zahra tayi, dagajin muryansa yayi fushi da ita na xuwa dakinta ta kwanta bayan yasha mata korafin bayason ya dinga binta dakinta

Cikin sanyin murya tace

"Sweety nice"

Tashin hankali

A raxane Bature ya xaro blue eyes dinshi, idan dai ba karya kunnensa ya masa ba kamar muryan Zahra yaji


"Ke wace"

Yayi tamvayar in unbelievable voice

Murmushi Zahra tayi kasa kasa tace

"Kajimin Mutumin nan da rainin sense"

Ta dora murya a dage

"Zahra ce"

"Zahra"

Ya maimaita cike da mamaki

"Idan Zahra ce a waje wacece a ciki?"

Ya tambayi kansa

Hannu yasa ya kunna wutar dakin, ya kai dubansa kan bed

Da Ma'u yayi toxali tana kwance naked don ya rabata da komai na jikinta

Kawar da kansa gefe yayi cike da tsoro

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"

Kawai yaketa maimaitawa

"Tayaya akayi Ma'u taxo dakinsa har kan gadonsa? Akwai banbanci tsakanin Ma'u da Zahra meyasa dayake neman natsuwa da ita bai fahimta ba?"

"Pls Honey kayi hakuri baxan sake ba kullum xan dinga xuwa dakinka"

Muryan Zahra ya katseshi

"Kada ki yadda na fito na sameki a wajen, idan kina son kanki da lfy ki gaggauta barin bakin kofar nan"

Yayi maganar cike da bacin rai don duk ita ta jaxamishi komai, idan da tana kwanciya a dakinsa ai Ma'u xata tarar da ita da hakan bai faruba, idan badon Allah ya kiyaye ita Zahrar taxo ba ai sai mai afkuwa ta afku


Kamar walkiya Zahra tabar kofar dakin don tasan waye Baturen


Kusan 8 minutes Bature na tsaye bakin kofar yana nemawa kansa mafita

Komawa kan bed din yayi ya maidawa Ma'u kayanta, a hankali ya dagata kamar 'yar tsana yana Allah Allah Kada ta tashi ko ya gamu da wani a hanyar kaita dakin ta


Cikin Sa'a ya kaita har ya dawo bata tashiba bai kuma hadu da kowa ba


"Alhamdulillah"

Bature yace daya kwanta kan bed dinsa

Sai dai sam bacci yaki xuwa mishi sai tunanin abunda ya faru daxun yake Yawo a kwakwalwarsa, yana rufe ido kuma sai Naked surar Ma'u ka masa gixo ga wani mugun felling dake ratsashi ga Hajiya Babba na neman agaji


Bbu yadda ya iya haka ya dau wayarsa ya dannawa Zahra kira

Tana kwance tana kuka taji ringing din wayarta

Murmushi mai hawaye tayi kan ta picking

"Kisa in jiraki"

Kat ya katse wayar

No wasting of time Zahra ta mike ta nufi bedroom dinsa


Gangan jikinsa ce kawai ke tare da Zahra amma ruhinsa na wajen Ma'u da tunanin yadda ya dibi ganima a jikinta daxun, duk yadda yakai ya mance komai ya gagara, sai yau ya gane mata suna suka Tara

Washegari Balarabe da Jiddarsa suka koma Lagos yayinda Abdallah da Hisham suka wuce Kaduna



Bature Estate

"Ya kuka samu Ma'uta, nasan ta rame tayi baki tsabagen wahalar da Bature ke bata"

Ammi ce ke maganar yayinda su Abdallah suka kewayeta


Murmushi Hisham dake xaune kusa da Shukra yayi yace

"Don Allah kujimin matarnan maimakon ki fara tambayarmu ya gajiyar hanya angama karatu lfy amma sai ki taremu da wata wai Ma'u"

Dakuwa Ammi ta mishi tace

"Ma'un tawace wata don kaniyarka, anki tambayarka komai sai Ma'u"

Daria Abdallah yasa yace

"Ma'unki lfyrta klau sai kinga inda ta kara kyau da kiba tacema a gaisheki"

Washe baki Ammi tayi

"Ashe Turawan( wataran haka take kiran Bature) an fara hankali"

Hiran gundurar Shukrah yayi tace

"Ya Abdallah kun gama kenan bbu komawa ai"

Kada kai Abdallah yayi yace

"Bbu komawa mun dawo kenan sai kuma idan nai aure muje honeymoon da matata"

Batool da tunda ta shigo falon take satar kallon Abdallah ta limshe ido, a hankali tace

"Ya Allah cikamin burina"

"Kayi budurwa kenan Mijinah"

Ammi ta hurga mai tambaya

"Eh na fidda matar aure dai tafi karfin budurwa"

Baki Ammi ta tabe tace

"Budurwa dai ai sai ta mana kafin ta xama matar aure"

Hisham kwantar da kansa kan hannun kujera yace"

Ta gama miki ma don ta gida xaiyi"

Xuciar Batool ne ya fara dukan uku uku

Shukrah tace

"Pls Ya Abdallah wacece?"

" sai lokaci yayi xaki Santa don ko itama ban fada mataba"

Ajiyar Xucia Batool tayi tana Allah yasa itace

Guda Ammi ta rangada

"Nasan ko wacece"

Hararar wasa Abdallah ya mata yace

" wai tsohuwar nan wayo xata mana mu fada mata, to baxamu fada ba"

Lami yar aikin Ummi ce ta shigo palon da sallama ta durkusa ta gaidasu

"Hajiya ce tace su Abdallah suxo anxo gaidasu"

Fuska Abdallah ya hade yace

"Su wayene?"

"Hajiya Turai ce"

Cewar Lami

Hisham yace

"Kice muna xuwa"

Tashi Lami tayi ta fice

Kwafa Ammi tayi tace

"Isassu an iso, tsabagen takai ma ban kai taxo ta gaidani ba sai dai ta turo kuje"


Mikewa Hisham yayi ya tallafawa Abdallah ya mike suka fice

Ammi ta dubisu Batool tace

"Baxa kuje kuma Ku gaida Turai din ba"

"Babu inda xani wlh sai dai ita Shukrah"

Cewar Batool tana mike kafarta

"Nima bbu inda xani"

Shukrah ta fada tana gyara kwanciya akan 3siter


Hajiya Turai addar Ummi ce uwarsu daya ubansu daya, itama kamar Ummin take karyar arxiki da son suna, tana auren Senator tana ji da kanta ssai

Yaranta Hudu duka Mata biyu sunyi aure sauran biyu Teema da Zee


"Nikam wai uwar me suke har yanxu basu karasoba"

Cewar Hajiya Turai tana kada kafarta

Bata gama rufe bakiba su Abdallah suka shigo

Gaisheta sukai ta amsa da sakin fuska

"Kai yarana sun girma sauran musha bikin kyece raini, ya hanya? Ya karatu?"

"Lfy Klau Alhamdulillah, daman munyi niyar xuwa wajenki a Abuja sai Zahra kice mana kuna nan"

Cewar Hisham

Abdallah ya dora

"Ina su Zee? Koda shike muna gaisawa ma a WhatsApp"

Baki Hajiya Turai ta tabe tace

"Suna can gidan Baba Kabala"

Ummi dake duba materials da Addartan ta kawo mata tace

" kuma gobe ya kamata kuje Gidan Baba Kabala don kullum naje sai ya tambayeni Ku"

Sun dan jima suna hira kan su Abdallah suna Mike suna wuce part din Mami



Bayan wasu watanni

Ma'u ta sake ssai a Gidan Bature don ya rage takura mata da kuma dukanta, sai dai tsoronshi har yanxu yana nan don a jininta yake


Zahra kam tamfar kawa ta dauketa komai Anty Zahra komai Anty Zahra

Makaranta Bature ya maidata ssai ta maida hankalinta, Gashi yanxu suna kokarin rubuta Weac

Takanje gidan Falmata sa'i da lokaci, ssai take dauken duk abunda Falmata ta koya mata, tuni ta saje ta koma diyar KanuShuwa ( har tafi Amiratul Arab haduwa)

Humra ne ya xama tularenta shiyasa duk sanda ta gamu da Bature take tafia da imaninsa, yakanji kaman ya janyota jikinsa ya rumgumeta ko xai kashe kishinta dayakeji


A fannin Bature kuwa tun yana ganin lamarinsa da Ma'u xallar sha'awaetace ke dibansa har ya ankara sontane ya mai kamun kaxan kuku


Duk sanda sukaje family meeting wadda suke bayan wata biyu yakanji kamar ya furta abunda ke ransa amma idan ya tuno da wacece Ummi? Kuma wacece Zahra da kishi? sai gwiwarsa tayi sanyi

Amma ya kudurta a ransa Ma'u na candy xai bayyana abunda ke ransa komai ta fanjama fanjam

Abunda Bature bai saniba kuwa shine soyayya mai karfine ya shiga tsakanin Abdallah da Ma'u, wadda tuni Abdallah ya saye xuciarta da dadadan kalamai


A gefe daya kuma ga Batool nata haukan son Abdallah kuma duk wawwatarta ita zai zaba a matsayar matar aure

Zee autar Hajiya Turai kuwa ta mace a son Abdallah kuma ta takurawa Hajiya Turai, har Ummi ta sani kuma ta musu alkawarin Abdallah baida mata sai Zee

Yayinda Shukrah da Ya Hisham ke xuba love dinsu hankali kwance


Bayan Shekara daya

Falon Ammi ya samu hallartar duk wani dan Gidan Bature don gudanarda Family meeting kamar yadda suka saba

Tunda Ma'u ta bar Kaduna sai ya taxo, duk sunyi mamaki yadda ta kara girma ta kuma cika ta koma Babbar mace

A yau ne Bature ya dau kudurin Neman alfarman auren Ma'u don ta rigada tayi candy


A yaune Abdallah xai samu damar nuna Ma'u a matsayin matar aurensa

A yau ne Ummi takeson bayyana bukatarta ta hada Abdallah da Zee aure

A yau ne Abba da Abbu sukeson sanarda ahalinsu hukuncin da suka yanke na hada Abdallah da Batool aure


Hmmmmmm...................

Ma'uBature
Ma'uAbdallah
ZeeAbdallah
BatoolAbdallah

#Team Ma'uBature 😜😜😜😜


Ummu Subay'a❀
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: πŸ›πŸ› GIDAN BATURE πŸ›πŸ›
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🀝🏻


Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE

1⃣1⃣

Da Addu'a Abbu ya bude meeting din, yayinda Abba ya dora da

"Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'ala wa barkatu"

Duk ahalin falon suka amsa sallaman

" da farko xan fara da godewa Allah daya bamu lfy tsayon rai ya kuma hadamu wani family meeting, wannan meeting din akan Abdallah da Hisham ne sai kuma masu korafi ko neman shawara, duba da mukayi kun gama karatu sa'annan kuma kun samu aiki kafarku ta dafe kasa shine muka bijero da maganar ajiye iyali ma'ana batun aure"

"Abba nikam na riga na samu matar aure, damar rana kamar haka nake kira"

Abdallah yayi saurin katse Abba kamar yasan meke ransu

Duk sai kallo ya koma kansa

"Haba Abdallah wannan wani irin gaggawane, baxakabar Yaya ya dasa ayaba sai ka katsesa"

Cewar Abbu yana mikawa Abdallah mugun kallo

Kwafa Ammi tayi tace

"Ai idan baiyiba sai an tambayesa jinin isassu nefe a jikin sa"

Murmushi kawai Ummi tayi don ta jima da sabawa da muggan kalaman Ammi

Numfasawa Abba yayi yace

"A'ina ka samu matar Abdallah"

Keya Abdallah ya shiga sotsawa, yayinda Ma'u ta sunne kai tana murmushi, Batool ko ta kafeshi da ido xuciarta na bugun uku uku, Ummi kuma na Allah Allah yace Zee ce matar

"Kayi magana mana, bafa aikinka mukeba, daman kasan kanada kunya ka fara kawo batun"

Bature yayi maganar cikin umarni

Zahra datasan komai tace

"'Yar gidan nan ce fah, Ma'u ce"

A raxane Batool ta dago tana kallon Ma'u dake gefenta kamar ita tai maganar, xuciarta ne ya tsananta bugawa kamar xai ballo kirjinta ya fito

Ummi ko ji take kamar an watsa mata ruwan xafi, ji take kamar tayi dirar mikiya gaban Zahra ta shakota

Goga Bature kam dafe xuciarshi yayi dake baraxanar fita, rintse idonsa yayi don gudun kada wani ya gane halin dayake ciki

"Uban wa ya tambayeki, ko dake ake maganar"

Ummi ta fada tanama Zahra mugun kallo

"Ummi haka maganar yake"

Abdallah yayi maganar kansa a kasa

Maida dubanta Ummi tayi kan Ma'u da itama kanta a kasa

" Ma'u kina son Abdallah "

Kai Ma'u ta gyada alamar "eh"

Ammi dake binsu da ido tace

" Fateema uwata kin gama? Tambayar ki nake kin gama? Idan kin raina su Ahmad to nikam nafi karfin reni wajenki ko ubanki bai kai ya renani ba, Muna xaune a kasa kike bidirinki gabanmu Abdallah dai yanason Ma'u itama tana sonshi ko bakya so auren nan sai anyishi, kai kuma Hisham maganar ka da Shukrah na nan ne?"

Kai Hisham ya tsadda kasa yace

" eh tana nan"

Abba daya karanci kowa amma banda Bature yace

"Toh Alhamdulillah tunda duk na gidane, insha Allah cikin lokaci kalilan xa'ayi bikin, akwai mai magana"

Har Ummi ta bude baki xatayi magana Abbu ya watsa mata kallon "kada ki fara"

Bbu yadda ta iya taja bakinta ta rufe

Mami dai shiru tayi ta xubawa Baturenta ido tana karantan yanayinsa, murmushin tausayinsa tayi don tasan xa'a rina mugun kiyeyya xai koma mugun soyayya


Haka aka rufe meeting din, masu farin ciki sunayi masu bakin ciki sunayi




Daga falon Ammi direct part dinsa Bature ya nufa yana shiga bedroom ya danna key ya kulle, fadawa kan bed dinsa yayi ya hau kuka kamar karamin yaro hade da sambatu

"Yanxu inaji ina gani Ma'u xata kufcemin, meyasa ban fahimci Ma'u na soyayya da Abdallah ba? Duk girman kaina ya jaxamin gashi na rasa Ma'u"

Kai ya kada kamar mai magana da wani

"Ina sam baxaiyuba, Allah baxan bari wani ya auri Ma'u ba muddi inada rai"

Mikewa yayi ya xauna

"To mexanyi mena iya?"

Ya tambayi kansa

Dirowa yayi daga kan bed din, ya hau buga kansa jikin bango yana kuka gwanin tausayi

"Why me? Why Bature?"

Cikin lokaci kalilan Bature ya fita hayyacinsa kuma ya fita kamanninsa, fuskarsa tayi jayur abunka da farin mutum, blue eyes dinshi sun rine sun koma jajayur

Allah sarki Bature duk wadda ya gansa dole ya tausaya masa ( Soyayya ce)


Garden Batool ta nufa ta yada xango, kwanciya tayi kan carpet grass ta shiga rera kuka kamar marainiya, tun farko jikinta na bata baxata taba samun gurbi cikin xuciar Abdallah ba amma xuciarta ta tirsasata ta ci gaba dasa sammani gashi yau ta shiga mugun hali

Wani abu takeji yana mata yawo a kahon xuciarta, ssai taji tari na taso mata

Tari take kamar ranta xai fita, tana kuka tana tari
( Zafi biyu)


Safa da Marwa Umma ta shiga yi a bedroom dinta komai ya kwance mata, ji take kamar ta rusa ihu, ta ko'ina anfi karfinta

Da wani ido xata dubi Anty Turai tace mata Abdallah baxai auri Zee ba Ma'u xai aura, idan tai haka xata yadda girmamawanta a gidansu, ya xama dole ayi duk mai yiyuwa Abdallah ya auri Zee

Zahra ce ta shigo tana duban Ummin da mamaki

" Ummi meya farune, naga kamar hankalinki a tashe"

Cewar Zahra tana kokarin xama bakin bed

Harara Ummi ta watso ma Zahra tace

" ya hankalina baxai tashiba keda Abdallah xaku xubarmin mutunci gidan Kabala, Anty Turai fa xuwa tayi ta nemi alfarmata akan tanason ta hada Abdallah da Zee aure, na nuna mata bbu komai ta kwantarda hankalinta yanxu kuma keda Abdallah Ku daukomin fitsarerriyar yarinyar nan Ma'u "

Duk dunia bayan Ummi bbu wadda Zahra ke ji da ita kamar Hajiya Turai, kuma itama Hajiya Turan naji da ita

Ajiyar xucia Zahra tayi tace

" Wayyo wlh Ummi ban San abunda ke gudana ba kenan, da ban bawa Abdallah goyon bayan neman Ma'u ba, Anty Turai tamana komai ya kamata muma mu saka mata, yanxu me abunyi?"

Xama Ummi tayi kusa da Zahra tace

"Shi nake ne tunani"

Shiru dakin yayi nadan wani lokaci

Kan Zahra tace

"To Ummi mexai hana mu nemi shawarar Anty Lubna"

Murmushi Ummi tayi

" good idea insha Allah Lubna xata sama mana mafita"

Mikewa Zahra tayi tace

"Bari naje naji Yaushe xamu koma, idan ba yau ba sai muje gidanta anjima"

"Toh"

Ummi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login