Showing 21001 words to 24000 words out of 45410 words
tace tana murmushin kwanciyar hankali don tasan idan sun samu Lubna komai ya kare
Ruwan xafi Bature ya hada ya matse goshinsa daya kumbura yayi ja yayi wanka ya shirya, ya fara hada kayansa don ya yanke hukunci baxai kwana anan ba balle bakin ciki ya kasheshiba, gwara ya koma Abuja ko xaiji sassauci
Tsaf ya hada kayansa yaja trolley, yana fitowa Falo Zahra na shigowa
Mugun kallo ya jefeta dashi yaci gaba da tafi'arsa
Da mamaki take kallonsa tace
" Honey ina xuwa, kada kacemin dai xamu koma yau"
Kamar badashi takeba ya nufi kofar fita, da gudu ta sha gabansa
"Magana fah nake Sweety"
" bacemin daga gaba Zahra"
Ya fada cikin kakkausar murya
"Bari na dauko veil na mu tafi"
Ko sauraranta baiyiba yayi ficewarsa da gudu ta bi bayansa
"Don Allah Sweety kayi hakuri, ka tsaya kajini, me aka makane"
Dakyar ta cimmasa yana kokarin bude kofar motarsa
Rike kofar tayi ta marairace masa tace
"Ka dubi girman Allah ka fadamin abunda na maka, ka dubi yadda idonka yayi ja ka dubi yadda fuskarka ya xama, wai meke faruwane"
"Pls Zahra ki kyaleni, banason damuwa ni xaki munafurta a gidana ni xaki boyewa Soyayyar Ma'u da Abdallah"
Durkusawa tayi gabansa tace
"Don Allah Honey kayi hakuri wlh shiya nemi ayi hakan"
Shigewa yayi motarsa yace
"Ai sai kije ki xauna sai an gama auren ki dawo Abujan, king a lokacin kin gama xama mai dalilin auren"
Jan motarsa yayi ya fice gidan a dari fa hamshin bai sallami kowaba
Kai kawai Mami ta gyada data gama kallon duk abunda ya faru tsakanin Zahra da Bature yace
" Allah ka kawo mana dauki"
Up up up up up
#Team Ma'uAbdallah♥
Dole na nemo bodyguard saboda
#Team Ma'uBature
Kada Ku babbalani😜
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
DA BAXARKU NAKE RAWA
Batool Adam Jatco (Amfanin Soyayya)
Zainab Goni
Rufaida Omar (Taurari)
JINJINA
Batul Mamman (Kashe fitila)
Beebie Isah (Dan Makaho)
Phertymerh Zahra ( El-Mustapha)
Sadnaf (Makobtan Juna)
Lamtana (Asabe Reza)
Phertymerh (Yusrah)
Sameena Aleeyo ( A duniarmu)
Ainadimple (Hasken lantarki)
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
1⃣2⃣
"Nidai mun bata, tunda na tafi ko ki kira Anty Zahra ta bani kin samu Shukrah kin manta dani"
Ma'u ke maganar tana shuna bakinta
Janyo Ma'u jikinta Ammi tayi
"Haba ta wajena ai baxamu bata ba, me Turawa ke bakine kika cika kika wani jiki haka"
Murmushi Ma'u tayi tace
" ya rage dukanane kawai kuma ni baxan komaba na dawo kenan tunda aure xanyi"
Harara Jidda ke hurga musu tace
"To fitsarerriya kin dawo da rashin kunyarkiba, ko kunya bakyaji kina ce mana aure xakiyi"
Kukan shagwaba Ma'u tasa
"Ammi wai me na tarewa Anty Jidda ce sam batason ganin walwalata"
"Rabu da ita kishi take dake, kinga yanxu ita kishiyar balbalinkice"
Cewar Ammi tana shafa kan Ma'u
Shukrah ce ta shigo ta xauna kusa da Anty Jidda tace
"Wash nagaji wlh"
"Aikin me kikayi?"
Cewar Jidda
Wasa da Amal dake koyon tafia Shukrah ta shiga yi tace
" Ya Abdallah ne yasani na gyara masa part dinsa, wlh Ma'u sai kin dage son jikin Ya Abdallah yayi yawa komai a barbaje yake a dakinsa"
"Sai dai su dawwama a bolansu amma Ma'u da lalacinta bbu abunda xata iya tafi'arsu daya da Zahra"
Cewar Ammi tana dariar tsokana
Shukrah ta kannewa Ma'u ido
"Dama Batool xai aura xata kintsashi, Ma'u kam sai dai ta dada lalata manashi"
A harxuke Ma'u ta tashi ta xauna tace
"Anyi walkiyi naganki 'yar bakin ciki, duk yadda nake haka Ya Abdallah ya kyasa, shegiya mai hana ruwa running"
Haba Anty Jidda ta rike tana kallon Ma'u
"Baiwar Allah meyayi xafi daga wasa, ai kanwar mijinkice"
Baki Ma'u ta tura tace
"To sai tace da Batool xai aura"
Murmushi Shukrah tayi tace
"Allah ya huci xuciarki Anty Masifa"
Hisham ne ya shigo falon ya dauki Amal yana mata wasa tanata kyalkyalewa da daria
Yaxo saitin kunnen Shukrah yace
"Wataran diyarmu xan ma wannan wasar"
Tafin hannunta Shukrah tasa ta rufe fuskarta tana murmushi
Jidda dataji abunda yace
"Kai Ya Hisham a idon Ammin"
Baki Ammi ta tabe tace
"Kinga Ma'u dagani nabar nan don bbu abunda yaran nan baxasu aikata a gabanaba, basukiba suyi Daren farkonsu a kan gadona"
Duk daria suka saka
Hisham ya xauna kusa da tsakiyarsu Jidda yace
"Ke dai kishi kawai kike, kuma first night din baxai gagara kan bed dinkin ba"
"Allah ya sawwake kishin me xanyi ai gidan nan Turawane kawai Mijinah kuma Zahra ce kawai kishiyata"
Ammi ta fada tana kokarin janye Ma'u daga jikinta
Text ne ya shigo wayar Ma'u daga Abdallahnta
"Ki sameni a Garden"
Murmushi tayi, a tare suka mike da Ammi, Ammi tayi hanyar bedroom dinta yayinda Ma'u tayi hanyar barin falon
"Ina kuma xaki uwar gantali"
Shukrah tayi tambayar
Kai tsaye Ma'u tace
"Zance xani ko xaki hanani"
Kai Shukrah ta kada
"Na isa ni a wacece?"
Ficewa daga palon Ma'u tayi ba tare data tankaba
Tashi Jidda tayi itama ta nufi hanyar barin falon
"Bara na barku kusha love"
Hisham daya matso ssai kusada Shukrah yace
"Zoki dau diyarki mai shegen kiriniya kamar Ma'un nan"
Daria Shukrah tasa tace
"Anya Anty Jidda ba little Ma'u muka samuba"
Dakuwa Jidda tama Shukrah tace"
"Xonan Babyna, daga na barki ki tayasu lobewa shikenan sai dangantamin ke da ma'u Allah ya isan miki"
Take Amal ta isa gaban Jidda, Jidda ta dagata ta fice
Cikin so da kauna Hisham ke duban Shukrah yace
"Madam kinga yau dai an tabbatarmin dake, wani irin tanadi xaki faramin kafin ranar da muke jira taxo"
Murmushi Shukrah tayi ta shiga wasa da yatsunta batace komai ba
Marairaice mata hisham yayi
"Haba mana Madam pls talk, nifa kunyarkice ki hadani dake wlh, sai kace yar 1970s"
A sanyaye Shukrah tace
"To mexance Sweety wannan maganar tafi karfina"
Murmushi Hisham yayi yace
"Tabbas tafi karfinki, sai first night dinmu xaki san tafi karfinki"
Bbu shiri Shukrah ta mike xata gudu don maganar tayi mata mugun nauyi
Cikin xafin nama Hisham ya kamota ya dawo da ita ta xauna inda ta tashi yana mata daria
"Village girl"
Da kuka Zahra ta shigo bedroom na Ummi
Cikin mamaki Ummi ke tambayarta
"A'a Zahra me kuma ya faru?"
Cikin kuka Zahra ta xayyana mata duk abunda ya faru
Tsaki Ummi taja tace
"Ji nake kamar na hauki da duka kiyi kuka mai dalili, sai kace ke bakuwar Baturene bakisan mugun ra'ayinsa ba da dan wannan abunda yayi xai tada miki hankali hadda kuka, tun farko ma Uban me ya hanaki sanar dashi"
"Ya Abdallah ne yace kada na sanar dashi"
Zahra ta fada tana share hawayenta
" ki biyewa Abdallah sai ya kashe miki aure wlh, nikam jeki ki wanke fuskarki mu tafi gidan Lubna, abunda ke gabanmu yafi wannan shirmen din, gwara ma da hakan ta faru xamu samu damar warware matsalar idan yaso daga baya na kira Baturen na basa hakuri"
Babu musu Zahra ta shige toilet don wanke fuskarta
"Subhanallah, Batool lfy? Meya sameki?"
Abdallah yace lokacin da ya sami Batool kwance tana tari mai xafi, dagota yayi ya kwantar da ita kan cinyarsa ga jikinta ya dau xafi
Salati Ma'u tasa data iso garden din ta samesu, durkusawa tayi gaban Abdallah
"Hayati meya sameta?meke damunta"
"Hayati " tsayawa sunan yayi a kahon xuciar Shukrah wadda ya ingixa tarin kara hardeta ssai, ji take da xata bar duniar ma xai fiye mata sauki
Mikawa Ma'u wayarsa Abdallah yayi
"Kiramin Hisham kice ya samemu a part din Mami Batool ba lfy"
Yana fadin haka ya daga Batool din kamar yar tsana ya nufi part din Mami
Itama Ma'u mikewa tayi tabi bayansu tana kiran Hisham din a waya, ta gama rudewa sai kuka take
Gidan Bature
Ikon Allah ne kawai ya kai Bature Abuja, don Sam baya cikin hayyacinsa, gudu yayi ta shararawa kamar shi kadai akayi titin
Wuni yayi jimami da kuka kamar karamin yaro
bai san haka so yakeba sai yau
bai san ya afka kogin son Ma'u da nisa hakaba sai yau
bai san xafin soba sai yau
Da yanada iko daya mayar da son dayakewa Ma'u kan Zahrarsa amma ina bashi ya sakaba balle ya musanya
WhatsApp dinsa ya bude ya shiga Dpn Zahra ya kurawa pic din Ma'u dake Dpn ido, sonta sai dada ninkuwa yake a xuciarsa
Pic din ya jasa ssai murmushin datayi ya kara bayyano da xalalan kyaunta
Bature Estate
Kamar da wasa ciwon Batool gashi ya kara tasannanta, agajin gaggawa Hisham ya bata a matsayinsa na likita, taimakon ubangiji jikin ya lafa ta samu tayi baccin bayan tasha allurar bacci
Sai a wajen ciwon ne akasan Bature ya koma Abuja, fada ssai Abba yayi, da'aka kira numbersa duk switch off don wadda yake kallon pic din da ita tana fly mode ne
Dole su Ummi suka dage tafiarsu gidan Lubna sai gobe
A Balcony part din Mami Ma'u da Abdallah suka xauna a resting chair suna hira
"Pls Ruhy ki daina sa wannan turaren idan xamuyi hira yana dagamin hankali ssai, idan naji kamshin ji nake kamar na janyoki jikina"
Baki Ma'u ta tura tace
" nidai suna turarena, kuma gaskia baxan iya daina sasuba don sunamin dadi ssai, sai dai mutum yayi hakuri"
Kai Abdallah ya kada yace
"OK bbu damuwa ranarda kika kaini makura xaki gane ai"
Baki kawai Ma'u ta tabe bata tanka mishiba
"Ruhy Allah kina rikitani dayawa ga pink Jan bakinda kike sawa sexy lips dinki nan na tafia dani I wish watarana in shanye miki Jan bakin tas"
Yayi maganar yana kashe mata ido
Bbu xato bbu sammani Ma'u taji wani abu na sauka daga kasanta, limshe ido tayi taji sauyi ssai a jikinta, tasan dai wannan abun na faruwa da ita only if tana gaban Bature idan ya tsareta sa blue eyes dinsa
Yau kuma meya kawosa wajen Abdallah
"Baccine Ruhy?"
Abdallah yayi maganar yana kallon yadda tayi sanyi
Kai kawai ta gyada mishi alamar "eh"
Har bakin bedroom na Mami Abdallah ya raka Ma'u, sanda ta shige kan ya fice
Duk wani shirin bacci Ma'u ta gama gefen Batool dake bacci taje ta kwanta ta xubawa enlargement din Bature ido, wadda ya dauka da inform dinsa ta Air force yayi mugun yin kyau kamar wani cikekken Bature, haka kurum ta tsinci kanta tana murmushi
"Turawa case"
Ta fada a hankali tana limshe ido
#Team Ma'uBature
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
INA ALFAHARI DAKU
Meela Adeel
Meena parrot (mai fitsarin kwance)
Zee Madagwal
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
1⃣3⃣
Shiru falon yayi bayan Ummi ta gama watsafoma Lubna abunda ke faruwa
Kusan 3minutes Lubna ta dauka tana naxari daga bisani tace
"Gaskia Anty Hauwa Idan har Abdallah bai auri Zee ba akwai babban tashin hankali a family, kinsan Anty Turai batasan hakuriba kuma akan farin cikin yaranta xata iya batawa da kowa kuma taciwa kowa mutunci"
Ajiyar xucia Ummi tayi tace
"Duk nasan da wannan Lubna mafita naxo nema wajenki"
"Don Allah Anty Lubna ki taimakemu kin san Momy tamini komai Idan muka samu matsala da ita akwai babban damuwa"
Cewar Zahra kamar xatayi kuka
Murmushi Lubna tayi tace
"Kwantar da hankalinki Zahra, kin manta nifa na sama muku mafita lokacin da kika mace kan son Bature"
Harara Ummi ta hurgawq Lubna
"Banda tuna baya kuma mana Lubna"
"Babbar matsalar wannan Ammin takuce xata hana ruwa gudu amma nasan yadda xa'ayi, kawai ku xuba musu ido kowa yayi yadda yakeso sai ranar daurin auren xa'a daura da Zee"
Cike da mamaki Ummi da Shukrah ke kallonta
Gyada musu kai tayi tace
"Kawo kunnenku kuji"
Magana ta fada musu a kunne wadda nima banji ba
Shewa suka saka da tafi
Ummi tace
"Wlh kwatakwata ban taba kawo wannan a kainaba ai shine hanya mafi sauki bbu tashin tashina bbu kuma Uban da zaiji haushina"
Daria Zahra tasa tace
"Inaji dake Antynah wlh kanki naja"
Murmushi Lubna tayi daga bisani kuma ta dan hade rai tace
"Ya kamata mu sabarda Anty Turai komai kada taji waiwai taci ubanmu"
"Gaskia kam kin san Anty Turai fire to fire ne"
Cewar Ummi
Gyara xama Lubna tayi tace
"Ke Zahra har yanxu bbu labarine, ga Jidda da diyarta tufarkallah"
Maiko idon Zahra yayi alamun hawaye cikin sanyin murya tace
"Wlh Anty bbu inda bamu xagaya da Ya Bature ba amma ance lfyta klau kawai lokacine baiyiba"
Baki Lubna ta tabe tace
"Ya kamata lokacin yayi tun kan Amminku tasashi kara aure don bbu abunda baxata iyaba"
Hannu Zahra ta dafe a kirjinta tace
" na Shiga uku aure kuma? Wlh ta kuskura tasashi aure xan musu borin hauka, yadda nakeson Ya Bature wlh baxan iya sharing dinsa da wataba har abada bbu Zahra ba kishiya"
Harara Ummi ta aika mata tace
"Ki tsaya kina cewa bbu ke bbu kishiya kada ki haihu"
Lubna tace
"Bari mu gama kashe wutar dake gabanmu xan dawo nata"
A wajen suka kira Hajiya Turai a waya suka xayyana mata komai, jan kunne ta musu da babbar murya akan kada a samu matsala don baxata lamunci kukan diyarta ba
Bature Estate
Zaune suke su uku a dining space a falon Mami suna breakfast
Ma'u ta dubi Batool tace
"Jinyan rana daya kin xube gabaki daya, katon kumatunkin nan duk ya xube"
Shukrah dake kokarin kai Spoon cike da soyeyyen egg tace
"Wlh ta xube ssai, wai meke damunkine Sis"
Sipping na tea Batool tayi tace
"Zazzabine wlh ya bugani kuma ina ganin aikin girkin danayine mai ya hau kaina"
Cikin tausawa Ma'u tace
"Ayyah Sannu Sis, Allah ya kara sauki"
Duk suka amsa da Ameen
"Har wajen cin abinci ma baxaku bar surutuba, xan fita xamuje gaisuwa da su Alhaji, Batool ki tabbatar kinsha magungunanki, Shukrah ki tabbatar tasha"
Cewar Mami data fito daga bedroom dinta tana kokarin barin falon
Baki Ma'u ta tura tace
"Ni baxa'a barmin amanar shan maganinba"
Baki Mami ta tabe tace
"Jirgin daya dauko Bala shiya dauko Audu"
Mami na ficewa Abdallah da Hisham suka shigo
Tsayawa Abdallah yayi tsakankanin kujerar Ma'u da Batool yayinda Hisham ya xauna a kujerar dake gefen Shukrah ya dau spoon ya fara tayata cin abincin
Gaishesu su Batool sukayi
Abdallah yace
"Ya jikin naki Batool"
"Da sauki Batool"
tace tana dubanshi
Hisham ma ya jikin ya mata
Rankwafo da wuyarsa Abdallah yayi saitin kunnen Ma'u yace
"Anything for me Ruhy"
Fari da ido Ma'u tayi tace
"Nothing Hayati"
Baki ya bude mata alamar ta saka mishi indomie data dibo a folk, bbu musu ta saka mishi ya fara taunawa a hankali yana limshe ido
Wani abune ya tokare Batool a kahon xuciarta, ji take kamar tasa ihu ko xataji sauki
Gefe daya ga Hisham sai kwantarwa Shukrah murya yake don ta saka mishi abinci a baki yadda Ma'u tayiwa Abdallah amma kunya ya hanata
Badon Batool ta koshiba ta mike da niyar barin dinning space din
"Baidai har kin koshiba"
Shukrah ta tambayeta
Kai kawai ta kadawa Shukrah alamar "eh" tana kokarin sauka daga space din
Ma'u tayi sauri tace
"Maganin fah bakishaba, ke Shukrah soyayya ta mantar dake amanar Mami"
A fakaice Batool ta xabgawa Ma'u harara ta dawo ta dauki maganin tasha tabar wajen da sauri kada xuciarta ya buga
A kwana a tashi asarar mai rai, yau sauran sati daya bikinsu Ma'u, duk wani tanadi an gama Mami da Ummi sunsa kaimi wajen gyara yaransu ga Ammi ma tana basa nata gudumawar
Kada kaso kaga yadda Ma'u ta koma ta kara cika fatarta ta goge tayi haske sai sheki take, abunka da farar mace sai haska waje take
Goga Bature kam ya gama fita hayyacinsa ya rame ya koma kamar wadda yayi jinya (koda yake yayi jinyar xucia), damar yaya lfyr kora bare ya fara xayo miskilancine yaci Uban nada
Koda Ummi ta kirasa maganar komawar Zahra cewa yayi ya hakura amma tayi xamanta sai bayan biki
Bai so xuwa bikinba amma baida excuse ne yasa yanke sai ranar alhamis xaixo ana gobe daurin aure
Allah sarki Batool tayi kokari ssai wajen danne xuciarta ta fawwalawa Allah komai tashiga cikin ribibin bikin aka dama da ita ssai ssai
Bikin axo a gani akayi tun ranar litinin aka fara event na biki, ummi da 'yan uwanta sun fito sun nuna su isassune sunyi ruwan kudi, yayinda a gefe guda sukewa Ma'u daria don sunsan kawai bayyanowa xatayi a wajen event amma daurin auren bada ita xa'ayiba
Ranar alhamis da yamma Bature ya iso, duk wadda ya gansa sai ya bincikesa ko ya tashi daga jinyane, wadda yake ganin damansu baya tanka musu wadda kuma yake ganin damarsu yace "eh"
Mami datasan dawan garin ko tambayarsa batayiba ido kawai ta xuba masa
Sai bayan ya dawo daga sallar isha'i ya shiga wajen Ammi don daxun mutane sunyi yawa a part dinta shi kuma baison hayaniya
Yanxun ma akwai mutane amma basu kai na daxun ba, ratsasu yayi ya kamar baisan wasu daga cikinsu ba ya wuce direct bedroom na Ammi
Bbu kowa a bedroom din karar ruwa a toilet ne yasa Bature nade kan bed dinta yayi kwanciyarsa yana jiran fitowar Ammi daga toilet don duk xatonsa itace ke wanka
Kurawa pic din Ma'u dake manne a bangon dakin ido yayi, yanajin sonta na kewayawa dukkan gabbansa
Fitowa Ma'u tayi daga toilet daga ita sai dan karamin towel dako cinyarta bai kaiba tana rausaya jikinta wai ita tana practical abunda mai Falmata ta koya mata
Tunda ta fito Bature ya kura mata ido ko kiftawa bayayi, ta gama tafia dashi, idan badon ya mata farin saniba daxaice ba ita bace, take kasala ya mamayeshi ya kasa tabukawa kansa komai
Ma'u ko bata san ma da akwai mutum dakinba, Salle tayi ta fada kan bed din tanacewa
"Ayyah bed dinmu da Ammina bari na miki kwanciyar bye by......."
Sauran maganarne ya makale mata sakamakon fadawa kan Bature datayi
Bude bakinta tayi da niyar sa ihu, don ta gama tsorata
Cikin xafin nama Bature ya hade bakinsu