Showing 12001 words to 15000 words out of 45410 words
yace
"Man pls kada ka dinga dibo alluran sojanka kana saukewa Ma'un Ammi"
Hararar inda Ma'u ke tsaye Bature yayi yace
"To naji Abba, nidai kabimin kanwa a hankali don nasan yanxu kana hannu kada bayan 2months muji wani cikin"
Ya sauya topic da Balarabe ya dauko
Bayanshi Balarabe ya duka yace
"Banason sa ido bbu ruwan mutum dani"
Sake juna sukayi suna murmushi
Ma'u take tsaye tana binsu da ido a cikin ranta tace
" Niko Uban me ya kawoni inyi anan? Yayi ya tafima mutum ya huta wlh, ya saura Anty Jidda itama ta tattara na koma free world na (rashin sani yafi dare duhu inji hausawa)"
Bayan sun gama sallamar juna Bature ya shiga driven site ya xauna, abunda yake burge Family dashi kenan duk matsayinshi a Soja duk kudin gidansu Sam baya bari driver yayi driving dinsu shida iyalinsa, shida Kansa ke driving
"Ma'u shige muje"
Cewar Zahra tana kokarin shiga motar
Ido Ma'u ta xaro tanama Zahra kallon mamaki
"Baxaki ji menace bane ko sai Ya Bature yaxo ya miki da yaren da kikafi fahimta"
Zahra ta sake cewa tana rufe kofar motar
Ganin kofar side din Bature na girgixa yasa Balarabe saurin tura Ma'u data tsaya kamar mutum mutumi tana kallonsu don Neman Karin bayani cikin motarta ya kulle
Ta bashi tausayi ssai Sam bayason tun anan Bature ya kirbata
Jam motar Bature yayi ya fice a Bature estate
Mamaki, firgici, da tsoro su suka lullube Ma'u da hawaye keta ambaliya a fuskarta, tanason karin bayani amma bbu mai fahimtar da ita
Saura kiris fitsari ya xobo mata lokacinda taga suna fita daga garin Kaduna
Zahra kam ma ta manta da wata Ma'u sai hira ta ke ma Bature na mugunta ya murmusa don baya murmushi sai ta baci
Wani raxanennen ihu Ma'u tasa mai raxana duk wadda yaji
Karfin ihun yayi tasiri a kunnen Bature sake siterin motar yayi yana kokarin toshe kunnensa yama manta yana tuki
Tangal tangal motar ta fatayi kan titin, ga tank na Total oil ya nufo saitin motar
Sautin Haduwar karfe da karfene ya cika wajen wani kiyyyyyyy........... Kakeji
Me kuke xato xai faru?
Idan bbu abunda ya faru wani irin xama Ma'u zatayi a GIDAN BATURE?
Ya kuma 'yan GIDAN BATURE xasu kare da Ammi idan ta fahimci Ma'unta bata BATURE ESTATE?
Kuyi hakuri da karancin page nan Night duty nake banda isheshen lokaci ga Fans ta ko'ina suna bidar ci gaba
My Fans ❤
Duk inda kuke ina yinku ssai
Irin ssai nan fah
Heart you all♥
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
Allah ya baka lfy Admin of Admins Yahya Hayat
Allah yasa kaffarane😥😥
Jinjina ga
Fikra Writer's Association
Mussamman
Rufaida Omar
Bingel
Allah ya kara basira nagode da kaunarda kuke nunamin❤❤
Gaisuwa
Maman Fauwaz
Aisha Bala
Maman Abdul
Da duk wadda ban ambaci sunansuba
Ina yinku irin totally nan RUFAIDA OMAR FANS (ROF)
Allah yabar xumuncin soyayya🤝🏼
0⃣6⃣
Cikin xafin nama Bature ya kama siterin motar don kaucewa Tank din, Amma sanda Tank din ta goge jikin motar
Suna wucewa Bature yayi Hamdala tare da limshe ido, Zahra da ta gama sadarkarda rayuwa da sauke ajiyar xucia tace
"Alhamdulillah"
MA'U kam bbu magana don har ta fara digar fitsari tsabagen tsoro, sai raba ido take kamar mage
Ta mirror mota Bature ya balla ma Ma'u harara yace
"Shegiya mayya wlh sai dai ki kashe kanki badai niba"
Duk da firgicin da Zahra ke ciki bai hanata sa daria ba tace
"Allah ya kare na gaba"
KUJE BARRACKS ABUJA
Sunan kawai da Ma'u ta kalla tasan ta kade ba karamin jin jiki xatayi anan ba ga Ya Bature Anty Zahra (sey ko Allah wadi inji Fulani)
Suna shiga cikin GIDAN BATURE Zahra ta xabawa Ma'u bedroom mai kyau tasa masu aikinta suka kai kayan Ma'un
Duk kyau da tsaruwar bedroom din bai burge Ma'u ba damuwarta kawai ta ganta a Bature Estate kusa da Amminta
Kasan tiles ta xauna ta fara fanshe kukan da bata samu tayi a mota ba
Wucewa bedroom dinsa Bature yayi wanka ya fara kan yaxo ya haye kan bed ya fara baccin gajiyar dayayi kwanaki
Ga Zahra ma hakane wanka tayi ta haye bed dinta tayi bacci
Kuka Ma'u taci ssai har ta fara kallon dishi dishi fararen idanunta sun koma jaja wur
Anan kan tiles baccin wahala ya kwasheta
1:10 alarm na wayar Bature ta tasheshi daga bacci, mika yayi hadeda salati ya nufi toilet yayi alwala ya fito ya nufi bedroom na Zahra
Gaban mirror ya sameta tana make up daga bakin kofar ya tsaya yace
"Tun daxun kika tashi kenan?"
Murmushi ta sakar masa tace
"Eh tun 12:30 na tashi"
Baki ya tabe yace
"Barin wuce masallaci kan in dawo ki tabbatar kin kintsa min bedroom na"
"To ranka shi dade"
Zahra ta fada tana mikewa don ta iso gabanshi
"Dakata Madam masallaci fah nace miki xanje so kike ki karyamin alwala"
Bature ya fada yana kokarin barin dakin
Murmushi Zahra tayi a hankali don kada ya jiyota tace
"Mutum sai jarabar tsiya"
Fita Zahra tayi ta nufi bedroom na Ma'u
A hankali Zahra ta Shiga tada Ma'u, dakyar Ma'u ta tashi tana goge idanunta da suka kumbura ssai
"Tashi kije kiyi wanka kixo kiyi Sallah"
Kuka Ma'u ta saka data tabbatar ba mafarki bane Gidan Ya Bature ta dawo
"Kukan fah, Oyo tashi kiyi abunda nace kiyi"
Zahra ta fada cikin daga murya
Ko a jikin Ma'u sai ma kara sautin kukanta datayi tana cewa
"Nikam bbu abunda xanyi a maidani gida ni baxan xauna dakuba"
Tsawa Zahra ta daka mata
"Ina wasa dake Ma'u baxaki tashi ba ko sai na dakaki"
Sarai tasan kirbata Zahra xatayi shiyasa ta mike tana kukanta ta shiga toilet tana gunaguni
"Ni wlh gida xaku komar dani, dukkanku mugayene shiyasa Allah ya hadaku aure"
Kai kawai Zahra ta girgiza ta nemi waje a bakin bed ta xauna tana jiran fitowar Ma'u don idan bata tsaya a wajenba Ma'u xata bata musu lokaci wajen cin abinci
Kusan 13 minutes Ma'u ta dau kan ta fito daga toilet tana tuttura baki tana hararar Zahra kasa kasa, kai tsaye closet ta nufa ta ciro kayanta a gaban Zahra tasa ko'a jikinta, Zahrar cema ta kauda kan ta
Bayan ta idarda Sallah ta daga hannunta
"Allah gani a hannun mugayen bayinka, ya Allah ka fiddani daga hannunsu cikin gaggawa, nasan Allah ka hukuntani ne don jiya banyi sallar isha'i ba sai yau da asuba shine ka hadani dasu, Allah na tuba ka yafeni Allah kamin katanga dasu ka raba tsakaninmu har abad..........."
A fusace Zahra takaiwa bakin Asma'u duka
"Shegiya rashin kunyarkin yakai a gabana kike addu'ar nan, to bari na fada miki xama a gidan nan daram dakam bbu ke bbu barin gidan nan sai aurenki"
Hannun Ma'u tasa tana shafa labbenta don duba ko jini ya fita ba karamin bugu labbun suka shaba
Wani kukan Ma'u tasa tana gunaguni kasa-kasa
Kara hasala Zahra tayi ta daka mata tsawa
"Ki rufewa mutane baki, nan ba Gidan BATURE bane nan Gidan Ya Bature ne kuma barrack na sojoji idan kikace xakima mutane abunda kike gaban Ammi sai na dakaki na kuma turaki gard room, kafin Ya Bature ya dawo ya miki tsinennen duka kinfini saninshi ai"
Ma'u har ta manta da a Gidan Bature take, sharewa hawayenta ta shiga yi da hijab datayi Sallah tana kukan xuci
Bature na dawowa daga Sallah ya shiga bedroom dinsa, da mamaki yake kallin daki yadda ya barshi haka ya samu
Abunda yafi tsana yabada umarni akiyi ssai abun ya bata masa ransa
A fusace ya fito daga dakin ya shiga kwadawa Zahra kira
Zahra najin irin kiranda Bature yake mata tasan bbu lfy, case din Ma'u ya mantar da ita aikinda ya bata sai yanxu ta tuna, ido ta xare tace
"Nashiga uku Ma'u kin yanjomin"
Ita kanta Ma'u ta tsorata da irin kiran
"Ashe ba ita kadai kewa wannan Mugun kiranba"
Kasa amsa kiran Zahra tayi tana zulumin mexai faru don baxata manta ranarda ya mata dan banxan duka akan yasata hada masa tea ta manta tayi bacci bata hadaba
Tausayi da daria su suka haduma Ma'u lokaci gudu
"Ji yadda take xare ido kamar mata sun tare barawo a daki kamar ba yanxu ta gama xaxxaremin idoba, ko bbu komai yanxu nadanji dama dama tunda bani kadai xai dinga na dukaba"
Turo kofar Bature yayi da karfi ya shigo, wani mugun kallo yake aikawa Zahra data fara hawaye, da sauri taje gabanshi ta sunkuya ta kama kafarsa
"Don Allah Sweetheart kayi hakuri wlh na manta ne ina nan ina shirya Ma'u"
Duban Ma'u yayi wadda ta tsadda kanta kasa don gudun kada ya sauke mata haushin laifinda ba nata ba don ba yau suka saba hakan ba
"Ita Ma'un jaririyace dasai kin shiryata?"
Bature yayi tambayar har yanxu idonsa nakan Ma'u
"Taki shiryawa ne sai kuka take wai a maidata gida"
A raxane Ma'u ta dago kanta tana dubi Zahra daga bisani ta maida kallonta ga Bature wadda ke mata kallon xan babbalaki
Fashewa itama tayi da kukan neman afuwa
"Wlh na daina, Allah baxan sakeba xan xauna anan har karshen rayuwana"
Yadda tayi tsosai ya bawa Bature daria amma ya kunshe kayansa yajanye kafarsa daga rikonda Zahra ta masa ya fice yana cewa
"Saura na rigaki isa dakin"
Da gudu Zahra ta mike tabi bayansa , yayinda tabar Ma'u na share hawayenta tana mitar wai Zahra ta mata sharri so take kawai Bature ya daketa(kujimin Ma'u)
Bature Estate
"Fateema, Fateema, Fateema" tun daga bakin part din Mami, Ammi ki rangadawa Mami kira
Mami dake bedroom a lokacin ta idda Sallah Isha'i ta fito da sauri don tasan za'a Rina
A falo sukaci karo daga ganin fuskar Ammi ranta yayi baci
"Wato kina kallo Ma'u taxo ta kwashi kayanta na part na gaba daya ta dawo dashi part dinki, don ki nunamin uwa daya uban dayane keda marigayiya Asma'u sai kika amsheta ko, tokada ki manta anan(ta nuna cikinta) Muhammad ya fito, kuma Abdullah (babansu Mami) ni na bar mishi nono ya kama kinga ta ko'ina na fiki iko da Ma'u"
Kai kawai Mami ta tsadda kasa daman tasan komai kanta xai dawo shiyasa ta hana wannan al'amari nan ma wai Ammj batasan tafia Bature yayi da Ma'u ba
" ke baki san Ya Bature ne ya tafi da Ma'u ba"
Cewar Batool dake xaune a falon tana assignment
Kirji Ammi ta dafe ta kalli Mami ta kalli Batool
"Ke don ubanki me kikace, Bature Mugu shiya tafi da Ma'u, kinga bana wasa da ubanki balle ke don haka fadamin gaskia"
Baki Batool ta tura tace"ai nima ba wasar dake nakeba shiyasa na fada miki gaskia "
"Fateema abunda ta fada hakene?" Ta tambayi Mami tana kallonta
"Ammi nima bada bakina ya tafi da ita ba"
Daka salle Ammi tayi ta dire tace
"Kan uba wlh baxai sabu ba, ina karyane duk wadda ya bawa Bature bakin tafia da Ma'uta wlh a yanxu yanxun nan ba sai anjimaba xai bashi bakin dawomin da ita, ke don ubanki tashi ki kirawomin kowa da kowan Gidan Bature suxonan su ina son ganinsu kuma duk wadda ya batamin lokaci yasan sauran"
Yadda Ammi tai maganar bbu wasa yasa Batool saurin mikewa gudun kada ta kawo wargi Ammi ta mammaketa ta fice
Dakyar Mami ta lallaba Ammi ta xauna a kan kujera tanata mita
Bayan 10 minutes kowa da kowan Gidan Bature ya hallara a falon Mami, duk wadda ya iso yaga fuskar Ammi sai yasha jinin jikinsa
Cikin bacin rai Ammi ta fara magana
"Wani Uban Asma'u ne ya bawa Bature ikon tafia da Ma'u don wannan umarni sai daga bakin Moddibo Hamman Ubana kenan, shi sai xai iya bada umarni bada neman shawarata ba kuma umarnin ya xauna, ganin kuma yanxu shi Modibbon ya rasu to sabon ubana din yayi gaggawar kiran Bature kamar yadda ya bashi umarnun tafiya da ita ya dawomin da ita yau din nan basai gobeba"
Baki Jidda, Batool da Ummi suka tabe lokaci guda
Cikin rarrashi Abba yace
"Don girman Allah Ammi kiyi hakuri ki bar Ma'u ta xauna a can"
Mugun harara Ammi ta hurga ma Abban
"Yanxu nasan ashe Kaine ka bawa kanka matsayin Modibbo Hamman"
Cikin sauri Abba ya girgixa kansa
"A'a Ammi bbu wadda ya bawa kansa wannan matsayi"
"Toh ga xahiri ga abu a bayyane"
Cesar Ammi
Jidda data kagu a sallameta don har ta fara bacci aka tasota tace
"Wai nikam Gidan Ya Baturen kabarine da Ma'u baxata iya xama ba, akan annoban Ma'unki kinbi kin dagawa mutane hankali"
Kuka Ammi tasa hadda hawaye
"Shikenan dunia taxo karshe, yar uwarki kike kira da annoba, Ku kuma kuna kallonta tana ciwa ni uwarku mutunci"
"Idan na sake jin kin bude bakinki a wajen sai na bata miki rai, don Allah Ammi kiyi hakuri"
Cesar Abba dayaxo ya durkusa gaban Ammi, haka Abbu ma yayi suna lallashinta Amma Sam Ammi ta dire tace
"Wlh baxan bar kukan nan ba sai kun kira Bature ya maidomin da Ma'uta Allah nasan ko kwana daya Ma'u tayi a Gidan Bature sai na kabari ya fita jin ddi"
Ba don Abba yasoba ya dau waya ya kira Bature
Yunwa ne ya fito da Ma'u daga bedroom dinta rabonta da abinci tun jiya daddare don ko da Zahra tace taxo suci lunch banxa da Zahra tayi Bature kuma yace abarta ai yunwan ba kanin Ammi bane balle ya raga mata
Ai kuwa ya mata mugun kamu dakyar ta samu ta idda Sallah isha'i, ta nufi inada ta tabbatar dining space ne
Cikin sa'a taci karo da abinci kala-kala da chief Samuel ya hada na dinner
Har Ma'u ta dau plate xatayi serving kanta ta hangi wata tana kokarina shiga wani daki da alama yar aikine
Da karfi tace
"Ke xonan"
Bbu musu Tawa mai aiki taxo gaban Ma'u cikin gurbataccen hausarta tace
"Gani Madam( su Madam Ma'u)
Wani dadine ya xiyarci Ma'u don tanason girmamawa haka take da masu aikin gidansu ma duk wadda kece mata Hajiya Ma'u to suna shiri ssai
Jan dinning chair tayi ta xauna irin xaman Madam tace
" kiyi serving dina"
Marairaice fuska Tawa tayi tace
"Sorry Madam sai anyi serving na Sir kan ake na kowa"
"Uban Uban Sir Oyo xok..........."
Sauran kalaman tayi saurin hadiyesu ganin Bature da Zahra a kanta
Ba karamin raxana tayiba da sauri ta mike daga kan kujerar tana raba ido
Bbu shiri Tawa tabar wajen tayi inda ta fito don daman ba itace mai serving dinsu ba
Ganin baida niyar hukunci yasa Zahra ja masa kujera ya xauna itama ta xauna tayi serving dinsu, har a lokacin Ma'u na tsaye kamar an dasata
"Zauna kici abincinki idan kin gama sai ki nunamin Uban Ubana din, idan xaki kabari ki tono sa nema ya rage naki"
Kasa kasa Zahra ke dariar mugunta, yayinda Ma'u ta xauna tana hawayen tausayin kanta
Sun dau kusan minti 15 suna cin abinci jefi jefi Zahra kema Bature magana sai dai ya kada kai kawa tsabagen miskilancinshi
Itako Ma'u dakyar take hadiye abinci don ko taste nashi bata ganewa tsabagen tashin hankali
A tare Ma'u da Bature suka bar kan dinning din suka koma kujerar cikin falon suka xauna
Ma'u ko baxan kunne tayi Rana jiran Cesar Bature
" da a gidane iron wannan Samar da tuni na waske gun Amm...."
Bata karasaba jin muryan Bature na magana
"Da alama kin gama tashi ki fara favorite dinki kan kixo ki nunamin Uban Ubana din"
Bbu musu Ma'u ta mike ta hau frog jump duk da ranta bayaso amma bbu halin musu ya bubbugeta kuma tayi
Bai kai minti 1 da farawa ba wayar Bature ta hau ringing
Zahra dake kwance a jikinka tasa hannnu ta miko mai wayar ganin sunan Abba yasata sa daria tace" To Ammi ma ta fara tata"
Baku Bature ya tabe yayi picking call din
Ummu Subay'a♥
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
Gaisuwa ta musamman ga
Ummu Muneeb
Happy Anniversary🎂🎂
Kainuwa Writer's Association
Allah ya kara mana Basira, hikma, Fikrah da haxaka
Allah ya kara mana son junanmu
Jinjina ga
Batool Adam Jattko
Anty Fauxy (Mrs Talba)
Maman Rufaida
Zainab Goni
Maimuna Matar Abdullah
Halima Mk
Khairy
Da duk WRITER'Sna KAINUWA wadda ban ambaci sunansuba
KAINUWA DASHEN ALLAH BA DASHEN MUTANEBA
0⃣7⃣
Handsfree Bature yasa bayan yayi picking na wayar
Maimakon yaki muryan Abba sai yaji na Ammi
"Ba Bature kake ba ko Nasara kake ka dawomin da Ma'u ko na wanke kafa naxo Abujan don kasan Abujan ba bako na bane tun kan na haifi ubanka nake xuwa Abuja"
Hannu Zahra tasa ta rufe bakinta da daria ke shirin kubce mata kada Ammi taji ta samu nata kason
Tsayawa cak Ma'u tayi tana Allah Allah Bature ya yadda ya maidata
"To ni meya dameni da sanin Abujanki, Ma'u dai gata da yardarta naxo da ita, idan kuma kin musu gata kiji daga bakinta"
Cewar Bature yama Ma'u dake kallonshi alama taxo
Jiki bbu karfi Ma'u taje gaban Bature ta durkusa,idonta sai tsiyayar kwalla yake
"Ko kunne dubune a jikina wlh baxan yadda Ma'u ce ta amince xata bika ba dan rainin hankali"
Mikawa Ma'u wayar yayi tare da mata mugun kallon kashedi
Jiki na rawa Ma'u ta amshi wayar cikin sanyin murya tace
"Hello Ammi"
A dayan bangaren Ammi tace
"Ma'uta ya akayi kikabi Bature, ni nasan ba da amincewarki