Showing 15001 words to 18000 words out of 45410 words
bane koh"
Kai Ma'u ta daga alamar "eh" kamar Ammin na gabanta, kafarta Bature ya shure, tayi saurin cewa
"A'a da amincewata ya tafi dani, ni nafison xaman nan"
Ganin kuka na shirin kubce mata ne yasa Bature hanxarin karbar wayar yace
"To ai kinji da kunnenki sai kibar mutane su huta"
"Duk wannan mana kisanka ce dan goyon Hauwa ai bbu abunda baxaka iya......."
Kyat Bature ya katse kirar don bayason a xaga masa Umminsa
"Oya tashi kiban waje Mayya"
Cewar Bature yana kara janyo Zahra jikinsa
Tashi Ma'u tayi ta nufi bedroom din tana kuka a hankali gudun kada Bature yaji ta kuma wani laifin
Bature Estate
Mikawa Abba wayarsa Ammi tayi tace
"Nidai wlh ban yarda Ma'u bace ta amince tabi Bature kawai makiyane suka shirya koma kuma nasan manakisankine Hauwa"
Murmushi Ummi tayi don idan da sabo ta saba jin irin wannan daga bakin Ammi
"Kuma ya xama dole Shukrah ta tattara kayanta ta koma part dina don baxan xauna nidai kamar mayyaba"
Ammi ta dora xanceta hadi da mikewa don barin falon
Abbu da Abba suka Mara mata baya hadi da lallashinta
Ummi ma mikewa tayi tace
"Oya Shukra mike muje ki tattara kayanki ki koma tun kan ta biyoki"
Daria Batool tasa tace"second Ma'u saura kema ki dinga hada bomb"
Duk daria suka saka Jidda tace
"Su Ma'u ansan an shiga Barrack bakuji muryanta har wani laushi yayi Ba"
"Idan kika bibiyema lokacin tana punishment"
Cewar Batool tana kokarin shiga bedroom din Mami
Haka duk suka watse suna dariar Ma'u
Washegari sai 8:30 Ma'u ta fito daga dakinta, Zahra ta hango xaune tana kallon tashar Zee Tv
Fuska a hade taje ta xauna kusada Zahra tace
"Ina kwana Anty"
Janyota jikinta Zahra tayi tace
"Lfy klau Ma'un Ammi, ya kuka? Ya bakunta? Ya kewar Ammi?
Hawayene ya taru a idon Ma'u kamar xatayi kuka tace
" don Allah Anty Zahra ki taimakamin ki roki Ya Bature ya maidani Kaduna wlh na daina rashin jin, xan kiyaye komai Allah"
Murmushi Zahra tayi tace
"Idan kinason ki koma Kaduna sai kin natsu ssai Ma'u, daga gidannan ki fara natsuwa idan Ya Bature ya ga kin natsu nasan dakansa xai maidaki basai an rokaba"
Tura baki Ma'u tayi tace
"To kiramin Ammina mu gaisa kinga ko wayata ban daukaba"
Kada kai Zahra tayi tace"bbu ruwana so kike Ya Bature ya sassaba mana"
A hankali Bature ke saukowa daga stair case, uniform ne a jikinshi ya amsheshi ssai sai wani kyalli yake a ciki, fuskarsan nan tanan kamar yadda take bbu wata walwala a tattare da ita
Harara Ma'u ta watsa mishi ta gefen ido tace
"Ga kyau bbu kyaun hali"
Murmushi Zahra tayi dataji me Ma'u tace, dan buginta tayi a baya kasa kasa tace
"Bakyason komawa Kaduna"
Dan tura bakinta tayi tace
"Ina kwana"
Baki Bature ya tabe ya wuce dinning space ko kallo bata isheshiba
Itama Ma'un tabe bakin tayi
Rabata da jikinta Zahra tayi tace
"Dagani kigani naje nayi serving Babyna"
"Hmmm"
Ma'u tace ta gyara kwanciyarta kan 3sitern
"Baxakiyi breakfast din bane"
Cewar Zahra dake tafia dinning space
"Sai kun gama"
Ma'u tace ta maida hankalinta kan TV
A yangance Bature ke cin abincin yayinda Zahra ta tsaresa da ido tana murmushi
"Madam kallon fa na menene"
Sipping na tea yayi kamar bada ita yake maganar Ba don idonshi nakan Ma'u
"Honey wlh kullum kara kyau kake, kamannin Turawan sai kara bayyana yake, inda na godewa Allah Mijinah bbu ruwanshi da wasu matan duk da kasancewarsa mabukaci"
Zahra tayi maganar tana kokarin kai spoon din Russian Potato's bakinta
Murmushin Rabin baki Bature yayi yace
"Saboda Zahrarsa na bashi dukkan hakkinsa kuma tana masa yadda yakeso"
Murmushin jin dadi Zahra tayi bata kara wani kalmaba don tasan halin abunta bayason Jan xance
Tsab Bature ya karanci Ma'u tanason kallon fina fanan soyayya, duk inda take Zee TV na wajen, idan ana xuba love har wani limshe ido take kamar wata mai Masoyi
Ko yanxu ma love ake xubawa a film da ake haskawa a Zee TV limshe idonta tayi hadda wani dan mika duk Bature yana kallonta
Dafe kansa yayi da wata xucia tace masa
"Kodai ta dau irin Sha'awar kane"
Kai ya girgixa
"No idan ta dau akwai matsala ai baxata taba iya jurewa ba"
" tunanin me kake Sweety"
Muryan Zahra ce ta katse mai tunanin dayake, ya sauke ido daga kan Ma'u ya mayar kan Zahra yace
"Abunda ya shafi aikine Darling"
Bbu wadda ya sake magana har suka kammala break fast Bature dai jefi jefi yana kallon Ma'u
After One Month
Shakuwace ssai ta shiga tsakanin Ma'u da Zahra ssai sun fahimci juna
Ma'u ta fahimci xafin Zahra sai an tabota ne take nuna, ita kuma Ma'u bbu hanyar daxata tabota shiyasa take jin dadin xama da ita
Itama Zahra ta fahimci fitinar Ma'u ganin idon Ammi ne don yanxu kamar ba itaba, sai dai son jikin har yanxu yana nan wannan nema kesa wataran ajisu
Ma'u da Goga Bature kam bbu yabo bbu fallasa, idan Bature sukayi nisa Muhammad yaxo suna hira da shima tare da Zahra, idan Bature na goshi kuma ko kulasu bayayi
A satin ne Bature suke shirye shiryen xuwa England don hallaran yayesu Hisham da Abdullah daga Cambridge University
Ana washegari xasu tafi Balarabe da Jidda suka iso Abujan
Jidda da Balarabe sunji dadin yadda sukaga Ma'u ta sauya, Jidda hadda wani doronta wai ta iya bada shawara
Zaune kan bed Bature yake yana aiki a laptop dinsa yayinda Zahra ke hada musu kaya
Bayanta gama ta xauna a bakin bed din tace
"Sweety har yanxu banji kayi magana akan inda Ma'u xata xauna kan mu dawo, ko xa'a barta anan ita dasu Tawa"
Kamar badashi take maganaba sanda ya gama abunda yake cikin laptop din ya rufe ya ajiye a kan bed side table, ya janyota jikinsa yayi kissing na neck dinta kan yace
"Nariga na gama magana da lieutenant Shehu xata xauna a can kan mu dawo"
Shigewa ssai Zahra tayi jikinshi tace
"Ai kuwa Matarsa Falmata tanada kirki, Ma'u xataji ddin xama wajenta"
Bakinshi ya tura cikin nata ya farasha abun mamaki sai xuciarsa na xayyano mass kalar bakin Ma'u dashi yakesha xaifi wannan dadi
Rintse idonsa yayi yana kokarin kawarda tunanin a xuciarsa amma ina ya kasa, komai ya taba na Zahra sai ya dinga imaging da nake Ma'u ne dayafi wannan dadi
Pls kuyi hakuri da wannan
Heart you all fans♥
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
0⃣8⃣
Bature Estate
Zaman Gidan Bature yayi dadi ssai ga ahalinta, bbu tashin hankali da raba fada ko fargaba kowa jin dadin rayuwarsa yake
Hatta 'yan aikin Gidan sun samu sariri don suma Ma'u tasa su a gaba
Zaman Ammi da Shukrah gwanin sha'awa bbu uhmm bbu uhm uhm
Ita kanta Ammi ta samu kwanciyar hankali har tadanyi kiba, gudun kada a mata daria ne yasa take maganar Ma'u
Xaune Shukrah da Batool suke a garden
Batool na chatting yayinda Shukrah ke karanta The Still Born na Zainab Alkali
Kowa ya maida hankali kan abunda yake
Ihu Batool tasa dataci karo da status na Hisham da Abdullah sunyi posting pics na Graduating dinsu
" wooow wannan damuwar kyaun fah,Sis dubi yadda Bature Family muka haskaka a England "
Karbar wayan Shukrah tayi
"Woow kyau kenan, ji yadda Ya Bature ya saje cikin Turawan nan"
Karbe wayarta Batool tayi taci gaba da kallon pics din tana yabawa
Hade rai Batool tayi ta tura wayarta kan table dake gabansu taja dogon tsaki
Da mamaki Shukrah ke kallon Batool tace
"Sis meya faru kuma?"
Wani tsakin Batool taja tace
"Dubi yadda Ya Abdallah ya rumgume yar iskan nan kamar wata matarsa"
Daukar wayar Batool Shukrah tayi ta dubi pic din da Batool ke magana
Daria Shukrah tasa tace
"What's wrong, nidai banga komai anan ba Sis, kodai kina cikine"
Harara Batool ta ballawa Shukra tace
"Waje nake ba cikiba yar renin sense"
Daria Shukrah ta kuma sawa tace
"Idan tayi tsami maji"
Kwantarda kanta Shukrah tayi kan kujerar datake xaune, ta limshe idonta, a xuciarta tace
"Koda son Ya Abdallah xai kasheni baxan bawa kowa damar fahimtar meke cikin raina ba"
(Toh fah wata sabuwa)
Kuje Barrack
Xaman Gidan Shehu yayiwa Ma'u dadi ji take kamar kada su Bature su dawo
Falmata irin matanan ne da'ake kira kaitsatattun mata, ta iya komai don janyo hankalin miji
Tunda ta dora idonta kan Ma'u jininsu ya hadu jinta take kamar kanwarta uwa daya uba daya
Fahimtar wacece Ma'u yasata cin alwashin sai ta xamar da Ma'u katsaitacciyar mace
Da dabara Falmata ta fara nunawa Ma'u hanyar xama katsaitacciyar mace
Yau kwanar Ma'u biyu a Gidan Shehu
Suna kitchen Falmata na kirki Ma'u na kallon komai
Falmata ta dubi Ma'u tace
" Asma'u ki kalla da kyau inaso idan kin koma gidanku kije kidanga ma Oga Bature"
Baki Ma'u ta tabe tace
"Sai dai idan nayi aure nama Mijinah amma baxanwa Ya Bature ba, kinga ma can chief Samuel ne keyi"
Cike da mamaki Falmata tace
"Kina nufin Zahra batawa Oga Bature abinci"
Kwafa Ma'u tayi tace
"Tab wlh bata girki, bana tsammanin ma ta iya don gidanmu masu aikine ke girki, Mami Umman Ya Bature ce kawai ke girki a Gidan mu"
Kai Falmata ta kada tace
"Ya kamata ki koyi girki idan kinason ki xama Tauraruwa a wajen mijinki"
"Toh ai banda wadda xata koyamin"
Cewar Ma'u tana tura bakinta cikin shagwaba
Murmushi Falmata tayi tace
"Drama Queen shiyasa Babynah yace yanason dramarki, yanxu abunda xa'ayi idan kin koma sai ki dinga xuwa ina koya miki"
Wanke hannuwanta Ma'u tayi data gama yanka albasa tace
"Ai Ya Bature baxai yardaba"
"Xai yarda mana idan na rokeshi"
Falmata tayi maganar tana dauko flask don juye kunun gyadar data gama
Satinsu Bature daya a England suka tattaro suka dawo Nigeria tare dasu Hisham
Gidan Bature
Zaune suka a Palo bayan kowannensu ya kintsa kansa
Hira suke ssai suna daria banda Bature dayayi kicin kicin da ransa kamar yadda ya saba jefi jefi yake tsoma bakinsa cikin hirar
" yaushe xaku gangara Kaduna ne"
Jidda ta tambayi su Hisham
"Jibi insha Allah xamu gangara"
Hisham ya bata amsa
Daria Abdallah yasa yace
"Ammi ikon Allah"
"Ammi dake Kaduna meya hadaka da ita"
Balarabe ya jefa masa tambaya
Ajiye wayarsa gefensa Abdallah yayi yace
" yanxu Shukrah ke isarmin da sakonta wai mu dawwama Gidan Ya Bature kada mu dawo"
Duk sukasa daria banda Bature daya tabe baki
Hisham yace
"Yanxu kuma mutum xai koma ya tararda bakin cikinta da Ma'untan nan"
Jidda dake bawa Amal Nono tace
" ai kana tare da Ma'u, tuni ta dawo nan"
Cike da mamaki Su Abdallah suke kallon Jidda
Kai Abdallah ya girgixa yace
"Ban amince ba Jidda, na tabbatar da Ma'u na Gidan nan bbu abunda xaisa hanata fitowa"
Daria Zahra tasa tace
"Ma'u damuwa hadda kuma kun San halinta, tana can anguwa mun bada ajiyarta kan mu dawo"
"Allah sarki duk wadda aka kaiwa ajiyar Ma'u an hada da aiki"
Hisham yayi maganar yana daria
"Silent pls"
Cewar Bature lokacin da yake kiran Wayar Shehu
Gidan Shehu
Daga wanka Ma'u ta fito, shafe jikinta tayi da lotion dinta masu kyau tasa Riga da sikat na atamfa, tana kokarin daura dankwali Falmata ta shigo dakin da sallama
Amsawa Ma'u tayi tace
"Yawwa Anty pls xoki dauramin Dankwali irin yadda kika daura taki jiya?
Murmushi Falmata tayi tace
" fuskarki ma yaci make up Drama Queen don kayan yayi matukar amsarki kamar Celebrity "
Murmurshi Ma'u tayi taji dadin yabonta da Falmata tayi
Rangadawa Ma'u make up Falmata tayi, takuwa yi kyau ssai, dauri mai matukar kyau Falmata tama Ma'u
Nan kyaun Ma'u ya bayyana na aslin fulanin Congola
Farace Sol Ma'u irin hasken Fulanin Congola, fuskarta dogone mai dan fadi, fararen idanuwantane ya karawa Fuskarta kyau, lips dinta masu dan kauri hadda wani layi layi a jiki masu matukar kyau
Baxa'a kirata doguwaba kuma bata cikin gajeru, shape nata 8figure ne wato akwai dukiyar Fulani ga kuma maxaunai tare da hips, cikinta kuma a shafe kamar wadda bata cin komai
"Tabarakhallah Mashallah"
Cewar Falmata data gama shirya Ma'u tsaf kamar wata Amarya
Juyawa Ma'u tayi ta dubi kanta a mirror sai murmusawa take don tasan ta gama kyau, ji take kamar na ita bace
"Kinga ina trolleynki, muje driver ya maidake yanxu Babynah ya kira Oga Bature yace a maidake"
Kwabe fuska Ma'u tayi kamar xatayi kuka tace
"Nidai bbu inda xani kawai su barni nan nafi jin dadin xaman nan"
"A'a Drama Queen rufamin asiri kixo muje, ko ni ban goyi bayan xamanki nan ba, kina wannan daukar wankan ai sai Baby yace shidai sai Drama Queen ya korani Maiduguri"
Ma'u batasan lokacin da tasa daria ba tace
"Na shiga ukuna wlh baxan auri Uncle Shehu ba"
"Koma yayane muje nikam"
Har bakin Mota Falmata ta raka Ma'u
"Wlh xanyi missing naki Drama Queen"
Cewar Falmata tana rufe murfin motar
"Nima xanyi Missing dinki Antynah"
Ma'u ta fada tana maida hawayen dake shirin xubo mata
Gidan Bature
Cilla Amal Abdallah keyi sama, sai daria yarinyar ke barewa dashi
Zahra dake kallonsu tana sha'awa inama diyarta ce tace
"Amal batada tsoro Sam kamar Goggonta Ma'u"
"Kai Zahra pls daina hada diyata da Ma'u, ai idan Amal ta dauko Ma'u sadakarta xan baku"
Jidda tayi maganar tana duban Amal din
Tawa ce ta shigo falon da sallama dauke Trolleyn Ma'u
Zahra na ganin trolley tace
"To Ya Hisham ga mutumiyarka ta iso"
Duk duban Tawa sukayi Jidda tace
"Ina Ma'un take"
"Tana xuwa"
Tawa ta bawa Jidda amsa ta wuce Bedroom Jidda
Da sallama Ma'u ta shigo falon tana cat walk da Falmata ta koya mata
Duk ido suka xuba mata cike da mamaki
Bature kam kamar wani mutum mutumi kafe Ma'u da ido yayi wani abu da bai tantance ko meye bane ya shiga yawo a xuciarsa, wani felling na musamman yakeji
Hakama wajen Abdallah har wani limshe ido yake yana jin wani bakon yanayi na xiyartarsa, take ya tantance Sone
"Mr Bature kana cikine"
Balarabe yaxo daidain kunnen Bature ya rada masa
Wani mugun kallo Bature ya watsawa Balarabe yace
"Allah ya sawwake Zahrata ta isheni, mexanyi da wannan kucakar"
Ganin hankalin Zahra na dawowa kansu ne yasa Balarabe Jan bakinsa yayi shiru
"Woow Ma'un Ammi kece haka kamar wata celebruti"
Cewar Jidda tana murmushin ganin Ma'u tayi fes
Itama Ma'u murmushi ta sakar musu, wadda yasa Bature Mutuwar xaune hadda wani limshe idonsa
Duk halinda yake cikin Balarabe na lura dashi, murmushi kawai Balarabe yayi yana hasaso budurin daxa'ayi nan gaba
Nagode da addu'arku Fans
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
Ina taya daukacin al'ummar duniya murnar Babban Sallah
Allah ya maimata mana ya nuna mana ta badin badada
Mahajjatan mu kuma Allah ya karbi ibadunsu ya dawo dasu lfy
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
Fans banida bakin godia da irin addu'o'in da kuka sambadamin
Nagode ssai sai dai nace Allah yabar zumuncin Kaina
Dirar mikiya nayi a garina BORNO da YOBE, duk da ku bayinane amma jininku dake gudana jikina yasa baxan mantaku ba
Yakaru
Yakura
Yagana
Falmata
Fanni
Hawwa
Mrs Zanna
Mrs Barma
Mrs Indimi
Mrs Mandira
Mrs Banki
Mamin Gana
Mamin Ari
Ummu Sarki
Ummu Maina
Ummu Shuwa
Amiratul Arab
Da duk 'yan kungiyar
KANUSHUWA
Ina alfahari daku
Kuma ina muku BARKA DA SALLAH
0⃣9⃣
Zama kusada Zahra Ma'u tayi a kujerar dake kallon nasu Bature
Dan tura bakinta tayi tace
"Sannunku da dawowa"
Duk suka amsa mata banda Bature dake satan kallonta lokaci xuwa lokaci
Kwantarda kanta tayi a jikin Zahra tace
"Nayi missing dinki Anty"
Shafa bayanta Zahra tayi tace
"Nima nayi missing dinki Ma'un Ammi, yaki ka bar Falmata?"
"Tana lfy tace tana gaidaki ma"
Cewar Ma'u tana kara shigewa jikin Zahra
Baki Jidda ta tabe tace
"Allah yasa baki mata ta'asa ba"
Tura baki Ma'u ta kuma tace
"Bbu abunda na mata har cewa take dana xauna amma tana tsoron kada na kwace mata Miji, kamar ance Mata inason mijinta"
Duk.sanda ta basu daria, Abdallah yace
"Babu ruwanki da Mijinta auren gida xakiyi"
"Wannan kam sai Gidan don bbu wadda xai iya xama da ita sai na Gida"
Cewar Hisham
Shiru Ma'u tayi bata tanka musu ba
Kiran Sallah Azahar ne yasasu Bature mikewa don tafia masallaci
8:30pm Bature ya raka Balarabe wajen business partner sa yayinda Abdallah da Hisham suka fita xaga gari don Abba ya kira gobe gobe su dawo Ammi ta daga musu hankali
"Ma'u Ma'u Ma'u"
Jidda dake shirin Shiga wanka ta kwadawa Ma'u kira
Ma'u na kwance kan 3siter tana kallon Turkish series, film din na tafia mata yadda takeso
Tanajin kirar da Jidda ke mata taki amsawa
"Nikam Ma'u bake Jidda ke kiraba"
Cewar Zahra data shigo falon yanxu, bata rai Ma'u tayi tace
"Ni banjiba"
Daidai nan su Abdallah suka shigo dauke da manyan ledoji a hannunsu
A cikin falon suka yada xango Zahra ta musu sannu da dawowa
"Ma'u ki kiyaye nifa"
Zahra tayi maganar a dan tsawace
Tashi Ma'u tayi ta xauna tace
"Me kuma nayi"
Harara Zahra ta watsa mata tace
"Ban saniba, tun ina daki nakejin Jidda na kiranki kuma sarai kinji kika shareta, idan kin samu love story kamar wadda aka bawa aljannah, idan aure kikeso.sai ki fada a miki, ga Yah Abdallah naga kamar yana ciki"
Mikewa Ma'u tayi tana gunaguni
"Ni banasonshi kuma bazanyi aure yanxuba sai nayi Master's, ita kuma Anty Jidda sai iya kiran mutane axo a dauki Amal tasan baxata iya riketa ba meye na haifarta"
Tashige cikin bedroom da Jidda ke ciki
Kai Abdallah ya kada yana murmushi yace
"Drama Queen nifa yanxu duk abunda take burgeni take"
Daria hadda shewa Zahra tayi tace
"Ya Abdallah ka fito fili kace kana ciki musha biki, amma dai ka dibo ruwan dafa kanka, mai xama da Ma'u sai ya shirya"
Bude ledan dasuka shigo dashi Hashim ya fara yi yace
"Ya shiryan kenan tunda ya fara xancen, nidai wlh baxanyi makobtaka dakaiba don ko makobtaka kayi da Ma'u sai kaji jiki"
Bugun