Showing 63001 words to 66000 words out of 154708 words

Chapter 22 - DOCTORS FAMILY COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

8033

kina nufin Maman Sumayya?" Cewar Ɗahiran tana kallon ta

"Wlh ita fa, har a asibiti an kwantar da ita, ai asibitin mu ne ma aka kwantar da ita, baki sani ba ashe?"

"Wlh kuwa ban da labari, wani ciwo take yi?"

"Ciwon ƙoda ne take fama dashi, amma yanzu an sallame ta ai".

"Allah Sarki! Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne".

"Amen amen". Daga Aunty Zulaiha har Aunty Amarya da ta fito daga kishen yanzu suka amsa.

       Ɗahira fita tayi ta wuce Part ɗin Kaka, inda ta same shi a ɗakin sa yana Sallah, Ilham kuma na wasa a ƙasa da kayan wasan da Kaka ya zube mata, dayake ba ya rasa kayan wasa a wajen sa, sabida ita da Jinior ɗan wajen Aunty Zainab, duk idan sun zo suna kawo masa su, sai ya zube musu kayan wasan saboda kar su riƙa masa kuka.

       Ɗaukan ta tayi, ta hau mata wasa tana shilla ta tare da mata rawa

Lokacin da Kaka ya idar ya kalle ta yana murmushi yace, "dayake ai akwai me gadon zinare waje na, ga shi kin biyo ta". (sunan Umma Ilham ɗin taci, Bilkisu, kuma sunan Mahaifiyar Kaka ne dama Umma taci)

Dariya Ɗahira tayi tana tashi daga kan kujeran ta dawo gefen gadon sa, tunda dama gadon ya fi kusa da wheel chair ɗin sa, tace dashi, "kai Kaka.. dama ai ina zuwa duba ka, kwana biyu ne kawai ban samu na shigo ba, amma yanzu ɗin ma ai sabida kai na zo".

Murmushi yayi yace, "naga alama ai".

Dariya ta sake yi tana cewa, "baka yarda ba ko?"

"Na yarda Matata, to ya ƙarfin jikin?"

"Alhmadulillah Kaka, ai yanzu na samu lafiya har na kere ka ma".

"Ah Masha Allah Abu yayi kyau, fata na kenan dama Matata ta fi ni lafiya". Ya faɗa yana dariya

Itama tana taya sa

Lokacin ne Aunty Zulaiha ta shigo tana faɗin, "Mata da Miji sun haɗu waje ɗaya, hira ba ya ƙare wa, to na zo ɗaukar ɗiya ta zan wuce".

"Kai Aunty yanzu fa na zo". Cewar Ɗahira tana ɓata fuska

Shi kuma Kaka yace, "Ja'ira ko kunya ta ma ba kya ji kin zo ɗaukar ɗiyar ki ko?"

Dariya ta kwashe dashi tana cewa, "Kaka wani kunyan ka zan ji? Tafiya fa zan yi, amma idan kana so in bar maka ita, ai Ni abu me sauƙi ne a waje na, wlh sai in tafi in bar maka, gaba ta kai Ni wai gobaran titi a Jos".

"To ban ce ba, ɗauki ɗiyar ki ki tafi, me zan yi da wannan mummunan ɗiyar taki?".

Dariya suka saka gaba ɗaya, ganin yanda Kaka ya taƙume fuskar sa yana kallon Ilham kamar ya ga kashi

Aunty Zulaiha tace, "ai Kaka kai ta biyo wlh, kaima ka sani, kar ka wani tsine ta. Kuma Maman ka ce babu ruwana".

Taɓe baki yayi yace, "jaaa can da Allah! Ki ɗauki ƴar ki ki wuce kin ji, duk kin cika min kunne da surutu".

"Shikenan Kaka, kora ta kake yi ko? Babu damuwa ai, dani kake zancen wlh". Cewar Aunty Zulaihan tana ƙarisa wa ta ɗauki Ilham tana saɓa ta a baya

Dama sun saba irin haka sosai, kusan a jikokin gidan, Kaka da Aunty Zulaiha sun fi wasan jika da Kaka, idan suka haɗu waje ɗaya bakin ɗayan su ba ya shiru.

Tashi Ɗahira tayi, tace wa Kakan "zata je ta raka ta". Sannan suka fice tare.


⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           *WASHE GARI*
                *12:30pm.*

             Shigowar motan Usman ɗin cikin asibitin, yasa Ayush buɗe motan Safra tana leƙa wa, sai kuma ta juyo ga Safran dake latsa waya tace da ita, "Ga shinan ya shigo".

Ɗago kai Safra tayi, tana bin waje da kallo tana faɗin, "ina yake?"

"Wannan motan". Ayush ta nuna mata motan Usman da ya ƙariso kusa da na su ya tsaya

Da ido Safra tabi motan da kallo, shi kansa motan ba ƙaramin burge ta yayi ba, bare kuma sanda tayi tozali da mamallakin Motan, hohoho ai da sauri ta buɗe motan ta fito tana sake ƙare masa kallo

Itama Ayush fitowan tayi tana bin sa da kallo tamkar zata cinye sa, a duk socond ɗaya ƙaunar sa na ƙara ruruwa a zuciyar ta, sosai yayi mata kyau tare da ƙara mata kwarjini fiye da kullum, yana sanye cikin ƙananan kaya ne, wanda koda yaushe shigan da ya saba yi kenan, sai ƙyalli yake yi, kai da gani kasan hutu da jin daɗi ya zauna masa, kuma duk wanda ya kalle sa ya san cewa ba ƙaramin haɗaɗɗen Guy bane, sosai yake da son gayu fiye da tunanin mutum, shiyasa yake fita daban duk inda ya shiga, yana zama tamkar wani tauraro me haska waje, bare shi Fari ne, ga kyawu na ban mamaki.

       Duk abun nan be ma san suna yi ba, tafiyan sa kawai yake yi ya shige cikin Hospital ɗin, fuskar sa kamar dai yanda take babu fara'a, illa kwarjini da take dashi, wanda idan ka kalle sa dole ne fuskar tasa ta burge ka, duk da kuwa babu ko ɗigon annuri, amma kwarjinin sa shi yake ƙara masa kyau.

"Gaskiya Ayush dole ne ki haukace saboda wannan Guy ɗin, Ni kaina ba ƙaramin tafiya da imani na yayi ba a kallon farko duk da Maza ba sa burge Ni, bare ke da kika saba ganin sa kullum". Cewar Safra tana kallon Ayush ɗin

Numfashi Ayush taja, kafin tace, "hmm yanzu kin yarda da Ni Ko?"

"Ƙwarai kuwa.. shiga mota mu je, ina da hanyar da za mu ɓullo masa, idan ya san wata ai be san wata ba, na saba haɗuwa da irin waɗannan guy ɗin masu murɗaɗɗen hali, kuma mun ci galaba a kansu". Ta yi maganar tana taunan cwhengum

Murmushi Ayush tayi, kafin suka koma cikin motan, Safra taja suka bar Hospital ɗin.




.



_Ko Me Za su shirya? 🤔 Muna dai biye da su ai._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

               *NASIHA*
_Muna iya lura cewa ga al'ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A'ARAF, aya ta 31:_
_"ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci"_
_Allah yasa mu dace._

.


         *EPISODE Thirty Three*

"Kina da kuɗi a tare da ke? Domin kai tsaye wajen Malami na za mu wuce".

Kallon ta Ayush tayi, sai kuma ta girgiza mata kai alamun "A'a" kafin tace, "Malami kuma Safra? Wanne irin Malami? Me kuma zamu yi a can?"

Dariya tayi still tana taunan cwhengum ɗin ta tace, "neman biyan buƙata mana Ƙawata, Ai dole sai da haka, don wlh bari kiji, irin waɗannan Guy ɗin ba naki bane, kee wlh bazan yi kaffara ba, idan har kika ce ta haka zaki jawo hankalin sa, babu taimakon Malamai, to, zaki dauwama baki yi aure ba, domin wlh sai kin ruɓe a gidan ku. Yanzu dai za mu wuce wajen Malam, inyaso zan ranta miki kuɗi idan muka dawo ki bani".

Ayush dai ta kasa cewa komi illa kallon titi da take yi, tana me tunani a zuciyar ta, "anya wannan hanyar da ta ɓullo wa kanta me ɓulle wa ne? Domin tasha jin yanda mutanen da suke zuwa wurin boka suke ƙare wa, to amma dogon burin ta fa? Hakan na nufin muddin bata nemi taimako wajen su ba, to, har abada baza ta taɓa auren Usman ba?..".

         Kai tsaye hanyar Zaria suka nufa, sun kusa shiga Zarian, sai suka karya kwana suka bi wata hanya, tafiya miƙaƙƙa suka yi a cikin hanyar me kama da jeji, domin ko kaɗan babu gida gaba bare baya. Sun yi tafiya sosai kafin suka soma hango ƙauyaku, inda suka sauka a wani ƙaramin gida da aka zagaye shi da kara, sai bukka da aka yi su da yawa a wajen, shiga suka yi gidan, inda Ayush sai kalle-kalle take yi tana biye da Safra dake tafiyan ta kai tsaye, ba tare da wata fargaba ba, ga duk kan alamu ta saba da zuwa

A bakin wani bukka dogo suka dakata, inda Safra ta hau faɗin, "an gaishe ka Malam, an gaishe ka Malam".

Daga ciki dariya ne ya biyo baya, inda yace, "Hajjaju Safra da baƙuwar ta, maraba da zuwa, za ku iya shigo wa".

Shiga Safra tayi, inda Ayush ke biye da ita

Yana da faɗi cikin bukkan, babban mutum ne fari sol yake zaune a gaban wani ƙaton ƙwarya baƙi, yana ɗaure da zanin atamfa a jikin sa yayi tamkar yanda ƴan Saudiya suke yi idan za su yi aikin hajji, sai gashin kansa me yawan gaske tamkar na mace, ya zubo masa har kafaɗun shi

Da kallo ya bi su dashi har suka zauna, kafin yace, "an sanar min da zuwan ku tun kuna hanya, kuma na san abinda ya kawo ku".

Ayush ce kawai tayi mamaki da kalaman sa, ban da Safra da ba yau ta soma zuwa ba

Kallon Ayush ɗin yayi yana faɗin, "yanzu me kike so ayi masa?"

Kallon Safra tayi, itama kuma ta gyaɗa mata kai alamun "ta sanar masa"

"Malam ina ƙaunar sa matuƙa, kuma so nake yi a saka mishi ƙauna ta yaji duk duniya babu wanda yake so face Ni, ina son ya zo min da buƙatar auren sa".

Tsare ta da ido yayi tamkar be san me take cewa ba

Sai ta kalli Safra a tsorace, sabida ba ƙaramin tsoro jajayen idanun sa suke bata ba, musamman da ya ƙure ta da su tamkar zai cinye ta

Hannun ta Safra ta kama tana son kwantar mata da hankali

Muryan sa suka ji yana cewa, "kee yarinya! Idan har aka zo nan ba a shigo min da tsoro, tun wuri ki dena jin tsoro na, idan ba haka ba, to zan saka miki wasi-wasi a zuciya, kuma duk abinda zan miki baza ki taɓa ganin dai-dai ba".

Da sauri Ayush ta gyara zaman ta tana cewa, "kayi haƙuri, bazan sake ba".

"Da yafi miki". Ya faɗa yana taɓa hannun sa a cikin ruwan dake gaban sa cikin ƙwarya, zane ya soma yi na ɗan mintoci, kafin ya ɗago yana kallon ta yace, "leƙo nan".

Matso wa tayi ta tura kanta ta yanda zata ga cikin ƙwaryan, Usman ta gani zaune a Office ɗin sa, yana shingiɗe a kan kujera idanun sa a rufe, kujeran na faman juya sa

"Wannan shi ne ko?"

Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin, "eh shi ne Malam".

Ci gaba yayi da zanen sa na ɗan wani lokaci, kafin ya ɗago yana duban su yace, "kina da rabon auren sa, sai dai a nan gaba, domin na ga gagarumar matsala tana kunno wa daga dangin sa, suna shirin aura masa ƴar uwan sa nan ba da jima wa ba. Kuma na duba duk yanda za'a yi, babu ta yanda za'a hana auren nan, dole ne sai ya aure ta".

"Malam kana nufin dai sai ya auri wata kafin ya aure ta?"

"Eh haka nake nufi".

"Amma meye mafita Malam?". Safra ta sake tambayar sa

Numfashi yaja kafin yace, "wannan yarinyan ƙaddaran sa ce, kuma dole ne sai ya aure ta babu yanda za'a yi, bazan iya muku aiki ba yanzu har sai sanda aka yi auren nasu, sannan ku dawo akwai abin yi, a nan ne nake da daman raba su ke kuma ki shiga, in har ba haka ba kuwa, babu ta yanda zaki aure sa tana cikin gidan sa". Ya ƙare maganar da nuna Ayush da duk ta gama firgita da jin abinda yake faɗa

"Yanzu Malam babu abinda zaka iya yi a kai? Ya kamata kayi wani abun, domin mun san zaka iya ne".

Cikin amon muryan sa yace, "babu abinda zan iya a kai yanzu, duk abinda kuke so ku dawo bayan auren su, a nan ne zan iya muku komi, ku tashi ku tafi".

Da sauri suka tashi sabida jin tsawan da ya danƙara musu, suka fice suka nufi motan su, hawa suka yi suka bar wajen, babu me magana cikin su har sanda suka fito bakin titi

Da damuwa a fuskar ta tsantsa Ayush tace, "yanzu ya za mu yi? Ga shi mun zo wajen Malamin, memakon samun mafita, sai faɗa min abinda ya ɗaga min hankali yayi, kuma ya ƙi mana aikin".

Numfashi Safra taja kafin tace, "ke a naki tunanin, wace ce yarinyan da kike ganin za'a haɗa su aure?"

"No bazan taɓa sanin hakan ba gaskiya, domin Familyn su babba ne, kinga babu ta yanda zan yi in gane wacce zai aura, kuma kwanan nan duk ƙannin sa suka yi aure na cikin gidan su, illa mutum ɗaya ce wacce yanzu tana gida bata yi aure ba, ban san kuma meyasa ba".

Murmushi Safra tayi tace, "tabbas ina ji a jiki na, ita ce za'a haɗa su aure, sai dai baza mu fara aiki a kan hakan ba, har sai mun tabbatar da maganar Malam, kar ki damu idan sun san wata basu san wata ba, tunda Malam ya gaza wannan aiki, uhmmm makircin mu shi ne zai yi aiki a nan".

"I don't understand?" Ayush asked looking at her

"I mean. duk ta hanyar da za mu bi don hana yiwuwar hakan za mu yi, domin cin ma burin mu, ke dai kawai ki tabbatar kin samo yarinyan ko wace ce, a nan ne zan tabbatar miki da shirin mu a gaba, inyaso sai mu koma ga Malam ya saka mishi ƙaunar ki a zuciya".





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         *AFTER TWO WEEKS*

        Gaba ɗaya ahalin gidan suna zaune a babban Parlourn gidan, yau har da Aunty Zulaiha da Aunty Zainab duk sun samu zuwa taron Familyn da suke gabatar wa a duk ƙarshen wata, haka ma Shakira da Yusra duk sun hallara, har Sa'adatu tana a cikin parlour'n, kasancewar itama yanzu ta zama ƴar gida

Abba ya soma buɗe taro da addu'a, inda Kaka ya bi su bayan ɗaya yana jin matsalolin su, tare da tambayar zaman nasu a gidajen mazajen su. sai da komi ya nitsa kafin ya kira sunan Usman

Usman dake zaune a gefen Baffa kan two seater, ya amsa mishi yana me ɗago kai ya kalle sa

"Ina muka kwana a zancen mu na auren ka?"

Dama ya san kwanan zancen, duk da an kwana biyu ba'a tayar da maganar ba, shiyasa ya sake ɗaure fuska, cike da isa yace, "har yanzu ban samu wacce tayi dai-dai da ra'ayi na ba Kaka, Ni a gani na gwara a dena zancen aure na yanzu, because I'm not ready to do it now."

Big Dady ne yayi ninyan magana, sai Kaka ya katse masa hanzari da faɗin, "to shikenan, tunda baka shirya ba, ai mu mun shirya aurar da kai yanzu". Sai ya juya ga Ɗahira yace, "What about the My wife? Are you still silent?"


Gyaɗa masa kai tayi kanta a ƙasa tana wasa da kwalliyan rigan ta

"To duk wani dama da Yakamata mu baku mun rigada mun baku, tunda har yanzu baku samo abokan zaman ku ba, mun yanke shawara Ni da iyayen ku, Kai Usman, da ke Ɗahira, za mu haɗa ku aure a tsakanin ku, ina fata dai..."

Zumbur Usman yayi ya miƙe yana dakatar da Kaka da faɗin, "haba Kaka! What are you saying? Dani da wa zaka haɗa aure?"

"Dan uban ka With you and your younger sister Ɗahira". Cewar Big Dady yana tsare Usman ɗin da kallo

Huci Usman ɗin ya soma, kafin yace, "It is not possible at all. You must change your mind soon. I will never marry this girl." Yana gama faɗa yayi hanya zai fice

Big Dady yace dashi, "Wlh if you go out, ranka zai ɓaci, come back and sit down, ka dawo nace ka zauna ko baka ji bane?"

Lumshe idanun sa yayi yana dakata wa daga inda yake, dunƙule hannun sa yayi yana faman huci, kafin kuma ya juya a zuciye ya dawo inda yake da zama ya koma ya zauna, gaba ɗaya fuskar sa ta haɗe tayi murtik, jira kawai yake yi ya amayar da abinda ke cikin sa.

Hannun ta da Kaka ya riƙo, shi ya dawo da ita hayyacin ta, ta ɗago kai tana kallon sa da idanun ta da suke zubar hawaye tun soma jin zancen Kaka

Hannun ta ya sake riƙe wa ƙam yana faɗin, "Nafeesa mene ne ya saka ki Kuka?"

Kasa magana tayi illa kallon sa da take yi, sai da taji saukar muryan Abbun ta ne kafin ta sake ƙifta ido tana mayar da idanun wajen sa, jin abinda yake cewa ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba

"Sakarci ne irin nata, amma in ba sakarci ba meye na kuka a wannan maganar?" Ya ƙare maganar yana balla mata harara

Gaba ɗaya mutanen wajen, idan ka ɗauke Sa'adatu da tayi murnan jin zancen nan, sai kuma su Abba da su sun san da maganar, amma babu wanda haɗin nan yayi masa daɗi, musamman Hajja da take jin tamkar ta shaƙe Kaka da maganar ya fito daga bakin sa, baƙin cikin ta ma har ya fi na Hajiya da take uwar Usman ɗin

Ita kanta Aunty Amarya bata san meyasa ba, sam ta ji zuciyar ta ta karye da wannan haɗin, tana ji a ranta tabbas ɗiyar ta zata shiga wani hali a kan wannan auren, tamkar dai wani abu zai same ta, "shin sun manta da cewa Ɗahira da Usman ba sa shiri ne suke son haɗa su aure?" Tayi wa kanta tambayar a cikin ranta..

Muryan Big Dady ne duk ya dawo da kowa hayyacin sa, yace dasu, "mun tsayar da ranan auren nan da wata ɗaya me zuwa, don haka ban yarda ko inji ko in gani wani ya yi maganar akasin abinda muka faɗa ba, sai kowa ya soma shiri tun yanzu, za ku iya tafiya".

Baffa ne ya riga kowa tashi ya bar parlour'n yana me riƙe da kansa

Da sauri Sa'adatu ta miƙe tabi bayan sa zuciyar ta fari karrr, ko ba komi tana gani an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login