Showing 126001 words to 129000 words out of 154708 words

Chapter 43 - DOCTORS FAMILY COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

8045

buƙatar yi, shi ke taimaka mata, ta gummaci shi ya taimaka mata da Usman ya taimake ta, shiyasa abun ya soma ba wa Usman haushi, yana a matsayin mijin ta ai shi ne ya kamata yaga jikin ta ba wani ba, shiyasa da abun ya dame sa wajen kwana huɗu da bata yi ba, sai kawai ranan na biyar ɗin dai ya cire baki ya tambaye ta "ko tana jin Kashi ko fitsari ne ya taimaka mata?"



Sosai tambayar ya baƙanta mata rai, sai ta kalle sa kamar zata make shi tace, "ba na ji ko dole sai nayi?"

Tsaki yaja yace, "na san kina ji tunda kin kwana biyu baki yi ba, sai dai idan Ni ne ba kya son na taimaka miki sai Baba Jaure".



"Allah ya kiyaye na nemi taimakon ka, abubuwan ma da kake min da zaka fasa da nafi kowa murna, ba na ƙaunar ganin ka wlh ko kaɗan a kusa dani, ji nake yi kamar zan haɗiye zuciya na mutu, mugu azzalumi kawai".

A zuciye yace, "Nafeesa Ni kike faɗa wa haka? Wato kina ganin ina ƙyale ki shi ne yasa kike faɗa min duk abinda kike so ko?"

"An faɗa ɗin, ka kashe Ni ka huta shi ne zan san ka isa". Ta ƙare maganar tana sakar masa kallon tsana


Hannun sa ya saka ya murɗe mata baki yana cewa, "bakin zan fasa ko zaki dawo hankalin ki kisan da wa kike magana, Ni ba sa'an wasan ki bane, ina ƙyale ki ne kawai domin ina tausaya miki".

Kuka ta fashe dashi jin ya murɗe mata baki sosai


Ganin tana kuka sosai sai ya sassauta riƙon amma fuskar sa a ɗaure yace, "ke ki shiga hankalin ki kisan da wanda kike magana, Ni ne Usman kuma na san baki manta halina ba, wlh bar ganin kina halin lalura biji-biji dake zan yi".



Bata iya cewa komi ba illa kuka da take faman yi


Ganin haka sai yaja tsaki yana tashi zai fice


Ƙasa-ƙasa tace, "mugu azzalumi Allah zai saka min wlh, kuma kashi ne bazan yi ba, kuma ma ina jin yi har da fitsarin ma".

Dariya taso ba shi sai dai be juyo ba yayi ficewar sa


Ita kuma taci gaba da kukan ta tana yi tana tsine masa a ranta


A haka har Baba Jaure ya dawo, yana shigo wa ya ganta tana kuka ya tambaye ta ba'asi

Sai tace mishi, "Usman ne ya murɗe mata baki sannan ya falla mata mari". Har da riƙe kumatun ta tana me fashe wa da wani kukan

Salati kawai Baba Jaure yake saki yana faɗin, "ashsha.. be kyauta ba, wannan ai mugunta ne, ba ya ganin halin da kike ciki ne?". Sai kuma ya koma kwaɗa wa Usman ɗin kira


Usman dake waje duk yana jiyo ƙaryan da Ɗahira ta shirga mishi, ci je leɓe kawai yayi yana jinjina kansa, sai ya miƙe ya nufi ɗakin ba tare da ya amsa ba, yana shiga idanun su suka shige na juna


Sai ta balla mishi harara tana kawar da kanta

Shi kuma fuskar nan a ɗaure kamar ko yaushe yake sauraron faɗan Baba Jaure ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba, duk da kuwa ba kallon sa take yi ba, "zan kama ki ne yarinyan nan zai fita ai, zan mare ki sai ki sami faɗa mishi da hujja tunda ke baki da mutunci". Yayi maganar a ranshi


Sai da Baba Jaure ya gama mishi faɗan kafin yayi ficewar sa be ce komi ba

Ita kuma sai a lokacin ta dawo da kallon ta ga Baba Jaure tace mishi, "tana buƙatar zata yi fitsari".


"To kuma sauri nake yi ina da rubutu a gaba na, meyasa baki ce Usman ɗin ya taimaka miki ba?".


"Baba na Ce mishi amma yace bazai taimaka min ba, shi ne dalilin da yasa ya mare Ni".


Baba Jaure yace, "be kyauta ba kuwa, bari in taimaka miki to, zan yi masa magana daga yau bazai sake ba".


Taimaka mata yayi ya ɗan ɗaga ta ya saka mata wani Robber me faɗi, sai ya koma bakin ƙofa har sai da ta gama ta gyara kafin ya dawo shi kuma ya gyara mata kwanciya ta yanda baza ta motsa ƙafafuwan ba.




     Duk abinda ta sake faɗa a kunnen Usman ya faɗa, kaɗa kai kawai yayi ya yi ficewar sa a gidan, ransa babu daɗi duk haushi ya cika sa, haka kawai yake jin haushin Baba Jaure Wanda be San dalili ba, "don me shima zai yarda ya riƙa taimakon ta bayan ga shi shi ne mijin ta? Ai wannan ma cin zarafin sa ne da kuma keta mishi haddin aure". Sosai zuciyar sa ke a ɓace shiyasa ya nufi jeji kansa tsaye don keɓe kansa, amma wani zuciyar nasa tana faɗa masa, "kai meye naka na jin haushi bayan sakin ta zaka yi? Ko ka manta ka tsane ta ne? Sannan ma Baba Jaure ai kamar Kaka yake a wurin ta, halin lalura ne ya kawo haka dole sai an taimaka mata". Dogon tsaki kawai yaja a fili ya furta, "to Ni ina ruwa na.. yayi mata wanka ma idan zai iya be shafe Ni ba".
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




            *EPISODE Fifty Eight*


           Sannu a hankali Ɗahira ta soma jin sauƙi, domin babu laifi yanzu tana iya ƙoƙarin ta wajen jure wa da zaman nata, ba ta motsa ƙafafuwan kullum kaffa-kaffa take yi, a haka rayuwa taci gaba inda kusan watanni huɗu kenan da soma jinyan nata, yanzu har ta soma taka wa


Baba Jaure ya haɗa mata sandan nan guda biyu da zata riƙa dogara wa


Tun ba ta iyawa da taimakon Usman da Baba Jaure ya saka shi yana koya mata tafiyan, har yanzu tana iya fita zuwa waje wani lokacin ba tare da taimakon shi ba, zaman jinya ba wasa ba, gaba ɗaya ta sauya tamkar ba ita ba, tayi wani irin haske kamar mara jini a jiki, sai kuma ƙara ramewa da tayi a fuska, sai kuma ɗan kumbura da tayi a jiki, sai dai jikin nan nata luwai-luwai kamar ka taɓa jini ya tsiyaya, saboda zama wuri ɗaya da ta jima tana yi, duk ta sauya dai. Yanzu haka har wanka tana yi da kanta, inda Baba Jaure ya samo mata itama kayan su na Fulani tana sauya shiga.



              Ga shi yanzu har sun gabatar da azumi a wannan ƙauyen, sai dai ita Ɗahira bata samu tayi ba saboda halin da take ciki, an yi sallah an gama lafiya kuma sun yi farin ciki matuƙa kasancewar sun fita sun kalli wasan sallan mutanen ƙauyen.



                Duk da gefe ɗaya kuma gaban su da Usman kullum daɗuwa take yi, kusan kullum sai sun yi faɗa, ita bakin ta bazai yi shiru ba babu ranan da baza ta sanar mishi ta tsani ganin shi a rayuwar ta ba


Shi kuma hakan na mishi zafi sosai, sai ya biye mata suyi ta yi tana ƙara ƙona mishi rai, shi kuma a ganin shi yana ƙyale ta ne don halin lalura, ba don haka ba zane mata jiki zai yi, amma duk da haka tsaban mugunta be fasa mangare ta ba ko kuma ya kwaɓe mata baki idan tana gaya mishi maganar da yayi mishi ɗaci a zuciya.



Yau ma tana zaune a waje tana shan iska


While Usman na zaune can gefe ya buga tagumi yana bin ta da kallo, sai dai a baɗini tunani ya faɗa be ma san idanuwan sa na kanta ba


Ita kuma ganin yaƙi dena kallon ta tun ɗazu sai taja tsaki tana yinƙura wa zata tashi

Tsakin nata ya dawo dashi hayyacin sa, sai ya bi ta da kallo kawai har ta miƙe, ganin ta nufi ƙofar gida zata fice sai yace, "ina zaki je?"


Bata juyo ba bare ta tanka shi, taci gaba da ɗingisa wa a hankali zata fice


Shima sai be sake ce mata komi ba ya kawar da kansa gare ta, ya ɗaura tunanin sa daga inda ya tsaya.



              Ɗahira na fita ta soma bin garin da kallo, tun ranan sallah da ta fita sai yau ta sake saka ƙafafuwan ta a wajen, shiyasa kawai take ta bin ko ina da kallo, yanda ko ina yayi kore sharr da bukkokin gidaje sai ya bata sha'awa, tamkar dai babu kowa a garin haka wajen ya ɗaɗe, takawa ta soma yi tana ci gaba da tafiya tana kallon ko ina, jefi-jefi kuma ta soma ganin Mutane, yara a waje suna wasa da kuma hayaniyar mutanen cikin gida


Yanda suke wasan ne sai ya ɗauke mata hankali ta shagala tana kallon su


Suna ta wasan ƴar gala-gala ne maZan su da matan su, sai dai sun raba ne idan mata suka yi sai maza su yi, kowa yana son ace su ne gwani. Duk basu lura da ita ba duk tsayuwar ta


Har ta soma gajiya tana shirin juya wa sai sandan nata ya gurɗe zata faɗi, sai ji tayi an tare ta ta faɗa jikin mutum. Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa zuciyar ta na wani irin bugawa a lokaci ɗaya da nashi, waro ido tayi kawai tana kallon shi tana ɗauke numfashi tsamm sabida yanda taji wani abu ya tsarga mata a cikin jikin ta wanda baza ta iya fasalta shi ba

Shima haka zalika abinda taji shi ya ziyarce shi, shi nashi ma har wani nauyi zuciyar tashi tayi mishi tare da tsantsan tsoron da ya saba ziyartan shi a duk sa'ilin da ya haɗa ido da ita, sai dai kuma yanda yake jin wani iri kamar an manne masa idon cikin nata ya kasa ɗauke su a kanta


Illa ita ce da tayi ƙoƙarin fizgar kanta sa'ilin da ta gama tantance a jikin wanda take, wani irin fisga tayi wa kanta saboda haushin ganin ta a jikin sa da saura ƙiris ta gurɗe ta zube ƙasa


Sai ya ƙara azamar riƙo ta da sauri yace, "ke kina da hankali kuwa?"


Wani kallo ta sakar masa cike da baƙin ciki ta kasa ce mishi uffan, ta sake yinƙurin janye jikin nata da ƙarfi duk dan ta raba kanta dashi


Yana shirin sakin ta ganin abinda take so kenan, sai sandan ta ɗaya ya faɗi, dole ta ɗage ƙafa ɗaya don baza ta iya ba da ƙarfin ta a ƙafafuwan gaba ɗaya ba, tuni hawaye sun cika mata ido saboda azaban da take ji tayi saurin ƙanƙame mishi hannu, shi kuma sai ya duƙa ya ɗauko mata sandan


Yaran wajen tuni hankalin su ya dawo gare su sun tsaya suna ta kallon su kamar wasu t.v

Su kuwa basu san ma suna yi ba, domin tuni Ɗahira ta bizge sandan nata ta daidaita su ta soma ɗingisa wa a hankali


Yanda take yi ne kamar zata sake faɗi sai yayi saurin kawo hannu zai sake tare ta yana cewa, "Please kiyi a hankali manaaaa". Ya ƙare maganar cikin jan kalman ƙarshen in a cool voice

"Kar ka sake taɓa Ni?" Tayi maganar hawayen idanun ta na sauko mata a kunci. Sai ta sake janye jikin ta sosai kafin tace, "ko kaɗan ba na buƙatar taimakon ka. Ko ka manta a baya ma baka taimaka min ba sai yanzu? So please zan iya da kaina ba tare da taimakon ka ba, kar ka sake yinƙurin taimaka min na roƙe ka".


Kalaman ta sun ba shi haushi sai yace, "kina tunanin zaki iya wani abun ne ba tare da taimako na ba? Idan da ban taimaka miki ba babu yanda za'a yi ki kawo yanzu a raye. Waɗannan mutanen da suka ɗauke ki da tuni yanzu sun aikata nufin su a kanki da ban amso ki a wajen su ba, so ki iya bakin ki Please ba na son cika baki, kar kuma ki ga ina kula ki ki ce komi ne zaki riƙa faɗa min". Yaja dogon tsaki yayi gaba abin shi fuuuu kamar ana tunƙuɗa shi


Ita kuwa da kallon banza ta bi shi hawaye na sake kwaranya a fuskar ta kamar an kunna famfo, tana jin zuciyar ta na mata ƙuna da maganganun sa. Shiyasa ko jirgau ta kasa yi duk da kuwa yanda yaran nan suka mamaye ta suna bin ta da kallo sai surutu suke yi, amma ba ta jin su illa bin hanyar da yabi da kallo da take yi ta kasa ɗauke idanun ta..





"Nafeesatu lafiyan ki kuwa? Me ya fito dake waje?"


Maganar Baba Jaure da yayi ya dawo da ita tunanin ta. Saurin kallon sa tayi


Sai ya sake cewa. "Subhanallah.. kuka kike yi lafiyan ki me ya faru? Ina Usman ɗin?"


Duk bata iya amsa mishi tambayoyin ba illa hannu da ta sanya tana share hawayen ta

Yaran ya kalla yace, "kai ku tafi kuyi wasan ku kunji ko?"

Hakan yasa suka dare a wajen sai dai basu tafi ba sun tsaya suna kallon Ɗahira

Shi kuma hannu yasa ya gyara mata sandan da kyau yana cewa, "zaki iya tafiyan dai ko?"

Gyaɗa mishi kai tayi sannan ta soma tafiyan a hankali yana biye da ita a baya.





      Suna shiga gidan ya nufi ɗakin da Usman yake kwana ganin be ganshi a waje ba


Yana ciki kuwa ya kwanta idanun sa a rufe, sai dai tunani ne fal cikin ransa da kuma haushin Ɗahira da yake ji, sosai ransa yake a ɓace

Nan Baba Jaure ya ɗaura masa da faɗan "barin ta da yayi ta fita ita kaɗai".

Kanzil be ce mishi ba har ya gama ɓaɓatun shi shi kaɗai yabar wurin.





     Itama Ɗahira tuni ta shige ɗaki ta zauna tana ci gaba da zubar da hawaye, baƙin ciki ne sosai ke nuƙurƙusan ta na rashin mayar mishi da martani har ya tafi, ga tsantsan tsanar shi dake ƙara rufe ta, ta tsani ta buɗe idanun ta ta ganshi kusa da ita, babu abinda ke tuna mata illa rayuwar ƙuncin da tayi sanadiyar shi, da kuma azabtarwan da yayi mata. Ita a yanzu burin ta su koma gida su Kaka su amsar mata takardan sakin ta. Nan kuwa kewan ƴan gidan su ya cika ta, ta kwanta nan tana ta murƙususu tana faman tunani.



      A kwana a tashi kamar yau ne suka zo cikin wannan ƙauyen, sai ga shi sun shafe kimanin watanni shida a karkaran, wanda ciwon Ɗahira ne ya tsayar da su har wannan lokacin domin tuni an samu hanya, shiyasa tana warke wa suka yi haraman tafiya



Inda sosai Baba Jaure ya nuna rashin jin daɗin sa, domin ba kaɗan ba ya shaƙu da su a wannan watannin da suka yi tare da shi, bare shi ba me kowa ba, shiyasa rabuwar nasu zai yi masa ciwo, sosai yayi musu nasiha a kan riƙe addu'a domin shi ne takobin mumuni, duk wani halin da suke ciki su dage su riƙa kare kan su da addu'a don suna da maƙiya masu bin su da sharri, sannan yayi musu nasiha kan zamantakewar aure da ya taɓa musu zuciya ainun, kuma yace "idan da hali su zauna su sasanta su riƙe auren su hannu bibbiyu, duk wani saɓani dake tsakanin su su yi ƙoƙarin ganin sun daidaita kan su, domin ba ƙaramin dace wa suka yi da juna ba".


A sanda yake faɗan wannan kalaman nasa har ɗago kai Usman yayi yana kafe Ɗahira da ido, inda yake son ganin abinda yasa Baba Jaure ya faɗi hakan, a kuma ƙasan ranshi yana jin wani nishaɗi da be san na mene ne ba, ko kaɗan memakon maganar tashi ta ba shi haushi sai be ji hakan ba, har yana ji a ransa a yanzu zai iya yin ma iyayen sa biyayya ya riƙe ta a matsayin matar sa ba tare da ya sake ta ba, wanda kuma a ganin sa Nasihan Baba Jaure ne ta taɓa masa zuciya ainun har yayi wannan tunanin

While ita kuma Ɗahira ko kaɗan bata yi tunanin wai zata iya ci gaba da rayuwa da shi ba, ta rigada ta saka wa ranta zaman su ya ƙare har abada, shiyasa ko ɗar bata ji ba a zancen Baba Jaure, kamar yanda yake shiga ta wannan kunnen haka yake fita ta wancan kunnen, har ya kuma gama ɗin. Sai dai zuciyar ta fal da kewar sa da za su yi, har a ranta ta ƙudura wata rana zata kawo mishi ziyara ko da ita kaɗai ce.

       

     Sun fito inda Baba Jaure yayi musu jagora suka yi sallama da mutanen ƙauyen, daga nan aka ɗauke su a motan ɗiban kaya aka fita dasu har titin da zai kai su cikin gari, inda aka sauke su suka sami abin hawa suka miƙa gida, zuciyar ko wannen su cike da wani irin farin ciki da murna na ganin yau za su koma su haɗu da ahalin su. Ɗahira tsaban zumuɗi bakin ta ya ƙi rufuwa sai wani zillo take yi ta kasa zama waje ɗaya

Inda Usman kawai kallon ta yake yi yana sake jin wani irin nishaɗi a ranshi


Dayake waje ɗaya suke zaune kuma motan a cike take fal, ita tana ƙarshen baya; shi kuma yana kusa da ita, sosai suka matsu da juna


Amma hakan be sa Ɗahira ta damu ba, ta ma manta shaf illa tunanin gida da take yi da ƙosawan su kai


Sai shi ne da zuciyar sa ta hana sa sukuni, da kuma yanayin da yake ji sanadiyyar haɗuwar cinyoyin su wuri ɗaya, lumshe idanu kawai daga ƙarshe yayi yana amsar baƙon yanayin da ya zo mishi, wanda ya kasa fassara ko mene ne, tare da tunanin abinda ya kasa ɓace mishi a rai.




     _Fans ku sanar dashi idan kun sani._







⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



      Kwana biyu kenan da farfaɗowar Baffa, wanda ya sanya ahalin farin ciki matuƙa, duk da jikin sa babu daɗi sosai amma kuma sun ji daɗi matuƙa. Haka aka ci gaba da kulawa dashi sosai kuma alhmadulillah yana samun sauƙi, tunda har ya soma magana kaɗan, sai dai abin mamaki babu abinda yake faɗi sai sunan Ɗahira, maganar tashi kenan Ɗahira.  Ɗahira, wanda hakan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login