Showing 135001 words to 138000 words out of 154708 words

Chapter 46 - DOCTORS FAMILY COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

9550

saboda tana taya uwar ta kishi

Su kuwa duk yaran gidan suna sashin su Ɗahira, dayake yafi girma nan, a nan suka shantake suna ta hira. har da su Fadila da su Salma ita ma da babyn ta ita da Shamsiyya duk sun zo

Ɗahira na cikin su ana ta washe baki, duk kansu sun yi ankon kamfala doguwar riga me ruwan zuma da ratsin fatsi-fatsi na milk

Yanzu haka ma abinci suke ci shi ne suke ta shewa

Uwar surutu Firdausi ta kalli Ɗahira tace, "wai ke yaushe ne mu kuma zamu dawo musha sunan ɗan mu? Kin wani ƙaƙabe tunda kika shige gidan Yaya Usman kin ƙi sulluɓo mana ɗa".

Dayake su ba su da labarin zaman da suka yi, iyakan iyayen su suka ji labari

Ɗahira hararan ta tayi tace, "sai ranan da kika yi naki auren kika fara sulluɓo ɗanki kafin Ni in diro nawa".

Dariya suka yi

Inda Salma ta amshe zancen da faɗin, "ai wannan rasa kunyan ba yanzu ba, zaki sha wahala kuwa idan kika ce zaki jira ta".

Gyara zaman ta Firdausin tayi tace, "faɗa mata dai, sai kun yi yara bibbiyu ko uku-uku kafin Ni nawa ke tafe".

Su Aunty Zulaiha dake zaune saman gadon Fadila na da, sun yi ɗai-ɗai suna ci a saman, a tare suka haɗa baki ita da Aunty Zainab wajen faɗin, "keee Firdausi kiji tsoron Allah, da gaske kike yi?"

Sai duk ɗakin suka kwashe da dariya

Yusra da ta bigi bayan Firdausin tana cewa, "ai kuwa da kin shiga uku kuwa, kiyi ta zama a gida babu Aure, ko da kuwa da gaske kike yi zan sami Gwaggon namu in kitsa mata ayi-ayi kema kin ƙosa tunda shigowa cikin manya kike yi kina kwasan gulma".

"Oh su Yusra manya, wlh kin daɗe baki ce mata ba, ga ƙuda can zai riga ki". Cewar Firdausin tana fuske wa

Ɗahira tace, "wai ba batun wasa ba da gaske kike yi don Allah?"

"Da gaske ne mana". Tafaɗa tana kai loman tuwon ta

Sai duk suka tsaya suna kallon ta

Shamsiyya da ta miƙe da kwanon tuwon ta, dayake ita kaɗai take ci tace, "kin ga banu kuwa, ki zauna har sai kin tsofe". Ta ƙare maganar da fice wa

Salma tace, "ku kun dauka da gaske ne? Ku dena biye ma wannan wlh an kusa saka mata rana, domin Ni da Daddy muka yi zancen nan kwanaki da naje gida".

Sai Firdausin ta ɗaka mata duka a cinya tace, "wato dama ke kika ziga shi ko? Ashe shiyasa yazo min da zancen in turo Wanda nake so, ga babban muna-fuka a gefe ina tare da ita".

"Kambu... Ni kika duka Firdausi? Dan Allah Ɗahira riƙe min yaron nan wlh sai na rama, zan ga dani dake waye muna-fuka kina so kina kaiwa kasuwa".

"To kaji kun fara ko? Dama babu daman ku haɗu waje ɗaya". Inji Aunty Zulaiha

Ita kuma Firdausi tunda taga ta yunƙuro ta tsame hannun ta cikin tuwon ta ruga aguje tabar ɗakin

Salma na mara mata baya tana cewa, "wlh ko cikin Momy kika koma sai na ƙwaƙulo ki na rama, gwara ma ki tsaya".

Me za su yi ƴan ɗakin ba dariya ba, sosai suke dariya. Inda Aunty Zulaiha take ta kwaɗa wa Salma Kira a kan "kar ta bi ta ta dawo". Amma ina tuni ta fice


Ɗahira dake ta faman dariya tashi tayi tana girgiza yaron Salman tace, "ai gwara ta bi ta ta zane mata jiki tunda Firdausi ta raina ta, kamar ba yayar ta ba".

Aunty Zulaiha tace, "to ai ga shi nan ta bar miki wannan yaron me shegen kukan jaraba, kema ki bi ta wlh duk ya kure mana kunne".

"Haba Aunty. Kema fa kin kusa haihuwar ba'a san ke kuma wanda zaki haifa ba, kin manta goyon Ilham da idan kika zo da ita gidan nan har Abbu sai yayi Magana tsaban jaraban kukan ta?"

Ai kuwa sai suka koma yiwa Aunty Zulaiha dariya

Ita kuma tana cewa, "dalla can ina Ilham tayi kukan wannan yaron, ai wlh ita idan kin ga tayi kuka sai dai abinci take nema".

Ajiye yaron tayi tsakiyan su tace, "to ga shi ku riƙe mata shi, tunda ku ne babu yara a hannun ku bari inje in dawo".

Har ta juya zata tafi caraf Aunty Zulaiha ta riƙe mata hannu tace, "dawo. Dawo nan babu inda zaki tafi ki bar mana yaron nan wlh, ki bari uwar sa ta dawo".

Su Yusra sai dariya suke musu da Shamsiyya da ta dawo sawo miya

Inda ita kuma Ɗahira ta nace sai ta tafi ta bar musu

"Ke wlh bar ganin yanzu kin soma kumari ba fi na ƙarfi kika yi ba, yanzu sai in zaune ki a nan, ki ɗauke shi kinji ko?"

Kama haɓa Ɗahiran tayi tace, "kai Aunty har da kuma sharri. Don Allah wlh yanzu zan dawo zan je wajen Kaka ne". Tayi maganar cikin marairaice fuska

Hararan ta tayi kana ta kalli Aunty Zainab da itama dai dariya take musu tace, "gane min hanya Zainab, wannan yarinyan ba tayi ƙiba ba?"

"Tayi mana, wlh da gaske Ɗahira kin yi kumari kamar ba ke ce silindiyan gidan mu ba, duk ɗauka na ma yanda kike kamar a huren nan babu abinda zai saka ki ƙiba, amma tunda kika dawo ƙauyen can naga kin sauya sosai, da alamu furan ruga ya karɓe ki dole in ce aunty Amarya ta nema miki fura ya zama abincin ki idan har tana son ɗiyar ta ta zama irin mu tubarakalla". Aunty Zainab ta ƙare maganar nata da dariya

Sai duk kan su suka fashe da dariya kowa na faɗin, "ai wlh da gaske ne yanzu duk ta sauya".

Itama dai Ɗahiran murmushi kawai tayi don ta san zancen su ba ƙarya bane

Fadila da ta shigo ɗakin yanzu take cewa, "wai me ake tattaunawa ne babu mu?"

Nan Shamsiyya take sanar mata suna dariya

Sai itama tayi dariyan tana cewa, "kin ji sister ki riƙa addu'a kina tofa wa wlh, idan ba haka ba sai dai ki tashi ki ga kin tsiyaye tsaban idanu dake yawo a kanki, ba dama dai aga mutum yayi kumari yayi ɗan kumatu sai a saka shi gaba, dama waye yace baza kiyi ƙiba ba? ai ba haka zaki zauna ba kamar ana ɗiban ki ana miya. komi da lokacin sa".






Da haka dai suka yi ta hiran su inda suka canza zancen kuma da labarin Amaryan da za'a kawo musu, kowa na faɗin albarkacin bakin shi.




       Da yamma aka kawo Amaryan Abba me suna Jamila, tare da yaran ta guda biyu Suhail da Abdulra'uf, an sauke ta ɗakin Abba inda aka gyara mata shi aka cika mata maƙil da kaya sai son barka. Su kuma yaran ta za suna kwana a ɗakin Shakira na da, don Abba har ya saka an gyara musu


Babu abinda ya kai wannan baƙin ciki wajen Hajja, tamkar ta mutu sai dai babu yanda zata yi ne, tana ji tana gani wata banza ta zo zata mallake mata gida, ina bazai saɓu ba dole ne sai ta samar wa kanta mafita.





        Haka a ranan dai aka sha biki duk aka watse don ba wanda ya kwana sai ƴan nesa.






         *************


           Washe gari Usman na Office ɗin shi wani staff ya shigo kamar yanda ya saka a nemo mishi shi

Gaishe shi yayi cikin girmamawa kafin yace mishi, "ga shi ya zo".


Kallon shi Usman ɗin yayi sosai, kana kuma yace, "kai ne wanda aka taɓa aiko ka da envelope ka kawo min?"

"Eh Ni ne". Ya amsa shi shima idanun shi a kanshi

"Ok zaka iya gane wanda ya aiko ka?"

Shiru yayi na ɗan daƙiƙu, kana yace, "eh insha Allahu idan har na ganshi zan iya gane shi".


"Ok you can go".


Fita yayi a Office ɗin


Shi kuma Usman ɗin sai ya jawo drowan table ɗin shi ya yago pepper a jikin wani memo, rubutu yayi kafin ya ɗago pepern yana kallo, tabbas idan be manta ba wannan address ɗin shi ne ya gani a jikin pictures ɗin, sake ƙura wa peppern idanu yayi yana sake nazartan rubutun, sai kuma ya lumshe idanun sa yana jan numfashi, ya buɗe su yana cije leɓen bakin sa, kana kuma ya ajiye takardan tare da ɗaura biron akai.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Sixty Two*






           *AFTER TWO WEEKS*

          Yana cikin ɗaura agogon sa daga hannun sa na hagu, sai yaji wayan sa ta soma ƙara, sai da ya ɗan leƙa ya tabbatar da wanda yake tsimaye ne kafin ya ɗauka yana karawa a kunne

Daga can mutumin yace, "ranka ya daɗe! gani tare da su na gama aikin".

"Ok turo min address ɗin". Daga haka ya kashe wayan yana ajiye wa

Ci gaba yayi da ɗaura wrest watch ɗin, bayan ya gama sai ya miƙe daga bakin gadon shi da yake zaune, takalman sa ya zira cover shoes baƙi sannan ya ɗauki wayan sa ya zira a aljihun gaban rigan shi ya fito ya rufe gidan ya fice, kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, yana shiga da sallama ciki-ciki

Hajiya ta amsa mishi da ke zaune a kan dainning tana yin kari

Wajen ta ya nufa ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun, sannan ya gaishe ta a miskilancen da ya saba

Amsa mishi tayi tana bin shi da kallo, sai kuma dai tace, "ina zaka je da safen nan?"

Hannu ya saka yana haɗa tea yana bata amsa, "zan je wani wuri ne".

Bata sake mishi magana ba haka suka zauna Kamar kurame

Sai kuma can yace, "Dady ya tafi ne?"

"Eh ya fita tun ƙarfe 06:30am. Amma kai ya batun maganar ku da Ɗahira? Ka san cewa ya zura maka ido ne yaga iya gudun ruwan ka da ya neme ka kaƙi kazo, ya kamata tun wuri ka kawo mishi takardan yarinyan nan kafin haɗuwar ku, idan kuma ka ce baza ka sake ta ba kamar yanda kace ɗin ne, to, tun wuri ka neme shi ka ba shi haƙuri, don na san shi ne yafi ɗaukan zafi, idan kuma ba son zama da ita kake yi ba gwara ka sake ta ka dena cutan ƴar mutane da auren ka a kanta".

Shiru yayi be ce komi ba, illa shan tea ɗin shi da yake yi, amma kuma abaɗini juya kalaman Hajiyan yake yi

Ganin be kula ta ba itama sai ta tashi ta wucewar ta ta bar shi nan

Be ƙara mintuna biyu cikakku ba shima ya tashi ya fice, kai tsaye gidan su ya koma ya ɗauki mota ya fice, a lokacin ne ya duba wayan sa yaga address ɗin hotel ɗin da aka turo mishi, sai ya wuce can.




              Har ciki ya shiga da motan shi yayi parking, kafin ya fito sai da ya saka baƙin glasses a fuskar sa sannan ya fita ya nufi room ɗin da aka turo mishi, yana zuwa dai-dai ɗakin yayi Nocking

Sai ga wani saurayi ya buɗe mishi ƙofan

Ya shiga yana bin ko ina da kallo ta cikin glasses ɗin sa yana yatsina

"Suna cikin wancan ɗakin". Cewar saurayin kanshi a ƙasa

"Ka tabbatar su ne?" Yayi maganar yana kallon sa fuska a ɗaure

"Eh wlh su ne suka bani aikin, bazan manta su ba tunda na san ɗaya daga ciki".

"Ok mu je". Yafaɗa yana yin gaba cikin bedroom ɗin

Shi kuma mutumin yabi bayan shi jiki na rawa

Da shigan shi ya sauke idanun sa a kan Safra da Ayush dake zaune an ɗaure musu hannu da ƙafa kuma an rufe musu baki, zare idanu kawai suke yi ganin Usman sai zufa ya fara keto musu tsaban tsorata fiye da yanda suke a farko

Sai da ya gama ƙare musu kallon wulaƙanci fuskar sa babu alamar rahama, sarai ya gane fuskar Ayush tunda ba yau ba ya rigada yayi making ɗin ta, kai komo ya riƙa yi yana sake bin su da kallo, sai da ya mula kafin yace, "wato ku ne sheɗanun da har ƙananan ƙwaƙwalan ku ya saka muku tunanin ku shiga gona ta ko?" Sai ya ci je baki yana saka hannayen sa cikin aljihun wandon sa kana yaci gaba da faɗin, "har kuna iya ɗaukar picture ɗin ƴar uwan ku mace ku yi mata wannan ƙazafin saboda cikan burin ku? To yau zan maida sharrin ya koma kanku, ku sani da kyau Ni Usman ba na yafiya ko misƙala zarratan ga ire-iren ku..." Sai ya datse haƙoran sa be ƙarisa abinda yake son faɗa ɗin ba, ɗan jan numfashi yayi kana ya kalli mutumin yace, "ka tuɓe kayan su gaba ɗaya ba na son ganin komi a jikin su, sannan ka ɗaukar min su hoto kowacce kuma da fuskar ta a ciki. Ko wacce sai na kaima uwarta ta gani, idan kuma babu me uwa a cikin ku na san kuna da uba da dangi..." Sai ya sake yin shiru yana bin su da kallo da idanun sa da suka soma canza kala. "Common kayi min abinda na sa ka ka tsaya kana kallo na, saura kaima zan dawo kanka". Yayi maganar cikin tsawa

Da sauri jiki na rawa mutumin ya nufe su ya soma cire musu kayan

Ko waccen su na tsiyayar da hawaye kamar ƙasa ta tsage su shige ganin cin mutuncin da yau za'a musu. Har Ayush da zuciyar ta ke cike da ƙaunar Usman ɗin amma yau sai da taji dama bata san shi a rayuwar ta ba, da wani ido zata kalli dangin ta muddin abinda ya faɗa ɗin ya aikata musu? Wayyo.. wayyo kaico da wannan ranan a wurin su

Usman na wurin be jirga ba har aka gama cire musu kayan su kaf, kana ya miƙa wayan shi mutumin ya amsa ya soma ɗaukan su hotuna

Haka suke kuka amma babu halin roƙo sabida bakin su dake rufe

Sai da ya gama tass kafin ya amshi wayan shi ya tura wa mutumin a tashi wayan

Kallon shi yayi yace, "ka tabbatar kayi min aikin da na saka ka nan da gobe, ina son hotunan su fi na yarinyan muni haka nake son gani, kuma kayi zaman tsare su nan da kwana biyu kafin ka sake su, ko abinci ba na buƙatar ka basu illa ruwa, wannan aikin kawai zaka yi min na yafe maka, idan ba haka ba ka san sauran zancen..." Daga haka ya juya ya fice abin sa

Yana shiga motan shi yaja yayi gaba, agogon hannun sa ya duba yaga ƙarfe 09:20am. Ne, duk da yanzu ba time ɗin shiga Office ɗin sa bane, kuma yana da wurin da zai je amma yana buƙatar ya sanya Ɗahira a idanun sa, don haka can Hospital ɗin ya nufa. Yana yin parcking ya fito ya shige, kai tsaye Office ɗin ta ya wuce ba tare da yayi Nocking ba ya buɗe ya shige

Da sauri ta ɗago kanta tana zuba mishi idanun nan nata masu saka shi a wani mawuyacin hali

Ɗan lumshe nashi idanun yayi yana buɗe wa a kanta

A lokacin tuni ta ɗaure fuska tamau tana jiran taji me yazo mata a Office

Sai ya ɗan sosa kansa yana kawar da ƙwayan idanun sa a kanta, domin yanda ta kafe sa da kallo kamar zata haɗiye shi ɗanye, hakan yasa yaji gaba ɗaya natsuwar sa ya gushe wanda ya saukar masa da kasala nan take, ɗan ƙasa-ƙasa yake kallon ta cike da isa da sanyin murya can ƙasa yace, "ina son zamu yi magana ne Nafeesa, ki bani aron hankalin ki, na san..." Dole ya tsayar da maganar ganin ta tashi ta nufi Toilet zata shige, sai yayi saurin taka wa ya isa wajen ta, tana buɗe ƙofan caraf ya riƙe mata hannu

Lokaci ɗaya ta juyo tana kallon sa hawaye na cika mata ido, cike da haushin sa tace, "Please Yaya Usman ina ganin girman ka kar ka saka nayi maka abinda baka zata ba, wlh wlh idan har baka fita harka na nayi rayuwa ta Ni kaɗai ba duk abinda nayi maka kai kaja".

Murmushi yayi memakon yaji haushi, sai ya sake riƙe mata hannun gam yana haɗa shi da nashi ta cikin yatsun ta, a hankali yace, "common Babe ba hayaniya ne ya kawo Ni wajen ki ba, neman sulhu ne... Kuma kin san an ce sulhu alkhairi... Anyway ki manta komi Nafeesa ki yafe min, haƙuri nazo baki dama ba wani abu ba, na san nayi miki ba dai-dai ba wanda yasa nake ta faɗan abubuwan da na san ba haka bane". Sai yaja numfashi a hankali yana kallon fuskar ta sannan yace, "ki amince ki koma ɗaki na mu rufa wa junan mu asiri kinji?"

Hannun ta tayi ƙoƙarin janye wa amma yaƙi saki, cike da yanayin fusata a muryan ta tace, "to Ni na ce ba na ƙaunar ka! ba na ƙaunar zama da kai ko dole ne? Ko kana tunanin don ka san wace ce Ni a yanzu wani abun alfahari ne a wuri na? Da sanin ka da rashin sa duk ɗaya ne a wuri na. Usman bazan taɓa zama da kai ba domin na tsane ka fiye da yanda kake zato.."

Hannu ya saka ya rufe mata bakin ta sabida ya gaji da jin waɗannan munanan kalaman nata, sosai zuciyar sa ke tafarfasa da jin ɗaci a cikin ta wanda tuni har idanun sa sun soma yin ja suna ƙyallin ruwa

Hannu ta sanya zata janye nashi hannun

Sai kawai ya janyo ta ya haɗe bakin su wuri ɗaya

Lokaci ɗaya gaba ɗayan su suka ji su a wani irin yanayin da basu taɓa shigan shi ba, wanda har ita tsaban tsuma tuni jikin ta ya fara rawa, sai kuma tashin zuciya da nan da nan sai ga amai ta guntso shi ta bakin ta ya shige nashi

Ai sai yayi saurin sakin ta yana tare aman ba tare da ya shige can cikin shi ba

Ita kuma tuni ta shige Toilet ɗin da gudu ta dinga kwarara shi kamar zata amayar da kayan cikin ta

Da gudu yabi bayan ta ba tare da ya damu da abinda tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login