Showing 75001 words to 78000 words out of 154708 words
duk sun zo
Duk wani shiri da ake yi na Amare Ɗahira bata a ciki, su Fadila da su Firdausi, da sauran ƴan matan Familyn su suke yin komi, ita dai tana ɗaki sai dai ta ƙule taƙi fitowa, gaba ɗaya ma ba jin daɗin jikin ta take yi ba, saboda zazzaɓi da take fama da shi, shiyasa babu wanda ya takura mata, gyaran jiki ma tace "ba ta so" dole aka ƙyale ta, daƙyar ta bari ana gobe bikin aka yi mata saloon da lalle.
Washe gari 27 April 2021. Aka shaida ɗaurin auren *DR. USMAN NOOR AL'AMEEN* tare da Amaryan sa *DR. NAFEESAT AL'AMEEN AL'AMEEN (ƊAHIRA).* bikin da ya tara dubbannin jama'a, sai mu ce masha Allah
Daƙyar Usman ya halarci ɗaurin auren nan, ana gama wa aka neme sa aka rasa, dama be gayyaci kowa ba, bare abokan sa ma ba ƴan nan bane, sai dai wasu sun ji labari kuma sun halarta, sai dai shi be ma gansu ba ya arce.
Ana ta neman Ango an rasa, haka dai aka gama gaishe-gaishe ƴan uwa da abokan arziƙi aka soma watse wa.
Cikin gida ma ana ta shagulgulan biki, babu abinda za'a yi a bikin, tunda daga Amaryan har Angon babu me halarta, Ɗahira na fama da kanta, tunda tun sanda aka ɗaura auren jikin ta ya rikice, dole aka ɗaura mata drip aka yi mata alluran barci don zuciyar ta ya huta, dayake Abbu ne ya duba ta shiyasa ya gane damuwa ce kawai da yayi mata yawa
Lokacin da ta tashi har ɗakin ya shiga, ya zauna daga shi sai ita, yayi mata nasiha me ratsa zuciya, kuma ya roƙe ta "ta dena saka damuwa a ranta, ta riƙe auren ta da amana, tayi biyayyan aure", nasiha sosai yayi mata wanda take ta faman kuka.
An rigada an shirya mata Part ɗin ta ya tsaru, dayake duk na gida ne, Big Dady da Abba suka ɗau nauyin yin mata komi, an shirya mata ɗakin ta irin na ƴan gata, komi sai dai ace Masha Allah.
Zuwa dare aka kai ta ɗakin auren ta, wanda tasha kuka ba Ni da kuka ba, aka watse aka bar ta ita kaɗai tunda baza a kwanan mata ba.
Sai da Big Dady ya kira wayan Usman ya shaida masa "muddin be kwana a gida ba tare da matan sa ba, sai ya saɓa masa". Kuma ya basa umarnin yayi maza-maza ya dawo gare ta.
*******
Be dawo gidan ba, sai ƙarfe 01:00am. Na dare. Lokacin tuni Ɗahira tayi barci abin ta, bayan ta gama kwankwaɗan kukan ta son ranta, wanda ya haddasa mata zazzafan zazzaɓi, daƙyar ma barcin ya kwashe ta tana ƙudundune a kan gadon ta.
.
_to nan ake yin ta fa, ya zaman Ɗahira da Usman zai kaya? Wani irin zama za su yi a rayuwan auren su? Hmm ku dai gyara zama kawai Ni dai abinda zan ce muku kenan, yanzu ne za'a soma chakwakiyar._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*NATSUWA A SALLAH*
_Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman._
_A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu'uminun ana faɗa mana cewa:_
_"Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali'u ne."_
_Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa. Allah yasa mu dace._
.
*EPISODE Thirty Eight*
*WASHE GARI*
Tunda aka yi sallan asuba Usman be dawo gidan ba, be kuma bari kowa ya gansa ba ya bar masallacin.
Ita kuwa Ɗahira tunda ta tashi tayi sallan asuba itama, ta sake komawa barcin, dayake akwai zazzaɓi a jikin ta shiyasa har gari yayi haske bata farka ba, sai da taji hayaniyan ƴan biki da wasu suka zo su sake ganin ɗakin nata, kasancewar a lokacin za su tafi, shi ne ta farka, lokacin 12:00pm.
Har ciki suka shiga suna ta mata tsiya, ganin ta da suka yi tana ta barci
Ita dai bata ce musu kanzil ba, illa murmushi da take tayi, sai kuma daga baya ta gaishe su.
Ba su wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi.
Sake koma wa tayi ta kwanta, don sosai kanta yake sara mata sakamakon tashin ta da suka yi, ta rufe ido kenan taji an hankaɗo mata ƙofan ɗaki, da sauri ta buɗe idanun ta tana bin Yusra da ta shigo da kallo
Ita kuwa sai faman taɓe baki take yi tana girgiza jiki, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Ɗahiran tace, "baƙar munafuka! burin ki ya cika kin auran min Yaya, to wlh ki saka a ranki, kamar auren nan ya rabu ne, ba ke ba zama a gidan Yaya Usman, domin ba ya ƙaunar ki, ba kuma zai taɓa ƙaunar ki ba, wlh dani dake yanzu ma muka soma ƴar tsama".
Yanda ka san t.v haka Ɗahira take bin ta da idanu, har sai da ta dire Aya kafin ta tashi zaune tana bin ta da kallo sosai, ko kaɗan ba ta jin daɗin Jikin ta, kuma har ga Allah ba ta son ta biye mata, amma kuma gani take yi idan har ta bar ta ta tafi bata mayar mata da martani ba, to, tabbas nan gaba ma zata dawo tayi mata irin wannan cin mutuncin, kuma zata ga kamar tsoron ta take ji, don haka ta saki guntun murmushi tana kallon ta tace, "wa kike da suna? Yusra ko? Ni ba sa'an yin wasan ki bane, tun wuri ki kama kanki, domin shiru-shiru ba hauka bane, wlh ina ƙyale ki ne kawai don Ni ba Kaza bace da zan zauna kullum ina sa'insa da ke, na san mutuncin kaina; na kuma san kima ta, amma wlh muddin kika sake shigo min gida na, kika yi min irin wannan halin karnukan, zan baki mamaki Yusra, zan nuna miki Ni ba'a sha na a warke, domin zan nuna miki ainihin hauka na wlh".
Shewa Yusra ta saki tana tafa hannu tace, "an yi miki duk abinda zaki yi ki yi, ai Ni dama so nake yi ki ɗau mataki sai in San kin cika ke tatacciyar mara mutunci ne, kuma ke baki isa ki hana Ni zuwa gidan ɗan uwa na ba wlh, kin yi kaɗan, nonsense..."
"Wai hayaniyan me nake ji ne? What's going on here?" Cewar Fadila da ta shigo da sauri, dama Breakfast ta kawo musu shi ne ta jiyo kamar hayaniya
Ɗahira tace, "Ask her to come and find me in my room,"
Tsaki Yusra taja tace, "wlh mu zuba dani da ke". Tana faɗa ta juya ta fice.
Ƙarisowa Fadila tayi bakin gadon tana zama tace, "wai me ke faruwa ne? Me ya haɗa ki da ita?"
"Babu komi Fadila, kin san halin ta ba tun yau ba, ban san me na tsare mata ba ita da Yayan ta suka bi suka tsane Ni, ban san me nayi musu ba". Ɗahira ta ƙare maganar cikin damuwan da ya nuna a muryan ta
Ajiyan zuciya Fadila ta sauke, sai kuma tace, "ki yi haƙuri da duk halin su, Ni ban san meyasa Yusra take wannan ɗabi'an banzan ba, amma yanzu ba ta Ita zaki yi ba, ta Mijin ki zaki yi, duk hanyar da ya dace shi zaki bi domin samo soyayyar shi, ke ba yarinya bace Ɗahira, kin san abun kuma da ya dace, batun tsana ko rashin sa duk be taso ba yanzu, yanzu kun zama ɗaya ke da shi, aljannan ki kawai zaki nema, kar ki soma ki biye mishi, na san zaki iya ƴar uwa, haƙuri shi ne zai sa ki cin ma Nasara kinji? Domin auren ku muna fata mutu ka raba ne".
Murmushi Ɗahira ta saki tana jin hawaye na son cika mata idanu, sai tayi saurin kawar da kai tana ɗan rufe idanun ta tare da komar da su
Fadila tace, "yanzu ina Angon naki? Ga abinci can na kawo muku sai ki je ki tashe shi. Amma kin ban mamaki fa".
Kallon ta Ɗahira tayi da son ƙarin bayani
"Kya waro min Ido mana, ji be ki don Allah mana, kin zauna har sha biyu da rabi baki yi wanka kin shirya ba, ta hakan ne zaki dai-dai ta gidan ki?"
Wannan karon dariya Ɗahira tayi, sai ta tashi kawai ba tare da tayi magana ba, domin sosai take jin jikin ta babu daɗi
"To Ni bari in tafi, zuwa anjima zan sake leƙo ki, zuwa gobe insha Allahu duk zamu tarkata, na san ma yanzu su Momy suna nan shigo wa". (Tana nufin mahaifiyar K.B Hajiya Ikram) tunda ta koma can sai ya zamana itama Momy take ce mata kamar sauran ƴaƴan ta, saɓanin a baya da suke kiran ta Gwaggo Rabi.
Har Fadilan zata fice, sai Ɗahira tace mata, "ta zo mata da maganin ciwon kai".
Amsa mata kawai tayi Sannan ta fice
Ita kuma ta shiga wanka, sai da ta fito ta shirya cikin atamfa baƙa da kalan fari da coffee, ɗinkin riga da zani raffer, tayi kyau sosai, sai dai yau komi bata shafa a fuskar ta ba duk da kasancewar ta me son kwalliya, ɗankwalin kawai ta ɗaura ta fito Parlour
Da kallo kawai take bin ko ina, har ta isa kan dainning ɗin, duba abinda aka kawo musu tayi, sai kuma ta juya ta nufi ɗakin da ta gani kusa da na ta, tsaya wa tayi a bakin ƙofa tana tunanin shiga ko a'a, don ta san nan ne ɗakin Usman, sosai gaban ta yake faɗi, don har yanzu bata san wani irin zama za su yi ba
Bismillah tayi kawai ta tura ƙofan da sallama, bayan tayi Nocking ba'a amsa mata ba. Sai dai babu kowa ciki, sai da ta gama ƙare wa ɗakin kallo gunun ban sha'awa irin nata komi da komi, sai dai kayan ɗakin ta ya fi yawa tunda ita mace ce, amma har ta colours ɗin ciki iri ɗaya ne
Fitowa tayi ta koma kan dainning ta hau yin breakfast ɗin ta, sai dai har ta gama a tunani tayi Breakfast ɗin
Ɗaya daga cikin ƙannin K.B suka kawo mata maganin da tace a kawo mata, amsa tayi tasha ta zauna a kan kujera tana faman tunani
A haka sauran mutanen gida sukai ta shigo wa ganin ɗaki, da masu tafiya da waɗanda sai gobe za su tafi, ƴan Maiduguri dai duk yau suka watse
Daga ƙarshe su Shamsiyya da Shakira, Firdausi, Salma da sauran sa'annin ta duk suka cika sashin, suna ta hira
Tun Ɗahira ba ta biye musu har dai ta saki jiki ana ta yi da ita, tuni ta wartsake abun ta
Suna ta tsokanar ta wai "daga aure ango ya tafi ya bar ta," masu kare mata suna yi, har da Shakira Iyayen gulma, ita dai sai dai ta bi su da dariya kawai.
Sai magriba duk suka watse suka bar ta, ta shiga tayi sallan magriba, sannan ta dawo Parlor, tunda nan ya ɗan fi haske, da wayan ta ta haska tayi zaman ta tana ci gaba da faman tunanin ta, babu abinda ke tsaya mata a rai, sai yanda za su yi zama da wanda ya tsane ta; itama kuma ta tsane shi
Kafin a kira sallan isha'i aka kunna musu gen, tunda duk generator ɗin su haɗe yake dana Part ɗin Baffa
A lokacin ne aka sake kawo musu abincin dare, tana amsa ta ajiye saman dainning ta wuce ɗakin ta ta rufo ƙofa, alwala tayi ta gabatar da sallan isha'i, sannan tayi shafa'i da wutri, ta roƙi Allah buƙatun ta, sannan ta sauya kaya zuwa rigan barci doguwa tayi kwanciyar ta, da haka tana tunani har barci ya ɗauke ta.
*********
Kamar jiya, haka ma yau Usman sai ƙarfe 01:00am. Ya dawo gidan. Ko kallon ɗakin ta be yi ba ya shige nasa, wanka yayi ya sauya kaya zuwa na Barci, dama ya rigada yayi sallan sa a masallaci, sai yayi kwanciyar sa, tare da kitsima abubuwan da yake son aiwatar wa, don samun mafita daga wannan kaddararren auren.
Washe gari haka ya sake tsallake wa ya fice a gidan, shi fa sam ganin ta ne ba ya son Yi ma, shiyasa yake fice wa. Ga shi Big Dady yace masa kar ya soma ya ga ƙafafun sa a Hospital idan har ba two weeks yayi ba.
A yau duk sauran mutanen da suka zo biki suka watse, dama duk yawanci ƴaƴan Kaka ne su Hajiya Ikram da Hajiya Laila, sai ƴaƴan su wasu da ba su tafi ba, sai kuma ƙannin Kakan, su Hajiya Baseera da Hajiya Hannatu (Ihsan). Duk dangi na kusa ne. Kuma duk yau suka gama watse wa
Aunty Zulaiha CE kawai ta kai yamma, itama don tana jiran mijin ta ne, da zata tafi sai da tazo har Part ɗin Ɗahira, a nan take ce mata "ta shirya taje Part ɗin su Usman ta gaishe da Hajiya, idan da hali ma ta zauna a can sai zuwa dare ta dawo"
Tana tafiya ta shirya kamar yanda tace mata, doguwar riga abaya baƙa ta sanya, me kwalliya sosai a gaban rigan na flower, sai ta yane kanta da gyalen abayan, ta saka turare a jikin ta tare da takalmi ta fito riƙe da wayan ta
Tana fito wa Part ɗin ta suka haɗa idanu da Baffa dake zaune saman farandan gidan sa, ya haɗe ƙafafu ya ƙura wa Part ɗin nata idanu yana faman tunani. Ganin ta yasa ya sauke ƙafafun ƙasa yana mata murmushi
Sosai taga ya sauya mata, gaba ɗaya ya rame ya rage haske, sai ƙasumba da ta ga ya ajiye, kamar dai ba shi ba ɗan gayen nan
Murmushi tayi masa itama, tana ƙarisa wa inda yake ta gaishe shi
Amsa wa yayi yana cewa, "amarya ba kya laifi.. ko da kin kashe ɗan masu gida".
Dariya tayi tana ɗan rufe fuskar ta tace, "kai Yaya ka dena don Allah ba na so. Ina Sa'ada tana nan mu gaisa?"
"A'a ta fita, tana Part ɗin Hajja".
"To bari inje Yaya".
Daga nan ta wuce tayi ƙofan da zai sada ta da gidan su
Da kallo Baffa yake bin ta dashi, sai ya lumshe idanu yana jin hawaye na cika masa idanu. har yaushe zai jure da abinda yake ji? Yanzu ta zama matar ɗan uwan sa amma soyayyar ta ƙara wanzuwa yake yi a ransa
"Ya Allah ka cece Ni, ya Allah ka bani baiwar Allan nan idan har alkhairi ne ita a rayuwa ta.."
"Da wa kake yi ne haka?" Cewar Sa'adatu da ta tsaya gaban sa tana kallon sa, sai dai bata san me yake cewa ba
Buɗe idanun sa yayi yana kallon ta, sai kuma ya kawar da kai yana miƙe wa ya shige cikin parlour'n su
Itama bin bayan shi tayi fuskar ta tuni ya nuna damuwa, yanzu sam Baffa ya dena kula ta, sai tayi magana sau dubu be amsa mata ba.
⚫⚫⚫⚫⚫
Da sallama Ɗahira ta shiga Part ɗin Hajiya, sai dai babu kowa a ciki, sai ta samu wuri ta zauna tana aza idanun ta kan t.v dake aiki
Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito riƙe da Plate a hannun ta daga kichen. Ganin Ɗahira sai tayi kicin-kicin da fuska ta nufo cikin parlour'n
Da sauri Ɗahira ta zamo daga kan kujeran, ta zauna a ƙasa tana gaishe ta
Sai da ta zauna ta ɗan kalle ta a fizge, kafin tace, "Lafiya".
Jiki a sanyaye Ɗahira ta sake duƙar da kanta ba tare da ta sake cewa uffan ba
Itama Hajiya bata sake kula ta ba, ta soma cin abincin ta.
Har ta gama Ɗahira bata ɗago kai ba, tunanin kawai yanda zata iya rayuwa da su take yi, da kuma yanda suka tsane ta, nan da nan taji idanun ta sun ciko da hawaye, bata ankara ba taji sun soma zubo wa, saurin saka hannu tayi ta share tana ɗan ɗago kanta tabi Hajiyan da kallo, wanda ta fito daga kichen ajiye Plate ɗin; ta wuce ɗakin ta
Ɗan ajiyan zuciya ta sauke tana me lumshe idanun ta. sallaman Usman da yayi ciki-ciki ne ya saka ta ware ido sai a kan sa
Wanda shima ya sauke nasa idanun yana bin ta da wani irin kallon da ta kasa fassara shi.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Thirty Nine*
Saurin ɗauke kanta tayi daga kallon sa, ta duƙar da kanta tana jin gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar su haɗa idanu, saboda kallon da yake mata sosai yake cutar da ita.
Takowa yayi ya shige ɗakin Hajiya
Sai a lokacin ta sake ɗago kanta, ta ɗan kalli hanyar da ya bi, sai kuma tayi zugum ita kaɗai a parlour'n, ta rasa me zata yi, kar kuma ta tafi tayi laifi, sai ta tashi kawai ta shige kichen ɗin Hajiyan, duba wa tayi ko akwai wanke-wanke tayi, amma ƴan ƙwayoyi ne. Dayake ɗazu kafin su Aunty Zainab su wuce duk sun wanke.
Wanke sauran tayi ta kife ta fito tana gyaran mayafin ta, sai kawai idanun ta suka faɗa cikin na Usman dake zaune saman