Showing 102001 words to 105000 words out of 154708 words

Chapter 35 - DOCTORS FAMILY COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

8108

tsaye gida suka wuce, sai da suka koma ne suka sanar da Kaka duk abinda ya faru

Gaskiya be ji daɗi ba, domin ya nuna ɓacin ran sa matuƙa a kan Hajja, wanda su kansu sun sha mamaki, duba da yanda Kaka yake son Hajja Fatu sosai, kasancewar ta ɗiyar abokin sa kuma ɗiyar ƙanwar sa, amma kuma sun san yanda yake matuƙar ƙaunar asibitin sa ba ya son ko kaɗan wani abu ya faru, yanzu idan duniya suka ji shikenan za'a fara ma asibitin baƙin fenti. Sosai yayi mata faɗa daga baya ya haɗa su yayi musu nasiha sosai ganin Abba yana ta kumbura da shirin ya aikata wani abun

Abba dai be bar wajen ba sai da ya kafa mata sharaɗi, domin yace "dole sai ta bar aiki," amma Kaka ya hana sa, shi kuma yace, "to idan haka ya sake faruwa wlh dole ba ita ba aiki a ko wani asibiti ba Asibitin su kaɗai ba, idan kuma tace a'a sai dai ba a ƙarƙashin sa take ba, tunda da sa hannun ta ake son ganin bayan asibitin su, da goyan bayan ta ake shigowa da ƙwayoyi tare da maganin asibiti, nan gaba ma da ita za'a haɗa baki da maƙiyan su don ganin bayan asibitin".

Abba fa ya shaƙa sosai, ba don Kaka ba babu me tanƙwara shi, sai dai su rabu da Hajja Fatu. Tunda shi Abba duk a cikin su ya fi su zafi, yana da sauƙin kai matuƙa, amma idan ya tashi faɗa ba ya ji ba ya gani, duk wani rashin son raini irin na mahaifiyar su shi ya biyo ta, ba ya shiga harkan mutum, to, kaima kar ka shiga nasa, yanzu zaka ga haukan sa matuƙa, shi kuwa Abbu sak Kaka ne babu ruwan sa, yana da sauƙin kai, haka ma Big Dady, shi kam ya fi su haƙuri, duk da shi ne babba yana da haƙuri matuƙa, idan ka ga yana faɗa kawai yana yi ne domin gyaran ƴaƴan sa, amma duk abinda zai faɗa zai yi wuya ya aikata shi a zahiri, idan ma kayi masa abu kafin zuwa anjima ya manta ransa yayi sanyi, sai dai idan zai ɗaure maka fuska domin ka koki gaba, shima sak halin Ummin sa ya biyo babu ruwan sa.

           Da haka magana ya watse, ranan dai Hajja ta ga banu, domin a zaune ta kwana, sosai hankalin ta ya tashi, ƙarshe ma washe gari ƙin zuwa aiki tayi.

    A ranan ne shi kuma Baffa suka dawo da Sa'adatu, tunda tun jiya da Hajja ta ba shi umarnin zuwa ya ɗauko ta be je ba sai sakaliyan yamma, to, a can ya kwana yau suka dawo.

       Fannin Shakira ma tun a asibiti Sahabi yaje ya bata haƙuri suka koma gida

Wannan dalilin ne yasa Hajja ta ɗan samu sukuni da matsalolin ta, tana ga kamar aikin Malam ya ci tunda ga shi komi ya zama normal Kan yaran ta, sai dai matsalan yana ga Abba, domin tun abin be sake kallon inda take ba, ya ƙi mata magana ya dena cin abincin ta, hakan yasa tayi tunanin why not ta Kai shi wajen Malam domin magance mata matsalan ta, wannan tunanin zuciyar nata tabi ta wuce kanta tsaye wajen Malam ko bi ta ƙawarta bata yi ba, shi ne kaɗai wanda zai iya mata maganin matsalan dake shirin afkuwa ita da mijin ta, wanda tana ganin ɓaraka ne babba da rashin yarda yake shirin Kunno Kai a tsakanin su, wanda kuma hakan ne babban tsaiko ga rayuwan ta, yardan Miji ya fi komi a rayuwar aure.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

            *TURKEY*

       A kwanakin nan da suka shuɗe, Ɗahira tayi rayuwar ƙunci ba ni da ƙunci ba, ko kaɗan ba ta da walwala, ta zama tamkar wata wacce bata da gata, ta rame tayi baƙi kamar ba ita ba, bata da aiki kullum sai kuka da saka damuwa a ranta, ta kasa saba wa da halin da take ciki, komi na gidan ita take yi, da ta tashi da safe zata gyara gidan tayi wa kanta abinci domin shi ko bi ta kanta be yi bare tasa ran idan tayi abinci zai ci, bare kuma bata taɓa kwatanta hakan ba, ta gummaci ta girka ta zubar da tayi masa girki, ita take masa wanki da gyara ɗakin sa ko ina, idan ma bata yi ba ranan ya dinga caɓa mata magana kenan, kuma yace "idan bata yi ba sai yaci uban ta". Kalman cin uban ta shi yake matuƙar ɓata mata rai ainun, sai ta zauna tayi kukan ta son ranta ta share hawayen ta, haka zata yi masa wankin ta shanya masa a Toilet ta gyara masa ɗaki ko ina, domin ba ta son ko kaɗan ya sake taɓa lafiyan jikin ta, a haka take ta ƙare wa tana ciwo a tsatstsaye, kullum fama take yi da kanta sakamakon damuwan da ta kasa cire wa a ranta, kuma tun ranan da ya bata waya suka gaisa da ƴan gidan su be sake bata ba, sosai take buƙatar jin muryan ƴan gidan su amma ba hali, dole ta haƙura domin ko magana ba ta ƙaunar tayi masa bare ta tambaye sa wani abun

Duk idan taje gyara masa ɗaki, sai tayi binciken ko zata samu keey ɗin ƙofa, amma duk inda ta duba bata taɓa cin karo dashi ba, haka zata mayar masa da komi a muhallin sa ta gyara masa ta koma inda ya zame mata ɗaki, kusa da kichen. Idan damuwa yayi mata yawa sai dai tayi ta karatu, da dare kuma ko ishashshen barci ba ta samu illa sallah da take faman yi ko yaushe tana kaiwa Allah kukan ta

Rashin zaman Usman a gidan ya fi mata komi daɗi, tunda idan ya fita tun safe ba ya dawowa Sai dare, wani lokacin ta ɗan sami barci ya fizge ta, wani lokacin kuma idanun ta biyu zai shigo, ita yanzu har ta saba da duhun gidan, domin sabida tsaban mugunta irin nasa ya lalata komi na na'uran gidan, ko NEPA babu a gidan, bare dama ita ba gwanar kallo bane bare ya ɗebe mata kewa, haka take rayuwar ƙunci da duhu a gidan, koda da safe ne gidan babu wani haske sosai, sai idan ta yaye cootin, wani lokacin kuma sanyi ya addabe ta ta rasa yanda zata yi, dole ta mayar ta rufe.


           Yau ma tana kwance kamar kullum, ko kaɗan ba ta jin ƙwarin jikin ta, daƙyar take iya taɓuka wani abun saboda rashin ƙarfin jiki, ga ta ba auki ba

Tunda ya fita take kwance ta kasa yin komi, ko karya wa ta kasa, tunani ne kawai ta afka tana ta faman yi. Can kuma sai ga hawaye ya silalo mata a kunci, sai ta yunƙura ta miƙe ta nufi kichen kamar zata faɗi, ruwa ta samu ta dafa ta haɗa tea me kauri, shi ne ta samu ta ɗan sha ko zata samu ƙwarin yin aiki

Tana gama wa ta dawo parlour'n tana bi da kallo, ganin ba wani datti ne ba sai ta wuce kanta tsaye ɗakin sa, nan ne yayi mutsu-mutsu da gadon sa, duk ya jefar da kayan sa, haka ta tattare sannan ta gyara gadon, ta wuce Toilet ta wanke masa, wankin sa dake shanya tun jiya da tayi masa ta kwashe ta ninke, sai ta ɗaura masa a kan gado, kana ta koma Parlour ta shiga wanka, tana fito wa ta zira riga da skert ko lotion bata shafa ba, rabon ta ma da shafa wani abu a gidan nan tun lokacin da tayi ciwo, komi yanzu ya fitan mata a rai

Tana zaune tana gyara kayan nata tana mayar wa cikin akwati, sai ta jiyo motsin buɗe ƙofa, tsayawa tayi kawai tana kallon ƙofan, ta san ba ya dawo wa da rana shiyasa tayi mamaki

Shi ne kuwa ya shigo ciki, wani saurayi na biye dashi a baya. Be bi ta kanta ba ya shige ɗaki, yayinda saurayin nan sai bin ta yake yi da kallo, sai kuma ya gaishe ta da harshen turanci

Amma ko ci kanka bata ce mishi ba, illa ɗauke kai da tayi fuskar ta babu fara'a taci gaba da abinda take yi.

     Usman ne ya fito da Trolly  babba ya miƙa wa saurayin, dayake shi yake ba wa gugan kayan sa, duk kwana uku zai haɗa masa kayan ya zo ya amsa da safe kafin ya fita, yau kuma be zo ba sai yanzu, shi ne ya kira sa ya sanar masa zuwan sa, wannan dalilin ne Usman ya dawo domin ba shi kayan.

    Saurayin fita yayi da Trolly bayan sun Yi sallama, shi kuma ya koma ɗakin sa.

     Sanda Ɗahira ta gama gyara kayan nata, sai ta rufe Trolly ta janye sa gefe, kana ta koma ta jingina da bango ta lumshe idanuwan ta, ta hau tunanin da ya zame mata jiki, ko ta so bari ba ta iya wa.

      Can sai Usman ya fito da waya ya nufo inda take

Takun takalman sa dake tafiya da ƙarin bugun zuciyar ta, shi yasa ta buɗe idanu da sauri ta sauke su kansa

Fuskar sa ɗaure tamau ya miƙo mata wayan ba tare da ya ce uffan ba

Kamar kar ta amsa, sai kuma tayi tunanin ko gida ne, da sauri ta miƙa hannu ta amshi wayan, ilai kuwa gidan ne, mahaifin ta ne a kan layi.

     Yana kanta be tashi ba har ta gama wayan da mutanen gida

Itama ko kallon sa bata sake yi ba, kuma bata yi wani abun da zai saka yayi mata magana ba, bare ya sauke mata tijara, iyakan gaisuwa ya haɗa ta dasu bata ce musu komi ba

Amsar wayan sa yayi ya wuce kan kujera, zama yayi yana ta faman latsa wa

Ita kuwa haɗe ƙafafun ta tayi ta rufe idanun ta, sai ga hawaye, "Allah gani gare ka, Allah ka fitar dani a hannun wannan azzalumin bawa naka, na tsane shi!". Tafaɗa a hankali zuciyar ta na ƙuna kamar ta fashe. Motsin sa taji, sai ta ɗago kanta tabi bayan sa da kallo da har ya shige ɗakin sa, wani ƙunci ne ya sake tokare mata maƙoshi, sai ta lumshe idanu tayi shiru tana sauraron bugun zuciyar ta, bata ƙara motsa wa ba har sanda taji motsin fitan sa. A haka ta wuni har dare bata sake tashi ba, illa sallah da ke tayar da ita, ko abinci taƙi ci a haka har dare yayi ta kwanta, nan da nan yau barci ya ɗauke ta saboda ta tara shi da yawa bata yi ba.

     Bata farka ba sai washe gari ƙarfe 07:00am. Sosai taji daɗin barcin da tayi, sai duk wani gajiya ya saukar mata, sosai ta ɗan ji sauƙin kan nata, miƙe wa tayi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala, sai da ta gabatar da sallah tayi lazami sosai har wajen tara da rabi, sannan ta miƙe ta shiga kichen, Breakfast ta haɗa sannan ta ɗaura ruwan wanka, a nan kichen ɗin ta karya tunda a nan take cin abincin ta

Ruwan na zafi ta sake ta kai Toilet, sai da ta sirka shi yanda take so kafin ta fito ta hau tuɓe kayan ta, ta cire riga tana shirin ɗaura zani sai ji tayi ya buɗe ƙofa

Usman ne ya fito cikin shirin sa da ya saba ko yaushe na ƙananan kaya, babu ƙarya ya ƙure wanka yau, sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake yi. Da kallo ya bi ta ganin yanda ta ƙudundune jiki lokaci ɗaya ta tsorata, har tana zame wa ƙasa saboda tsaban tsorata

Ita duk bata yi tunanin yana gidan ba, tunda da safe yake fita shiyasa ta cire kayan a Parlour.

    Shi kuwa tsaki yaja me sauti, ya sake ɗaure fuska tamau ya fice da sauri abin sa.

      Ajiyan zuciya ta sauke bayan ta raka bayan sa da harara, "ɗan iska. Allah ya isa tsakani na da kai". Ta faɗa a fili tana shige wa Toilet. Wanka tayi ta sanya doguwar riga ja, tayi Rolling da gyalen sa, kai tsaye ɗakin sa ta nufa, sai da ta gama share masa tana shirin fita ta hangi wardrobe ɗin sa kamar be gama rufe wa ba, da sauri ta ƙarisa har tana cin tuntuɓe, tana jan shi ya buɗe, washe baki tayi kai tsaye bincike ta soma yi ko Allah zai sa taga keeys ɗin gidan, tunda be taɓa barin wardrobe ɗin sa a buɗe ba, ilai kuwa sai taci Sa'a ta samu keeys da yawa a ciki, har da passport ɗin su a ciki, nan jikin ta ya hau rawa tsaban farin ciki, da sauri ta kwashi keeys ɗin ta fita da gudu, ƙofan ta nufa ta hau gwada mukullan, nan ta samu na ƙofan, sai ta buɗe ta watsar da mukullan a nan, ko mayar masa bata bi ta kai ba, passport ɗin ta na hannu ta wuce wajen kayan ta taja Trolly ɗinta ta fice da gudun ta, domin ba ƙaramin rawa jikin ta yake yi ba, gani take yi kamar kafin ta fita zai iya dawowa gidan.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Forty Nine*

        Tafiya take yi tana waigen bayan ta, duk ta gama tsorata matuƙa, ta san haɗuwar su dashi bazai mata daɗi ba, ita kuma tarigada ta ɗau alwashin sai dai tayi yawo cikin ƙasar nan, amma baza ta taɓa koma wa gidan sa ba, ko bata sami taimako ta koma ƙasar su ba sai dai tabi duniya

Har ta fice a layin gidan, ta yanki hanya ɗoɗar, tafiya me nisa tayi Kafin ta samu wata mata me shago a bakin titi, nan ta tuna da Numban Zakeeya ƙawarta da tayi a cikin jirgi, wani zuciyar tace mata "ta gwada neman taimako ko Allah zai sa a dace". Da sauri ta isa wajen ta tana maida numfashin gajiya, kafin ta ƙarisa wajen ta sai da ta ɗan samu ta daidaita kanta, sannan ta isa tana mata sannu da harshen turanci

Matar kallon ta tayi, duk da ba wani turanci ta iya ba, amma tana ji kaɗan-kaɗan, ta amsa mata cikin fara'a tana tambayan ta "me take so?" Cikin turancin

Nan Ɗahira tayi mata bayanin "don Allah ta taimaka mata da Aron waya, ita baƙuwa ce yau ta sauka, amma wayan ta ya faɗi, ta rasa ya zata yi ta isa gidan da tazo, tana buƙatar yin waya dasu ko za su san inda take".

Matar bata wani tsawaita ba, duba da yanda taga Ɗahiran duk tayi laushi ta wani yamushe, da alamun tana matuƙar buƙatar taimako, nan tausayin ta ya kamata ta, ta ɗauki wayan ta miƙa mata tana bin ta da kallo kamar zata haɗiye ta

Ita kuwa bata damu da kallon da take mata ba, jiki na rawa ta buɗe jakar ta a ƙaramin Zip ta ciro takardan, kofewa tayi a wayan tayi kira, ba'a ɗau lokaci ba kamar ana jira aka ɗauka

Muryan mace taji tayi sallama

Sai Ɗahiran ta amsa mata tana cewa, "da Allah da Zakeeya nake magana?"

"Ita ce. wace ce?".

Cikin Hausa take magana don kar matar taji me take cewa, ganin yanda idanun ta ke yawo a kanta, "suna na Ɗahira, Ni ce wacce muka haɗu dake a jirgi last three weeks, kin tuna Ni? Har muka zauna waje ɗaya muka yi exchanging number".

Cike da ɗoki Zakeeya tace, "Laa Ɗahira ke ce? Wlh nayi tunanin baza mu haɗu ba, sabida yanda nake ta kiran wayan ki ba ya shiga, kuma ke baki kira Ni ba".

"Haka ne. Amma ina buƙatar taimako, don Allah ki taimaka min".

Yanda tayi maganar yasa Zakeeyan ta gane akwai matsala, nan da nan ta tashi hankalin ta tana tambayan ta "me ya faru?"

Ɗahira tace mata, "maganar ba ta waya bace, ki taimaka ki zo ki tafi dani in yaso sai muyi maganar".

"Ok.. ok aina kike yanzu?"

Tambayar matar nan tayi, ita tayi mata kwatancen inda take

Zakeeyan tace, "gata nan zuwa yanzu, basu da nisa da wurin ma".

Sosai zuciyar Ɗahira tayi mata sanyi a wannan lokacin, gani take yi zata iya tsira ba tare da Usman ya sake ganin ta ba. Matar ta miƙa wa wayan tana ta mata godiya sosai kamar zata yi kuka.

      Babu jima wa kuwa sai ga Zakeeya a motar ta, da sauri ta fito ta nufo Ɗahiran

Itama Ɗahiran wajen ta ta nufa domin ta shaida ta

Sosai Zakeeya take ware idanun ta a kan Ɗahira gani take yi kamar ba ita ba, har sanda suka kusanci juna ta gane tabbas ita ce, amma kuma yanda ta sauya mata fiye da tunani, ga baƙi da tsananin rama da tayi, duk ta bushe kamar babu jini a jikin ta. Cikin sauri ta riga ta magana da tambayar ta, "Ɗahira ke ce? Ke ce haka meke faruwa ne?"

"Don Allah mu je sai in Yi Miki bayani, ke kaɗai na sani a ƙasar nan ina buƙatar taimakon ki Zakeeya".

Jiki na rawa kuwa Zakeeyan taja hannun ta ganin har ta soma hawaye, motan ta buɗe mata ta shiga daga ita har kayan ta, itama ta zagaya ta shiga taja motan da sauri. Sun yi tafiya me nisa babu me magana cikin su

Kai tsaye Zakeeya gidan su ta wuce da ita, suna isa suka fito taja hannun ta suka yi ciki

Auntyn Zakeeyan na zaune a Parlour suka shigo Zakeeya na sallama

Amsa mata tayi tana bin su da kallo, ganin ta da baƙuwa sai ta bi su da ido har suka zauna, kana kuma ta soma tambayar Zakeeyan "aina ta samo ta kamar ƴar ƙasar su?"

Zakeeya tace mata, "eh Aunty, ƴar Nigeria ce, domin a jirgi muka haɗu da ita sanda na dawo nan, tana buƙatar taimako ne shi ne ta kira Ni".

"Ok Allah Sarki, Allah yasa dai lafiya baiwar Allah? Sannu ko? Zakeeya kawo mata ruwa tasha naga kamar hankalin ta a tashe yake har kuka take yi".

Zakeeyan bata amsa ta ba illa miƙewa da tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login