Showing 75001 words to 78000 words out of 215266 words
da bata wuce sha takwas ba tsabar a ja masa raini, me zaiyi da Batuul yarinyar cikinsa? shi if he can clearly remember ma ai Massa ke sonta tun kamin ya bar gari, tunawa da yayi da Massa ne ya sashi saurin ciro wayarshi daga cikin aljihu ya lalubo number shi Massan, dialing biyu ya ďaga, "dama ana jinka a gari", abunda Massa ya fara faďa kenan, share tambayar da Massa ke mishi yayi yace "Kana inane?, inaso mu haďu", ya tsaya jin mey Massan zaice mishi, cewa yayi na fita yanxu bana gida but i will b back in an hour", yace "Aii then, zanje gida yanxu before ka dawo zan shiga in gaida Yaa Mera, sai ka dawo ďin, i need to discuss some issue with you", da haka suka katse wayan, suna gamawa ya murďa k'ofan ďakinshi ya shiga ya ďauko key ďin mota ya fito waje, direct hanyan gidansu Massa ya ďauka, cikin y'an minutes ya isa gidan yayi parking bayan an buďe mishi gate ya shiga, Side ďin Yaa Mera yayi, tayi mamakin ganinshi, dan rabonshi da gidan tun aurenshi da Ajiddeh da yazo yi mata sallama, mamaki shimfiďe fuskanta tace "Wata sabon gani Babana kaine a gidan nan yau, ashe ka shigo gari", k'arasowa yayi gabanta ya zauna yace " *Yaa Nda dubdo, aaah u' bèlan amma tusen gèi*, "ina wuni Yaa, ehhh na shigo amma banma daďe ba", ya k'arashe maganan da murmushi a fuskanshi, hira sukayi sosai da Yaa har tana ce mishi matarshi dai ba 'a ganinta, har sun manta kamanninta,suna nan zaune Massa ya shigo da sallama, tun daga can ya tsaya k'are ma Abutturab dake gaban Yaa Mera kallo, ba makawa Abu ne sai dai ya ďan rame, ko meye dalili oho yaci gaba da shigowa abunshi cikin ďakin, hannu ya mik'awa Abutturab tareda cewa "Man an dena ganinka, rabona dakai fa tunda naje wajenka kamin kazo gida, that is two months after your wedding, i tot baza ka shigo bama sai aure na ai", Yaa Mera ce tace "Abunda na gama faďa mishi kenan, nace gashi matar bata haihu ba bare mu muje can suna tunda su sunqi su zo gunmu", sauk'ar da kanshi yayi k'asa dan shima abin nan da yayi na damunshi, gashi nan har yana son zame mishi matsala, Massa ne yasa dariya yace "Kaji ko, ashe su Yaa zaman jiran jikansu suke, sai kayi k'ok'ari ku samo musu kai da Ajiddeh, kaga sai suji daďin bin naku can garinku mai daďi da baku son bari", wani kallo ya sakarwa Massa da ya sashi k'ara yin dariya yace "toh ba gaskiya bane", mik'ewa Yaa Mera tayi ta shige daga ciki su kuma suka wuce chamber ďin Massa, suna shiga ďakin ya zauna a ďaya daga cikin kujerun ďakin tareda mik'e k'afafuwanshi, Massa ya dubeshi yana buďe fridge zai ďauko ruwa yace "wai gajiya kayi ne haka na ganka so slow, ko kuma duk cikin canjawan da kayi ne", wani irin glare ya wurgawa Massa ya tashi daga kwancen da yake ya zauna, k'arasowa Kujeran Massan yayi shima ya zauna tareda mik'awa Abutturab ruwa, karb'a yayi bayan yasha ya rufe ya ajiye bottle ďin daga gefenshi ya fara msgana kamar haka "Musty, kwanankin baya lokacin biki na kamar naga you showed interest akan yarinyar nan, har yanxu kuna tare ne?", yayi tambayar yana kallonshi, gaba ďaya kan Massa ya ďaure dan shi baisan ma wace yarinyar yake tambaya ba, cewa yayi "wacce yarinyar wai, dan ni ban gane wacce kake nufi ba", ce mishi yayi yarinyar nan k'arama mana, yarinyar Aunty", tsaki Massa yaja yace "kaji ka da wani zance, Aunty ďaya muke da mai k'aramar yarinya, specify inji", shiru yayi ya kasa furta sunan nata, da k'yar ya iya buďe bakinshi yace "Batuul", "ohhh dama wai Batuul kake nufi kake ta wannan abin, wait!, dont tell me bakasan zancen aurena ba", da mamaki Abutturab ya dubeshi yace "kayi aurene?", kai ya girgiza yace "No banyi ba but nan da two weeks za ayi", kan Abutturab ne ya ďaure, yaushe Massa zaiyi aure har bai sani ba, kuma wa zai aura inba Batuul ba, yes ba Batuul bace tunda har su Ammah sukace ya aureta, da sauri ya juya ya dubi Massan da ya zuba mishi ido ganin yadda yake abu kamar ba shi ba yace "Tell me wacece zaka aura inba Batuul ba, kuma ya akayi haka bayan at that time kace min sonta kakeyi", murmushi Massa yayi yace "Toh kai duk mey ya kawo zancen nan, kai da kace mey zanyi da yarinyar tayi k'arama shiyasa na rabu da ita", kai Abutturab ya girgiza yace "c'mon jokes apart, ba wasa nake ba, mesa ka rabu da ita kuma wa zaka aura?", Massa ne yace "Rahama mana zan aura, y'ar Sultan, Batuul tun lokacin ta nuna bata sona shiyasa ma ban kai abun wajensu Ammah ba, but naso in aureta, she will make a good wi.....", wani tsaki Abutturab yaja yace "hold it, okay?", gaba ďaya ranshi ya b'ace, sai da ya ďan nutsu tukunna yace "Mustapha am in a problem, kuma babu mai iya fiddani sai kai, kasan auren nan da nayi shekara kenan, kuma su Ammah suna ganin shine ya hanani zuwa inda suke, and ni inason Ajiddeh, like banima da ra'ayin mata biyu, i cant cope, toh ďazu su Ammah suka tareni da zancen sai na k'ara aure, da nace suyi hak'uri, amma ganin ransu ya b'aci yasa nace na yadda, toh shine da na tambayesu wa suke so in aura, dan ni i have no one in mind shine sukace min wai Batuul", yadda ya k'ira sunan nata kamar ba daga bakinshi sunan ya fito ba yayi maza ya ďauke idonshi daga kan Massa , dariya Massa yasa harda kyakyatawa ya kwanta akan kujeran, sai da ya gaji dan kanshi ya gama dariyan tukunna ya mik'e ya zauna, Abutturab ko kallonshi baiyi ba har ya gama dariyanshi, sai da yayi shiru tukunna yace mishi "ka maidani ďan iska ma ko, inyi maka serious magana shine kake dariya", ya k'ara tamke fuska ya tashi zai bar ďakin, da sauri Massa ya sha gabanshi yace "No baza muyi haka ba, mu koma ka faďamin how am i of help dan ni gaba ďaya zancen ne yazo min a bazata, kaga kuma tunda bazanyi kuka ba ai sai inyi dariya", ya faďa yana k'ara smiling, wani siririn tsaki yaja ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, sai da dukkansu biyu suka zauna Massa yace "ina jinka, mey kakeso inyi maka?", shiru yayi ya kasa magana dan baisan ya Massa zai ďauki zancen ba barema da yace aurenshi nan da sati biyu, iska ya furzar daga bakinshi sannan yace "Inaso kaje kacewa su Ammah kai ke son Batuul, zaka aureta", a razane ya juyo jin abinda Abun ya faďi yace "Are you really okay, duk yadda akayi Ajiddeh har brain ďinka ta tab'a, toh in naje nace musu inasonta sai inyi yaya da ita bayan inada mata", kai ya girgiza yace mishi "ai dama kana sonta, kuma kasha faďamin kai baza ka zauna da mata ďaya ba, and as crowned prince kaga zaka k'ara wata, kaga tunda sooner or later zakayi, y not do it now", kai ya girgiza yace "No way, thats not happening with me, bazanje inyi abunda ban shirya yinshi ba besides ai Batuul ďin na faďa maka da kanta tace min bata sona, kaga there is no way zan auri yarinyar da bata sona", kai shima ďin ya girgiza yace "Musty you are not understanding the whole thing, am telling you......", katseshi Massa yayi yace "hold on, kai mesa baza ka auri Batuul ďin ba, she is perfect, beautiful, simple, religious, mey kuma zaka nema bayan wannan, like menene aibun Batuul, ni wlhy da zata soni zan aureta but ta riga da tace min bata sona, so i will b living with that intuition a cikin kaina shiyasa bazan nemeta ba, kuma tunda har su Ammah ne suka nema maka auren nan i bet its for everyones welfare, they have seen the best in her, kuma ni nasan they have a genuine reason for all this, Batuul is your sister, you can tell others who she is, kafi kowa sanin asalinta", kanshi ya sauk'e k'asa ya rasa ya za ayi ya fahimtar da Massa akan bazai iya auren yarinyar nan ba, yafi minti ďaya kanshi na dafe kan hannunshi tukunna ya ďago a fusace har idonshi ya canja launi yace "Na faďa maka bazan iya aurenta ba", sai kuma ya sassauta murya jin ihun da yayi yace "Mustapha i cant marry her, like i cant withstand her for a day, bare kuma har aure da yake for eternity, i just cant, i dont know but there is this effect she have on me anytime nake tareda ita and am never comfortable with what i feel", ya k'arashe maganan yana mai sauk'e idonshi daga kallon Massa, Ajiyar zuciya Massa yayi ya dafa Kafaďan Abu yace "okay calm down, kasan mey za ayi yanzu, ka kwantar da hankalinka, addu'a kawai zakayi akan lamarin nan, zamuyi magana daga baya, kuma kada ka nunawa su Ammah baka so dan ransu zai b'aci", shima Abun ajiyar zuciya yayi yayi patting hannun Massa dake kafaďanshi yace "In sha Allah zanyi", da haka suka canja zancen suka shiga na wajen aiki da bayan rabuwa, duk da Abuturrab Sam hankalinsa bae jikinsa.
Bayan Batuul ta dawo daga makaranta gida ta dawo kamar yadda Aunty ta ce mata, da sallama ta shigo taga babu kowa a palo, kitchen ta shiga taga Aunty dasu Esther na aiki, k'arasawa tayi ta gaida Aunty tayiwa sauran sannu da aiki duk suma suka mata sannu da dawowa, jikinta ne yayi sanyi ganin yanayin da Aunty ta amsa mata gaisuwan, hawaye ne ya fara taruwa a idonta don ita a tunaninta tun maganan ďazu da safen nan ya ke b'atawa Aunty rai, maza tayi ta fita daga kitchen ďin dan tasan kuka zata fara gashi akwai masu aikinsu a gun, anjima zataje har ďaki ta sake bata hak'uri akan maganan duk da dai batasan mey ya fara kawo zancen aure ba, sama ta haura bayan ta fito daga kitchen ďin, hanyan ďakin k'annenta tabi, buďe k'ofan tayi ta shiga , ta ga dukkansu shirin Islamiyya sukeyi, wasu na saka uniform wasu sun gama, shiga tayi ta samu waje ta zauna daga ďaya daga cikin gadajen ďakin, ita da kanta batasan mey ya shigo da ita ba, Khalil yace "Yaa Batuul wannan takwarar taki tazo", ya faďa yana b'ata rai, Mus'ab ne yayi maza ya karb'e maganan tareda zumb'uro baki yace, "mtsew ni Allah kullum bana son zuwanta", hararanshi Batuul tayi tace "bana son rashin hankali, Mamar Baba cefa kake cewa bakason zuwanta, ita da gidan ďanta", Ahmad dake fesa turarene yace "ehh mana ai gaskiya suka faďa, abu duk randa tazo sai tasa ran Aunty ya b'aci, ni bana ganin amfanin zuwan nata, gara mu mu rik'a zuwa wajen nata mu kaďai,ni da tace bata son Abuja ma daďi naji, kuma fa kamar sunanki naji tana k'ira tana ta faďa, ai Aunty ce tace mu hau sama shiyasa banji mey suka faďa ba", tsawa Batuul tayi musu tace "bafa na son iskanci, waye yace muku ita take b'atawa Aunty rai, wato dukkanku gulma kuke koya ko", Sa'eed da dama tun can shi bamai magana bane yace musu "ku shirya mu tafi dan Allah, its getting late", ya ďauki wayanshi kan mirror ďinsu ya saka a aljihu ya fita, Su Yusra ne suka shigo ďakin su sun gama shiryawa sukace Yaa Ahmad mun gama shiryawa fa, inji Aunty mu k'ira ka mu tafi kar muyi latti, dukkansu fita sukayi daga ďakin bayan sun gama shiryawa sukayi mata sai sun dawo, jiki a sanyaye tace "okay sai kun dawo, kuyi karatu sosai kunji ko, in kun dawo zan baku chocolate", ta faďawa su Mahir da ďan dariyan yakenta, suna fita ta tashi itama tabi bayansu tayi hanyan ďakin da tasan zata tarar da kakarta da k'annenta ke cewa tazo, tasan duk gaskiya suke faďi, duk yadda akayi ma itace tasa ran Aunty b'aci, batasan meyesa bata sonta ba, tunda tasanta, tasan kakarta bata tab'a son Aunty ba duk da kyautatawan da Aunty keyi mata dan Aunty tasha yiwa Yayya abun kirki tun suna Maiduguri harda suka dawo Abuja ma kuma ba tareda sanin Baba ba, amma bata tab'a appreciating ba, zuwanta bakin k'ofar ďakin ne yasa ta kawar da tunanin da take ta murďa k'ofan ďakin.
💖💝BATUUL💖💝
37
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Daga gaban gadon Abdallah ya tsaya a tunaninsa Abuturrab xae basu waje sae ya ga otherwise, don kujera gogan ya ja yyi xaman sa yana facing dinsu, Abubakar na ganin hka ya xauna gefenta ya shiga mata magana murya can k'asa da damuwa, Batuul ta k'asa ďago kai ta kalleshi, sake matsowa yayi kusa da ita yace "Habibty tok to me mana, mey doctor yace na damunki", a hankali kamar bata son aji mey take faďi tana wasa da fingers dinta tace "nima ban sani ba, but i think doctor ya faďawa su Aunty, ni ban sani ba", ta k'arasa maganan tare da ďago kanta, ido hudu suka yi da Abutturab dake kallonta ko kiftawa bae yi, ya watsa mata wani irin kallon da ya sata saurin sadda kai, haka Abdallah yaci gaba da yi mata tambayoyi da yi mata sannu da damuwa, bata cewa komai daga "um", sai "um um", banging k'ofa suka ji suka juya, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ganin shi ne ya fita, juyowa Abdallah yayi yace "Habibty who is he? your uncle", girgiza kai tayi tace mishi "brother ďin Farida ne", juyawa yayi ya sake kallon k'ofan sannan ya mik'e tsaye yace " Shknn Habibty i will b going, Mum na mota tana jirana get well soon, i will b back tomorrow in'sha Allah", yayi mata wani lallausan murmushi da itama maida mishi, daga haka ya fita yana waigen ta, a bakin k'ofa ya tarar da Abutturab na waya, tsayawa yayi ya gama wayan su yi sallama, ganin ya kusa minti biyar tsaye kuma ya ki k'are wayar yasa ya ďaga mishi hannu ya wuce, Abuturrab na ganin ya wuce ya katse wayan ya tura k'ofar ďakin, hawayen dake idonta take gogewa da tissue, tsayawa yayi yana kallonta daga bakin k'ofa, snn ya shigi tare da tura k'ofan ya rufr, jin k'aran k'ofan ne ya sata ďagowa da sauri, duk da rashin k'arfin jikinta hkn bai hanata mik'ewa cikin sauri tayi hanyan toilet ba, da gudu taje zata buďe k'ofan, taji ya fixgota, tsayawa tayi a wajen ta kasa motsi gabanta na faduwa, ya juyo da ita yana kallon yadda ta rintse ido hawaye na zubowa, fuskanta ya tsura ma ido da ďan k'aramin lips ďinta da ya koma ja, hannunshi ya ďaura kan kafaďunta ya matso da ita gabanshi yana kallonta da kyau yace "waye shi?" Kin cewa komae tayi har lkcn idonta a runtse, ya daga kafada yace "As if i care, kina jina dama Aunty na shigowa ki ce mata kin warke a maidaki gida kuma ke kina da wanda kike so, nasan wannan da yazo ya saki gaba yana miki surutu kmr radio saurayinki ne, toh dama kice musu shi kikeso kuma keh shi zaki aura, is dat clear?", sai da taji yayi shiru har lokacin tana hawaye ta buďe ido a hnkli tace "kai mey zai hana ka faďa musu, kaima ai kasan su kuma zaka iya samun su ka faďa musu kace kana da matarka basai an sani aurenka ba dan ni bbu abinda xanyi da mai mata, sabon jini dama ai sai sabo, mey ma zanyi da......", ganin yadda ya zuba mata lumsassun idanunshi yasa ta maida sauran maganan tana gogewa hawayen dake fuskanta, bin fuskanta yayi da kallo har idonshi ya sauk'a kan k'irjinta dake ta heaving, dariya abun ya bashi amma ya dake, yasan duk maganan da tayi a tsorace take, saketa yayi yana mata wani irin kallo yace "Really?, Fine then, zamu haďu ne tun da bakiji abinda na faďa miki ba, ki yadda ayi auren, xagi gane mai mata kuma tsohon jini kika aura yarinya", yana kaiwa nan ya juya ya fita daga ďakin, a nan wajen ta tsuguna ta sa kuka kamar wacce aka aikowa lbrn mutuwa, a nan Aunty ta shigo ta sameta, da gudu Aunty tazo ta ďagata tana tambayanta mey ya sameta, kasa magana tayi sai kukan da take tayi, Anty ta maida ta kan gado ta rungumeta hankali tashe tana lallashin ta, a nan tayi bacci jikin Aunty.
11 o'clock bayan doctor ya dubata yayi discharging ďinsu akan zai na zuwa har gida yayi mata alluranta da suka rage sannan yace a guji duk wani abu da zai rik'a b'ata mata rai kuma kar a rik'a faďa mata maganan da bata expecting har ya rik'a shocking ďinta tana zama unconscious, Baba ne yayi magana yace zasu kiyaye, da haka suka yiwa doctor sallama, suna komawa gida tace ita baza taje ďakinta ba a ďakin Aunty zata zauna, wanka tayi bayan ta shiga ďakin sannan ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai k'arfe biyu, tayi alwala ta tada Sallah, tana idarwa Aunty ta shigo rik'e da tray a hannunta, ajiyewa tayi ta zubawa Batuul abinci sannan tace mata ta sauk'o taci, da kyar taci kaďan tace ta koshi,
Da yamma wajen k'arfe biyar tana zaune tana kallon E.tv Aunty na haďa kayan Aabid Baba ya shigo ďakin, kan gadon da Batuul ke zaune ya zauna, tashi tayi zata sauk'a ta gaisheshi yace mata "Yaanyi" (Mamata), ďagowa tayi ta kalleshi da idonta da ya fara kawo ruwa, hannu yasa ya goge mata hawayen ya matso da ita jikinshi ya fara mata magana kamar haka "Ya jikin ki Batuul", jiki a sanyaye ta amsa mishi da