Showing 162001 words to 165000 words out of 215266 words

Chapter 55 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

15752

sauk'esu, ido ya wara shima ya matso kan gadon ya d'agota sai ji tayi ya rungumeta jikinshi, ya kai minti biyu rungume da ita bata yi k'ok'arin k'wace kanta ba har saida ya saketa ya d'ago hab'arta yace "Ina ke miki ciwo yanxu Fatima?", murmushi tayi mishi kawai ta shiga k'ok'arin tashi ta zauna, da kanshi ya d'agata ta zauna yana making sure bata takura ba, ganin yanda Farida ta tsaya tsuru tana kallonta ya bawa Batuul dariya, tace "Hey what's up duk kin zama wata iri, am okay fa", murna ne ya cika Faridan tayi maza ta dawo kan gadon ta zauna, tace "Don't get sick pls, you scared d hell out ta me pls kinji?" murmushi tayi kamar ba ita ke ciwo ba d'azu snn ta kalli Abu da yake lumshe ido yana bud'esu yana kallonta ta d'an shagwab'e fuska tace "Mu tafi gida Yaa Abu, ni bana son asibitin nan", kai ya girgiza mata yace "No sai kin fad'amin mey ke damunki, baza mu tafi ba bamusan mey ke damunki ba", had'e rai tayi tace "Yaa Abu nifa na warke, mu tafi gida", ta fad'a tana k'ok'arin sauk'owa kan gadon, hannunta ya rik'o ya k'ura mata hazel brown idanunshi, cikin wani irin murya yace "Fatima mana, I want you to fully get better, bana son kina shan wahala kamar na yau, nafiso ki zama under medication, under proper care kinji?", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh fa na warke ni, bazan sake yin rashin lafiyan ba", Ido kawai ya zuba mata yanason ta gano abinda yake hange amma baya son stressing d'inta tunda ba isasshen lafiya bane da ita, a sanyaye yace mata "ina zaki yanzun?", ta zumb'uro mishi baki tace "toilet", da sauri Farida ta mik'e ta riqota tace muje in rakaki, kai ta kad'a tace "zanfa Iya da kaina na warke", kamar jira yake ta rufe baki ya sunkuceta yayi toilet da ita itako sai wuntsila k'afa takeyi ya sauk'eta, bai bi ta kanta ba har saida ya Isa toilet snn ya ajiyeta a hankali, d'an murgud'a mishi bakin tayi snn ta kalleshi tace "Toh ka tafi", wani irin kallon da yayi mata yasata yin shiru ta kasa motsi, ganin ta nemi waje ta tsaya yasashi k'arasawa gabanta ya shiga k'ok'arin d'age mata skirt d'inta, ihu ta fasa ta riqe skirt d'in da k'arfi tace "Bafa komai zanyi ba, alwala nakeson yi", kallonta kawai yakeyi snn ya kamata suka koma gaban hand wash basin d'in, kamar wata yarinya shi yayi mata alwalan, bags d'in da ya shigo dasu ya janyo bayan ya sata ta zauna kan gadon, pack d'aya ya Ciro mai d'auke da malted custard roast da Lamb Kebab salad, da kanshi ya bata abinci har saida tace ta k'oshi snn yace tayi sllhn shi kuma ya fita wajen doctor yayi maganan discharging d'inta, bai jima ya shigo lokacin har ta idar da sllh suna hiransu da Farida, ce musu yayi zasu tafi, murna Batuul ta shiga yi dan ta tsani asibiti ita kam, da murnarta ta shige gaba kamar ba ita aka kawo a galabaice ba, driving yakeyi amma duk bayan seconds biyar sai ya juyo ya dubeta, cikin lokaci kad'an suka isa gida lokacin ana k'iran Magrib,saida sukayi sllh snn suka kafa hira ita da Farida, ganin ya shigo d'akin yasa Farida fita, daidai tazo wuceshi yace " You should Get ready gobe flight d'in by 8 ne", sai a lokacin Batuul ta tuna da tafiyan Farida, jiki a sanyaye ta amsa da "toh", sam hankalinta bai kwanta da barin Batuul ba gashi shi bama zama yakeyi ba, cikin d'akin ya k'araso ya zauna bakin gadon yana kallon Batuul da har idonta ya cicciko yace "How you feeling now?", baki ta bud'e zatayi magana hawayen dake tare idonta ya shiga gangarowa, har ranshi ya ji zubowansu da hanzari ya gyara zamanshi kan gadon ya rungumota tareda cewa "Yasalam, Fatima what is it again?, I told you mu zauna asibitin amma kikayi insisting mu dawo gashi nan yana damunki kuma koh", ji yayi ta sake lafewa jikinshi a hankali tace "Does she have to leave tomorrow?", sai da ya tsaya for some seconds snn ya gano abinda take nufi, ajiyar zuciya ya sauk'e jin ba ciwon cikin nata bane ta d'ago kanta yace "School zata koma, dama mid semester break ta zo", a hankali ta d'ago ta dubeshi tace "toh ni yaushe zaka kaini gidan, I want to go home" muryarta na rawa ta kare maganar, rungumota ya sakeyi jikinshi yana shafa kanta yace "very soon, ko har kin manta deal d'inmune?, ba nace zan kaiki gida da kaina ba in kika haifa min baby na", d'an zumb'uro baki tayi jin ya ambaci Babyn shi ta kauda kanta, murmushi yayi tareda juyo da kan nata, idonshi kan lips d'inta yace "I like them when you pout, I miss them so much", kamin ta ankara har kai nashi lips d'in kan nata, passionately yake kissing d'inta kamar yau ya fara kissing d'in nata idonsa lumshe, haka yayita tarairayarta har wajen sha d'aya bayan yayi mata wanka ya jasu Sllh Isha ya kwantar da ita ya shiga sata bacci, a jikinshi tayi baccin wajen 11:30, saida ya tabbatar tayi nisa a baccin tukunna ya saka mata temperature d'in d'akin ya koma moderate, ya tabbatar she is fine snn ya fita, a parlourn k'asa ya tadda Farida ta kashe wutan ko ina tana kallon CBS, Ce mata yayi ta koma d'aki gun Batuul snn yayi mata sai da safe ya fita akan gobe da safe zaizo kaita airport ta zama cikin shiri, sai da ya shiga mota tukunna ya tuna da wayoyinsa, missed calls ya gani babu adadi daga mutane daban daban amma duk na Ajiddeh yafi yawa, d'an murza goshinshi yayi snn yayi igniting motar ya d'au hanyan gida, lokacin da ya isa Ajiddeh na kwance parlour tayi bacci da alama tasha kuka ba kad'an, tausayinta yaji Sosai har cikin ranshi yasan bai kyauta mata ba, kashe appliances d'in yayi snn ya dawo ya d'auketa yayi sama da ita





Washegari kamar kullum da ya tashi sllh saida ya tashi Ajiddeh amma bata tashi ba, shi kam daga masallaci d'ayan gidan ya wuce, a kitchen ya taddasu su biyun duka Farida har ta shirya, k'arasowa yayi cikin kitchen d'in yana amsa gaisuwan Farida ya isa inda Batuul ke jingine jinkin Fridge, yana zuwa ya jawota jikinshi ya d'aura hannunshi kan mararta a hankali, da sauri ta d'aga ido taga ko Farida na kallonsu, ai kuwa ido hud'u sukayi da Faridan, maza tayi ta d'auke idonta cike da kunya snn ta riqe mishi hannu, rankwafowa yayi daidai wuyanta da muryan shagwab'a da ya sauqe mata kasala gaba d'aya yace "Ina duba Baby na", cike da jin kunya a hankali tace "Yaa Abu Farida fa na nan" kallon Faridan yayi, suna had'a ido ya sakar mata wani irin kallo, babu shiri ta bar abinda takeyi ta rage wutan stove d'in tayi waje da sauri, tana fita ya juyo da Batuul d'in, y'ar rigar dake jikinta ya d'age ya shiga making circles a flat tummy d'inta da yasata jin wani sabon feeling na daban na ratsata, a hankali yace mata "Meh zaki bawa Farida?", sai lokacin abin ya fad'o mata d'ago kai tace "Nima ban sani bafa, kawai zan bata kosu bracelets d'ina ko?", ta tambayeshi, murmushi yayi ya janye hannunshi cikin rigan nata ya kamota yace "muje ki gani sai ki duba ki ga In yayi a bata", babu musu ta bishi a baya suka fita waje, Farida na ganin fitansu ta koma kitchen taci gaba da abinda takeyi tana murmushi cike da jin dadin irin xaman Bestyn nata da yayanta, suna shigowa daidai nan Faridan ma ta fito riqe da bowl d'in oat a hannuta tana jujjuyashi, a nan ya bar Batuul ya haura sama, ba a jima ba ya sauko yace su wuce, cikin y'an minutes suka isa airport, sai lokacin Batuul ta dad'a tabbatar da tafiyan Farida, kamar kar su rabu harda k'wallanta, k'ok'arin fitowa ta shigayi daga motan zata raka Farida yayi maza ya rik'ota yana kallonta yace "Ina zakije haka?" , zumb'uro mishi baki tayi cike da shagwab'a tace "zan rakata mana", kai ya girgiza yace "kinada hankali zaki fita a haka ko mayafi babu?, dubi kayan dake jikinki?", kallon kanta tayi taga koh kayanta are, wandone jikinta sai jacket iya gwiwa da hood amma yake fad'a mata wai kada ta fita a haka, rai b'ace ta koma ta kwanta sai Faridan ce ta zagayo tayi hugging d'inta, dan takaici kasa magana tayi sai hawaye da ta dinga yi, shi ya d'auki jakan tsaraban ya rakata dashi yace mata inji Batuul, ya k'ara mata da kud'i masu yawa, har saida yaga ta shiga jirgi sannan ya juyo, a mota ya tadda Batuul har tayi kukanta ta gode Allah, ko sau d'aya bata kalleshi ba bayan ya dawo, haka ya k'arashi surutunshi suka isa gida, yana parking ta bud'e mota ta fita a guje, a gujen shima ya bita dan har ranshi yakejin gudun nata snn gashi ba lafiyane da ita isasshe ba, daidai takai k'afanta kan 5th stair case ya cimmata, wani razanannen k'ara ta saki da yasata durk'ushewa k'asa, binta yayi ya kamota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "Fatima ban hanaki tsalle ba?, bakida hankali koh?, next time you try this shit I will slap you", gaba d'aya bata sanma mey yake fad'i ba sai yarfe hannu da takeyi, kuka sosai ta shiga yi tana k'iran sunan Auny tana riqe da cikinta, rud'ewa yayi ganin da gaske take ya d'agota yace "Batuul talk to me, cikin ne?", a hankali ta shiga gyad'a mishi kai a wahalce, duk ya rasa mey ma zaiyi dan duk ya rud'e, cak ya d'auketa sukayi asibiti, ikon Allah ne kawai ya kaisu lafiya dan baisan irin driving d'in da yayi ba, likitocin this time ma cikin gaggawa suka amsheta, sai kukan wahala take tana k'iran sunan Aunty, har dare likitocin na kan Batuul sun kasa gano Ina matsalar take gashi duk wani taimako da zasuyi sun mata shi amma babu wani ci gaba, Abu kam tsayawa kawai yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, kamar shi ke ciwon har fad'awa yayi daga yini d'aya. Sai karfe takwas da wani abu na daren bacci ya dauketa shi ma sai juye juye take, Abuturrab dake xaune gefenta ya tsura mata ido cike da tausayinta ganin yanda ta wani rame daga safen xuwa dare, mikewa yayi da kyar ya nufi office din likita, nan ya shaida ma likitan in dai cikin xai bada matsala kawai a cire sa, ficewa yayi daga office din ya nufi gida kafin ta tashi don dauko wayarsa, Ajiddeh na xaune parlor kamar ko da yaushe, yau dai sai ya gaya mata ma'anar fitar da yake da asuba ko sallama babu baxa kuma ta kara ganinsa ba sai dare, bin sa da kallo tayi ganin ko kallonta bai yi ba ya haura sama, mikewa tayi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado, da ganinsa kasan akwai matsala, ta karaso da sauri ta xauna gefensa tace "Me ya faru babe? What's wrong?" Rike kansa yayi bai ce komai ba, ta dago kansa tace "Talk to me mana, me ya faru" Da kyar ya iya bude baki yace "Batuul!" Ji tayi kamar ya soka mata mashi, lokaci daya xuciyarta ya shiga tafarfasa, ta dake tace "What about her?" Cike da confusion yace "I just don't know, tana asibiti" wani farin ciki ya lullube Ajiddeh, sai dai cike da damuwa kamar gaske tace "Ayya, Allah ya bata lafiya" mikewa yayi da kyar ya dau wayarsa xai fita, tace "plss xan bi ka muje in dubata babe" bai tanka ta ba ya fita, ta mike cike da murna ta dau hijab ta sa ta bi bayansa da sauri, har ta shiga motar bai ce mata komai ba ya tada suka kama hanyar asibitin, ba karamin tashi hankalinsa ya kuma yi ba ganin likitoci a kanta, su Ajiddeh kamar na kirki ta dinga kwantar masa da hankali wai she will be fine. Likitocin na fita ya shiga Ajiddeh na biye da shi a baya, rungumeta yayi ta kankamesa tana kiran sunansa cikin kuka, a rikice yace "Don't worry Fatima xa a cire babyn ki huta kin ji" girgixa masa kai kawai take tana kuka sosai, Ajiddeh ta xauna gefenta tana '' tana kallonta lokaci daya jikinta yayi sanyi jin ta ambaci mutuwa.
[11/15, 11:14 AM] β€ͺ+234 810 957 2036‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’







78




By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




A hankali Ajiddeh ta shiga girgixa kai da kyar tace "No! Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya kin ji" Abuturrab da ya gama rudewa jin abinda tace ya rike hannayenta yace "Noo no baxa ki mutu ba Fatima, don't worry xa a cire babyn ki huta, bana so kuma, xa a cire soon kin ji, kar ki kuma cewa xa ki mutu plss" ko kadan Batuul bata san abinda suke cewa ba don ita kadai tasan abinda take ji a lokacin, tayi wani kara da ya kuma rudar da Abuturrab da Ajiddeh tace "Don Allah Anty ki ce ya kai ni gun Antyna nasan mutuwa xan yi, wayyo cikina" Abuturrab ya rungumeta a rikice yace "Stop this Fatima, ki daina kiran mutuwa plss" hawaye ne ya ciko idonsa yace "No! Baxa ki mutu ba wife, baxa ki mutu" Ajiddeh da duk jikinta yayi sanyi ita ma ta shiga hawayen a hankali tace "Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya" mikewa tayi da kyar ta fice daga dakin, ta tafi nesa da ward din, layin Mum dinta ta shiga kira, bugu uku aka daga, bangaren Mum tace "yauwa 'yar gari dama yanxu nake kokarin kiran ki, ya ake ciki kin ga alamar...." A sanyaye Ajiddeh ta katse ta tace "Mum kinsan me? don Allah kice a dakatar da aikin nan tukun....." Cike da mamaki Mum tace "A dakatar da aiki? Saboda me?" Da kyar Ajiddeh muryarta na rawa tace "Mum kinga fa kila mutuwa xata yi, kuma..." Sai ta fashe da kuka tace "Mum ni dai a dakata tukunna....." Wani uban ashar mum ta kunduma mata a fusace tace "Shegiya sallamammiya, kin san nawa na kashe 'yar abu kaza kaza, a dakatar da aiki??? Wani irin zagi Mum ta kuma k'undumo mata da har saida ya tsorata ta, a fusace ta diro daga kan gadon da take cikeda masifa tace "Keh kinsan mey kike cewa? to kinyi kadan Ajiddeh, a xuri'armu bbu warce ta taba zama da kishiya, baxa kuma a fara a kan 'yar cikina ba, Aliyu naki ne ke daya don ubanki, Ajiddeh cikin kuka tace "Mum nifa bance zan zauna da ita ba, kawai dai bana son ta mutune", Fusata Mummy ta sakeyi har wani gumin masifa ke tsattsafo mata a goshi, rai a b'ace tace "keh don ubanki ki fita idona kinaji, shegiyar yarinya da bata san abinda takeyi ba, zur'armu kaf babu wacce ta zauna da kishiya, mey ma za ayi da zama da kishiya, Allah bai d'aura mana ba kema kuma baki zama da ita, ita da take gantalalliyar kishiya ma har aka munafurce ki akayi komai shine kike tausayinta, indai ni haifeki kika kuma tausayin yarinyar nan sai. na tsine dan haka in zaki dawo hankalinki tun wuri ki dawo kisan inda dare yayi miki, wawiyar yarinya kawai, kina abu sai kace bani na haifeki ba, K'anwar uwarki ce yarinyar da zakice mituwa zatayi ko kuma in ta mutun asara ne dake, mutuwa kuma kamar tayi shi daga ita har shegen dake cikinta, kaji min wahalalliya mara wayo, to kin yi k'adan yanxu ma shiri nake xan koma kauyen don ba a gama aikin ba" Ajiddeh ta fashe da kuka sosai tace "Allah mum ni dai ba ruwana, kar ta je ta mutu...." Wani raxanannen tsawa Mum ta daka mata ta dinga kunduma mata zagi tace ", Ajiddeh ta katse wayar ta jingina da bango hawaye na sakko mata, da kyar ta ja kafa ta koma ward din, hankalin ta ya kuma tashi ganin halin da Batuul ke ciki, likitoci biyu a kanta, karasawa tayi da sauri ta xauna kusa da ita jin abinda take ta cewa, ta rike hannunta hawaye na sakko mata tace "Baxa ki mutu ba, sai lokacin ki yayi" Abuturrab dake xaune ya rike kai ya d'ago da kyar yana kallonsu da idanuwansa da suka kada, ya karbi wayar Ajiddeh don bai ma san inda nasa yake ba, ya fita don kira Ammah shi da likitocin xa su ji ta nasa da an cire cikin a nn take kawai amma sun ki wai sai bayan awanni idan suka gama binciken da suke, rungume Batuul Ajiddeh tayi, sai ce mata take cikinta, dubara ne ya fado ma Ajiddeh ta shiga tofa mata addu'a a hankali, Abuturrab na fita ya kira Ammah, tana d'agawa ya kasa ce mata komai, tayi sallama yayi uku kafin da kyar yace "Ammah, Batuul...." Jin muryarsa Ammah tace "Abuturrab, lafiya me ya faru" da kyar ya kuma cewa "Batuul..." Nan hankalin Ammah ya tashi ba kadan ba tace "Kayi min magana mana Aliyu, me ya samu Batuul din" k'asa bata amsa yayi hawaye na sakko masa, nan hankalin Ammah ya kuma tashi barin da taji yayi shiru kuma tasan hawaye yake shirun nan, don ita ta haifi abunta, tsawa tayi masa tace "Kana da hankali kuwa Aliyu, baxa ka fadi abinda ya samu Batuul din ba" da kyar ya bude baki yace "Bata da lafiya ne" tayi kokarin boye tashin hankalinta tace "Subhanallah! Tun yaushe?" Yace "jiya" sosai hankalinta ya tashi don tasan ba abu kadan bane Abuturrab xai ma hawaye, tace "Me ya sameta?" Ya girgixa kai bai ce komai ba, Ammah tace "ka bude baki ka min magana Aliyu, farida fa?" Da kyar ya iya cewa 'Daxu na Kai ta airport " Ammah tace "Dawo min da ita immediately" "toh" kawai ya iya ce mata ta katse wayar hankali tashe tayi part din Abui. Juyawa yayi ya koma ward din, har lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login