Showing 18001 words to 21000 words out of 215266 words
pocket ďin seat ďin gabansu ta sake mak'ala ear piece ďin a kunnenta taci gaba da jin karatun qur'anin da takeji ďazu, hostess ďince ta dawo da coffee ta ajiye mishi ta juya.
k'arfe 12:10 daidai jirginsu yayi landing a filin jirgin Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, jirgi na tsayawa Batuul ta tashi zata fita daga seat ďin da sauri fuskar nn tata a daure, k'in matsawa yayi ta fita har saida mutanen dake can economy class suka gama fita na first class ďin ma sun k'are, ita dae bata ce mishi komai ba har ya gama zaman mulkinshi ya mik'e cikin isa, ko gama barin wajen be yi ba ta bangajesa ta fice ta ďauko jakanta, sae da ya gama bari ta dauki jakarta snn ya fixgo ta yace "Are yhu blind" buge hannunsa tayi ta fita da gudu, tana fita taga y'an gidansu a waje ďaya, Aunty ce tace mata "mey kika tsaya yi ke baki fito ba sai yanxu", cewa Aunty tayi "bana so inzo fita ina jiran mutane shiyasa na jira kowa ya gama fita", Abutturab ne ya k'araso inda yake fuskarshi a sake kamar ba shi ke ďaure fuska ba ďaxu a cikin jirgi, Hannu ya mik'awa Baba tare da ce mishi "Baba ya gajiyan jirgi", murmushi Baba yayi yace mishi "Alhamdulillah Aliyu, mun godewa Allah mun iso lafiya" juyawa yayi ya dubi Aunty ya ďan sunkuyar da kanshi tare da gaisheta, itama amsa mishi tayi cikin sakin fuska, hannu ya mik'awa duka k'annen Batuul suka gaggaisa, Aabid ne kawai bai gaisa dashi ba sai kanshi da ya shafa tare da murmushin da ya bayyana dimple ďinshi yace mishi da "Hello champ" dariya sosai Aabid ya saka kamar yasan abinda aka faďa mishi, tsayawa Batuul tayi tana kallonshi da mmki a ranta take cewa "Yaushe yasan su Baba kuma" shi kam ko kallon inda take bae yi ba, tab'e baki tayi ta juyar da kanta, suna tsaye motoci suka k'araso inda suke, Baba ne yacewa Abutturab "toh Aliyu sai kaje ka huta ko gobe za a fara aiki" da murmushi ya amsawa Baba da "In sha Allah", sai da ya jira sun shiga motocinsu sannan ya shiga nashi shima da aka zo ďaukanshi dashi, hanyan Gwarimpa su Batuul sukayi, motar su Abutturab kuma tabi hanyar Asokoro.
💖💝BATUUL💖💝
12
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR* , Thank you sister, you are one in earth, you are truly an inspiration, Thank you soo much for being there for me, we love you❤
A hanya Baba ke tambayan Batuul abubuwan da take buk'ata na graduation ďinta, ce mishi tayi "Baa dama kayan graduation ne ,prom da zamuyi a ranan da yamma sai walima shi kuma inada kayanshi", kallonta Baba yakeyi har ta gama sannan yace mata "Sai kuje ko Dubai ne ku duba tunda babu time kuma shi kaďai kuke da visanshi, sai ki siyosu a can", murmushi tayi tace "Baa ai nayi magana ma da designer ďita har na gama faďa mata yadda nakeson kayana, next wek ma tace zata gama", tambayanta Baba ya sakeyi "are you sure babu matsala Mamana zaki samu yadda kikeso", kai ta gyaďa tace ehh Baa In sha Allah", murmushi yayi ya shafa kanta yace, "Allah ya miki albarka" daďin addu'an ne ya sata saurin jnfrr da "Amin", hira suketayi suna tafia, k'arfe biyu daidai suka isa gaban wani gate saboda nisan tafiyar dake tsakanin airport ďin da cikin gari ga hold ups hornsukayi, gidan exactly irin gidan da suka baro ne a Maiduguri, sai dai wannan cream paint ne da brown gate wancan kuma farin paint ne da black gate, masu gadi ne guda biyo suka taso suka buďe musu, a lokaci ďaya suka ce musu sannu da zuwa tare da yi musu ya hanya, cikin sakin fuska suka amsa musu da Alhamdulillah Friday da Jonathan driver ya k'arasa ciki dasu wajen parking, firfitowa sukayi daga motocin suka nufi cikin gida, shima cikin iri ďaya ne da wancan abinda kawai ya banbantashi da wancan shi cream and brown live wallpapers ne manne a bangon, sai wani large human size family picture daga gefe manne da bango, k'arasawa kowa yayi cikin gidan ya samu waje ya zauna a falon, Baba ne kaďai ya haura sama,khalil ne yace "Home sweet Home" Ahmad ne yace mishi "ai nan ba home bane, dole zamu koma maiduguri saboda Abuja ba garinmu bane", "but still this is where we live" inji kalil, tsakaninsu suke ta hiransu abunsu, Mus'ab ne ya tashi zaije ya kunna Tv, Aunty tayi maza tace mishi "koma ka kashe TVn nan ku wuce kuje kuyi alwala kuzo muyi salla" komawa yayi ya kashe TVn duk suka tashi suka tafi sama yin alwala, basu fi minti biyar ba suka sake sauk'owa bayan sunyi alwalan, Baba ne yajasu Sallah dukkansu kasancewar an idar a masallacin gidan, suna idarwa sukayi y'an addu'oinsu suka shafa, hannu suka mimmik'awa junansu har Baba da Aunty suna cewa *Baa nda dubdo, Auntu nda dubdo*, (Baba ina wuni Aunty ina wuni), "Wassalatu wassalamu ala Rasulillah" Al'adan gidan kenan indai sukayi sallah sai sun gaida junansu , suna gamawa wata mata siririya da baza ta wuce 25 yrs ba ta shigo falon ta k'ofan kicin , sanye take da kayan kuku tana rik'e da wani food flask mai kyau zatayi hanyan dinning su Yusra ne suka hangota suka ruga wajenta da gudu suna faďin "Aunty Esther mun dawo, ashe kina nan shine baki fito ba, mey kike dafawa, jawosu tayi jikinta tace muje kuga abinda na dafa in baiyi muku ba sai ku faďa min wanda kukeso, murna suka sa suna jin daďi, sai da tazo ta gaida Baba da Aunty sannan taja yaran suka tafi, Baba ma mik'ewa yayi yace yana da aiki gobe sosai yanxu zai fita, tare suka ce mishi "Baa adawo lafiya, Allah ya bada sa'a" , Amin ya amsa musu da sannan ya fita, Mik'ewa Batuul tayi ta k'ira janet tace ta hawo mata da jakanta, ana kawo jakan ta ciro Macbook ďinta ta kunna, skype ta shiga ta duba ko Farida na online, da taga bata nan ne ta ďau waya ta k'irata, tana amsa tace kixo skype sannan ta katse wayan dan tasan in Farida ta fara magana ba yanxu zata gama ba, connecting tayi da Farida, tana ganin Batuul ta mik'e cikin sauri ta zauna, cewa tayi "babe i missed you soo much, ji nakeyi kamar Nigeria gaba ďaya kuka bari ba Maiduguri, i just cant wait to be back, katseta Batuul tayi tana dariya tace "Riri you can talk for Africa, tun ďazu fa kike magana , har na tausayawa Affan", dariya Farida ma tayi tace " He loves me, babu yadda zaiyi, infact he enjoys surutuna and not only Africa, the whole planet", dariya suka sa dukkansu biyun a tare sannan Farida tace "Ya hanya, what time kuka isa", "Hanya Alhamdulillah , tun 12 but sai 2:00 muka isa gida" sunanta ta k'ira tace "Farida Yaa Abun ku yau ya dawoDawo Abuja ko" dan ita gani take ba shi bane, da sauri Farida ta amsa da "Ehh, kinji yadda gidan yayi daďi, dama so nake ya tafi, naji ance ma country ďin gaba ďaya zai bari, ni daďi nakeji, kinga ko yau da ya tafi har na samu na fita" Batuul ce tace nifa babu ruwana kullum kiyi ta gulmanshi, nidai babu ruwa", tsaki Farida taja tace "ai idan ka nuna kana tsoronshi ya fi baka wahala, ni yazo yayi aure ma ya tafi" dariya Batuul tayi tace "zaki sani, nifa about grads na k'iraki, gown zan saka , kefa" ta tambayi Farida , "Ni wando zan saka" inji Farida, "wane wando kuma sai kace su Hamra, its either gown or skirt, am not wearing any trouser" dariya maganan ya bawa Farida tace "woh calm down lady , am just kidding, yadda kikace haka zamuyi, but a ina zamuyi ordering", "dont worry about that, just send me irin wanda kikeso zan bayar ayi mana" inji Batuul, "aii zan tura miki details ďin duka " da haka sukayi sallama, suna gama wayan Batuul ta cire kayanta ta shige toilet ta watsa ruwa ta fito, wani doguwan riga ta saka mra nayi bayan ta shafa mai, ta ďan fesa turare
Abutturab na isa gida ya shige ciki yasa key ya buďe dan babu kowa, ďakinshi ya nufa yana shiga ya zauna akan gado, tunanin aikin dake gabanshi yayi, mik'ewa yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, kaya ya canja amma basu kai waďanda ya cire nauyi ba, sallah ya tada, uana idarwa bayan addu'oin da yayi ya mik'e ya sauk'a k'asa, kitchen ya nufa ya fara neman abinda zaici dan ko breakfast baiyi ba, coffeee ya haďa ya zauna a kujerun island ďin kitchen ďin ya fara sha, sai da ya gama juye saurin a wani ďan madaidaicin flask ya koma sama dashi, wani ďaki daban ya nufa na glass, komai na ďakin farine da glass, sanyi ke fitowa daga ciki, yana shiga ya isa wajen wani drawing board ya zauna a kan kujeran dake gaban board ďin, kayan aikin architects ne a ďakin irinsu irregular curves, french curves, desktop ďin apple, daga gefa akwai wani table akai an ďaura su set squares, CAD,pencils da sauransu, wayanshi ya ciro ya k'ira layin Amma, tana ďauka yace mata "Ammah ina wuni" da lafiya ta amsa sannan ta tambayeshi ya hanya, "Alhamdulillah ya amsa mata da sannan yace sun isa lafiya" tambaya yayi ko Abui na gida tace ehh, mik'awa Abui wayan tayi sannan shima suka gaisa, addu'a yayi mishi akan aikin da zai fara sannan Ammah ta karb'i cewa Ammah yayi "Ammah ki faďawa masu aikin dake BQ na dawo suzo su dafa min wani abu am hungry", cike da damuwa tace "Abu saida nace kayi breakfast kace ba yanxu ba gashi 2:30 yanxu, kuma kasan condition ďinka,zance suyi maza su shigo suyi maka " sannan ya katse wayan bayan yayi godiya, gaban desktop ďin ya koma ya fara danne danne, wayanshi ne yayi k'ara, ganin mai k'iran ya ďan saki tsaki sannan yayi recieving tare da sawa a kunnenshi, daga ďaya bangaren aka fara magana "Hello baby, ranan i called you kace min in ka koma gida you will call me amma baka k'ira ba", shiru yayi baice komai ba har saida ta gamana sannan yace mata "ya kk", cikin yanga da karairaya murya tace mishi "lafiya inata missing ďinka amma kai babu ruwanka dani, ko da kace zaka k'irani inata jira naji shiru", ce mata yayi "yeah i was busy shiyasa, Yasu Mum" bata ji daďin amsan da ya bata ba amma ya ta iya tunda tana aonshi haka zata hak'ura , ce mishi tayi "su mum lafiyansu rannan ma tace in garish ska", "ina amsawa, in kun dawo zamuyi discussing wani issue, i dont want to take long, so in kun dawo sai muyi magana", tunanin maganan da zasuyi ďin ta tsaya yi a ranta, tana ta addu'an Allah yasa maganan aurensu ne dan ta daďe ta nuna mishi ya fito ya ncewa ba yanxu ba, shirun da yaji yayi yawa ne ya sashi tambayanta "kina jina" da sauri ta katse tunanin tace mishi "Eh ina ji, amma baby wane magana ne baza muyi ba sai na dawo, ai waya ma ya isa" katseta yayi da cewa "nace sai kin dawo ba awaya zanyi maganar ba" jiki a sanyaye tace "okay sai mun dawo" ta katse wayan, sai da ya gama wayan ya koma wajen CAD ďin yana daddanawa
Batuul na saukowa ta nufi palo inda Aunty ke zaune, kusa da Aunty taje ta zauna sannan tace mata "Aunty sannu da hutawa", "yawwa sannu Batuul", magana ta gani a bakin Batuul dan taga yadda take ta fidgeting da zoben dake hannun ta, tace mata "Menene Kinxo kin sani gaba kin kasa mgana", a hankali Batuul ta buďe bakinta zatayi magana sai kuma ta fasa, da Aunty taga Batuul ďin tak'i magana ne tace toh Allah ya kyauta ta juyar da kanta taci gaba da kallon Tv, can da Batuul taga shirun bazai fissheta ba tace "Aunty dama inason ki faďawa Baba in munyi grads bayan result ďinmu ya fito ya kaini LONDON UNIVERSITY OF ECONOMICS, dgaske i promise zanyi karatu har in fito da first class" da mamaki Aunty ta waigo ta dubeta, tasan dai Batuul da Baba tare suke komai sai dai taji daga baya amma ya akayi yau take tambayanta, ce mata Aunty tayi "ban gane inyiwa Baba magana ba, kinyi magana ne yace bazai kaiki ba", cikin marairaicewar fuska Batuul tace tun ina school yace min wai inyi hak'uri da wajen nan duk inda nakeso a Nigeria zai kaini amma banda abroad", kallonta Aunty tayi sannan tace toh tunda yace baya son waje ai sai ki hak'ura, meye sai nayi mishi magana, its his decision i cant change" hawaye ne ya fara gangarowa idon Batuul tace "Aunty in kinyi magana zai yadda ni nafison wannan university", mamakine ya sake lullub'e Aunty, tasan Batuul bata yiwa maganan Baba musu amma yau harda hawaye, hawayen ne yasa ce mata "tashi kije, zamuyi magana", da murna Batuul ta tashi tana addu'a Allah yasa ya yadda, kitchen ta nufa taje tayi waffles da syrup ďin vanilla ta dawo dinning ta ci
Masu aikin gidan ne wata dattijuwa daga cikinsu ta hawo sama ďakinda yake taje , knocking tayi daga bakin k'ofa, baice ta shigo ba dan baya yadda kowa ya shigar mishi wannan ďakin, tashi yayi da kanshi ya duba yaga ko waye ke nemanshi, yana buďewa yaga tsohuwar, da sauri yace mata "Bawa ashe kece ai da kin shigo baki tsaya knocking ba" ce mishi tayi a ah babana ai nasan aiki kake shiyasa na k'wank'wansa, dama zance maka na gama yi maka abincin ne", da toh ya amsa mata sannan yace ai ban san kina gida ba da na k'ira na ce miki ina dawowa", ce mishi tayi "ai babu komai , yanxu ma Hajiyace ta k'irani take ce min ka dawo kana neman abinci shine na shigo na samo maka wani abun, a kawo nan ne ko a bari a dinning"," a ah Bawa ba sai an kawoshi nan ba zan sauk'a inci" toh tace sannan ta sauk'a ta koma k'asa
💖💝BATUUL💖💝
13
By phartiemarhk
Sai da ya gama aikin da yakeyi ya sauk'o yaci abincin, bai wani ci dayawa ba ya tashi ya shiga toilet ďin dake k'asa yayi alwala ya fita masallaci dan lokacin 3:50, da ya idar ya dawo gida, tunda ya shiga yaci gaba da aikinshi sai kuma sallah ke tadashi, bai kwanta ba sai after 12, yana kwanciya bacci ya kwashe shi, washegari 6 ya tashi bayan yayi sallah asuba yayi wanka, jeans blue ya saka da farar rigar max n spencer sannan ya ďaura blue Tuxedo ta giorgio Armani daga sama, kayan ba k'aramin kyau suka mishi ba kasancewanshi dogo, agogon ciélo ya mak'ala sannan ya fesa turaren karenbkelly da vesace eros, k'arfe bakwai daidai ya gama shirinshi ya fita, CLS golden ya buďe ya shiga ya fita daga gidan, office ya wuce, a nan yaci gaba da aiki har sai da minister yayi mishi waya suka tafi sighting area da zasu yi constructing, shi ya bada shawaran contractors ďin da ya kamata ayi aiki dasu, shi kuma yayi musu designing plan ďin yadda wajen ya kamata ya zama, satinshi ďaya yana aiki babu hutu, a ranar satin ne su Ajiddeh suka dawo, yana office 12:00 yaga k'iranta da number ta ta Nigeria, gaba ďaya ma ya manta da yau zasu dawo kuma yace mata zai ďaukota in sun dawo, tsaki ya ďan ja kamin yayi recieving call, kamin yayi magana ta riga shi da murna tayi mishi magana "Hello Baby mun dawo, we just landed, yanxu ma kai nake jira, bazan bi su Mum ba ni", sai da ta gama yace "olryt gani nan zuwa", key ya ďauka yayi magana da PA ďinsa akan duk wanda yazo neman shi ya tashi for d day sai gobe, cikin girmamawa ta amsa da "Okay sir, sai ka dawo", yana fita yayi hanyan airport, awa ďaya da rabi ya isa, side ďin international arrivals yabi, waya ya ďauko zai k'irata kenan yaji an sa ihu daga bayanshi "Baby am here" ko bai juyo ba yasan Ajiddeh ce, da gudu ta taho ta rungumeshi kamar za a k'wace mata shi, "i missed you soo so much baby" peck tayi mishi a kumatu sannan ta ďan sassauta rik'on da ta mishi ta ďan kwanta a kafaďanshi, shi mamakin halin Ajiddeh ne ya hanashi magana, duk y'an gidansu na wajen har Dad da Mum ďinta amma babu ruwanta haka tazo ta mak'aleshi, janyeta yayi daga jikinshi yayi mata magana a hankali "sweetheart baki ganin akwai jama'a a nan besides gasu Mum nan " zumb'uro baki tayi tace "ai dama nasan bakayi missing ďina ba, komai nayi is not right to you, wata ďaya we didnt meet, i was just happy, kuma su Mum ai sun san ina sonka ne" bai sake ce mata komai ba dan yasan she wont understand, k'arasawa yayi inda suke ya ďan risina ya mik'awa Dad hannu, gaisawa sukayi ya juya ya gaida Mum, da murmushi ta amsa sannan , juyawa yayi ya gaida Yaa xee, a dak'ile ta amsa mishi, bai bi ta kanta ba ya cewa Dad muje, Mum ce tayi saurin ce mishi "No ai drivers sunzo da su zamu tafi, sai dai kai ku tafi da Ajiddeh", cewa yayi okay, sai da ya bari suka isa inda driver yake sannan sukayi inda motanshi ke pake, unlock button ďin jikin key ya danna ya buďe, k'ofar ta buďe ta shiga shima ya shiga ta ďaya bangaren ya tada suka tafi, hanyar Wuse II yabi da ita, kalonshi tayi tace "baby kace zamuyi discussing wani issue in muka dawo", ta tsaya tana duban shi tana jira taji