Showing 87001 words to 90000 words out of 215266 words
yace "Tunda kika yrda aka hada mu dama akwae sharadodin da xan lissafo maki kafin mu bar kasar nn, nd yhu have to abide to them ol idan kina son kwanciyar hankalin ki da xaman lfyan ki, it's vry well knwn to yhu dat ni bana son ki, yea bana sonki sure, we 2 were neva on gud terms ryt frm d start! Duk da hkn baki yi making any effort ba wajen preventing parent dinmu frm hooking us up, rather yhu encouraged them ta hanyar amince masu dari bisa dari, So...." Wani matsanancin kuka ta fashe da ta durkushe wajen ta shiga rerawa, komawa baya yyi yana kallonta, lkci daya hankalinsa ya tashi, kofan da ke bude ya kalla ya karasa da sauri ya rufe, snn ta dawo ya durkushe gabanta shi ma yana kallonta yace "Na maki wani abun ne?" Kuka take ssae, kukan bakin ciki da kukan tausayin kanta, ji take kmr Allah ya dauki ranta ta huta kawae, ko bae fada ba tasan karshen farin cikinta ne a duniya ya xo, a dan rikice yace "Talk to me mana, me na maki kike kuka, why kike son hada ni da mahaifiyata ne wae, daga magana sae kuka," kin dagowa tayi bare yasa ran amsa, sae kukan da take har da sheshsheka, ji yyi an bude kofar dakin Ammah, ae bae san lkcin da ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, wani dad'da'dan sanyin kamshin da ya bugi hancinsa ya sa shi runtse ido da sauri, ita kanta sae da ta tsorata ta kasa ci gaba da kukan da take gabanta na faduwa, sun kusa minti biyar a hka, cikin sanyin murya idonsa lumshe har lkcn kmr me rada yace "Am... am.. I mean am srry!" A hnkli ya kuma cewa "Am srry" sae kuma ya bude idanuwansa ya daura kan gashin kanta dake fitar da wani fitinannen kamshi don gyalenta ya xame, d'ago kai tayi suna hada ido ya saketa ya mike da sauri, da kyar ita ma ta mike kanta a kasa xata fita ya fixgota ya wani hade rae kmr ba shi ba yace "clean those tearz" sunkuyar da kai tayi, ya ciro handki a aljihunsa ya dago kanta ya shiga goge hawayen fuskarta, yana mayar da handki din aljihunsa ta juya ta fice ya bi bayanta, ko da suka koma dakin Ammah bata ciki, Batuul taje can karshen gado ta xauna bayan ta daura mayafinta a kai, stool ya ja ya xauna shi ma ya fiddo wayarsa yana dannawa, lkci lkci yake satan kallonta ita ma hka, da sun hada ido kuma ya jefa mata harara, a hka Ammah ta shigo ta samesu, xama Ammah tayi yace "Gani Ammah" Ammah tace "Eh dama wa en can kwalayen xa ayi packaging kadda lkci ya kure ko ya kaga" kansa a kasa yace "Toh Ammah bari in kira sadiq," ya mike ya fita daga dakin, Ammah ta juya ta kalli Batuul, da sauri ta sunkuyar da kai cike da kunya don gani take kmr Ammah xata ji kamshin turarensa a jikinta.
Da yamma Ammah tasa Batuul ta sake shiryawa cikin wani kayan, atampa exclusive ta saka mai kyau, kayan yayi mata kyau sosai har ta gaji, k'asa suka sauk'o lokacin Abutturab shima yana k'asa yana jiranta, shima yayi kyau sosai cikin kaftan ďinshi fari da hularshi Rawaram, tunda take sauk'owa yake kallonta har sai da ta k'araso tazo kusa dashi tukunna ya ďauke idonshi daga kanta, Ammah ce tace "ku fara zuwa gidan Yaa Mera daga nan ku wuce gidansu", "Toh kawai yace ya juya yana jira ta fara fita, ganin batada niyyan motsi yayi ďan siririn tsaki ya fita, a hankali take ďaga k'afa tabi bayanshi, sai da ya buďe motar ya shiga ya zauna tukunna itama ta buďe ta shiga, babu wanda yace da wani uffan har suka isa gidan Yaa Mera, sosai taji daďin ganinsu, Nasiha tayi musu sosai tasa aka cika musu gabansu da abinci iri iri, suna zaune Massa ya shigo shima yayi ta tsokanan Batuul da ta kasa cewa komai, basu wuce awa ďaya ba suka yiwa su Yaa Mera sallama, itama tayi musu addu'a suka wuce, sai da ya ďau hanyan gidansu tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba "ki dena yiwa mutane wannan shirun naki, sai anyi miki magana kiyi kamar bakya jin abinda ake faďi idan aka tambayi dalili ki saka ma mutane kukan munafurci" kamar batasan mey yake cewa ba taci gaba da kallon window ta waje, jin tak'i cewa komai yayi k'wafa yaci gaba da tuk'inshi, suna zuwa gaban gate ďin gidansu, hannu tasa zata buďe k'ofan ta fita kamin masu gadi su buďesu musu gate, kamar yasan abinda take shirin yi ya danna lock ďin motar, murďawa tayi taji yaqi buďuwa, rau rau tayi da ido tana kallonshi, har idonta ya fara hawaye , mamakinta ya tsayayi yace "da akayi miki mey ďin zaki fara hawaye kuma", ďauke kanta tayi tare da ďan murguďa bakinta ta ďanyi murmuring wani abu sae dae fa duk ganinsu da tayi a kofar gidansu ne yasa ta samu wnn livern, kallonta yayi yace "Did you say anything", daidai lokacin aka buďe gate ďin yayi k'wafa ya ďauke kanshi daga dubanta ya sa kai cikin gidan, kin buďewa yayi bayan yayi parking har saida ta juyo ta kalleshi, yace "clean those tears , baza ki shiga gidannan da hawaye ba", ba shiri ta shiga share hawayen dake idonta, sai da ta goge ta juyo tana dubanshi ganin yaki budewa har lkcn a hnkli tace " na goge", daga gefenshi ya danna lock ďin, da sauri ta buďe motar ta fita a guje, murmushi yayi ya fito daga cikin motar, da gudu ta shiga palon gidansu tana k'walawa y'an gidansu k'ira a jere, Aunty Hafsat da ta fito daga kitchen ta fara haďuwa da, da mamaki Aunty Hafsat tace "A ah Batuul daga ina haka kika shigo kina ihu", tafiya taji kan stairs, juyawa tayi taga Aunty ke sauk'owa, da gudu tayi wajen Aunty ta rungumeta, tana jinta jikin Aunty ta fashe kuka, murmushin k'arfin hali Aunty tayi dan itama kwana ďaya da tayi bata gidan tayi kewarta sosai, ďagota tayi tana kallon fuskanta tace "Kukan na meye kuma Batuul", sake komawa tayi ta kwanta jikin Aunty taci gaba da kukan da takeyi, da sallama ya shigo falon, ďagowa tayi daga jikin Aunty tana kallon Aunty tace "Aunty su Mahir fa", Aunty tace "Ai yau babu wanda yaje Islamiyya cikinsu, Hafiz kam kuka ya dingayi wai sai an kaishi inda kike", hawayen dake idonta ne ya k'arasa gangarowa jin abinda Aunty tace, da gudu ta k'arasa hawa sama tayi ďakinsu, buďewa tayi tagansu kamar kullum ďakin yadda yake suna kallon ball, da gudu ta shige ta rungumosu, sai da suka sake juna Yusra tace "Yaa Batuul wai inji Baba zaki tafi Uk yau zamu daďe bamu ganki ba dagaskene?", ji tayi kamar zata fasa ihu tayi murmushi tace "a ah bazan daďe ba, ai zaku rakani airport ko", da sauri suka shiga gyaďa kai, ta kalli manyan da sukayi kamar basu san tana ďakin ba tace "y'an rainin wayo dama nasan jira kuke in bar gidan shiyasa kun ganni yanxu ma baku damu ba", dariya sukayi suka juyo sukace "penalty za a buga shiyasa", duk suka taso suka dawo kan gadon da take, zama tayi suna ta hira da k'annenta har saida Aunty ta tura a k'irata, kitchen ta samu Aunty, anty ta dubeta tace "Batuul wa yace miki haka akeyi, ya zaki tafi ki barshi shi kaďai ko ruwa baki bashi ba", baki ta zumb'uro tace "Aunty toh ba su Janet zasu bashi ba", Kai Aunty ta girgiza tasan akwai aiki sosai gaban Batuul dan ba wayone ya gama isanta ba gashi lokacinsu is limited, amma ba komai ko ta wayane zatayi mata magana, kai ta girgiza ta juya ta ďauko tray ta jera abubuwa tace "ďauki ki kai mishi", baki ta zumb'uro ta kinkimi trayn tayi palo dashi dungure masa tayi a kasa ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo har ta haura sama yyi murmushi, sai magrib lokacin suna shirin tafiya Baba ya dawo, shima ganinshi ta shiga sabon kuka, da k'yar ya samu tayi shiru, Abu kam suna haďa ido yake sakar mata harara, cewa Baba tayi sam sai k'annenta sun rakata airport, da farko da yaqi dan sai sun koma gidan Ammah zasu wuce, amma ganin yadda take kuka yasa driver ya kaisu, sai a lokacin Aunty taji baza ta iya jurewa ba itama taja Batuul sukayi ďaki, sunfi minti talatin har saida Baba ya shigo yace ya isa haka ta fito su tafi, kuka takeyi sosai har ta shiga cikin motar, bai ce mata komai ba shima ya shiga, motar su Ahmad na daga gaba nasu na baya sukayi gidan Ammah.
[8/22, 14:39] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝
42
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Kanta ta kifa tsakanin cinyoyinta ta dinga rusa kuka, shi dai bai ce mata komai ba sai kallonta da yake ta gefen ido yaga if she's fine, sai da suka shiga cikin gida bayan yayi parking ya juyo ya dubeta ganin batada niyyan tashi ya sa ya bude motar ya fito ya wuce gun motar k'annenta, sai da k'annenta suka fito suka nufi motar Abuturrab tukunna ta shiga goge hawayen dake fuskanta, dan murmushi tayi masu ta sauk'o daga cikin motar tana kallonsu tace "mu shiga mana", ba musu sukayi gaba, yana daga gefe yana kallonsu, yaran masu kyau duk sun fita haske, juyawa tayi ta dubi inda yake tsaye yasa hannu ďaya cikin aljihu, wani kallo ya shiga yi mata, ďauke kanta tayi daga dubanshi tabi bayansu, ita ta buďe musu k'ofa sai da suka gama shiga itama ta shiga da sallama, da murna Farida dake zaune tare da Ammah ta mik'e tana k'ok'arin ďaukan Hafiz, waje suka samu suka zazzauna daga k'asan rug ďin palon, da fara'a Ammah ta shiga ce musu "Ahmad ku tashi ku zauna kan kujera mana", babu abinda sukeyi sai murmushi, ta dubi Batuul tace "Bitti ce musu su hau kujera mana su tashi daga k'asan nan", kallonsu kawai Batuul tayi ta kasa musu magana, ganin sunqi tashi Ammah ta mik'awa Yusra, Mahir da Hafiz hannu alamun suzo wajenta, Yusrace kaďai taje dan ita tana da saurin sabo, Janet Farida tashiga k'walawa k'ira, babu b'ata lokaci ta fito tace "Aunty gani nazo", ta dubeta tace "kawo musu ruwa", ba b'ata lokaci ta juya ta tafi kawo musu ruwa, Ammah zatayi magana kenan ya turo k'ofa ya shigo yana tafiyarshi ta k'asaita, palon ya k'araso ya zauna, Ammah ta dubeshi tace " tare da su xa ku airport knn", Batuul da kanta ke k'asa taqi ďagowa yake kallo kamin ya kalli Ammah yace "Ehhh kuka tayi ta musu kamar yarinya wai tanaso su rakata", Ammah tayi dariya tace "Babu wani yarinta, ai gaskiyanta da tace su rakota su yi bankwana", baice komai ba sae tab'e baki da yyi ya mik'e yana kallon Ammah yace "Ammah Sadiq ďin ya fito ne, saura thirty minutes tafiyan namu", Ammah tace "Ai yanxun nan ya shiga wanka", daga jin haka ya wuce, Ammah ma tashi tayi tace "Bitti muje ki shirya kar lokaci ya k'ure kinji", ba musu ta mik'e amma har lokacin ta kasa yadda wai itace za a rakata airport zata bar garinsu dan tayi aure zataje zama da wani, take idonta ya fara kawo ruwa, jiki a sanyaye ta bi bayan Ammah, tana shiga bath tub ta dinga kuka dan kanta ta mik'e ta fito bayan ta kusa minti goma a ciki, wasu kaya ta gani Ammah ta ajiye mata kan gado, Lace maroon ne mai green designs da jewellery ďinsu na gwal, ba b'ata lokaci ta ďauka ta sakasu cikin rashin kuxari, riga da skirt ne, kayan sun mata kyau sosai, a bakin gado ta zauna bayan ta gama y'an shafe shafenta ta shiga tunanin irin rayuwar da xata yi ynxu.
D'akin Abuu Ammah ta shiga bayan Batuul ta shige toilet, har ya canja kaya lokacin yana zipping wani akwati, ganin Ammah da yayi ďakinshi ne ya sashi barin abinda yake cikin hanzari ya k'araso inda take, bata ce mishi komai ba har ta k'arasa shigowa tukunna ta zauna daga bakin gadon, rabon da Ammah ta shiga ďakinshi har ya manta, jiki a sanyaye ya bita ya zauna daga k'asa, ce mata yayi "Ammah ai da kin k'irani nazo ba sai kinzo da kanki ba" har ta buďe baki zata fara mishi magana ta fasa tace "in ka gama ka sameni a ďaki toh", daga haka ta mik'e tayi waje, ajiyar zuciya ya sauk'e dan yasan da magana bakin Ammah, koh minti biyu batayi ba da fita shima ya fita yabi bayanta, zaune ta tadda Batuul bakin gado har lkcn, ganin Ammah ta shigo yasa ta sauk'e kanta k'asa zata sauk'a k'an rug ďin Ammah tace mata tayi zamanta, kin zama tayi kan gadon ta sauk'o k'asa, da sallama ya shigo ďakin shima ya zauna kan stool ďin mirror, Ammah na kallonshi ta fara magana "Abuu ga amanan Batuul nan na baka da hannuna", da sauri Batuul ta ďago jin abunda Ammah tace, jiki a sanyaye ta sauk'e kanta dan har idonta ya fara tara ruwa, Ammah taci gaba tana kallon yadda ya sauk'e idonshi k'asa tace "tunda kayi aure kasa k'afa ka fita daga garin nan hankalina bai kwanta ba, ni bansan tsakaninka da matarka ba amma mu dai kam babu abin alheri da tayi mana, ni da kaina na sa aka nemo maka auren Batuul dan tun kamin aurenka da Ajiddeh Batuul naso ka aura amma Allah bai yi ba sai yanxu, ko sau ďaya ban yadda kasa hawaye zuba daga idon Batuul ba, ban yadda ko da wasa matarka ta wulak'anta min ita ba, yadda take zab'inka haka nima Batuul take zab'ina sannan amana na baka ita kamar yadda iyayenta suka aminta dakai suka baka y'arsu, ka kula da ita fiyeda yadda xa ka kula da kanka, sannan makarantarta ba denawa zatayi ba, an sama mata admission a can, ka taimaka mata da dukkan k'arfinka har sai ta kamalla dan tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah ya tayaka rik'o ya baka ikon yin adalci tsakaninsu", ta juya tana kallon da Batuul da ta jik'a gyalenta da hawaye a lokacin tace "Bitti ga yayanki nan xa ku tafi, na faďa miki duk abinda zaiyi miki mara daďi, don't hesitate in zama ta farko da zaki faďawa, ki zama mai respecting ďinshi kinji, he will be your guide In sha Allah, tsakanin ki da matarsa girmamawa, ki goge hawayenki kinji, kuma duk lokacin da kike son dawowa ki faďa mishi zai dawo dake kina yin kwana biyu kinji", Sadiq ne ya turo k'ofan tareda sallama, da murmushi a fuskanshi ya dubi Abu yace "ba dai kun fasa tafiya ba yau", Abuu ya dubeshi fuskanshi babu walwala yace "We are coming", Ammah ta dubi Batuul ta ďagota tace "Bitti share hawayenki ki tashi kuje, Allah yayi muku albarka, ya baku xuri'a dayyaba", da k'yar Batuul ta iya mik'ewa tana gyara gyalen dake kanta har wani shidewa take don kuka, Sadiq sai tsokananta yake sae dae shi ma xuciyarsa fal yake da tausayinta, suna sauk'a k'asa suka tarar da Massa shima yazo, gaba ďayansu suna zaune palon sun gama shanye drinks ďin da aka kawo musu, Ammah tace "jeka Abui ya shigo yanxu kuje kuyi sallama dashi, tare sukaje sukayiwa Abui sallama yana gaba tana biye da shi a baya, Abui ya sake musu Nasiha tareda yi musu Allah ya kiyaye hanya, mota uku suka yi suka nufi airport.
Tunda suka ďau hanyan airport take kuka ba k'akk'autawa dan tasan farin cikinta ragagge ne tunda har ta yadda tabi Abu wani garin da babu kowa nata, tausayin kanta take sosai tana kuka, sai da tabi y'an uwanta ďaya bayan ďaya tayi hugging ďinsu tana kuka su din ma kukan suke, har ta iso kan Farida dake kukan itama ta rungumeta, da k'yar suka sake juna don itama kukan da take ya hanata yin magana, ta kasa yin komai sai gyaďa kanta da takeyi, cikin hanzari ta sake Farida xata bi Sadiq da ya kasa ci gaba da kallon emotional scene din ya juya xae bar wajen, Abuturrab ya fixgota jikinshi, sosai ta shiga yin kukan kmr ana tunxura ta, dai dai saitin kunnenta ya sunkuyo a hnkli yace "control, its a public place baza mu tafi kina kuka kamar wacce na sato ba", kwanciya tayi jikinshi tayi lamo tana ajiyar xuciya, yana jin yadda heartbeat ďinta ke up and down, hannunshi ďaya ya ďaura bayanta, ďayan kuma yayiwa su Sadiq alamun suja su Ahmad su tafi, hakan kuwa akayi, takai minti biyar kwance jikinshi, can da ta tsagaita kukan ta fara dawowa normal ta ďago kanta, jinta jikinshi yasa ta kallon fuskanshi taga shima ita yake kallo, da sauri ta matsa baya ta juya bayanta ganin ko su Farida na nan, taga wayam babu kowa wajen, kallonshi tayi da idonta da yacicciko tace "Yaa Abu dan Allah mu koma kar mu tafi plss", wani irin kallo ya bita dashi yaja akwatin dake gabanshi yace "When you are done ina ciki", babu yadda ta iya haka tabi bayanshi a sanyaye tana share hawayen dake sakko mata, a departures waiting room ya xauna yana jiran jin announcement din departure'n su sanin few minutes ya rage, ya juya yana kallonta ganin a tsaye take, a hnkli ta xauna nesa da shi kanta a kasa, tabe baki yyi ya kauda kai, bayan kusan minti takwas akayi announcing cewar passengers din Abuja to UK su fara boarding ynxu jirgi xae tashi, mikewa yyi yana kallonta, wasu sabbin hawayen ne ke sauko mata duk jikinta yyi sanyi ta kasa tashi, har ya fara tafiya yana jan trolley dinsa ya tsaya, juyawa yyi yana kallonta ganinta xaune yasa ya dawo yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace " Ko in daga ki ne" a