Showing 15001 words to 18000 words out of 215266 words

Chapter 6 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

15723

tana ďauka tace "Janet ki kawo min fanta ďakina , na fridge ďina ya k'are, "Janet ta amsa da to anti za a kawo miki wani abu dinne bayan Fanta", Batuul tace No i dont need anything else, am okay" sannan ta katse wayan ta ajiye ta shiga toilet, warm shower bath tayi ta fito daga toilet ďin, tana fitowa akayi knocking k'ofar ďakinta karasawa tayi ta buďe, Janet ce ta shigo da square serving tray na ceramic ďauke da Fanta akai, akan table ďin ďakin ta ajiye ta juya zata fita Batuul ta k'ira sunanta "Janet ku shirya da wuri gobe zamu koma,ki faďawa Fa'iza da Aunty Tabawa, karku sake delaying ďinmu kamar lokacin da zamu zo, "Toh anti zan fada musu", "kuma ba sai kunyi breakfast dayawa ba,amma kije wajen Aunty ta faďa miki abinda za ayi goben", da toh ta amsa sannan ta fita, tana fita Baatul ta shirya cikin kayan baccinta na Lulu kitty purple, ta haďe gashinta cikin hula dark purple ta gama shafe shafenta ta hau kan gado, Laptop dinta na Apple ta ďauko ta ďanyi danne dannenta sannan ta kashe ta mayar kan side drawer, wayanta ta ciro a caji, kamar dama jira ake ta ďauki wayan ya fara ringing, ganin mai k'iran ya sa wani wide smile shimfiďuwa a fuskanta, dimple ďinta sai da suka lob'a deeply, wayan ta saka a kunnenta tare da tsuke fuska kamar ba ita ke murmushi ba yanxu ta Kuma yi shiru taqi magana, daga ďaya bangaren aka ce "shikenan since you wont talk, i will end d call, da sauri tace "Affaaannn" da k'arfi ta k'ira sunan har tana jiyo dariyanshi daga ďaya b'angaren, "woh lady so kike ki min bursting ear drums ko ko ya", sake k'iran shi tayi da Affanu, "ta yaya ma akayi kika zama friend ďita ya faďa yana dariya", "I know you love me" Batuul ta faďa mishi, ce mata yayi "waya faďa miki i love you, ai d moment you left for airport na manta da momeries and friendship ďinmu", "face ďinta tayi kalan tausayi dashi ta zumb'uro baki kamar yana ganinta tace mishi "ka manta dani, nayi fushi ma tunda ka manta ni" murya ta fara yi kamar zatayi kuka, da sauri ya fara ce mata "No no no Lulu, kar kiyi kuka mana, i didnt mean to hurt, kema ai kinsan you are my potential treasure, ai nima sai ki sani kukan" ya faďa muryanshi na rawa, kyalkyalewa ta kuma yi da dariya, ce mata yayi "dariya ma na baki ko, am offended shikenan ma goodnight", da sauri ta tare shi, "wait wait pls, dagaske dariya ka bani how you reacted, so you care, intersting", dukkansu biyu a tare suka sa dariya, ce mata ya sakeyi "Amish you dearest", a hankali itama tace mishi "Amishd you too", "so when y'all coming back", Affan ya tambaya, "Gobe ina Abuja by now", da sauri Affan ya tambayeta "Dagske Lulu gobe zaku dawo, baby na fa", dariya Batuul tasa sannan tace "masu baby, toh ba gobe zata dawo ba sai nextweek, hope kana kula min da ita da kyau, jiya ma i was with her, ce mata Affan yayi "i got to call her now in roqeta su dawo before next week dan i cant wait that long" Da dariya Batuul tace mishi "Aii best friend, good night", da haka suka katse k'iran, suna gamawa tayi adduan bacci ta shafe jikinta dashi, taje ta shafe duka k'annenta har way'anda ke kwana a ďakin Aunty, sannan ta tofe duka angles ďin gidan , ta kashe bedside Lamp ďinta ta kwanta





Bayan ya koma ďakinshi ne yaji komai baya mishi daďi, key ďin mota ya ďauka ya fita shehuri ba tare da ya cewa komai ba, kai tsaye dogarai suke buďe mishi k'ofa dan sanin matsayinshi da sukayi a fada, chamber Massa ya wuce kai tsaye ya shiga, Massa ya tadda kwance a makeken gadonshi na sarauta yana waya kuma da alama yana jin daďin wayan da yake, waje Abutturab ya nema ya zauna akan ďaya daga cikin royal chairs ďin ďakin, ganin wayan da Massa keyi bazai k'are bane ya sashi tashi ya fizge wayan ya katse, "dan wulak'anci na kai minti goma ina ďakin nan, amma kakeyi kamar ba kasan ina nan ba ka zauna kana ta waya kana k'yalkyala dariya, ni banga ma abin yiwa dariya ba a waya da budurwa,mtsewww", tsayawa Massa yayi yana kallonshi har sai da ya gama yace mishi "mik'o min wayata in ka gama" mik'a mishi wayan yayi ya nemi waje akan gadon ya zauna ya dafe kanshi, ganin da Massa yayi abokinshi ba wasa yakeyi ba yasa shi zama kusa da shi dan ya san ba komai ke sashi damuwa ba, komai girman abu yana danne zuciyanshi, dafashi yayi yace "Man whats wrong, you dont look yourself, you seem to be upset, hope dai lafiya, tell me whats wrong am dead worried right now", ajiyar zuciya yayi yace "Su Abui ne suka ce that sun bani two weeks i should introduce to them the girl i would marry , ko kuma su nema min da kansu, wai bazan tafi project ďina ba mata ba" kuma you know i have no one at hand da zance musu gata am ready to marry, cikin jimamin abinda ke shirin faruwa da abokinshi yace "Man toh baga Ajiddeh ba, you guys go along well dan naga babu wacce ke samun attention ďinka kamar ita kuma ma she is beautiful and everything" wani kallo Abutturab ya watsa wa Massa, "wa yace maka dan kyanta nake kulata, yeah i know there is this ounce of affection i have towards her but bai kai har ince zan aureta ba, su Abui should understand su k'aramin lokaci, i need time, bana son yin mata biyu, so kaga i should be given time dan in samu right choice ďina" k'arashe maganan yayi tare da nannauyan ajiyan zuciya" Massa ne yace mishi kawai kayi introducing Ajiddeh tunda tana sonka you can make her all you like, zatayi duk abinda kake so, Ko Shehu bazaiyi siding damu ba saboda shima damuwanshi kenan a kanmu, sai dai ma ya ce a k'ara dani, Man kawai muyi addu'an abinda yafi alheri", cigaba sukayi da hirar neman mafita daga k'arshe kawai suka yanke shawaran ya auri Ajiddeh tunda ita kaďai ce option ďin dan basu san wacce su Abui ďin zasu zab'a mishin ba, k'arfe goman dare ya mik'e yace da Massa zai koma dan yana da flight gobe by 11:00, sun fito waje Massa na rakashi inda yayi parking mota Massa ke tambayanshi, "Man ya akayi ne baka zo ba jiya inata jiranka", tambayan ne ya sashi tunawa da duk abinda ya faru tsakaninshi da Batuul, ďan k'aramin tsaki yayi daga ciki yacewa Massa "gajiya nayi", dariya Massa yayi yana ďan tab'a kafadarshi yace "ango tun bakayi auren ba har ka fara gajiya, toh in kayi auren kuma bazamu na ganinka ba kenan", Abutturab bai ce mishi komai ba ya buďe motarshi ya shige tare da ce mishi "sai munyi waya, ni zan wuce", Allah ya tsare hanya Massa yaayiwa Abutturab sannan sukayi sallama







Bayan sallah asuba babu wanda ya koma bacci, kowa shirin tafiya ya farayi, sai hayaniya akeyi a gidan, kowa ya tashi a gidan banda k'ananan k'arshe, Janet ce tayi knocking k'ofan, bayan an mata izinin shigowa ta shigo ďakin, tarar da Aunty da Batuul a ďakin tayi,Batuul na shiryawa Aunty kayanta da zata tafi dasu a cikin jaka, Aunty ce tace mata yarannan fa har yanxu basu tashi ba Janet, maza je ki k'irawo Fa'iza kuzo kuyi musu wanka dan 8 ya wuce, da toh ta amsawa Aunty sannan ta fita k'irawo Fa'iza dan suyi aikin da aka sasu, ďaya nayin wankan ďaya kuma na shafa musu mai da sa musu kaya, Batuul na gamawa tacewa Aunty "zanje in shirya sannan ta fita daga ďakin Aunty ta isa d'akinta, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atampa exclusive green da pattern ďin yellow da bak'i, ďinkin yayi mata kyau sosai, skirt ne with peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns ďin atamfar aka yi mata aiki dashi, ďan kunne kawai ta saka bata sa sark'a ba, agogon gucci ta ďauka ta mak'ala a hannunta, babu wani kwalliya da tayi sai kwalli kawai da ta saka a idonta, duk da ba tsayine da ita ba, bata saka takalmi mai tudu sai slippers din versace baqi da ta saka, luggage ďin kayanta ta jawo ta ajiye bakin k'ofa sannan ta ďauko k'aramin bak'in gyale ta ajiye a kafaďarta, fitowa tayi ta sauko k'asa taga kowa ya shirya cikin kayan alfarma suna breakfast, shiyasa ma bata fara saka abaya ba dan tasan Baba sai yayi mata maganan abayar, k'arasawa tayi itama ta janyo kujera ta zauna , Aunty da Baba ta gaida a tare suka amsa mata sannan duka k'annenta suka gaisheta suma, Bismillah tayi ta fara cin abincin itama, a nutse suka gama breakfast ,tara da rabi dai dai aka fara fita da kayansu, manyan mazan kowa da hand luggage ďinshi a hannu, na Aunty, Batuul dasu Hafix kuma yana hannun su Janet, Baba ne shima ya sauk'o daga bene rik'e da nashi, Batuul na hango shi da sauri taje ta karb'a ta k'arasa dashi k'asa ta bawa driver su fita dashi, Kanta ya shafa Yace ya gode , Baba na k'arasowa duk suka tashi suka fita suka nufi inda motocin gidan ke pake, Baa Liman ne da Sunday driver zasu kaisu airport, Batuul da Ahmad, Sa'eed, Khalil, Mus'ab mota ďaya suka shiga while Baba, Aunty, Yusra, Mahir, Hafix da Aabid na mota ďaya, sai da sukayi addu'an fita daga gida da ayatul kursiyu kamin drivers ďin su fita daga gidan





Hanyan Maiduguri international airport suka bi, goma da rabi suka isa, ana shiga cikin airport ďin heartbeat ďin Batuul ya k'aru idonta ya fara tara hawaye, addu'a ta soma har taji ya ďan ragu, bayan sun shiga har ciki sun sauk'a ta isa wajen Aunty ta ce mata, "Aunty tunda muka zo Maiduguri heartbeat ďina baya running at a normal pace, yanxu ma muna shigowa airport naji ya k'aru sosai", Aunty ce ta dube ta tuna da ranan da ta dawo idanunta sunyi ja, ce mata tayi "baki da gaskiya shi yasa yak'e karuwa, dariya sosai Batuul tayi sannan tace "kai Aunty, wane rashin gaskiya zanyi har heartbeat ďina ya rik'a karuwa, ni dai babu abinda nayi", ta juya ta tafi, binta Aunty tayi da ido dan itama ta tab'a shiga yanayi irin na Batuul na k'aruwan bugun zuciya, murmushi tayi ta girgiza kai sannan ta tattara kan yaran sukayi departures waiting room suna jira a k'ira su in jirgi ya shirya
💖💝BATUUL💖💝






11





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Suna zaune suna jiran jin announcement ďin departure su, Mahir yacewa Aunty zai sha smoothie, sauran yaran naji yace zai sha suma duka sukace zasu sha, Aunty ganin dukkansu na son sha kuma ba wai suna son bane dagaske kawai dan sunji ďaya daga cikinsu yace zai sha ne dan kawai suje yawo yasa faďin cewa za su sha Aunty cewa Batuul, "Batuul jeki da Fa'iza ku kawo musu , bazan iya da yawon yaran nan a cikin airport ďinnan ba , yanxu sai in nemi wani in rasa, Murmushi Batuul tayi sannan ta mik'e ita da Fa'iza suka karb'i kuďin a hannun Aunty suka tafi, suna tafiya yaran na ihun faďan shi ice cream yake so wani kuma yace milk shake yakeso, bata kula kowanne daga cikinsu ba tayi tafiyar ta, mutanen dake zazzaune sai kallonsu sukeyi ,suna tafiya suna ďan hira da Fa'iza har suk'a k'arasa eatery ďin dake airport ďin, order ďin smoothie ta bayar ta zauna jiran a gama packaging su tafi, ana gamawa aka mik'o musu Fa'iza ta karb'a, suna juyowa zasu tafi taji bugun zuciyanta ya sake k'aruwa, saurin tafiyanta ta rage tana Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel, juyowa Fa'iza tayi ta dubi Batuul tace "Yaa Batuul lafiya ,naga kina tafiya a hankali, Ce mata tayi "Lafiya Fa'iza, muyi sauri mu k'arasa" Suna cikin tafiya daga gefe ta hango Abui da wani mutum a tsaye, bata ga fuskanshi ba dan ya juya bayanshi, Abui ke facing ďinsu sai bayan mutumin kawai take gani, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel ta sake sabida yadda bugun zuciyanta ya k'aru, da sauri ta k'arasa inda ake zaman jiran , a ranta tana cewa in sun koma gida zata faďawa Aunty dagaske bugun zuciyan nata ya k'aru, suna zuwa suk'a mimmik'awa kowa abinda yace yana so suka koma wajensu suka zauna, basu fi minti biyar da zama ba akayi announcing passengers ďin Maiduguri to Abuja su fara boarding yanxu jirgi zai tashi, mik'ewa sukayi suka isa inda jirgin Med View ke tsaye suka hau matakalar suka shiga ciki, a first class suka sami waje suka zazzauna, Batuul ce k'arshen shigowa, duk seats ďin sun cika sai last two seats ďin k'arshe ne da daga shi sai economy class babu kowa a wajen ta k'arasa ta zauna, tana zama ta cire wayarta daga cikin jaka da ear piece sannan ta saka jakar daga sama inda ake ajiye luggages, wayarta tasa a flight mode ta jona ear piece ďin da wayan ta mak'ala a kunnenta, a hankali ta jinginar da kanta a kujerar tare da lumshe idanuwanta, heart beat ďinta ne ya k'ara k'aruwa kamar zai fito daga ciki, seat belt din jikinta tayi unfasten snn ta shiga karanto addu'a a hnkli a xuciyarta tana dan jujjuya kanta, ji tayi kmr mutum na tsaye kanta don wani dad'da'dan kamshi ne ya bugi hancinta, duk da hka ba ta buďe idonta ba sai da ta gama addu'ar da take snn ta bude idonta a hnkli, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin Wanda ke tsaye kanta idonsa a kanta ko kiftawa baya yi, dauke kai yyi da sauri fuskar nn tasa a daure yace "Excuse me" sae a snn ta lura da handbag dinta da ke ajiye kan seat din dake gefenta, daukewa tayi ta mayar cinyarta snn ya xauna, mamaki ne ya cika ta ba kadan ba, mikewa tayi ta ajiye handbag dinta xata fita duk da bbu takamaiman abinda xata je yi amma ya ki bata hanya, ita kuma taki cewa ya matsa mata, komawa tayi ta xauna ranta yyi mugun baci, to wae shi wnn guy din me yake daukan kansa, me ma yasa zai zo kusa dani ya zauna at d first place, ko ina ne sae mun hadu, su Farida ma basu dawo ba shine shi zai tafi ya barsu, ko mey zaije yi shi kaďai oho" ďan k'aramin tsaki taja ta kawar da kanta tana kallon waje ta window, tsakin da taja ne ya sashi kallonta, lokaci ďaya yyi kwafa ya dauke kansa da yaga hankalinta baya wajen, announcement aka shiga yi nacewa " passengers on board should pls fasten their seat belts, Med view flight is about to take off" fasten din seat belt dinsa yyi ganin bata da niyar yin hkn ita yasa ya juya yana kallonta, a lumshe ya ga idonta snn ga earpiece a kunnenta, da farko dan tsaki ya ja ya kawar da kansa, amma ganin few minute ya rage flight yyi take off yasa ya dan buga hannun seat dinta, ko kadan batuul bata ma san yana yi ba don kure Karatun da take saurara tayi, ya kuma buga handle din seat dinta da karfi nn ma bae ga alamar tasan yana yi ba, jin announcement din da ake yasa yyi saurin jawo seat belt din ya shiga kkrin fasten din mata, Batuul kam kawae jin hannun mutum tayi jikinta, ta bude ido da sauri tare da cire earpiece din kunnenta tace "What...." Shiru tayi ganin har ya gama sa mata ya dauke kai, lkci daya ya lumshe ido kamar mai bacci, takaici ne ya isheta bata san lkcn da ta furta "Hw dare yhu!" Bude ido yyi da sauri ya xuba mata manyan idonsa yana kallonta, murya can kasa yace "fuck does words of urs!" hawaye ne ya cika idonta, lkci daya ta rufe fuskarta da mayafin jikinta, dauke kai yyi ba tare da ko dar ba, bayan yan mintuna Batuul ta bude fuskarta suka hada ido, hawaye ya gani fuskarta, lkci daya jikinsa ya dan yi sanyi don ya tsani kukan mace, a hnkli ya furta "Damn her, ita kenan kullum hawaye, ko meh nayi mata oho," kusan a zuciyanshi ya faďi haka, handkerchief ďinshi dake aljihun jeans ďinshi ya ďauko ya mik'a mata ba tare da ya kalleta ba fuska daure, k'in karb'a tayi, haushi ne ya kamashi ya maida handkerchief ďinshi ya ruk'o kafaďanta da k'arfi, "clean that face, bana son sake ganin hawayen nan, don bbu abinda nayi maki I only helped yhu, ko kuma you leave this seat immediately" saketa yayi dan k'aruwa hawayen sukayi, ya ja dogon tsaki ya ďauke idonshi daga wajenta, sake juyowa yayi bayan y'an mintuna yaga har lkcn hawayen take, da kanshi ya ďauki handkerchief ďin ya fixgota ya shiga goge mata hawayen , ture hannunshi tayi daga fuskanta tace mishi "malam ka rabu dani da hawaye na, ai fuskana ne kuma hawayena ne, let me be plss" ta juyar da kanta tana kallon gajimare da sauri , magana zaiyi mata kenan hostess ďin jirgin ta tsaya a daidai kujeran da suke, plate holder ďin seats ďin nasu ta jawo ta ďora musu ruwa akai a ďan k'aramin disposable cup, hak'oranta ta washe ta gyara murya tana yiwa Abutturab magana, "Sir what would you like to have", bai ďago kanshi ba yace mata "Get me coffee", okay tace sannan ta dubi Batuul tace mata "Ma'am what would you like to have", k'in juyowa Batuul tayi, sake tambayanta matar tayi sannan ta juyo tace mata, "am okay, i need nothing" murmushi matar tayi sannan ta wuce" wayanta ta ďauko dake mak'ale a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login