Showing 99001 words to 102000 words out of 215266 words

Chapter 34 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

15772

watsar, a k'irata ta gyara mana", da mamaki ya ke kallon yadda take mishi magana, matsowa yayi gaban gadon, da sauri ta shige cikin bargon tana cewa "nikam in ka tab'ani zan faďawa Ammah", ce mata yayi "tashi ki tattare kayanki", ba musu ta yaye bargon ta taso ta shiga kwashe kayan, juyawa yayi zai fita daga ďakin, har yaje bakin k'ofa ya juyo yace "kin nemi abinda zaki cin ko kuma baki gama jan maganan ba", ganin batace mishi komai ba ya fita daga ďakin ya barta anan





Tana zaune ďakin har k'arfe 8 ďin dare, ga yunwa da ya addabeta, tsoron fita takeyi dan batason ko sake kallon Ajiddeh tayi, ta rasa mey zatayi kuďin wayarta ma ya k'are da ta k'ira ko su Aunty taji daďi, Affan ďinma da ya k'ira ďazu yaki k'ira har yanxu, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala ta tada sallah isha, sai da ta idar ta gama addu'anta tasha kuka ta tashi ta hau gado ta kwanta bayan ta kashe wutan, ta gwammace ta kwanta da yunwa da ta fito su haďu da Ajiddeh, jin an murďa k'ofan ďakin yasa ta k'ara tsorata, a hankali ta sauk'o daga kan gadon zata shige toilet taga haske ya gauraye duka ďakin, tsayawa tayi a tsakiyan ďakin ta kasa motsi, k'arasowa yayi cikin ďakin ya ajiye mata daya ledan dake hannunshi yace "in kin gama tsayuwan naki ga abinci ki ďauka kici, you get ready gobe by 11 zan kaiki school and mind you kina rufe k'ofar ďakinki da makulli", wani irin ajiyar zuciya ta sauk'e jin shine, bata juyo ba har ya gama maganan da zaiyi sai ji tayi an juyo da ita, "kina jina ina magana kika min shiru, na fara wasa da ke koh", a hankali tace "Ai naji", saketa yayi ya juya ya fita daga ďakin tare da kashe mata wuta. Dakin Ajiddeh ya nufa rike da wani ledan ya murda kofar ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadonta idon nn nata ya kumbura tsabar kuka, ya ajiye ledan hannunsa tare da sauke ajiyar xuciya ya nufeta, tana ganin hka ta mike da sauri xata bar wajen yyi hanxarin rikota tare da hade ta da jikinsa, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa tace " let me be Aliyu, ka kyaleni, 1st thing tomorrow morning am leaving yhur goddam house, with or without my divorce prove, bna auren kuma, ae ba kai kadai bne namiji a duniya, sae ka xauna da 'yar uwar taka....." Ya runtse ido yace "Stop this Jiddah, yhu pushed me into behaving the way I did, meyasa baki saurarata ne wae, na gaya maki Batuul is only here for sometime, karatu ta xo yi tana gamawa xata koma Nigeria, I love yhu Jiddah bana son duk abinda xae bata maki rai, had it been we are not this close da iyayen Batuul da baxan yrda da xaman ta gu na ba coz it's also a burden to me, plss nd plss Ajiddeh kiyi hkuri ki bar ta tayi karatun ta, her being here is nt for ever, if yhu love me do me this one favour pls babe," tsuke fuska tayi ta kauda kai, ya marairaice yace "Plss babe!" Kuka ta fashe da tace "Shine xaka mareni Aliyu" ya kuma rungumeta yace "Ohh! Am srry babe sharrin shaidan ne plss, idan kuma baki hakura ba ki rama" shiru tayi bata ce komae ba, kissing wuyanta ya shiga yi a hnkli yace "Say something mana babe" lumshe ido tayi don kiss din Aliyu na rikitata, cikin sarkewar murya tace "Naji" bae daina abinda yake mata ba yace "kin amince ta xauna gidan ki har ta gama karatun?" Runtse ido tayi tace "Yeaa!" Yace "Promise!" Da kyar tace "I do love" Kiss din bakinta ya shiga yi passionately tana mayar masa da martani, kan kace me sae ga su kan gado.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝

47

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Yana fita Batuul ta sauk'e ajiyar zuciya ta dawo kan gadon ta zauna, wayarta ta ďauka ta haska ledan da ya ajiye mata taga tambarin Mc donalds a jiki, ďan tsaki taja dan bata cika son abincin Mc donalds ba, amma tunda yunwa takeji babu yadda ta iya haka zataci, janyo ledar tayi ta shiga buďewa, kwalin chips ne a ciki sai chicken wings da dip in sauce, sai wani cup da aka sa strawberry shake da ruwa da pine apple drink, kaďan taci chips ďin, shake ďin kawai tasha da ďan yawa ta tashi ta ajiye sauran da bataci ba kan fridge, toilet ta koma tayi brush ta fito ta kwanta, tafi awa a kwance amma bacci ya k'auracewa idonta, hawaye ne ya fara zirara a idonta, she have never been this lonely gaba ďaya rayuwanta, dukda ba mai son surutu bace tafi son zama ita kaďai amma na yau ya dameta, ko ba komai a gida tana jin motsin y'an uwanta, amma yau hakan ma ya gagareta, tunanin gidane ya sata fashewa da kuka, wayanta ta janyo tana ganin hotunansu da shirmen da sukeyi, tanayi tana kuka wani kuma tayi dariya, tana nan zaune har k'arfe uku, yadda taga rana haka taga dare, gara ma da rana ta ďan samu ta rintsa, amma yanxu baccin ma ya k'aurace mata, tashi tayi taje tayo alwala, sai da tayi nafilfili tukunna tayi karatun Qur'ani a wayanta, tana nan zaune kan abin Sallah har asuba, tana idar da sllh taji wani irin bacci na fizgarta, nan kan abin Sallah ta gyara tayi kwanciyarta, tana kwanciya bacci ya kwasheta, cikin baccinta kamar a mafarki taji k'aran buďe k'ofarta, a ďan tsorace ta tashi ta zuba mishi lumsassun idanunta , k'arsowa yayi cikin ďakin yana binta da kallo, sai da ya shigo tsakiyar ďakin ya tsaya yace "wane irin bacci kikeyi anata knocking baki buďe ba", juyawa tayi ta duba inda ta ajiye makullin ďakin taga yana nan, k'ofan ta sake kallo taga shima da makulli mak'ale a jiki, cikin tsawa yace mata "ba magana nake miki ba, ko bakiji lokacin da nace miki ki shirya zan kaiki school bane kika kwanta kina bacci", sai lokacin ta lura da kayan jikinshi taga har ya shirya zuwa farin shirt mai stripes ďin bak'i da bak'in wando, windown ďakin ta duba taga har rana na fitowa ta kalleshi taga ita yake kallo har lkcn, ta ďauke idonta tace "ai bacci ne ya ďaukeni bansan safiya tayi ba", ta faďa tana zumb'uro baki, k'wafa yayi yana kallonta yace "get ready and come down in the next 15mins", daga haka ya juya ya fita daga ďakin, tab'e bakinta tayi a ranta tace masifaffe, daga haka ta cire dogon hijabin dake jikinta da rigar baccin ta shiga wanaka, ko minti biyar batayi ba ta fito daga toilet ďin bayan tayi brush, akwatinan kayanta ta buďe ta shafa mai ta ciro wata doguwar riga blue mai dogon hannu ta saka, chappette kawai ta shafa a lips ďinta ta taje gashin kanta sannan fesa turarukanta masu dadi'n k'anshi ta shafa, a hankali take sauk'owa daga stairs ďin har ta k'araso cikin palon, yana zaune kan ďaya daga kujerun palon, Ajiddeh na jikinshi sanye da wasu shegun kayan bacci da ya bayyana duk jikinta, ita ta fara hango Batuul, wani irin harara ta sakar mata kamar idonta zai zazzago ta k'ara shigewa jikin Abu dake k'ok'arin canja channel, cikin raďa tace mishi "baby i dont want you to leave", tana yi tana kissing wuyanshi, shima janyota yayi yace mata "dont you worry, i will b back for you, kinga school zan kaita ta fara processing", ita kam Batuul ko kallon inda suke batayi ba tazo ta wuce su zata fita waje, sai a lokacin ya ganta, da ido ya bita har ta fita daga palon sannan ya mik'e yana kallon Ajiddeh yace "Baby ki kula da kanki", ya manna mata kiss a bakinta, hade rae tayi tace " Babe ko gaisheni fa bata yi ba ta wuce" yace "ni din ma ae bata gaishe ni ba, kyaleni da ita" daga hka yayi waje, a bakin k'ofan palon ya tarar da ita tana tsaye, yace "Go back nd greet my wife" daga kai tayi tana kallonsa, ya hade rae yace "Do dat fast my frnd" juyawa tayi a hnkli ta koma falon, tsakiyar falon ta tsaya ba tare da ta kalli Ajiddeh ba tace "Ina kwana" a sanyaye tayi gaisuwan, Ajiddeh ta wurga mata hararan tsana tace "Da ban kwana ba kya gan ni, munafuka 'yan maula" Juyawa Batuul tayi ta bar falon ta fita waje, har lkcn yana tsaye inda ta bar shi, ba tare da ya kalleta ba yayi wucewar shi garage ďin gidan, tana nan tsaye ya fito da wata dank'areriyar Benz, a hankali take k'arasowa inda motar take ta buďe gidan gaba ta shiga, k'anshin turarenshi ne ya cikata, juyar da kanta tayi tana kallon wajen glass, bai ce mata komai ba yaja motar ya ďau hanyar makarantan, tafiyan minti goma suka isa k'ofar makaranta sae a snn ya juya ya kalleta yace "yhu look for wat to take for breakfast a sch din," ko kallonsa bata yi ba wani irin farin ciki ya ziyarceta ganinta a k'ofar university da kullum take mafarkin zuwa tayi karatu, batasan lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba tana kallon yadda students kowa na aikin gabanshi, jin sautin murmushinta da yasa gefen kumatunta lotsawa ya bayyana dimple ďinta ya sashi juyowa yana kallon yadda take murna, yau ne rana ta farko da ya fara kallonta tana dariya haka, driving yake amma gaba ďaya hankalinshi na wajenta har ya iso gaban wani building yayi parking motarshi, sai a lokacin ta juyo da murmushinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo, hararanta yayi ya buďe motar ya fito, ita dai bata fito ba dan baice mata ba, har ya fara tafiya yaga bata fito ba tana cikin motar a zaune, rai b'ace zagayo ya buďe mata k'ofan yana mata mugun kallo yace "zaman mey kikeyi da baki fito ba", baki ta zumb'uro ta sa k'afanta a waje, ita batada lokacinshi dan ji tayi duk bak'in cikinta ya yaye, k'wafa yayi ya juya yaci gaba da tafiya, biyoshi tayi a baya har lokacin da murmushi fuskanta, har sukazo k'ofan shiga wani office sannan ya juyo yana kallonta rai a haďe, haďe dariyanta tayi ganin yadda yayi kicin kicin da fuska sannan ya tura k'ofan ya shige, a sanyaye itama ta shiga a ranta tace masifaffe kawai, nidai yau is my happy day banida time ďin kowa ta shige cikin office ďin itama, Office ďin ta k'arewa kallo, an manna hotunansu su Adam smith, Alfred Marshal, David Ricardo, J.S mills da sauran manyan economists ďin duniya, wani bature ne zaune kan kujera a office ďin, da gani shekarunshi zasu kai 60, dogo sannan yana da jiki, hannu ya mik'awa Abu yace "Mr Kyaree you are welcome", baki ta kyab'e jin har sunanshi ya sani, juyowa yayi yana kallon Batuul yace "You can sit down madam", yayi mata nuni da kujeran gefen Abu, kallon Abu tayi taga shima kallonta yake da lumsassun idanuwanshi, kujeran ta jawo ta zauna, tana zaune suka gama maganganun da zasuyi, mutumin ya ďago yana kallonta yace "Mrs Fatima are you single?", question ďinne ya zo mata bazata, ta ďago tana kallon Abu dake danna wayarsa, a hankali ta ďauke kanta ta kalli mutumin da taga sunanshi Stephen xata yi magana ta ji Abuturrab yace "No! She's nt, she's married" kallonsa tayi sae kuma ta sunkuyar da kai, mutumin yyi murmushi yace "Dat's Gud, yhu are welcome to London University of Economics Mrs Fatima kashim Goni" murmushi Batuul tayi jin ynda yyi pronouncing sunan nata, nan Mr Stephen ya shiga yi mata bayanin abubuwan da ya kamata, shi dae Abuturrab danna wayarsa kawae yake, sun kusa minti ashirin office din bayan ta cike wasu forms din da ya bata ta kuma yi signing kafin ya dauko ID dinta na makarantar ya bata, ya kuma yi mata maraba snn ya mika mata timetable da wasu textbuks har uku yyi directing dinta zuwa dept dinta, godiya tayi masa tana murmushi, Abuturrab ya mike ya kuma yi masa godiya mutumin ya basa hannu snn suka fita office din, bin bayansa kawae take farin ciki shimfide fuskarta, da alama ya san kan makarantar sosae ganin ynda yake tafiya with courage abunsa kuma short cut yake bi, xaro ido tayi da ta tuna ae shi ma makarantar yyi if she remembered rightly, ko kadan bata damu da ynda ya hade rae ba farin cikin da take ji a lkcn baxae ma bari ta damu da hkn ba, jefi jefi tana ganin bakaken fata kmr su suna wucewa, har gaban dept din ya kai ta, wata baturiya ce ke tafiya rungume da litattafenta, ya karasa inda take yace "Excuse me Ma'am!" D'an kallonsa tayi tace "Pardon?" Yace "Just a minute or two" Tambayarta ya shiga yi da harshen turanci ko a Dept din nn take, ta masa nodding tace "Yea!" Murmushi yyi yace "Dat's gud Ma'am, am handing my sister over to yhu, assist her for today, yhu know! she's new in here" Baturiyar da baxata wuce shekaru 18 ba tayi murmushi tana kallon Batuul tace "She's welcome, she will really like it in here, from Africa I guess!" Yace "Yea! Exactly Africa! Africa Nigeria." Karasawa gun Batuul dake kallonsu tayi ta kamo hannunta tare da shaking dinta tace "Welcm frnd, yhu will really enjoy it in here, I am Samantha Brown, yhu" Batuul tayi murmushi tace "Am Fateema kashim" k'asa pronouncing din sunan yarinyar tayi Batuul tayi dariya, yarinyar ta bude deep green eyez dinta tace "your looks are more like dat of Britney Smears a pop artiste, just dat yhu are a dark, I will cal yhu Britney! Nyc meeting yhu Britney" kallon Batuul dake dariya bakin rai Abuturrab yyi, sae ta basa dariya don bae taba ganinta cikin farin ciki haka ba, murmushi yyi yana kallon Samantha yace "Dat's a gud start! I will take my leave now Miss Samantha, it's nyc meeting yhu for the first time" hannu tayi masa stretching ya karba tace "Nyc meeting yhu too Mr..." Yana murmushi yace "Aliyu Ahmad" murmushin ita ma tayi tana nodding ta sake hannunsa, karban timetable din hannun Batuul yyi yana dubawa, snn ya mika mata, ya ciro 20 pound sterling hade da wayarsa d'aya ya mika mata yace "Driver xae kira ki anjima" risinawa tayi ta karba kanta a kasa tace "Nagode" bae tanka ta ba, ya ma Samantha waving ya juya ya bar su wajen.

Karfe biyar saura suna xaune ita da Samantha da wata Linda sae 'yar uwarta yar Nigeria Aisha, ba karamin farin cikin haduwa da Aisha tayi ba ko ba komae ta samu 'Yar uwa a makarantar, sae dae ita a hostel take, fitowarsu lecture knn suna ta hiransu ita kuma tana duba textbuk din hannunta, wani guy ne ya karaso inda suke yana kallonsu yace "Hi" duk suka amsa bnda Batuul da bata dago ba, xauna wa yyi daga gefenta yana kallonta yace "Assalamu alaikum!" D'agowa tayi da sauri tana kallonsa, sae a snn ta ga bahaushe ne me kyau, sunkuyar da kai tayi ta amsa masa sallamarsa, da harshen hausa yace "Ya lecture 'yar uwa" tace "Alhmdllh tnxx" ya d'an yi murmushi jin ynda ta amsa masa yace "Am Shaheed Mukhtar by name, yhu?" Wayarta ne ya shiga ring ta mike tana kallon screen din tace "Srry Shaheed, I will be on my way ynxu" kallon Aisha dake ta kallonsu tayi tace "Plss ki d'an rakani outside gate, driver ya xo dauka na" bata jira cewar Aisha ba ta shiga yi ma su Samantha sallama, daga nn tayi gaba da sauri Aisha ta bi bayanta, binta da kallo Shaheed yyi yana murmushi, sae da suka yi nisa Aisha tace "me yasa xa ki yi masa hka Fatima, kinsan waye Shaheed kuwa, a vry popular guy a makarantar nn, he's so intelligent, course din mu daya, nd he is in his final year, ni na yi mamakin ganinsa wllh, don bin sa 'yan mata ke yi ba shi ke bin su ba" Batuul tayi murmushi tace "Gskya ne" tana ganin motar Abuturrab ta gane ta juya tana kallon Aisha tace "Toh sae gobe idan Allah ya kai mu, thnk for ur company frnd" murmushi Aisha ta mata ta gyada mata kai, Batuul ta juya ta nufi motar, duk a xaton ta driver ne, har xata bude baya sae kuma ta fasa ta bude gaba, ido hudu suka yi da shi, ta sunkuyar da kanta, yace "Baki ga daman d'aga call din ba knn" shiga motar tayi ta rufe ya tada motar suka bar wajen, a hnkli tace "Ina yini?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae da suka kusa gida yace "Ya lecture" kmr an tilasta sa tambayar don can ciki yyi ta, ta kallesa tace "Alhmdllh" yana gama parking ta bude motar ta fita, sae dae bata yi gigin tafiya ba ta jira har ya fito, sae da ya shiga gaba ta bi bayansa, Ajiddeh na kwance falo ta kure Ac tana kallo sanye da kananun kaya as usual, a hnkli Batuul tace "Ina yini" Ajiddeh ta d'an saci kallon Abuturrab, ganin kallonta yake yasa tace "Lfya lau" sama Batuul ta nufa, ajiye wayarsa dake hannunta da long notes din da ta siya a makaranta tayi ta kwanta tare da lumshe ido, ta kusa minti goma kwance snn ta mike ta cire watch din hannunta da jewelry ta cire doguwar rigar jikinta xata shiga bayi tayi wanka, bude kofar dakin taji anyi ta juya a rikice suka yi ido huda da shi, xaro ido tayi ta durkushe wajen, ya dauke kai ya juya da sauri ya fice daga dakin.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝






48






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Yana fita ta mike da sauri ta rufe k'ofar ďakin, har lokacin jikinta b'ari yake, she wasnt expecting anyone, komawa tayi ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login