Showing 30001 words to 33000 words out of 146814 words

Chapter 11 - YAR SENATOR BOOK COMPLETE BY UMMEETA

Umeeta   

13 Jul 2025

6569

Ko dai ba ta gane ku ba?"

Sultana ta ce "ba ta gabe mu ba?"

Salma ta ce "wallahi ta gane mu duk salon iskanci ne"

"Eh lallai akwai magana" cewar Anty Sameera

Anty Saudat ta ce "wane magana! Ai wallahu ubanta za ta ci, ba dai Sadeeq ba ne, in dai ta ce
da wannan halin za ta shigo to zai gyara mata zama"

Sajeeda tayi dariya ta ce "episode by episode kenan"

Anty Sadiya ta ce "hmm, Allah ya shirye ta to, amma sai nake ganin da ƙyar Sadeeq ya mata
wani abu, wannan miskilancinshi ma zai iya bari ya tsaya har ya fahimci halinta? Muyi mata

magana dai"

Anty Saudat ta ce "wa zai mata magana? Ni kin ga ban ma santa ba ko, amma wallahi har ta
bani haushi"

Anty Sameera ta ce "umm, Allah ya musu magani, ni dai bari in je in kwanta, kun san dai gobe
idan aka tashi da asuba ba zancen sake kwantawa" ta miƙe ta shige tsohon ɗakinta
Haka su ma su Salma, Sultana da Sajeeda suka wuce kowa ya shiga ɗakinshi, Anty Sadiya da
Anty Saudat kuwa sun daɗe suna fira kafin suka je suka kwanta

Su ma iyayensu gaba ɗayansu su na ɗakin Alhaji saboda ya kira su

Alhaji ya ce "abunda ya sa na kira ku, da zan dawo na biya wurinsu Baba(grandpa), nayi mishi
bayanin komai da ya shafi Sadeeq da Sunaiha ɗin, shi ne ya bada wata shawara kuma na ga
hakan zai fi"

Hajiya ta ce "wace shawara?"

"Ya ce a maimakon a ce anyi auren Safwan, sannan cikin kwanaki kaɗan a sake cewa za'ayi na
Sadeeq, duk mutanen da suka zo daga nesa kuma su sake dawowa, why not a ɗaura auren
lokaci ɗaya, in ya so daga baya ku mata sai kuyi bikinku, amma mazan nan da yawa aikin su
suka baro suka zo, kawai gwara a haɗa"
Kawu ƙarami ya ce "wannan shawara ce mai kyau kuwa, hakan ya kamata a yi, ko ya ka ce?"
ya ƙarasa yana tambayar Abba

Ya ce "a'a ai hakan yayi, ba wata damuwa, su ma dai dan sun mayar da bikin kamar dole ai da
ban ga amfanin yin bikin ba kuma"

Umma ta ce "a'a kamar ya ba sai anyi ba"

Hajiya ta ce "ai shi ne, biki kam wajibi ne ma sai anyi, idan ba haka ba ita kanta yarinyar za ta ji
ba daɗi ne"

Momi ta ce "ai auren ma dan Baba ne yayi magana, da sai in ce shi ma da bari aka yi a yi na su
daban, a tsanake kamar yanda aka yi na kowa"

Kawu ƙarami ya ce "ai kinji dalilin da ya sa za'a haɗa, kuma ma ɗaurin aure har wani shiri ake
masa? Dama mutane ne kawai ake buƙata, ku. A duk waɗanda aka gayyata a na Safwan su ɗin
ne dai kowa zai sake gayyatowa a na Sadeeq ɗin, da mu da su yaran su kansu"

Alhaji ya ce "haka ne... Yanzu dai gobe idan ɗaya daga cikinmu ya samu ganin Sadeeq ɗin ko
Safwan sai ya gaya musu, ko ni ko kai Usman ko kai Aliyu, dan nasan gobe iyayen nan na su

mata ba su da lokacin mu ma bare na yaran" ya ƙarasa da sigar zolaya

Dariya su kayi, Umma ta ce "ai ku ma kun sani kam"

Sun ɗan taɓa hira, kafin suka tashi kowa ya wuce part ɗinshi su ka kwanta........




♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️


*LIKE*
*SHARE*
*COMMENT*


♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️

_Full of Arrogance, Ego, Jealous And_ _Love_

*CREATED AND WRITTEN*
_BY_
*UMMEETA*


*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''*
مسِب الله نمحرلا ميحرلا
~~~~~~~~~~~~~~


_Do not count what u have lost, Just see what u have now, because past never comes back,
but sometimes future can give u back ur lost things…_

*PAGE 21-22*

Kamar yanda aka shirya events din da za'a yi, yau ake fulani's day, kap ƴan matan sun yi shigar
fulani tun daga sama har ƙasa, har yanayin kitson kansu na fulanin ruga ne, suka yi kwalliyar su
so simple ta ƴan ƙauye, ba ƙaramin kyau suka yi ba masha Allah, sai kyaun na su ya sake
fitowa kamar ka sace su
Haka suka fito suka haɗu da sauran ƴan biki suka nufi harabar gidan suka shige motoci, su
Sameer da Sauban, Aymaan da Saif (abokan nan su Safwan da Sadeeq), su ne suka ja
motocin har wurin bikin, su ma kayan fulanin ne a jikinsu, sai dai wando jeans suka sa, baƙi

Gaba ɗaya waɗanda suka halarci bikin duk irin shigar su suka yi, amarya na kayan fulanin ne
sai dai na ta blue ne ba fari ba, ta sha ado masha Allah, tayi kyau sosai, dama ita ma ba baya
ba in dai kyau ne

An daɗe ana ta hidimar biki abun gwanin burgewa, kafin Safwan da Sadeeq suka ƙaraso,
amma Sadeea bai fi minti goma ba ya bar wurin, su kuma sai kusan magrib sannan suka
kammala bikin

Sannan kowa ya wuce gida. Salma, Sultana, Sajeeda da Safna ne kawai suka bi tawagar
amarya saboda yanda ta dage sai sun biyo ta, a can suka yi sallar magrib da isha'i, sai kusan
ƙarfe goma sannan aka maido su gida


Ɓangaren Sunaiha kuwa, tun bayan la'asar suka fita da Najeeb suka zaga gari sai dab da sallar
magrib sannan ya dawo da ita

"Cutie i'm so happy, ban taɓa tsammanin za ki yarda muje outing ba"

Murmushi tayi ta ce "ba abun mamaki ba ne ai, ka san meyasa na yarda?"

"A'a sai kin faɗa"

"Saboda satin nan gaba ɗaya ina cikin farin ciki fiye da tunanin ka, shiyasa nake kokarin
kyautatawa wasu"

"Ke kuwa me ya faranta miki rai har haka?"

"Prince mana. Ka san kuwa nan da kwana uku za'a yi aure na da Prince!"

Drink ɗin da ya kurɓa ne ya sarƙe shi saboda yanda maganar ta razana shi, ya ce "aure?? Aure
fa kika ce Cutie! Within three days za kiyi aure?!"

"Eh mana, meye abun tsorata kuma bayan ka san da zancen, ai na gaya maka na samu Prince
ɗina, daga haka kuwa ai kasan sai zancen aure kuma"

Shiru yayi naɗan lokaci, ya ce "amma Cutie kin mu adalci kenan?"

Wani irin kallo ta mishi ta ce "adalci kuma? Dama na taɓa gaya maka ina sonka ne? Ai tun
farkon haɗuwarmu na gaya maka ina da masoyi, to meye abun ɓacin ran kuma?"

Maganar ma ƙin fita tayi saboda tsananin mamakin da yake ciki, kusan mintuna biyar bai ce
mata komai ba, ta ce "Meye kuma Najeeb!"

Da ƙyar ya ita faɗin "ba komai, i'm going home"

Ɗaga kafaɗa tayi ta ce "ok bye" ta buɗe motar ta fita, shi kuma ya daɗe cikin motar kafin ya iya
wucewa

Tana shiga gida kai tsaye ɗakinta ta wuce, sai da ta watsa ruwa tayi sallah sannan ta fito ta nufi
ɗakin Mummy, tana zaune kan sallaya tana karatun Qur'ani, sai ea ta kammala kafin tayi addu'a
ta miƙe tsaye ta ninke sallayar da hijab ɗinta ta ajiye a ma'adanarsu, ta nufi hanyar toilet

Sunaiha ta ce "Mummy ba ki ganni ba ne?"

Kamar ba za ta mata magana ba, sai dai ta juyo ta ce "na ganki mana, ya aka yi?"

"Hmm.. Mummy kin sauya, menene?"

"Babu" ta amsa mata a gajarce, ta shiga toilet

Lokacin da ta fito Sunaiha na nan a zaune tana chatting, kujerar mirror ta ja ta zauna tana goge
jikinta, Sunaiha ta ce "Mummy gobe zan tafi event ɗin su Prince, Arabian Night"

"Allah ya kaimu lafiya"

"Ameen Mummy" haka suka ci gaba da zaman kurame har Sunaiha ta gaji ta wuce ɗakinta kafin
Daddynta ya dawo, Mummy kuwa tana sane take ta ƙyale ta yau



Tiger kuwa da daddare yana ɗakinshi kasancewar abokanansu, Aymaan da Saif suna nan
parlour su na ta fira da su Sameer, sai ga Safwan ya shigo, lokacin ya tarar da yana waya, yana
shigowa, Sadeeq yayi sallama ya kashe wayar

Tiger ya ce "ango, ka kuɓuto?"

"Bari kawai, na gaji wallahi yinin yau kawai, to bare kuma jibi da za'a ɗaura auren.... Wai ma ka

ce ango, angwaye dai"

"Hmm"

"Sadeeq wallahi bari in gaya maka gaskiya, na rantse da ina da iko ba za ka auri yarinyar nan
ba, ni sam ba ta burge ni, amm na rasa meyasa Abba ya nace akan sai ka aure ta, ita ma Anty
Sadiya ta haka wannan shawarar.. Da yake ma dai her wish is your command, yanda take so
haka kake yi, amma wannan yarinyar ba matar aurenka ba ce, ba ku dace ba"
Kallonshi kawai Sadeeq yake yi, ba abunda ya ce mishi, sai ga su Aymaan sun shigi, Saif ya ce
"wai Tiger ba zaka taɓa sauyawa ba ko, ɗazu sai nemanka nayi na rasa, aka ce ai ka daɗe da
barin wurin, wai tsoron mutane kake yi ne? Kai kullum ka fi so ka zauna kai kaɗai"

Aymeen ya ce "dalla ƙyale ɗan rainin sense, ai yanzu dai aure zai yi, sai in gani idan kullum
yana ɗakinshi tana nata ne, mu yake ma wannan rashin mutuncin, matarshi kuwa gyara mishi
zama za tayi"

Dariya Safwan yayi ya ce "tirƙashi, wa ya ga mace ta gyarawa Tiger zama" ya sake sakin dariya

Saif ya ce "ni faɗan ma da nake so zanyi da shi kenan, yanzu Tiger ashe har da kai aure za kayi
shi ne ba sanarwa! Ka daina wannan rayuwar ba me kyau ba ce wallahi"

Safwan ya ce "ya ce zai yi Suprising ɗin mutane ne that's why" Safwan ya faɗi hakan ne dan ba
so suke a san auren dole Tiger zai yi ba

"Whatever dai Safwan, yanda muke da ku bai kamata a ce har mu muna cikin waɗanda za'ayi
suprising ba"

Safwan ya ce "to kuyi haƙuri "

Aymaan ya ce "shikenan.. To amma ban ga ta shi amaryar ba ɗazu"

"Za ku ganta in sha Allah"

Haka dai suka ci gaba da firar ba abunda Tiger ya ce musu sai kace wani kurma, har su ka gaji
suka wuce domin su kwanta

Washe gari ma haka aka tashi da hidimar bikin, tun safe suke ta hidima suna fama da mutane,
Sadeeq na so yayi magana da Anty Sadiya amma ya kasa shiga cikin gidan saboda yawan
mutane, ga wayarta a kashe

Sai kusan la'asar kafin ya samu wayarta ta shiga, ya gaya mata yana son ganinta, part ɗin su
Alhaji suka haɗu kasancewar ƙofar bayan gidan ta gefen su yake

"Oga Tiger ya aka yi?"

"Anty Sadiya kin ga auren nan an haɗa shi da na Safwan nan d three days, sannan kuma wai
sai a dawo a sake yin wasu events daban, wahalar za tayi yawa, kiyi ma Umma magana dan
Allah ba sai anyi wani event ba"

"Meyasa kuma? Ka taɓa ganin auren da ba event ko ɗaya? Sai ka ce wata bazawara!"

"Anty ba haka bane, ni wannan taron ne ba zan iya ba.. Please help me"

"Shikenan na ji, amma to tunda ka ga gobe za'ayi dinner sai a haɗa kawai, jibi kuma idan aka
ɗaura aure da safe da yamma za'ayi walima shi ma sai a haɗa"

"Walimar dai, amma ba zancen yin dinner"

"A'a Sadeeq... "

"Dan Allah Anty Sadiya, just say yes"

"Hmm, to zan mata magana"

"Yawwa, nagode" sannan ya miƙe ya fita ita kuma kai tsaye wurin su Hajiya ta wuce

Ta kira Umma gefe ta mata bayani, ta kuwa amince da hakan, dama tayi wannan tunanin ita
ma, ta gaya mata za ta yi ma Hajiya magana


Bayan sallar magrib aka fara shirin wucewa wurin arabian night ɗin, mata sukayi shirin jallabiya
baƙi maza kuma fari da makawiya, amarya kuma jallabiya kalar ja ta saka ango kuma baƙi,
arabian dishes aka yi da haɗin lipton ɗinsu, waƙoƙin larabawa ke tashi, daga bisani kuwa suka
fara gabatar da programs ɗin da suka shirya yi na larabawa
Sai ƙarfe takwas sannan Tiger ya zo, ya sa baƙin jeans da farar jallabiyarshi mai kyau, sai dai
bai saka makawiya ba, gashin kanshi kawai ya gyara, yayi kyau sosai kamar balaraben gaske,
yana nan jikin motarshi ya ga shigowar wata mota

Hajiya Sunaiha ce, ta sha jallabiyarta baƙa ita ma, da ɗan simple makeup ɗinta, kallo ɗaya ya
mata ya ci gaba da wayar da yake yi, sam ba ta ma lura da shi ba, tana tsaye a wurin sai ga
Salma da Sajeeda sun fito daga cikin hall ɗin, a hankali Salma ta gaya wa Sajeeda ga Sunaihar
Tiger
"Wow!! Masha Allah, Salma she's so cute"

"Yeah, she's cute amma ba hali... Wallahi ba dan da mutane ba Allah bazan gaishe ta ba"

Sajeeda ta ce "nikam gaida ita zanyi"

Wurinta suka nufa, suka gaishe ta, ba ta so amsawa ba, amma ganin Salma ya sa ta amsa ba
yabo ba fallasa, Sajeeda ta ce "zo muje ciki in gabatar da ke"

Cikin salon tafiyarta ta izza, ta bi bayansu suka koma cikin hall ɗin tana bin wurin da ido, ya sha
decoration sosai fari da baƙi, ballons kuma fari da ja, sai glubs multi colours da ke ƙara ƙayata
wurin, kallonsu kawai Tiger ke yi har suka shige, ya ce "Hmm" Allah kaɗai ya san abunda ke
ranshi, ya daɗe wurin kafin ya shiga ciki, daga farkon hall ɗin ya samu kujera ya zauna
Har aka kusa gama event ɗin sannan ya bar wurin, ƙarfe 9:21pm, Sunaiha ta fito ba tare da tayi
sallama da kowa ba, ta wuce gida, ƙarfe goma aka gama komai, suna shirin wucewa,
Nasreen(amaryar Safwan) ta tambayi Sultana ina Sunaiha, Safna ta gaya musu ai ta daɗe da
wucewa, murmushi tayi ta ce "an dace kenan, wannan kam da alama yanda mijinta yake haka
take"

Sultana tace "ke ma dai kya faɗa Anty Nasreen"

"To Allah ya kyauta" suka wuce wurin mota, yau Safwan yaraka amaryar shi har gida, Saif yayi
driving ɗinsu, su kuma su Salma yau ba su bi ta ba, gida suka wuce kai tsaye


Kafin dawowar ƴan bikin ne, Umma tayi Hajiya bayani a kan maganar su ta ɗazu da Sadiya, da
farko ta nuna rashin amincewarta, amma daga baya kuma ta yarda da hakan, ta ce za tayi ma
Alhaji magana zuwa dare idan ya shigo dan su samu su gaya wa Senator, su ma idan akwai
shirin da za suyi sai su sani
Umma ta ce "amma Hajiya kuma nake ganin ya kamata a ce by now mun san mahaifiyar
yarinyar nan, itama ta san mu"

"Ni kaina nayi wannan tunanin, ina ganin gobe sai ki tafi gidan na su sai ku tattauna da ita ma"

Murmushi tayi ta ce "to meye amfanin ki in har ni zan tafi? Sadeeq ɗinki ne fa"

Dariya tayi tace "haka ne, to Maman Salma(Momi) za ki raka ni sai mu tafi"

Momi dake jin su tun ɗazu tace "a'a Hajiya, idan ja bi ki wa zai taya ta kula da baƙin? Ki je kawai
mu muna nan"

"To ya muku kyau, zan tafi ɗin" dariya suka yi suka ci gaba da maganar, Momi ta musu sallama

ta wuce ɗakinta saboda ta gaya musu kanta na ciwo

Tana shiga part ɗinta ta ɗauki wayarta tayi kira, "Hello"

"Anty Basira, ya gajiya" aka amsa daga ɗayan ɓangaren

"Alhamdulillahi"

"Kiyi haƙuri ban shigo event ko ɗaya ba, wallahi uzuri ne, amma dai gobe zan zo"

"Ki ɗin kam, dan ina nemanki"

"Lafiya kuwa Anty Basira?"

"Da sauƙi dai"

"Subhanallahi, to Allah ya ƙara sauwaƙe mana... Sai gobe ɗin to"

"Yawwa, ki gaida mun Yaya"

"Za taji" suka kashe wayar


Ɓangaren Najeeb kuwa, tun jiya yake cikin damuwa, tabbas ya san da labarin prince kuma ta
gaya mishi ta ganshi, amma abunda ya ba shi mamaki wai har an sa ranar aurensu

"Yanzu yarinyar nan rasa ta zanyi kenan?... Impossible!!" ya faɗa da ƙarfi yana dukan kujerar da
yake zaune a kai

Yayanshi da ke zaune ya ce "Najeeb kana da lafiya kuwa?"

"Wane irin lafiya kuwa Bross, wacce nake so ce ke shirin yin aure"

"Aure fa? To kai ba ka sani bane? Dama ba ta sonka?"

"Wannan kuma it's secret, amma wannan abun ne ba zai yiwu ba"

"Me kenan? Auren ko me?"

"Cire ta a raina dai, wallahi Bross i'm in love with her"

"Daga baya kenan ai, dole ka cire ta a ranka yanzu tunda matar wani za ta zama"

"Wa?! Ai wallahi idan ka ga na cire ta raina to mutuwa nayi, amma wallagi ko aure tayi ina tare
da ita sai wurin da ƙarfi na ya ƙare"

"Ka na tare da wahala kuwa Najeeb, na ka wasa ne... Nikam sai da safe" ya miƙe ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login