Showing 120001 words to 123000 words out of 146814 words
ya bada, idan mai
muhimmanci ne ko waye ya kira shi, amma kai zan gaya maka, kar ka bari ko ya sani"
Sadeeq ya ji daɗi sosai, ya ce "kar ka damu, just tell me"
Nan ya kwatanta mishi gidansu Najeeb sai da ya tabbatar da ya gane sannan suka rabu
bayan ya ba shi kuɗi
Sadeeq kuwa bai wahala ba, har ƙofar gidan ya kai kansa, parking motarsa yayi gefen gidan
sannan ya je ya fara knocking ƙofar, mai gadi ya buɗe, gaisawa suka yi sannan Sadeeq ya ce
"Najeeb yana nan?"
"Eh yana nan, ya san da zuwanka?"
"Eh ya sani, dama ya gaya mun zan iya in same shi a gida, kuma zan iya tarar da ba ya nan"
"Ai kuwa yanzu ya dawo, bismillah" ya buɗe masa ƙofar ya shiga
Main door ɗin da ya gani ya nufa, bai tsaya komai ba ya tura ƙofar, Najeeb na tsaye yana
waya, ganin Sadeeq ya sa shi cewa "i'll call you back" sannan ya kalli Sadeeq da ke kallonsa
shi ma, ya ce "waye kai? Lafiya?"
Sai da Sadeeq ya ƙare masa kallo, kafin ya ce "Najeeb nake nema"
Murmushin rainin hankali Najeeb yayi, ya ce "Najeeb kake nema? Ni ɗin? Wa ya turo ka
neman wanda ba ka san....."
Kafin ya ƙarasa Sadeeq ya ɗauke shi da wawan mari sai da ya kusa faɗuwa, a fusace ya
ɗago yana kallon Sadeeq da fuskarsa ta koma ta ainihin Tiger ɗin da ake kiransa
Najeeb ya ce "how dare you slap me!?"
Yana gama rufe bakinsa, Sadeeq ya sake marinsa, ɗagowa ya sake yi da ƙarfi, ya ɗaga
hannu zai mari Sadeeq, amma ya riƙe hannun tare da murɗa shi, ya ce "i will keep on slapping
you har sai na sauya maka kamanni fuska, zan nuna maka wane ne ainihin ɗan iskan a
tsakaninmu" ya ƙarasa maganar yana tura shi da ƙarfi sannan ya kai mishi naushi a fuska, nan
dambe ya kicime a tsakanin su kamar ba za su bar juna da rai ba
Yayan Najeeb ne ya ƙaraso parlourn da sauri yana cewa "wai hayaniyar me nake ji ne
Najee..." Abunda ya gani ne ya riƙe mishi baki, zuwa yayi ya shiga tsakanin su, da ƙyar ya samu
ya raba su bayan shi ma ya samu rabonsa a fuska
Fuskantar Sadeeq yayi ya ce "lafiya Malam? Ta ya za ka shigo mana gida sannan ka dinga
dukansa haka?"
Sadeeq na huci ya ce "dukansa ma yanzu na fara wallahi, sai na gani tsakanin ni da shi wane
ne cikakken ɗan iskan, zan ga wa zai iya bada ransa akan Sunaiha, sai na nuna mishi Sadeeq
ba ya cikin irin mazajen da ake bibiyar matansu....kai ƙaramin kwarto ne wallahi, na rantse a
shirye nake da in ɗauki ranka a kan Sunaiha, kuma ka jira dawowa ta, dan ban gama ba, ko ni
ko kai, idiot!!" Yana gama faɗar hakan ya juya ya tafi
Sai a lokacin Najeeb ya san mako shi waye, Yayan shi ya kalle shi da kyau, duk ya kumbura
masa fuska, ya ce "Najeeb meyasa ba ka jin magana? Na sha fahimtar da kai abunda kake yi
bai dace ba amma ba ka saurare ni ba, yanzu wa gari ya waya? Kalli yanda ya sauya maka
kamanni, ka fita harkar yarinyar nan, tana da mijinta, kuma wallahi wannan mutumin ya fi ƙarfin
ka, ka ga dai tun kana taɓo waɗanda ka fi ƙarfin su yanzu har ka taɓi wanda zai yi maganinka,
Najeeb ka natsu ka haƙura da ita, ka ji da wannan raunin ma da ya bar ka da su"
A hasale Najeeb ya ce "keep quiet!! Enough dan Allah!!! What are you saying? Wanda zai yi
magani na fa ka ce, kuma in yi haƙuri? Impossible wallahi... ba'a taɓa yi mun irin wannan cin
mutuncin ba, kuma ba za'a fara akan sa ba, ba dai ya ce sai ya ga wanda zai rayu a tsakanin
mu ba? Then he shall see, na rantse sai ka ɗauki ransa ko da kuwa ba zan samu Sunaiha ba,
amma sai na ɗauki fansar wannan abun da yayi, ni ne zan zama ajalinsa"
Da mamaki Yayansa ya ce "Najeeb?! Kisa kuma? Bayan duk waɗannan halaye naka, kisan
kai kuma za ka fara? Najeeb wai kai wane irin mutum ne? Sai yaushe zan gaya maka magana
ka ɗauka? Ba za ka taɓa shiryuwa ba ne?"
"Yaya, ko zan shiryu, to sai bayan na kashe Sadeeq, that's it" bai tsaya sauraren komai ba ya
nufi ɗakinsa
Zama Yayansa yayi ya ce "innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun, wannan wane irin taurin kai ne
haka?"
Ɓangaren Sadeeq kuwa har ya iso gida huci yake, yana shiga parlour ya ji an rungume shi ta
baya, cike da murna ta ce "you're welcome dear!"
Ji yayi kusan kaso hamsin na ɓacin ransa ya gushe, kyawawan murmushi ya sauka kan
kyakkyawar fuskarsa. Juyowan da Sunaiha za tayi zuwa gabansa, ta lura da jinin da ke
hannunsa
Ta ce "meye haka? Meyasa same ka?....zo nan" ta ja shi ta zaunar da shi kan kujera, ta ce
"lafiya"
Shu kuwa kallonta yake yi sosai yana wani ƙayataccen murmushi, ganin ba ya da niyar yin
magana ya sa ta miƙe, da sauri ya riƙe ta ya ce "ina za ki je?"
"Zan ɗauko abunda zan goge maka jinin nan ne"
Jawo ta yayi sai da ta zauna ya ce "meyasa za ki goge mun shi? Ɗazu fa ke kika ce ko
mutuwa nayi ba ruwanki, amma meyasa yanzu ɗan wannan ciwon ya sa kika firgice haka?"
"Are you out of your mind? You're my husband, amma kake tunanin ban damu da kai ba? I
don't mean what i said"
Murmushi ya sake yi ya ce "ooh, haka ne ashe i'm your husband"
Ganin yanda ma ya mayar da ita abun dariya ya sa tayi tsaki tare da ƙwace hannunta, ta
miƙe tana faɗin "ni ka ƙyale in goge maka wannan jinin dan ba zan iya kallon ciwo a jikinka ba"
Sake zaunar da ita yayi sai ka ce wata baby, da hannu ɗaya yake jawo ta sai ta kai zaune, in
a serious tune ya ce "kika ce ba za ki iya kallon ciwo a jiki na ba?"
"Yes of course"
"To meye amfanin ki mun maganin wannan ɗan ƙaramin ciwon, amma kuma ki bar ni da
ciwon da zai iya kashe ni ma gaba ɗaya?"
"Stop saying that please, ka daina cewa za ka mutu ka bar ni, wannan wane irin ciwo ne? Ka
gaya mun, na maka alƙawari zan maka maganin shi, idan ma ba zan iya ba, zan iya kai ka ko
ina ne dan a maka maganin shi"
"A cikin zuciya ta yake, sannan duk faɗin duniyar nan, ba wanda zai iya warkar mun da
wannan ciwon idan ba ke ba, you're the only doctor"
"Me ya samu zuciyar ta ka? Wane irin ciwo ne? Ban yi tunanin kana da wani ciwo ba"
"Ina sonki sosai, sonki ya mun yawa, ina matuƙar kishinki, zan iya yin komai saboda ke,
amma kin bari Najeeb ya shiga rayuwarki da yawa, kina fushi da ni, and also, kin tsane ni,
sannan kuma kina zargi na..... Jewel a tunaninki waɗannan ba ciwo ba ne? Hakan zai iya illata
rayuwa ta, anything can happe...."
Rufe mishi baki tayi da sauri, ta ce "stop saying all this dan Allah, wa ya gaya maka ina fushi
da kai ko ina zarginka? Idan har zan iya tsanarka, to ba abunda zai hana in tsani kai na, duk
abunda ka ji na faɗa a kanka, sonka ne ya jawo hakan ba wai ƙiyayya ba, i love you so much,
ban taɓa zarginka ba saboda na yarda da imaninka, kishinka ne ya sa bana fahimtar komai a
lokacin, amma all thanks to Umma, dan ta mun bayanin komai... nothing can happen to you
matuƙar muna tare sai abunda Allah ya ƙaddara faruwarsa"
Ya ji daɗin maganganun ta har zuciyarsa, farinciki ya ziyarce shi mara misaltuwa, ya ce "da
gaske kike?"
"Hundred percent"
"I love you My Jewel"
"Love you too My Pri..." Sai kuma tayi shiru
Ya ce "ƙarasa mana"
Girgiza kai tayi ta ce "a'a, ka hana ni faɗar sunan ai"
"Oh no, just say it out, ni kai na na yi missing jin wannan sunan daga bakinki, say it please"
Murmushi tayi ta ce "I love you My....Boss"
Haɗe gira yayi ya ce "wane irin Boss kuma? Prince fa za ki ce"
"Noooo..ai tun da ka ce kayi missing jin sunan, to ba za ka ji shi so easily ba" ta ƙarasa tana
dariya tare da mishi gwalo
Ya kai hannu zai riƙe ta, ta miƙe da sauri tana dariya, ta ce "ɗazu ma da ka riƙe ni ɗin tausayi
ka ba ni, amma yanzu ba za ka iya ba"
"Really?"
"Yeah, ɗazu kaman ka ce it's not easy to defeat you right!?, To zan nuna maka i can defeat
you, catch me if you can, ni kuma zan faɗi sunan da kake so ka ji, idan kuma ba ka iya kama ni
ba, to tabbas ka yarda kawai Sunaiha za ta iya defeating ɗinka"
"Zan kama ki ne fa"
"Then let's see"
Kusan mintuna uku suna zagayar parlourn cike da farin ciki, sai ga Sunaiha a hannun
Sadeeq, ɗaukarta yayi cak, ya tsaya yana kallon fuskarta, sannan ya ce "kin gani, na gaya miki
zan kama ki"
Ɓata fuska tayi ta ce "ai na ce ka kama ni ba ka ɗauke ni ba, so let go of me"
"It doesn't matter, ko in kama ki ko in ɗauke ki, it's all the same, so ki faɗa kawai"
"Ba zan faɗa ba to sai ka sauke ni" ta faɗa a shagwaɓe
"Idan kika ga na sauke ki, to kin faɗa ne sai in sauke ki dan ki haɗa mun ruwa inyi wanka...kin
ga ma kin fama mun hannu na, sai ciwo yake yi"
Gaba ɗaya ta ma manta da ciwon hannunshi, ta ce "oops, i'm sorry My Prince, ka sauke ni in
ga hannun"
Murmushi yayi sannan ya sauke ta ya nuna mata hannun, ya ce "kin gani ba wani fama ni da
kika yi, kawai wayo na miki kuma kin faɗi sunan, so Malama je ki haɗa mun ruwan wanka" ya
faɗa yana murmushi
Ɓata rai tayi, ta wani tura shi gefe ta ce "ji kan shi" sannan ta haura sama, shi kuwa ƙara
faɗaɗa murmushinsa yayi ya ce "alhamdulillah"
Sai da ta haɗa mishi ruwan sannan ta fitar mishi da wasu kaya jeans da t-shirt of her choice,
sannan ta bar ɗakin zuwa kitchen, ta fito da abinci ta shirya musu shi akan dinning. Yana gama
shiryawa ya fito suka ci abinci, ciyar da juna suka cike da so da ƙauna, da kuma kulawa har
suka gama
Gaya mata yayi zai fita, sai kuwa ta ɓata rai, bata so ya fita, da ƙyar ya rarrashe ta tare da
mata alƙawarin ba jimawa zai yi ba, sannan ta yarda ya fita bayan ta mishi addu'a
Kai tsaye office ɗin Senator ya nufa, bai wani wahala da secretary ɗin ba, ya bari ya shiga,
cike da girmamawa ya gaida shi, ya amsa
"Takwara kwana biyu ka daina kawo mun ziyara ko?" Cewar Senator yana ƙoƙarin ture
computer da ke gabansa ya mayar da hankali wurin Sadeeq
Murmushi Sadeeq yayi ya ce "ba haka bane Daddy, aiki ne ya mun yawa shiyasa"
"Aiki kuma Sadeeq?"
"Eh... Daddy yanzu ma zuwa nayi in baka haƙuri akan abubuwan da suka faru tsakani na da
Sunaiha, Sharif ya gaya mun ranka ya ɓaci sosai akan hakan, har ma ka ce ba za ta dawo
gidana ba, Daddy ban yi dan in ɓata ranka ba, dan Allah kayi haƙuri"
Murmushi Daddy yayi ya ce "Sadeeq kenan, meye kuma na zuwa ka bani haƙuri? Ai nayi
zaton ba wannan a tsakanin ɗa da mahaifi ko! Sadeeq son da nake wa Sunaiha ne ya kawo
ɓacin ran ba wai dan kayi laifi ba, nima daga baya mahaifiyarta ta fahimtar da ni abubuwa da
dama waɗanda ya kamata a ce a irin shekaru na na fahimta, Sadeeq a matsayina na uba, ni
nayi jagaba wurin ɓata tarbiyar ƴa ta, amma a matsayinka na masoyin gaskiya sai ka gyara mun
ita, godiya ya kamata in maka ba wai kai ka bani haƙuri ba, na gode sosai Sadeeq, ba Sunaiha
kawai ka gyara wa ɗabi'unta ba, har da ni"
"Daddy, kamar yanda ka ce babu bada haƙuri tsakanin ɗa da mahaifi, to haka ma ba godiya,
kawai ka sa mun albarka ita na fi buƙata"
Murmushi ya sake yi, ya ce "albarka kam kullum a cikinta kake Sadeeq, sai dai an ce kogi ma
bai ƙi daɗi ba, Allah ya maka albarka Ya kuma tsare ka daga dukkan sharri"
"Ameen Daddy na gode sosai, Allah ya biya"
"Ameen takwara na"
Murmushi yayi ya ce "zan tafi Daddy" ya faɗa yana miƙe wa
"To Allah ya kiyaye, ka gaida Sunaiha"
"Za ta ji" daga haka ya wuce, Daddy kuma ya ci gaba da aikinsa
Bai tsaya ko ina ba dai gidan Anty Saudat, lokacin da ya tafi mijinta na shirin fita, gaisawa suka
yi, sannan mijinta ya ce "Sadeeq na ji daɗin ganinka ma, ga ta nan na ta son shan magani ko
kaɗan, ba ta kula da kanta ma bare kuma Babyn cikinta"
"Anty Saudat ai haka take, amma kar ka damu za ta sha"
"To Shikenan, bari in fita, ka gaida mun su Hajiya"
"To an gama yallaɓai" ya faɗa yana dariya, shi ma dariyar yayi kafin ya fita
Kusa da Anty Saudat ya dawo ya zauna, ya ce "Maman Baby how far"
"Ban sani ba, yanzu ka ganni?"
"Oh, sorry! Kin ga ai ina gaisawa ne da Babban Yaya"
"Uhm, yau ya ci sa'ar gaisuwar kenan....wai ma yau you look so happy, lafiya"
Murmushi ya ƙara yi wanda ke ma fuskarsa kyau sosai, ya ce "ai dole zan yi farin ciki, duk da
na san na ɗan lokaci ne"
"Kamar ya ban fahimta ba"
"Zan gaya miki, amma sai kin fara shan maganin nan"
Sanin yayi Anty Saudat akwai son labari shiyasa ya gaya mata haka, ba musu kuwa ta ɓalla
maganin ta shanye sannan ta ce "to yanzu gaya mun"
Ɗan ɓata rai yayi, ya ce "yau ɗin nan Jewel ɗina ta ƙara tabbatar mun da irin son da take
mun, kuma ta kusan shigowa rayuwa ta, amma na san very soon zamu rabu"
Da sauri ta ce "meyasa to?"
"Saboda ba kya sonta mana Anty Saudat, kuma kin san zan iya rabuwa da ita saboda farin
cikinki, amma ni kuma zan iya mutuwa"
"Stop it mana, ko da ba za ka mutu ba, ka san ba zan ƙi abunda kake so ba Bro, wace ce"
"Are you really sure, ko wace ce za ki so ta?"
"Of course in dai kana sonta"
"Are you sure?"
"Hundred percent sure mana Sadeeq, ba ka yarda da ni ba ne yau?"
"Na yarda da ke Sisto, kawai ji nake kamar ba za ki yarda ki so ta ba"
Riƙe hannunsa tayi ta ce "Sadeeq ka yarda da ni, na rantse maka ko wace ce in dai kana
sonta, zan so ta ko da kuwa ba na sonta a baya, kai ka sani Sadeeq, ina son duk abunda kake
so, abunda ba ka so