Showing 87001 words to 90000 words out of 146814 words
da safe" ta faɗa tana wucewa ɗaki
Sai da ta shige ɗaki sannan ya ɗauki wayarsa yana neman wata number yana murmushi ya ce
"My Princess Jewel, burinmu ya kusa cika"
Sunaiha kuwa tana shiga ɗaki tayi wanka ta zo ta kwanta, tana cikin tunani hawaye ya cika
idonta, ta miƙe ta zauna da sauri tana share hawaye, ta ce "it's over, i won't cry anymore, he
don't deserve my tears, kullum sai nayi kuka akan wanda bai san daraja ta ba!? Duk abunda
zan gaya mishi ba ya taɓa tsayawa ya fahimci damuwa ta, abunda ke ranshi kawai ya sa a
gaba, ya gama tabbatar mun da baya so na, to kuka kuma na me? I won't cry again, i don't
need u in my life Prince, although i still love you truly, but i deserve some respect and care, i'm
done with you Prince, Allah ya ba Grandpa lafiya kowa ya huta, Allah ya ba ni ikon iya zama da
Najeeb" magana take hawaye na bin fuskarta, ita kuma sai ƙoƙarin haɗiye kukan take yi tana
share hawaye
Sai da ta ban natsu kafin ta miƙe ta je ɗauko ruwa, tana fita ta ga Sadeeq yana parlourn har
yanzu yana waya, ba ma sai an faɗa ba, daga ji ta fahimci da mace yake wayar, yi tayi kamar
ba ta ma san da shi ba, ta shiga kitchen ta tsiyaya ruwa a cup ta sha, sannan ta dawo ɗaki ta
hau gado, ta kunna karatun ƙur'ani, ta saka earpiece sannan ta kwanta, kwata-kwata ba ta kai
mintuna goma ba bacci yayi awon gaba da ita
♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️
*LIKE*
*SHARE*
*COMMENT*
♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️
_Full of Arrogance, Ego, Jealous And_ _Love_
*CREATED AND WRITTEN*
_BY_
*UMMEETA*
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
مسِب الله نمحرلا ميحرلا
~~~~~~~~~~~~~~~~
_Luck is like sand in hands. It will sneak out through fingers, no matter gripped firmly or held
loosely. Only hands in the praying posture can save it._
*PAGE 59-60*
**RECAP FROM LAST PAGE**
Sunaiha kuwa tana shiga ɗaki tayi wanka ta zo ta kwanta, tana cikin tunani hawaye ya cika
idonta, ta miƙe ta zauna da sauri tana share hawaye, ta ce "it's over, i won't cry anymore, he
don't deserve my tears, kullum sai nayi kuka akan wanda bai san daraja ta ba!? Duk abunda
zan gaya mishi ba ya taɓa tsayawa ya fahimci damuwa ta, abunda ke ranshi kawai ya sa a
gaba, ya gama tabbatar mun da baya so na, to kuka kuma na me? I won't cry again, i don't
need u in my life Prince, although i still love you truly, but i deserve some respect and care, i'm
done with you Prince, Allah ya ba Grandpa lafiya kowa ya huta, Allah ya ba ni ikon iya zama da
Najeeb" magana take hawaye na bin fuskarta, ita kuma sai ƙoƙarin haɗiye kukan take yi tana
share hawaye
Sai da ta ban natsu kafin ta miƙe ta je ɗauko ruwa, tana fita ta ga Sadeeq yana parlourn har
yanzu yana waya, ba ma sai an faɗa ba, daga ji ta fahimci da mace yake wayar, yi tayi kamar
ba ta ma san da shi ba, ta shiga kitchen ta tsiyaya ruwa a cup ta sha, sannan ta dawo ɗaki ta
hau gado, ta kunna karatun ƙur'ani, ta saka earpiece sannan ta kwanta, kwata-kwata ba ta kai
mintuna goma ba bacci yayi awon gaba da ita.......
_BAYAN KWANA UKU_
Sadeeq ne a parlour, da dukkan alamu fita zai yi, dan ya gama shirinsa tsab, wayarsa tayo
ƙara, yana dubawa ya ga sunan Kawu Ƙarami, ɗagawa yayi cike da girmamawa suka gaisa
kafin Kawu Ƙarami ya ce "Sadeeq ina cikin asibiti, na ga ba ka ƙaraso ba har yanzu"
"Wallahi kuwa Kawu, amma gani nan zuwa yanzu"
"To shikenan.... Dama jikin Baba na duba, kuma na ga alhamdulillahi, kamar yanda muka yi
tsammani, ya ji sauƙi, dan har BP ɗin shi na duba, it's now normal"
Cike da murna Sadeeq ya ce "Masha Allah, nima jiya da na duba shi da daddare normal
ne.... Yanzu sai maganar sallama kenan"
"Eh, ka san dama one week muka yi, amma dai kar ka sallame shi ka bari dai gobe, saboda
maganinshi na dare"
Murmushi yayi ya ce "Kawu kar ka damu, dan maganin dare kawai zan je har gida in ba shi,
wallahi Grandma ta gaji da yawon asibitin nan, kuma taƙi yarda ta zauna a gida" ya ƙarasa yana
murmushi, hakan yayi dai-dai fa fitowar Sunaiha, ya tsaya tana kallonshi
"To shikenan duk yanda kayi, ni zan wuce ne ma yanzu, idan ka shigo sai ka ƙarasa duba
sauran patients ɗin, gobe ka zo mu je mu duba sauran chemists ɗin mu ga abunda ake buƙata"
"To, amma gobe akwai abunda zan yi mai muhimmanci, may be dai zan kira su sai su rubuto
mun duk abunda ake so ɗin"
"What's so special Sadeeq? A sanin da na maka ba ka wasa da aikinka, to me za kayi gobe?
"
Murmushi ya sake yi, ya ce "wani abu ne dai"
Sgi ma Kawu Ƙarami murmushin yayi, ya ce "to Allah ya taimaka... Sai ka zo"
"Ameen nagode" daga haka suka kashe wayar
Sai a lokacin ya kalli Sunaiha ya ce "sai da kika gama ɓata mun lokaci sannan za ki fito?"
Kallonshi kawai tayi ba ta ce komai ba, shi ma hai sake magana ba ya fita, ta ni bayanshi.
Suna hanya, ta ɗan kalle shi, ta ce "ɗazu na jo kaman kana cewa za'a sallami Grandpa yau ko?
"
"Umm" ya amsa mata
Numfashi ta sauke, sai ta ce "ina so za muyi magana zuwa anjima idan mun dawo"
"Allah ya kaimu, nima ina so zan yi magana da ke ai" ya sake amsa mata hankalinsa na kan
titi. Ita ma daga haka ba ta sake cewa komai ba har suka isa
Kai tsaye ɗakin da Grandpa yake ta wuce, Sadeeq kuwa sai da ya fara biyawa office. Tana
shiga ta tarar da su Sultana da Salma, da gidu suka zo suka rungume ta, sannan suka koma
suka zauna, ganin tayi Grandpa na bacci shiyasa ha ta gaida shi ba, ta kalli su Sultana ta ce
"ina su Sauban da Sameer? Ko ku kuka kwana anan ɗin yau? "
Salma ta ce "kaiii, a'a, ai Abba ba zai bari ba, su Sauban suka kwana, kasancewar yau za su
fara rubuta final exams ɗinsu, shiyasa muka zo da wuri sai suka wuce, su Umma sai anjima
kaɗan"
"Allah Sarki, Allah ya ba su nasara"
Suka amsa da "ameen" Sannan Sultana ta ce "wallahi Anty Sunaiha munyi kewarki sosak,
tun fa ranar da kika bar asibitin nan ba ki dawo ba sai yau, idan muka yi wa Oga Tiger zancenki
sai ya ƙyale mu"
Murmushi tayi, ta ce "nima haka nayi kewarku, amma ai yanzu ga ni"
Salma ta ce "kin san me Anty Sunaiha, sai yanzu nake jin haushin meyasa Alhaji bai ce su
Ya Sadeeq da Ya Safwan suyi part ɗinsu a cikin gidanmu ba tunda akwai wuri sosai, za suyi
part ɗinsu girman yanda suke so har a samu ragowa sosai ma"
Sultana ta ce "ni kaina nayi wannan tunanin, saboda yanzu nake jin kewar Anty Sunaiha yan
damu na"
Murmushi kawai Sunaiha ke yi tana bin su da ido, Sultana ta ce "amma yanzu ma ba
matsala, tunda yau za'a sallami Grandpa, daga gobe za kiyi ta ganinmu har sai kin gaji"
Sunaiha ta ce "me zai sa in gaji da ku? Kullum buri na in zauna tare da ku ai"
Salma ta ce "Anty Sunaiha kiyi haƙuri yanda muka yi miki a baya, kawai yanda kika yi mana
ne ya ɓata mana rai, amma kiyi haƙuri"
"Don't worry Salma, nima ban kyauta ba ai, kuyi haƙuri "
Sunaiha ta ce "ni dai bana jin daɗi in ji Antyna tana ba ni haƙuri" ta faɗa tana ɓata rai
Sunaiha murmushi tayi ta ce "to na daina my dear"
Shiru suka ɗan yi, Sunaiha a ranta ta ce "Allah sarki, lokacin da nake shirin barin gidanku, sai
a lokacin muka fara shaƙuwa da ku, ina jin sonku a raina kuma sosai... Amma hakan ba zai
sauya mun ra'ayi na ba, dole zan tafi sabida samar wa kaina daraja, za mu ci gaba da
zumuncinmu ko bayan tafiya ta, sannan ina fatan kamar yanda nake sonku a yanzu, Allah ya sa
ita ma Jewel ɗin Prince za ta so ku haka, kuma ku so ta" duk yanda hawaye ya so fitowa a
idonta, sai da tayi ƙoƙarin kayar da shi
Muryar Sultana ta dawo da ita, "Anty!!!! "
"Umm" ta amsa tana ƙirƙirar murmushi
"Where were u lost haka? Muna ta magana shiru"
"Oh, i'm sorry, wani tunani nake yi ne"
Murmushi Salma tayi ta ce "can i guess!? "
"Guess what" cewar Sunaiha
"Abunda kike tunani mana"
Sultana ta ce "ai ba wani ɓoye-ɓoye, mijinta take tunani" ta faɗa tana murmushi
"See this girl, wane miji kuma? Yanzu fa muka rabu"
Salma ta ce "and so!? Mu dai mun san shi kike tunani"
Kafin tayi wata magana, Grandpa ya ce "dan Allah ku ƙyale ni haka nan in yi bacci, yara sai
kace Parrot? "
Kallonshi suka yi da mamaki, idanunshi a rufe, amma yake maganar, Salma ta ce "dama ba
bacci kake yi ba Grandpa? "
Buɗe ido yayi ya kalle ta ya ce "ta ya zanyi bacci kuna ɗakin nan? "
Murmushi Sunaiha tayi ta ce "kayi haƙuri Grandpa, na ɗauka kana bacci ne ai"
"Kar ki damu Sunaiha, ai yanzu na tashi, shi ne na ji surutunsu"
"To ya jikin? "
"Alhamdulillah, ni wannan yarin ma nake so ya zo ya sallame mu haka nan mu tafi gida kowa
ya huta"
"Allah ya ƙara lafiya"
"Ameen"
Haka suka ci gaba da firarsu, har Sadeeq ya shigo ya duba shi ya fita, sannan su Hajiya suka
ƙaraso suka ci gaba da zaman su tare
Sai bayan magrib kafin Sadeeq ya cika musu takardar sallama, sannan syka wuce gida.
Gaba ɗaya gidansu Grandpa suka nufa har su Umma, Sannan Sadeeq ya wuce da Sunaiha
gida, ko gate bai shiga ba, ya ce "ki je, ni zan koma dan akwai maganin da nake so sai na
tabbatar ya sha, sanna zan dawo"
"Allah ya kiyaye" ta faɗa sannan ta fita, shi ma ya wuce
Tana shiga ta yi sallah, sannan ta dafa spaghetti, ta zuba a plate ta wuce parlour ta zauna, ta
fara ci kenan kiran Ikram ya shigo wayarta, cike da murna ta ɗaga
"Mutanen Abuja" abunda ta fara faɗa kenan
Ikram ma cikin fara'a ta ce "Hajiya ta, ai na baro Abuja, ina cikin garin Gombe"
Da mamaki ta ce "Gombe kuma? "
"Ƙwarai kuwa, a Gombe ma, a cikin gidanmu"
"Saukan yaushe kenan? What a surprise!"
"ai ba ma haka ma so inyi surprising ɗinki ba, na so samun flight ɗin safe yanda kawai gani
na za kiyi a gidanki, sai na samu na dare kuma, yanzun nan na dawo, wanka kawai nayi, nayi
sallah, shi ne na kira ki"
"Hmm, to sannu da dawowa.... I thought ma kin manta dani, shagalin biki ya rufe miki ido"
"Haba Sunaiha, ai ba abunda zai sa in manta da ke, yanzu ki shirya, gobe tun safe za ki
ganni a gidanki, kuma sai dare zan wuce"
Murmushi Sunaiha tayi ta ce "ba gobe ba dai kam, ki bari zan gaya miki ranar da za ki zo"
"Ban gane ba, ok, ke ce ma ba kiyi missing ɗina ba"
"A'a wallahi, i so much missed you My Iky, gobe akwai wani abu da zanyi, it's very important"
"Important? Me kenan?"
"Yeah, idan na gama, i'll let you know"
Shiru Ikram tayi, kafin kuma ta ce "alright then, Allah ya sa in ji alkhairi"
"Ameen... Ki gaida Umma"
"Za tajl ji, sai da safe" suka kashe wayar a tare
Numfashi Sunaiha ta sauke, ta ce "i wish zan iya gaya miki me nake shirin yi, but i can't,
saboda hana ni za kiyi"
Ɗaukar wayar tayi, ta kira Anty Najma, bugu biyu ba ta ɗaga ba, sai kawai ta ajiye wayar ta ci
gaba da cin abincinta. Tana haka har Sadeeq ya dawo, ya shiga yayi wanka sannan ya dawo
parlourn, abinci ta kawo mishi sannan ta zauna gefe
Tunani take ta yanda za ta fara magana, sai ta ji muryar sa yana cewa "ina jinki, ɗazu kin ce
kina da magana" ya faɗa yana kallonta
Tayi mamakin jin hakan daga bakinshi, saboda a tunaninta ya manta, sai ta ce "a'a ka fara
faɗa, ai kai ma ka ce kana da magana"
"Malama ba jayayya nake so muyi ba, umarni nake ba ki kiyi magana, ba shawara na
tambaye ki ba"
Sai da ta tattaro courage, sannan ta ce "Ya Sadeeq"
"Umm" ya amsa yana ƙoƙarin kai abinci baki
"I need a divorce"
Maganar ta daki kunnenshi, bai san lokacin da ya saki cokalin hannunshi ba, kallon mintuna
biyu ya mata, kafin ya ce "Divorce? Saki fa kenan kike nufi! "
"Eh Ya Sadeeq, ba ka so na, ba ka son zama da ni, muma zaune ne tare akan dole, Jewel
kake so ba ni ba, Ya Sadeeq ba zan iya ci gaba da zama da kai kana kwasar zunubi ba, saboda
ba ka taɓa sauke ko wane nauyi ma dake kanka ba, hakan kuwa babban matsala ne a wurinka
ran Allah zai tambaye ka, abu mafi sauƙi shi ne rabuwarmu Ya Sadeeq, dan haka dan Allah na
roƙe ka, ka sauwaƙe mun"
Numfashi ya sauke, kafin ya ce "wa ya ba ki wannan shawarar? Dan wannan ba dabararki ba
ce"
"What so ever Ya Sadeeq, ba abunda ya dame ka bane, ni dai dan Allah ka sake ni, dan
Allah "
"Shikenan na ji, amma yanzu dare yayi, ki bari sai da safe" ya faɗa yana ƙoƙarin tashi
A hankali ta rufe ido, hawaye suka biyo fuskarta sannan ta buɗe, tana ganin ya miƙe, tayi
saurin cewa "abincin fa? "
"Ki bar shi wurin"
Zai wuce, ta miƙe tsaye ta ce "Ya Sadeeq"
"Meye kuma? "
"Dan Allah kafin rabuwarmu, ina so zan roƙe ka wata alfarma guda ɗaya"
Kallonta yayi da kyau, ya ce "wace irin alfarma? Ki gaya mun zan miki, ba ki taɓa roƙo na
wani abu nayi miki ba, amma yau saboda yamda kika faranta mun, dole zan miki ko menene"
A tunaninta ya ji haushin rabuwar da za suyi, kenan daɗi ya ji? Ta tambayi kanta kafin ta ce
"Ya Sadeeq dan Allah, just once, ka nuna mun Jewel, please"
"Jewel? Why? "