Showing 144001 words to 146814 words out of 146814 words

Chapter 49 - YAR SENATOR BOOK COMPLETE BY UMMEETA

Umeeta   

13 Jul 2025

6561


firar da muka yi da Sultana last, ta faɗi cewa wata rana za ka tsaya mata, kuma za kayi nasara,
kamar ta san abunda zai faru, ka tashi mu tafi kawai, idan Ya Sadeeq ya tafi matsala kawai za a
samu" ya ƙarasa yana share hawayen da suka zubo masa
Ba musu Safwan ya miƙe suka fita ba tare da ya ce komai ba. Salma dai tana jinsu, kuka
kawai take yi har suka fita, wayar Sadeeq tayi ƙara, Umma ce, ba tare da ya ɗaga ba kawai ya
miƙe ya fita zuwa ɓangaren ta

Sameer na kwance a kujerar parlourn Umma shi kaɗai, haɗa ido suka yi da Sadeeq ba
wanda ya ce komai, saboda Sameer kan shi ba ya son magana da kowa yanzu, cikin ɗakin
Umma kawai Sadeeq ya shiga

Tana kan gado a zaune, da abinci kan bedside drawer, zuwa yayi ya ja wata kujera zuwa
gabanta sannan ya zauna, ya ce "Maa, gani"

Har yau idanunta a kumbure suke, a hankali ta ce "Sauban ya gaya mun kai da Sameer ba
kwa cin abinci, yanzu na sa Sameer ya ci, saura kai ka ɗauka ga shi nan"

Kallon abincin yayi, sannan ya ce "Maa na ƙoshi"

"Da ka ci me? Coffee ɗin da kake sha ne abinci? Sadeeq so kake kai ma in rasa ka? Ku uku
nake da su, ɗaya ta tafi saura ku biyu, Sadeeq ba ka gaji da ganin hawaye na bane?" Ta faɗa
hawaye na bin fuskarta

Hannu yasa ya share mata ya ce "stop it please Maa, ki daina kuka, nothing will happen to
me in sha Allah, zan ci"

"To ka ci in gani"

"Zan ci"

Anty Saudat ce ta turo ƙofar ta shigo, duk ta sauya, dama can ga ciki ga kuma wannan
rasuwar, zama tayi kusa da Umma, ta ɗauki abinci ta diɓa ta kai mishi baki, ba musu ya buɗe
ba ki ya ci

Sannan ta ce "Umma da haka kika mishi tsab zai ci, kin manta haka Sultana take yi wa
mutane idan ba sa da lafiya, idan mutum ya ƙi ci abinci, ba shi take yi a baki"

Murmushi Umma tayi ta ce "muna ƙaunarki Sultana, amma Allah ya fi mu ƙaunarki, kuma shi
kaɗai ya san dalilin da yasa ya karɓe ki a lokacin da kike ƙaramarki, Allah ya sa aljanna ce

makomarki ƴata, ku kuma Allah ya ƙara raya mun ku, Allah ya sa in ga jininku kafin mutuwa ta"
magana take tana kuka, hakan ya sa su Anty Saudat da Sadeeq zubar da hawaye, Anty Saudat
ta rungume ta, Sadeeq kuwa yana share mata hawaye

A station kuwa, su Alhaji sun gama magana da DPO, ya tabbatar masu da gobe zai aika da
case ɗin na su kotu, sun ji daɗin hakan sosai, suka mishi godiya sannan suka bar wurin

A hanya, Sauban na driving, Safwan na gidan gaba, su Alhaji su na baya, Alhaji ya ce
"Safwan da ka matsanta sai mun je kotu, kana da hujjojin da za ka tabbatar da cewa shi ya
kashe ta?"

"Eh Alhaji, tun ranar da abun ya faru ban zauna ba, na je har park ɗin na samu shaidun gani
da ido, sannan mai gadin gidan Najeeb ɗin ma ya taimaka mun sosai, saboda ya bani
information akan wani abokin Najeeb ɗin da ya ji su na waya ranar da yakan ta faru, ya gaya
mun ya ji ya kira sunan mutumin sannan ya gaya mishi wurin da za su haɗu dan ya ba shi
bindigarsa, shi ne ma ya raka mu har gidan abokin na sa dan ya san shi, yanzu haka shi ma
yana hannun ƴan sanda, kuma ya amsa cewa shi ya ara mishi bindigar, kuma ya gaya mishi me
zai yi da ita"

Kawu Ƙarami ya ce "amma ban ganshi a cell ɗin ba lokacin da na je duba Najeeb"

"Ai ba wannan station ɗin yake ba, wani station daban na kira saboda ba na so su haɗu da
Najeeb ɗin, kuma sanadiyar abokin na sa ma mun gama ɗayan yaronsa da aka yi a gabansa,
ɗayan ya gudu....Kawu ku kwantar da hankalinku, na shirya wa case ɗin nan sosai, ba yanda
za'a yi Najeeb ya kuɓuce"
Alhaji ya ce "to amma abunda ke bani mamaki shi ne, shi Najeeb ɗin ba ya da ƴan uwa ne ko
iyaye?"

"Iyayensa sun rasu aka ce, ɗan uwansa ɗaya, kuma na samu numbern sa na kira shi kwana
biyu da suka wuce, amma y gaya mun tun da har Najeeb zai iya ɗaukar ran ɗan adam, ya yafe
shi, ba abunda zai iya yi mishi dan ya san hukuncin kisa za'a yanke mishi, shiyasa ma ba zai
zauna a ƙasar ba"
Alhaji ya ce "kuma ɗan uwansa ne?"

Kawu Ƙarami ya ce "da wuya kam, idan ma har ɗan uwansa ne to ba ciki ɗaya suka fito, dan
da ba abunda zai hana shi tsaya wa Najeeb ko da kuwa ya san ba za suyi nasara ba"

Safwan ya ce "yanzu ma dai ko menene, can tsakaninsu, ni buri na kawai in ga wannan
mutumin ya bar duniya"

"To Allah ya bada sa'a" cewar Alhaji

Suka amsa da amin

Kwana ɗaya da hakan, aka shiga kotu domin sauraren ƙarar, an ba Najeeb damar kiran
lawyernsa kafin aka fara shari'ar, duk wasu gamsassun hujjoji sai da Barrister Safwan ya
gabatar da su a gaban kotu, kusan mintuna talatin ana abu ɗaya, duk iyalan Saraki's family
suna kotun idan ka cire Hajiya, Umma, Momi da Grandma, sai Salma, amma har Grandpa yana
wurin, Sadeeq ma da ƙyar Abba ya lallaɓa shi ya zo

Daga ƙarshe dai Barrister Safwan yayi nasara, domin kuwa alƙalin yayankewa Najeeb
hukuncin kisa, abokinsa ma da yaransa an yanke musu hukunci daidai da laifinsu, Saraki's
family sun ji daɗin hukuncin sosai, suka gode wa Allah tare da roƙarwa Sultana rahamar
Ubangiji
Ranar da Sultana ta cika kwana bakwai da rasuwa, aka yi sadaka sannan aka yi addu'a sosai
a gare ta da sauran waɗanda suka riga mu gidan gaskiya

Zuwa wannan lokacin, Salma ta samu sauƙi sosai, sai dai har yau ta kasa sakewa, amma
tana cin abinci sai dai tare da su Hajiya, su Anty Sadiya, Anty Sameera da Anty Saudat ma duk
Alhaji ya ba su umarnin koma wa gidajensu, duk da ba su so hakan ba amma dole suka koma.
Sadeeq ma ya fara zama mutum, dan ya daina zama shi kaɗai, tun ranar dasuka baro kotu
bayan an yanke wa Najeeb hukunci, ya ke jin an rage mishi wani nauyi da ke kansa

Da daddare Sadeeq suna ɗakin Sunaiha, zaune yake kan gado ya jingina, ita kuma ta
kwanta gefensa kan jikinshi, ta wani ƙanƙame shi kamar zai gudu, numfashi ta ja, a hankali ta
ce "Prince"

"Umm" ya amsa

"Prince ni na jawo Najeeb into our lives, ban taɓa tunanin he's capable of doing all this ba, i
always feel guilty, i think i'm responsible for everything Prince, could you please forgive...." Rufe
mata baki yayi, hawaye na zuba kan fuskarta, ya share mata kafin ya ce

"Stop blaming yourself, ban taɓa ganin laifinki ba ko da da rana ɗaya ne akan wannan, komai
muƙaddari ne daga Allah, ko da ke, ko babu ke, die Najeeb sai ya kashe ta saboda shi ne
ajalinta, dan haka kar in sake jin wannan maganar dan Allah"

Kallonshi tayi sannan ta sake rungume shi ta ce "i love you, Allah ya mata rahama"

"Ameen, i love you too" ya ɗora hannunsa kan gashin kanta yana shafawa, ya rufe ido,
Sultana kawai yake tunani da duk memories ɗin da suka yi sharing as usual, lokutan da yake
mata faɗa da lokutan da suke shiri, sannan da maganar da ta gaya mishi ta ƙarshe, 'Ka kula da
kanka, da iyayenmu, da Saraki's family baki ɗaya' hawaye suka biyo fuskarsa, yayi sauri

gogewa saboda yana so ya daina zubar mata da hawaye, sai dai duk lokacin da ya tuna ta, ya
mata addu'a

**BAYAN SHEKARA UKU**

Abubuwa da yawa sun faru cikin waɗannan shekaru ukun, ciki kuwa har da rasuwar Grandpa
wanda ya rasu bayan wata biyu da rasuwar Sultana, Grandma ita ma ta bi shi bayan watanni
huɗu da rasuwarsa, Wannan shekarar kam mutuwa ta waiwayi gidan Saraki, dam haka rayuwar
take, wani lokacin idan mutuwar ta waiwaye ku, sai ka ji tamkar kai kaɗai mutuwar ke tunawa,
sai ka ji tamkar ba ka taɓa farinciki ba a rayuwa, hakan wani darasi ne da ya kamata duk wani
ɗan adam ya fahimta, rayuwar ba ta taɓa tafiya a ɓangare ɗaya, dole sai ka ɗanɗana ko wane
ɓangare

Domin kuwa bayan sun gama jimamin rasuwar, a shekara ta gaba farin ciki ya fara ziyartarsu,
domin Anty Saudat ta haifi santalelen ɗanta wanda ya ci sunan Grandpa, wato Al'ameen suna
Kiransa da Ashraf. Bayan murnar haihuwar Anty Saudat, Nasreen ta haihu, ita ma kyakkyawan
ɗa ta haifa, aka saka mishi sunan mahaifinta Al-Mustapha, ana kiransa da Mukarram. Sannan
Anty Sameera ma ta sake haihuwar ƴa mace, aka saka mata suna Fatima, ana kiranta da
Zarah, gida ya ƙara cika masha Allah, Baba Sajeed ya sake tara yara

A shekara ta gaba kuwa hidimar aure ce, Salma ta kammala karatunta, ta zama cikakkiyar
nurse a asibitin su, bayan ta kammala ne aka ɗaura aurenta da saurayinta, ɗan abokin Alhaji
ne, mahaifinsa mai kuɗin gaske ne, shi kan shi yaron sanannen ɗan kasuwa ne, sannan anyi
auren Anty Najma da Yareema Muhsin, sai Ikram da Aryaan, Sarah kuma da Saif
An sha biki kam masha Allah, yanzu kuma auren Sauban da Sameer ake jira, duk da dai har
yanzu Sameer ya kasa mayar da hankali ya samu wacce yake so, Sauban yana da budurwa,
amma a cewarsa yana jiran sai ranar da Sameer ya tashi yin auren sai suyi tare shiyasa bai yi
mata alƙawarin aure a nan kusa ba, Su ma sun far aiki, Sameer na aikin banki, Sauban kuma
MD ne a ɗaya daga cikin kampanin Abba. Sai kuma sarkin ɗaukar rahoto, Sajeeda da kuma
Safna, waɗanda yanzu suna jami'a, Sajeeda na mataki na biyu, Safna kuwa mataki na farko,
duk da dai su ma ba shirya wa auren suka yi ba, amma iyayensu na jiransu, sai dai akwai
soyayya mai ƙarfi tsakanin Sajeeda da Sharif

Sai Oga Tiger, Sadeeq ya sake gina wasu asibitin guda uku a wuraren daban-daban, sai dai
guda biyu ya buɗe, ɗayan ya ce sai bayan haihuwar Sunaiha sannan za'a buɗe shi, tana nan da
tsohon cikinta, haihuwa yau ko gobe, tana wurin Hajiya kamar yanda ta riƙe Nasreen a wurinta
har ta haihu, haka take shirin yi a kan Sunaiha
Kamar yanda suke tsammani, a ranar da EDD ɗin ta ya cika, a ranar ta fara naƙuda, ba ɓata
lokaci aka garzaya da ita asibitin da Sadeeq ke yawan zama, da taimakonsa da wasu nurses
guda biyu, Sunauha ta haifi kyawawan twins ɗinta mace da namiji, murna a wurin Sadeeq
faɗarsa ma ɓata lokaci ne

Cikin ƙanƙanin lokaci, labari ya isa kunnen duk wani da ya shafi Saraki's family, kafin yamma
gida ya cika, kowa Allah-Allah ya ke a ba shi twins ya ɗauka, dan su ne ƴan biyu na farko da
aka fara samu a familyn. Parlour ya cika maƙil, sai gardamar ake yi wanda twins suka ɗauko,
wasu su ce Sadeeq suka biyo, wasu su ce Sunaiha ce, Sadeeq shi dai yana ɗakin Hajiya yana
jinyar matarsa

Kafin ranar biki ya zagayo, twins sun cika da kyaututtuka daga wurin iyayensu da
kakanninsu, kowa ji yake yi da su. Ranar suna kuwa an sha biki kamar ba gobe, gagarumin biki
aka shirya na ji da faɗi, shagalin bikin kusan duk wanda ke Jahar Gombe ya samu labari, masu
amfani da social media ma sun gani yanda shagalin ya gudana
Hassan ana kiransa da Sultan, Husaina kuma Sultana, a wannan ranar Sadeeq yayi farinciki
sosai saboda yau ya cika wasiyar Sultana na ƙarshe da ya rage, kuma ya sake godewa Allah
da ya ba shi ƴan biyun mace da namiji, wataƙila saboda ya cika wannan wasiyar ne

Bayan sati ɗaya da bikin, Sadeeq yayi bikin buɗe ɗayan asibitin, wanda sai a ranar ne kowa
ya san sunan asibitin, dan ya banbanta da saura gudu huɗu ɗin da ake kira Saraki's Hospital,
wannan asibitin sunansa SULTANA USMAN SARAKI HOSPITAL (SUS HOSPITAL) , tsarin
wannan asibitin ma daban ne, har kayan da ya zuba a ciki na daban ne, yayi kyau kamar ba
asibiti ba, sannan ya miƙawa Salma takardun mallaka mata asibitin, ba wai dan ta zama
shugabar asibitin ba, hakan ba zai yiwu ba saboda Nurse ce ita, ya ba ta shi ne halak, ko da
mutuwa yayi ba ya cikin kayan gadonsa, ba Salma kaɗai ba, kowa sai da yayi murna da hakan,
tayi mishi godiya sosai har da hawayenta

Rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin farinciki da kwanciyar hankali, duk lokacin da suka tuna da
waɗanda suka rasu, su kan bi su ne da addu'a da fatan rahama da gafarar Ubangiji, komai na
su sai san barka, fatanmu shi ne Allah ya raya yaran baki ɗaya, waɗanda suka rasu kuma Allah
ya gafarta musu, ma'aurata kuma Allah ya ƙara musu zaman lafiya da haƙuri da juna, ma su
soyayya kuma Allah ya nuna musu ranar aure, Allah ya ƙara mana lafiya baki ɗaya, ya mana
kyakkyawan ƙarshe.......Nayi nan, rahoton familyn Saraki ya isa haka nan (Hhhhhh).......






ALHAMDULILLAH, A NAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN NA WA NA ƳAR
SENATOR, INA ROƘON ALLAH DUK ABUNDA NA RUBUTA BA DAIDAI BA, ALLAH YA YAFE
MUN, KUMA DA KUKA KARANTA YA YAFE MUKU, WANDA KUMA NAYI DAIDAI ALLAH YA
BANI LADA, KUMA YA BAKU LADAN KARANTAWA. ALLAH YA BAMU IKON ƊAUKAN
DARASIN DAKE CIKI.

INA MATUƘAR GODIYA GA WAƊANDA SUKA JURI KARANTA WANNAN LITTAFIN DAGA
FARKO HAR ƘARSHE, NA GODE SOSAI DA KULAWARKU DA KUMA YAWAN ADDU'O'IN DA
KUKE MUN DA FATAN ALKHAIRI, BA ZAN IYA BAYYANA MUKU FARINCIKIN DA KUKE
SAKA NI BA KO DA YAUSHE, SAI DAI IN YI MUKU ADDU'AR ALLAH YA SAKA MUKU DA
MAFIFICIN ALKHAIRINSA KUMA YA BAR MU TARE, LOVE U ALL. KAMAR YANDA MUKA GA
ƘARSHEN WANNAN SHEKARA LAFIYA, ALLAH YA NUNA MANA SABUWAR SHEKARA
LAFIYA, KUSKUREN DA MUKA AIKATA A WANNAN SHEKARAR ALLAH YA YAFE MANA,
ALLAH YA SADA MU DA ALKHAIRAN DA KE CIKIN SABUWAR SHEKARA YA KUMA TSARE
MU DAGA SHARRINSA, ALLAH YA JI ƘAN WAƊANDA SUKA RASU MU KUMA YA SA MU
MUTU MUNA MASU CIKAKKEN IMANI....AMEEN

JINJINA TA MUSAMMAN GA ƳAR SENATOR FANS GROUP, INA MATUƘAR YINKU OVER,
INA ƘAUNARKU SOSAI, SON SO NAKE MUKU FISABILILLAH�.......KAR A CE NAYI
SON KAI�....MU TARA DA KU CIKIN SABON LITTAFINA DA ZAN FARA SAKI A SABUWAR
SHEKARA IN ALLAH YA YARDA WATO **HUMAIRA**, INA FATAN ZAI ƘAYATAR DA KU
KAMAR DAI YANDA ƳAR SENATOR YAYI, TNX ALOT

AKA CE DUK WANDA YA BAR GIDA, GIDA YA BAR SHI, TO BAN MANTA DA KU BA
JAMA'AR MOONLIGHT WRITERS ASSOCIATION, INA ALFAHARI DA KU OVER
OVER✨, ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKA MOONLIGHT DA MARUBUTANTA, KUMA YA
ƘARA HAƊA KANMU....AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM
ALHAMDULILLAH!!!





♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️


*LIKE*
*SHARE*
*COMMENT*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login