Showing 3001 words to 6000 words out of 146814 words

Chapter 2 - YAR SENATOR BOOK COMPLETE BY UMMEETA

Umeeta   

13 Jul 2025

6558

be sorry for something you choose to do that is right and true, because
right is right even if everyone else is wrong about it, and wrong is wrong even if everyone else is
wrong'''_


*PAGE 3-4*

Kamar yanda Daddy ya gaya mata, tun ƙarfe huɗu ta dawo gida, ta gaya wa Mummy yanda
suka yi da Daddynta

Mummy ta ce "ai ya kira ni, na sa a haɗa mishi abinci ma"

"Mummy wa za'a haɗa wa abinci kuma? "

"Ji wani tambaya... baƙonki mana, Sagir"

"But Mummy why? Ko so kike yayi tunanin na damu da shi ne? " ta faɗa rai a ɓace

Kallonta Mummy tayi da mamaki ta ce "Sunaiha abincin ne da za'a mishi kuma tashin
hankalinki? "

"Yes Mom"

Numfashi Mummy ta sauke, kafin kuma maganar ta bata haushi, sai ta ce "to dan ubanki sai an
girka mishi abincin sai dai ki mutu, wannan mugun halin na ki yayi yawa wallahi, me aka yi, aka
yi abinci, abincin da kin san kin fi ƙarfinshi!!.. Dalla ni wuce ki bani wuri kafin in mangare ki
Allah"
Bubbuga ƙafa ta fara yi ƙasa tana masifa kamar za tayi kuka, ta haura sama, Mummy ta bi ta da
ido kawai har ta wuce sannan ta zauna ta ce "Allah ya shirya mun ke"

Komai ya kammala a ɗakin baƙi, zuwan Sagir kawai ake jira, bai zo ba kuwa sai ƙarfe biyar, har
ɗakin baƙi ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya kai shi kafin ya je main parlour ya gaya wa
Mummy

Waya ta ɗauka ta kira numbern Sunaiha da ke ɗakinta, tana ɗagawa ta ce "ki sauƙo ga shi nan
ya zo" ba ta jira jin amsarta ba ta kashe wayar

Sunaiha kuwa ji tayi ranta ya matuƙar ɓaci, ko motsawa daga wurin da take ba tayi ba kusan
mintuna goma, kafin ta tashi ta je tayi wanka ta fito, bakin mirror ta zauna ta shafe jikinta da
lotions ɗinta sannan ta saka turare ɗan kaɗan, ta jawo wayarta ta fara chatting, kiran Mummy ya
sake shigowa, sai da ta ɓata rai kafin ta ɗauka
"Mummy gani nan fitowa" ta faɗa tana turo baki

"Kar ma ki fito, ki bari in zo in same ki, kuma saura ki fito kamar me takaba ki gani" ta kashe
wayar

Kallon fuskarta take cikin madubi, kyakkyawar gaske ce, ita kanta tana yaba irin kyaun da Allah
ya mata, wataƙila shiyasa sam kwalliya ba ya cikin tsarin rayuwarta, in dai za tayi wanka ta

shafa mai, to shikenan ta gama mai wuyar

Sai dai a cewarta dalili ɗaya ne ke hana ta yin kwalliya, wai tana taya Prince ɗinta kishin kanta
ne, bata so tayi kwalliya wani ya gani wanda ba Prince ɗinta ba

Ta daɗe tana kallon kanta a madubi, kafin tayi tsaki ta ɗauko kwalli kawai ta sa ma idonta shi
ma dan kar Mummy ta mata faɗa ne

Wardrobe ta nufa, doguwar rigar atampa kalar ja da baƙi ta ɗauka ta saka, kusan rabin kayanta
dogayen riguna ne, ta ɗauko gyalen kayan, shi ma ja , ɗan ƙarami ne, sai kawai ta ɗora shi a
kai ta zagaye wuyanta da shi, sai flat shoes ɗinta baƙi, sannan ta sauko parlour

Kallo ɗaya Mummy ta mata ta ɗauke kanta, ita ma bata tsaya wurinta ba kawai ta fita, sai a
lokacin Mummy ta ce "Allah yayi mace har mace, kyakkyawa ga iya ɗaukar wanka, son kowa
ƙin wanda ya rasa, amma ta ce ba ta da aiki sai na wulaƙanta masu sonta, wai ita matar
Prince... Mtsww" tayi tsaki ta ci gaba da abunda take yi


Sunaiha kuwa tana zuwa ɗakin ta tura ƙofar ta shiga babu sallama, akwai wurin da aka tanada
dan ajiye takalmi daga cikin ɗakin, amma ko kallon gefen bata yi ba ta wuce da takalminta ciki

Sagir na zaune kan kujera har ya fara gajiya, ba laifi yana da kyau dai-dai misali, tun shigowarta
ta kafe shi da ido, wani kallo take mishi har ta kai kusa da kujera ta zauna, kafin ta ɗauke idonta
daga kan shi tana kallon ƙaton tray ɗin da aka ciko mishi da kuloli, ruwa kawai ta ga ya buɗe ya
sha
Ta sake ɗaga ido ta kalle shi, ta jingina bayanta jikin kujerar, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya

"Sannunki da fitowa" Sagir ya faɗa yana kallonta

Kallo ta mishi mai kama da harara, sannan ta ce "ba ciwo nake yi ba bare ka ce mun
sannu....(nuna tray ɗin tayi da hannu tana yamutsa fuska) ya dai sarkin yunwa! Naga kamar ba
ka ci komai ba.. Ko dai a leda za'a juye maka ka kaiwa mutanen gida? "

Mamaki ne ya cika shi, buɗe ido yayi yana kallonta ,ya ce "ke!!! Me kika ce??! " ya faɗa yana
miƙewa tsaye

"Ni kake tambaya abunda nace? Ai bana magana biyu"

"Ni kike kira da sarkin yunwa? Kin san ko ni waye kuwa? " ya faɗa rai a ɓace yana nuna kanshi
da yatsa

Harara ta sake zabga mishi tayi tsaki ba tare da tace komai ba, Mamaki ne ya sake kama shi,
ya ce

"Sagir Abdullahi Makama, ni kike ma wannan rashin kunyar? Kin san waye mahaifi na a garin
nan kuwa? "

Miƙewa tayi ita ma, ta ce "Sagir Abdullahi Makama... Ina tunanin baka san wurin da ka zo ba ne
shiyasa kake gaya mun sunanka da gadara.. In har ka manta ne, to kana gaban Sunaiha
Abubakar Nuraddeen, ƳAR SENATOR, ka gane?"

"Ƴar senator?! Kina ƴar senator ɗin ne ake roƙon maza su zo su aure ki? "

A tsawace ta ce "kai Sagir!!! Dakata.. Ka koma gida ka tambayi Abdullahi Makama, wa ya miƙa
ƙoƙon bararsa? Sunaiha ta fi ƙarfin haka wallahi, Shashasha kawai" ba ta jira jin me zai ce ba ta
wuce bayan ta gama harararshi

Shi kuwa tsayawa yayi kamar wani hoto, ya ma rasa yanda zai yi da ita, har ta wuce kallonta
yake, haushin kanshi yake ji bai ma san dalilin da yasa mahaifinshi ya turo shi nan ba

Numfashi ya ja ya ce "zan yi maganinki tabbas... " a fusace ya bar gidan


Mutumiyar kuwa bayan ta koma parlour, ta cire mayafinta ta ajiye, ta zauna kan kujera ta ɗora
ƙafarta kan center table ta rufe ido tana tunani, ɗaya daga cikin mai aikinsu ce ta zo da fruit
salad cikin bowl, kasancewar wannan lokacin tana shan fruit salad

Ajiyewa tayi kan table ɗin ta ce "ranki ya daɗe ga fruit salad ɗin na haɗa miki"

Ko motsi ba tayi ba, hakan ya san tayi zaton ko bacci take yi, sai kawai ta ɗauka zata koma da
shi gudun kar tayi laifi, sai bowl ɗin ya suɓuce mata a hannu sai kan ƙafar Sunaiha

Da sauri ta tashi sabida yanda ta ji sanyi a ƙafarta, tana ganin ko wacece bata twaya jin komai
ba ta wanke ta da mari, ta ce "ke mahaukaciyar ina ce, wawiya kawai, duba ki ga abunda kika
yi"

"Dan Allah ranki ya daɗe kiti haƙuri, wallahi tsautsayi ne"

"Tsautsayi ko! Za ki ga tsautsayi"

Wucewa tayi dinning area ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa masu sanyi sosai ta tsiyaya a cup
sannan ta dawo kusa da ita ta watsa mata su a fuska, sai da ta razana, har numfashinta ta ji ya
tsaya kafin ta sauke ajiyar zuciya da ƙarfi tana shafa fuskar

Sunaiha ta ce "gobe idan kika sake ɗauko wani abu, ki bari tsautsayi ya sa ki zuba mun shi a jiki
ki gani yanda zan yi dake"

Mummy dake fitowa daga kitchen wurin duba abincin da suke girkawa, ta tsaya tana kallonsu ta
ce "lafiya? Me kuma ya faru? "

Kallonta kawai Sunaiha tayi, ta ɗauki wayarta ta haura sama, bin ta tayi da kallo kafin ta juya
wurin mai aikin, ta ce "me ya faru? "

Tana kuka ta bata labarin yanda aka yi, tsaki Mummy tayi tana girgiza kai, ta ce "kiyi haƙuri kin ji
ko... Je ki ƙarasa aikinki"

Ɗaga mata kai tayi, ta ɗauki bowl ɗin zuwa kitchen, sannan ta dawo ta gyara wurin tas

Tunda Sunaiha ta shiga ɗakinta bata sauko ba sai bayan sallar isha'i, shi ma lokacin ta ji
dawowar Daddynta

Da gudu ta sauko ta rungume shi, ta ce "you're welcome Dad"

Cikin fara'a ya ce "thank you Baby na, ya gida"

"Ɗazu dai ba daɗi, amma yanzu komai normal tun da ka dawo"

Murmushi yayi ya ce "to zauna ki jira ni bari in fito"

Ta wuce kan kujera ta zauna, shi kuma ya wuce ɗakinshi dan yayi wanka, Mummy na zaune
tana waya ko kallonsu ba tayi ba, har ta gama sannan ta bi bayanshi

Tsawon mintuna ashirin sannan suka fito, kai tsaye dinning area suka wuce dan a nan suka ga
Sunaiha

Daddy ya ce "Baby yunwa ne? "

Murmushi tayi ta ɗaga mishi kai, bayan an gama zuba musu, suka fara ci

Gyaran murya Daddy yayi ya ce "Baby"

"Umm.. " ta amsa dai-dai lokacin da take kai cokali bakinta

"Ba ki gaya mun ya kuka yi da Sagir ba ɗazu"

Sai da tayi tsaki ta ce "manta da shi kawai Daddy, wannan ya ma fi kowa raina ni wallahi"

Ƴar dariya yayi ya ce "ya raina ki fa kika ce.... Ni kuma mahaifinshi ya kira ni wai bai ji daɗin
yanda aka yi wa yaronshi ba"

"To ni gaya mishi aka yi naji daɗin abunda yaronshi ya mun ne? Wai har ni yake kallo ya
tambaye ni wai na san ko shi waye? "

Dariyar ya sake yi ya ce "yanzu dai Baby shi ma bai miki ba? "

"Ko kusa ma"

"Alright, gobe ma ɗayan zai zo kinji"

"Daddy ni fa na gaji" ta faɗa a shagwaɓe

"Yi haƙuri dai, kika sani ma ko shi ne Prince ɗin na ki? "

"Tab, God forbid, ba shi ba ne"

Mummy da ke ji kamar ta haɗa kansu wuri ɗaya saboda haushi, ta ce "wai Alhaji sai yaushe
kake so yarinyar nan tayi hankali ne? Yaushe kake so tayi aure? Kai shikenan duk yanda ta ce
haka ɗin za kayi? Wannan wane irin rayuwa ne? Yanzu fa uban yaron nan ya gaya maka bai ji
daɗin abunda ya faru ba, maimakon ka tambayi me ta mishi dan kayi magana ta gyara, a'a kai
wannan ba damuwarka ba ne... Alhaji ina tausaya ma rayuwar yarinyar nan ba ka ganewa
wallahi, a ƙalla ta kori samari sun kai sha takwas, Sagir ne na sha tara.. "

Rai a ɓace ya ce "Haba Hajiya, wai me yasa ke bakinki baya furta kalma mai daɗi akan Baby
ne? Idan ban faranta ranta ba wa kike so in farantawa? "

"Ni ba wai na hana ka farantawa ƴarka ba, amma dai a riƙa sara ana duba bakin gatari, kar
garin ruwan idon neman Prince ta je ta sa kanta a matsala, wulaƙancin yayi yawa"

"Ba wata matsala da za ta shiga in sha Allah, kuma sai wanda Baby ta ji tana so sannan zan
bada ita"

"To ai shikenan, sai kuyi tayi.... Ke kuma ki ci gaba da biye mishi" ta ƙarasa tana nuna Sunaiha,
sannan ta tashi rai a ɓace ta bar wurin zuwa ɗaki

Sunaiha ta ce "Daddy wai meyasa Mummy kullum sai ta mun faɗa ne, komai nayi ba dai-dai ba
ne a wurinta"

"ƙyale ta kin ji Baby, ai ni komai kika yi dai-dai ne a wurina, your Dad is always by your side"

Daɗi ta ji sosai, sai kawai suka ci gaba da cin abincinsu, har suka gama sannan kowa ya wuce

ɗaki

Washe gari da safe kamar yanda Mummy ta sa aka haɗawa Sagir abinci, haka ma ta sake sa
aka haɗa ma ɗan gidan Alhaji Sani, ƙarfe sha ɗaya da ƴan mintuna ya iso, sai da yayi zaman
minti talatin kafin ta je ta same shi

Ya ganinta ya miƙe tsaye yana bin ta da ido har ta tsaya kusa da shi, sannan ya ce "lallai tsarki
ya tabbata ga ubangijin halittu.... Ashe haka kike da kyau? Ba ke camera ke haskawa ba, ke ce
kike haska camera, dan kin ma fi kyau a zahiri Sunaiha ta... "

Da sauri ta katse shi ta hanyar ɗaga mishi hannu "kai Malam hold on, me naji ka ce?
Sunaiharka?"

"Eh mana, idan ban kira ki tawa ba, wa zan kira? "

"Hmm to bari ka ji, ya ma sunanka.... Umm.. I don't even know, abunda dai zan gaya maka shi
ne, tun wuri ka je ka nemi dai-dai da kai, saboda Sunaiha ba sa'arka ba ce, ko da wasa kar in
sake jin wannan ƙazamin bakin naka ya kira sunana ma, kai ko kunya baka ji ba? Dube ka dan
Allah ka zo da wani ƙaton kanka wai 'Sunaiha ta' wallahi ka kiyaye ni"
Duba jikinshi yake yi yana so ya ga me ta gani da har take mishi wannan wulaƙancin, amma ba
abunda ya gani wanda bai yi ba, ya ce "Sunaiha me.... "

Sake katse shi tayi "wai ba na ce kar in sake jin sunana a bakinka ba! Sunaiha ta fi ƙarfinka, ko
maza sun ƙare a duniyan nan wallahi ba zan taɓa aurenka ba, ka hutar da kanka kawai" tayi
tsaki ta fita daga ɗakin

Ya daɗe a zaune zuciyar na mishi zafi, sam bai ji haushin kalamanta ba saboda yana sonta
sosai, abu ɗaya ne ke damunshi da ta ce wai ba zata aure shi ba, hakan na nufin ba ta sonshi
kenan! Ya gaji da zaman ya tashi ya wuce

Lokacin da ta shigo parlourn, Mummy na ɗakinta, ita ma ba ta zauna a parlourn ba ta wuce
ɗaki, sake shiryawa tayi sannan ta fito ta wuce ɗakin Mummy

Tura ƙofar tayi ta shiga, Mummy na duba kaya a wardrobe ko juyowa ba tayi ba

"Mummy" ta kira sunanta amma ba ta kalle ta ba, ta ci gaba da abunda take yi

"Mummy kin kyale ni"

"Ki koma kiyi sallama" abunda ta ce mata kenan

Sai da ta turo baki kafin ta koma waje ta sake shigowa da sallama, Mummy ta amsa, sannan ta

ce "ina gaya miki ki daina shigo mun ɗaki ba sallama, duk in da zaki shiga kar kiyi sallamar,
amma dai ɗaki na dole sai kinyi, wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da zan sake yi miki
magana"

"Ai mantawa nake yi"

"Dole za ki manta tunda ba ki ɗauke shi da muhimmanci ba ai... Kin kori na ashirin ɗin? "

"Ni ban kore shi ba"

"Kenan yayi miki? "

"Allah ya kiyaye, da wani ƙaton kan shi ɗin zai mun? "

"Hmm, Allah ya kyauta"

"Mummy ina so zan fita ne dan Allah"

"Zuwa ina? Ke ba kya da aiki sai yawo wai? "

"Mummy i'm sorry, ba yawo zan je ba, Ikram ce za ta je shopping shi ne ta kira ni ko zan je sai
mu tafi tare"

"Ai saboda ta san ba kya da aiki sai na yawo shiyasa ta ce ki raka ta, to ba za ki je ba"

"Mummy dan Allah.... "

A tsawace ta ce "na ce ba za ki je ba ko!! Ki fita ki bani wuri"

Fashewa tayi da kuka, ta fita da gudu, Mummy ko kallonta ba tayi ba ta ci gaba da aikinta

Kusan minti goma sai ta fito, ta na kai wa wurin ɗakin Sunaiha ta ji tana waya

"Iky ki je kawai ba zan tafi ba"

"Amma shi ne kika ɓata mun lokaci kin san ba za ki tafi ba?"

"Mummy ce ta hana ni shiyasa, kin ga kuwa dole zan zauna"

"Shikenan"

Ta kashe wayar tana share hawaye, duk yanda Mummy ke mata ba wai dan bata jin haushi ba
ne idan ta ga ran Sunaiha ya ɓaci, tana mata wasu abubuwa ne saboda ta gyara rayuwarta

Shiga ɗakin tayi ta ce "me kike yi? kuka? "

Shiru tayi ba ta ce komai ba, Mummy ta sake cewa "saboda na hanaki zuwa shopping ɗin ne? "

Ta ɗaga mata kai tayi tana goge hawayen da ya gangaro mata, Mummy ta ƙarasa kusa da ita ta
ce "yi shiru to ya isa, ba na so yawonki yayi yawa ne Sunaiha, zaman ki a gida ya fiye miki,
amma tashi ki tafi kar ki daɗe kinji ko"

Daɗi ta ji, ta ce "to Mummy na, na gode, yanzu zan dawo"

"To Allah ya kiyaye"

Toilet ta shiga ta wanke fuskarta, sannan ta fito ta ɗauki mayafinta ta fita bayan ta kira Ikram ta
ce ta jira ta


A wannan ɓangaren kuwa, wani katafaren parlour ne mai girman gaske wanda aƙalla za'a iya
cire bedroom biyu manya a cikinshi, set ɗin kujeru biyu ne a ciki, ko wane da na shi ɓangaren,
da carpet ɗin shi, ɗaya royal ne ɗayan kuma normal cushions ne, parlourn ya haɗu ƙarshen
haɗuwa, abun sai wanda ya gani
Manyan mata ne su uku a zaune kan cushions ɗin, kana ganinsu za ka fahimci iyaye ne, sai dai
ko wacensu fuska sumul, alamun hutu, sai list ɗin kayayyaki suke ta faman yi, daga ɗayan
ɓangaren kuma ƴan mata ne su biyar kan royal cushions, gaba ɗayan su ba za su wuce
shekaru sha takwas zuwa ashirin ba, kaya ne a gabansu kan center table, atampopi, laces da
materials, suna ta dubawa, a taƙaice dai kallo ɗaya zaka yi musu ka fahimci shirye-shiryen biki
suke yi

Ɗaya daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login