Showing 123001 words to 126000 words out of 146814 words
kuma ba na so, that's your Sister"
Murmushi yayi ya ce "My Jewel is no one rather than Sunaiha"
Buɗe ido tayi ta ce "Sunaiha? Your wife?"
"Of course yes"
"Sadeeq let's be serious, Sunaiha ita r Jewel ɗinka, then why the hatred? A sani na ba ka
sonta, wanda hakan ya sa nima ba na sonta, why did you change your mind all of the sudden"
"I haven't change my mind or my love, ita ɗin ce dai tun farko, kuma ita ce har yanzu, kuma
ita ce har abada"
"But i'm confused"
"And i will clear up the confusion"
Labari ya fara bata tun daga farkon haɗuwarsa da Sunaiha har sonta da yayi ta yi, har plan
ɗin da suka yi da Anty Sadiya kafin auren, har dai zuwa ƙarshe, zuwa yau ɗin nan da suka
shirya
Shiru Anty Saudat tayi ba ta ce komai ba, ya ce "why are you silent? Kin ce fa za ki so ta, ko
ba za ki iya ba nima in haƙura da ita?"
"A'a Sadeeq, ina tunanin abunda na mata ne haɗuwarmu ta ƙarshe, ta ya zan sake fuskantar
ta har in ba ta haƙuri, kai ma na san you feel bad for that"
"Come on Sister, ni ba abunda na ji, saboda na san son da kike wa ƙaninki ne yasa kika taya
shi ƙin abunda ba ya so"
"But you love her Sadeeq"
"Amma ai ba ki san da hakan ba, yanzu kuma da kika sani sai ki taya ni sonta, ita ma
Sunaiha i'm very sure ta yafe miki"
"How are you sure about that"
"Na an ba za ta so ni sannan ta ƙi Yaya ta ba"
"Sai na ji hakan daga bakinta, bari in nemi permission, yanzu mu tafi ka kai ni in bata haƙuri,
bayan magrib sai ya je ya ɗauko ni"
"A'a ba za'a yi haka ba, ki bari sai gobe, da kaina ma zan nema miki permission ɗin"
"Meyasa, haka nace dai, goben ya fi kamata ki ba ta haƙuri"
"To shikenan as you wish"
"Aha, i'm going" suka yi sallama sannan ya wuce
Yana shiga mota ya kira layin Muhsin, bugu biyu ya ɗauka, suka gaisa sannan ya ba shi
labarin sun shirya da Jewel
"Congrats Dude, finally dai everything is back to normal"
"In sha Allah, yanzu ka san me, ina son ganinka, so that we can plan for tomorrow"
"Plan?!....oh yeah, na tuna, no delay kenan" ya faɗa yana dariya
"Eh mana, kai ma ka san na daɗe ina jiran wannan ranar"
"Haka ne, amma ka nemi Sharif da su Saif, saboda ina tunanin gobe zan tafi America kuma
in wuce Singapore, dama ina so in kira ka in gaya maka"
"No excuse Buddy, ba ruwa na, i just need you"
"Ka gane mana, yanzu ma booking flight zan yi fa"
"I don't care, i just need you kawai na ga maka"
Numfashi Muhsin ya sauke ya ce "shikenan, da kai da mai martaba idan kuka so abu dole sai
mutum yayi, ina dai bayan magrib ne komai, to zan nemi flight ɗin ko da na 11pm ne ko 12pm
idan zan samu, dan dai gobe zan bar ƙasar nan, abu ne da ya shafi aiki na"
"Whatever dai, tunda har za ka tsaya, thank you, zan zo yanzu in same ka" ya faɗa yana
dariya
"Sai ka zo, da wani kanka a wurin"
"Na dai ji" ya kashe wayar yana dariya...........
♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️
*LIKE*
*SHARE*
*COMMENT*
♦️♦️♦️
*ƳAR SENATOR*
♦️♦️♦️
_Full of Arrogance, Ego, Jealous And_ _Love_
*CREATED AND WRITTEN*
_BY_
*UMMEETA*
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
مسِب الله نمحرلا ميحرلا
~~~~~~~~~~~~~~~~
_A smile of a lover is joy and happiness, A smile of a strong person is confidence, A smile of a
child is contentment, A smile of a man is love and strength, A smile of a women is fondness and
appreciation, A smile of a mother is acceptance and gratification A smile of a father is safety, A
smile of a rich person is optimism, A smile of a weak person is praise and thanksgiving, A smile
of a poor person is satisfaction....So let's keep smiling, NO CONDITION IS PERMANENT_
**Page 81&82**
Bayan magrib, Sameer da Sauban suna parlourn su, su na fira, Sauban ya ce "yawwa
Sameer, wai sai yaushe za ka gaya wa Sultana abunda ke ranka ne? Ka ce sai mun gama
exams, to yau mun gama ai"
Sameer ya numfasa ya ce "nima ban sani ba Sauban, ina sonta sosai ka sani, amma wallahi
haka nake gani kamar ba za ta so ni ba, ka san yanda muke da ita a gidan nan kullum cikin
faɗa"
"Haba mana, ai kowa ya san wannan ba faɗan gaskiya kuke yi ba, kawai kuna tsokanar juna
ne, dan Allah kar ka bada maza mana, kawai ka gaya mata, idan ba haka ba kana zaune a
gidan nan za ka ga mutane sun zo neman aurenta"
"Ban son mugun baki fa, shikenan zan gaya mata"
"Wace ce za ka gaya wa? Kuma me za ka gaya mata?" Abunda Sultana ta faɗa kenan kafin
ta samu wuri ta zauna
Kallonta suka yi a tare dan a tunaninsu ta ji me suke cewa, Sauban ya ce "yaushe kika fara
shiga ɗaki ba sallama kuma Sultana?"
Shagwaɓe wa tayi ta ce "sorry, zan yi sallamar ne na ji ana cewa za'a gaya mata, wace ce?"
Sameer ya ce "ai dama gulma ba zai bari ki samu yin sallama ba, ana ganin Sajida na da
gulma, kin ma fi ta ai"
Sultana ta ce "eh ɗin anyi, ai kai ma gulmar wata kake yi yanzu" ta ƙarasa tana murguɗa
mishi baki
"Zan cire miki baki idan kika sake murguɗa shi"
"Ka shirya zaman kotu kuwa, saboda ina da Ya Safwan"
"Ba dai kin iya jan magana ba, sai ki wani ce kina da Ya Safwan ko!?"
"Eh, ni na san wata rana Ya Safwan sai ya tsaya mun a matsayin Lawyer na, kuma zai yi
nasara, ehe"
Sameer ya jinjina kai ya ce "ai dama wata rana kam hakan za ta faru, saboda rashin jin nan
naki sai ya ja an kai ki ƙara"
"Zan kai ka ƙara dai, saboda takura mun da kake yi da shanye mun ice-cream idan na ajiye"
"An shanye ɗin, ki ɗauki mataki"
"Zan ɗauka ai very soon"
Sauban ya girgiza kai ya ce "kai dan Allah, enough! Wai ku ba kwa da aiki ne sai na faɗa,
kullum"
Sultana ta ce "ai shi ke fara ja na, kuma ni ba ma wurin shi na zo ba"
"Ai dama me zai kawo ki wuri na?" Cewar Sameer
Sauban ya ce "ƙyale shi, gaya mun, menene?"
"Ya Sauban system ɗinka za ka ara mun"
Sameer ya ce "aikin kenan ai, daga ara mun system, ara mun wayarka, ka mun VTU, ka mun
transfer, shikenan fa aikinki, kai kuma dan ba kada wayo sai ka yi mata abunda duk tace, ban
ga amfanin kuɗin da ake sa musu each and every month ba"
Sauban ya ce "ba ruwanka dai, kana da sa ido"
Sultana ta ce "ƙyale shi dai, idan kuma wani yayi ya ce zai yi magana"
Muryar Abba suka ji yana cewa "ku da ba kwa da sa idon, ku tashi ku bamu wuri zan yi
magana da Sameer"
Dariya suka yi a tare, Sameer ya ce "Abba, ai da kira na ma kawai kayi sai in zo"
Abba ya ce "sau biyu fa na kira wayarka ba ka ɗaga ba"
Dubawa yayi, ya ce "oh, yi haƙuri Abba, silent na saka wayar na manta, kuma wannan
talkative ɗin ta dame mu bare in ji vibration ɗinta"
Sultana ta wani ƙara haɗe tana kallonshi, Abba ya ce "kafin ki samu abun faɗa, fita ku bamu
wuri, Sauban ja wannan shirmammiyar ku wuce"
Murmushi Sauban yayi sannan ya sa ta gaba suka wuce. Zama yayi kafin ya nuna wa
Sameer kusa da shi ya ce ya zauna, ba musu ya zauna, ya ce "Abba lafiya?"
"Kwantar da hankalinka Sameer, lafiya ƙalau.....wato Sameer, zuwa yanzu na san kayi
girman da za ka iya fahimtar abunda malam bahaushe ke cewa zo mu zauna, zo mu saɓa, ko?"
"Eh Abba na sani"
"To me ka fahimta da hakan?"
"Abba kowa ne zama ana samun matsala, duk yanda zama yayi daɗi kuwa, duk yanda ake
son juna wata rana sai an ɓata ran juna, hakan na faruwa tsakanin ƴan uwa, abokanai, masoya,
tsakanin ɗa da iyayensa, har tsakanin mata da miji ma"
Jinjina kai Abba yayi ya ce "alhamdulillah, na ji daɗin bayanin nan naka...um, Sameer"
"Na'am Abba"
"Ɗazu mahaifinku da mahaifiyarku sun samu saɓani kaɗan, wanda hakan ya jawo har shi
mahaifin naku ya ce wa Mominku ta tafi gida"
"Subhanallah, dama Momi ba fita tayi ba? I thought ta fita ne ai shiyasa ban wani damu ba,
amma Abba me yayi zafi har haka?"
"Sameer, ba abunda za ka ɗaga hankalinka ba ne, saboda ba sakinta yayi ba, ya ce ne ta tafi
gida sai ya neme ta...na gaya maka haka ne saboda kai ne babba a cikin ku huɗu, kuma ba na
so ka ji maganar wani wuri dan ban san a yanda za ka ji shi ba"
"To amma Abba me ya haɗa su har haka?"
"Idan lokacin da ya kamata ka sani yayi, da kai na zan gaya maka idan har da yiwuwar sai ka
sani, ba na so Safna da Sajid su ji wannan maganar, a bar shi a tunaninsu kawai ta fita, Salma
kuma za ka iya gaya mata ta sigar da za ta fahimta"
Shiru Sameer yayi kafin ya ce "shikenan Abba, Allah ya kyauta ya ba su haƙuri, kuma ya
daidaita su"
"Ameen ya Allah" daga haka ya fita
Kusan mintuna biyar yana zaune shiru bayan fitar Abba, sannan ya ɗauki waya ya kira
Salma, bugu ɗaya ta ɗauka
"Salma ki zo part ɗin mu yanzu"
"Haba Ya Sameer, sai yanzu da ka san ina kallo shi ne za ka kira ni, an fara series ɗin nan
wallahi" magana take kamar za tayi kuka
"Magana ce mai muhimmanci da amfani, ki bar kallon nan, ai ana maimaitawa"
Tana turo baki ta ce "gani nan" ta kashe wayar, sai da ta gama kallon wannan scene ɗin kafin
ta tashi ta fita da gudu
Zama tayi kusa da shi tana kallon yanayinsa, ta ce "lafiya dai? You look somehow"
Numfashi ya ja kafin ya mata bayanin komai kamar yanda Abba ya gaya mishi, a tsanake. Ta
ce "dama Momi ba fita tayi ba? Da na tambayi Umma fa ce mun tayi ta fita"
"Nima haka nayi tunani, amma ba na so ki sa abun a ranki sosai, komai zai wuce very soon,
although ba daɗi zama gida ba tare da mahaifiya ba, amma kar ki wani damu kanki, tun da nake
hakan bai taɓa faruwa tsakaninsu ba, so ko ma menene na tabbata Momi ta ɓata mishi rai ne
sosai, amma zai sauko"
Cikin ɓacin rai Salma ta ce "you're talking as if abun bai dame ka ba, ko ma me tayi ai bai
kamata ya kore ta ba a irin wannan matsayin da suka kai, at this age of hers a ce mijinta ya
kore ta? Bai ko duba ƴaƴanta ba? For the first time mahaifi na ya mun abunda ban ji daɗin sa
ba ko kaɗan, kuma sai na ji dalili"
Sameer ya ce "ba kya da hankali ne ko me? Iyayenki ne fa na ce sun samu saɓani ba
ƙannenki ba, da har za ki ce sai kin ji dalili, kan ki ɗaya kuwa? To ko ni da na girme ki ban damu
sai na ji ba, wataƙila hakan ne alkhairi shiyasa ban damu sai na ji ba"
"Dama kuwa ta ya za ka damu tun da ba ka san daɗin mahaifiya cikin gida ba saboda ba
zama kake yi ba, ni kuwa da kullum ina gida sai idan makaranta muka tafi, duk da ba wani
yawan xama nake yi da ita ba, mun fi zama da Hajiya da Umma, amma i can't live in this house
without her, dan haka zan je in same shi"
Gaba ɗaya ta gama ba shi mamaki, shiru kawai yayi yana bin ta da ido har ta fita, ya ce "lallai
Salma"
Tama fita kuwa ɓangaren su Kawu Ƙarami ta nufa, da sallama ta shiga, yana zaune a parlour,
shi kaɗai ya san tunanin da yake yi, ganinta ya sa shi gyara zama ya mayar da hankali kan ta
"Ya aka yi ne Salma?"
Shiru tayi tana tunanin ta in da za ta fara, sannan ta ce "Ina so ne in san dan Allah me ya sa
ka kori Momi? Me tayi har da ka kasa yin haƙuri sai da ka kore ta?"
Kallonta yake yi bai ce komai ba, hakan ya sa ta ɗaga ido suka yi ido biyu kafin ta sauke na
ta, ya ce "Salma, zuwa kika yi ki tuhume ni ko kuwa aiko ki aka yi?"
"Ba aiko ni aka yi ba, zuwan kai na ne, meyas...."
A tsawace ya katse ta, ya ce "keep your mouth shut!!! Ke har kin yi girman da zan aikata abu
ki zo ki tsare ni kina tambaya ta meyasa nayi? Ke ƴa ta ce, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba...
wallahi Salma idan kika sake zuwa mun nan da zancen mahaifinki, sai nayi mummunan saɓa
miki, ashe ba ki da kunya ban sani ba?"
Kanta na ƙi, ta ce "kayi haƙu...."
Sake katse ta yayi a karo na biyu "get out i said, mutumiyar banza kawai...to idan ba za ki iya
zama a gidan ba, ki kwashe kayanki ki bi ta"
Da gudu ta nufi ƙofa tana kuka, tana fita ta ci karo da Sultana, zagaya ta tayi za ta wuce,
Sultana ta dawo da ita, sannan ta rungume ta tana rarrashinta
Sai da ta tabbatar tayi shiru sannan ta ja ta zuwa part ɗin su suka zauna ta ce "Salma na ji
duk abunda ya faru tsakanin ki da Kawu Ƙarami, abu na farko da zan ce miki shi ne kiyi haƙuri,
na biyu kuma, kin aikata ba daidai ba, sam wannan ba tarbiyyarki ba ce, ya aka yi kika bari
mahaifinki yana faɗa kina faɗa? Me ma ya kai ki?'
"Sultana ba ki san meke faruwa bane shiyasa kika ga laifi na"