Showing 30001 words to 33000 words out of 45115 words

Chapter 11 - TRUE LOVE by Princess Meerah

14 Jul 2025

3582

gidan

ya na fita Brian ya ce ma Kevin " kai dai ba ka iya fadin al'heri da bakin nan naka , ga shi yanzu ka bata mishi rai "

" ai gaskiya ce na fada , tun baya kai ne da ba ka tsawatar mishi , ni ban ma san abun da ya ke cikin familyn mu ba "

da sauri Emilie ta dago kai ta ce mishi " no , our family , shi ma ya na cikin familyn mu , ka daina mayar da shi bare , little brother din ka ne "

cike da bacin rai Kevin ya ce " no , ni ba brother di na ne ba , kawai yaron da momy ne ta samu wajen cin amanar Daddy da ta yi "

" Kevin ! " Brian ya fada da dan karfi ya na zaro idanu dan maganar Kevin ta bata mishi rai

shi kuwa Kevin ko a jikin sa sai ma cewa ya yi " why za ka daga min murya ? ai ba karya na yi ba , ba banza ta mallaka mishi duk companyn ta ba saboda na uban shi ne , da a ce ba ta ci amanar ka ba da ba zai zo duniyar nan ba "

a hankali Brian ya kai hannu ya dafe saitin zuciya shi ya na yamutse fuska ya na kallon Kevin cike da takaici

Emilie na ganin haka ta zaro idanu ta na fadin " Daddy , are you okay ? "
murya a disashe ya ce mata " ban ruwa "
ba musu ta dauki ruwa ta mike ta kai mishi a baki ya sha sannan ta sauko shi ta koma ta zauna

wani dan karamin tsaki Kevin ya yi kafin ya ce " I'm sorry maganar ce ta fito haka kawai , amma ba haka na ke tunani ba , i'm so sorry "




MY BOOK IS ₦500
VIA

8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank




💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
__________________

💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞






( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH 💋






GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!




BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM





{P A G E 23 & 24 🕊❤}




Da Brian da Emilie duk babu wanda ya ce mishi ufan , amma har cikin zuciyoyinsu sun ji zafin maganar shi
duk abun nan da Kevin ya fada a kunnen Ayden , dan ya na tsaye bakin kofar da ga baya , bai tafi ba , abun da Kevin ya fada ya kara tabbatar mishi da abun zuciyar shi ke fada mishi na Kevin ya tsane shi , kawai ya na nuna mishi soyayya ne a fili ,
abun nan ba karamin zafi ya yi mishi ba dan har hawaye sai da ya zubar amma da ido guda

a hankali ya kai hannu ya goge sannan ya bar wajen ya yi tafiya shi


🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼


▪MISALIN KARFE 8 NA DARE


▪ESRA ❤🕊


Zaune ta ke cikin parlourn apartment din su ta na sanye da wasu kananan kaya blue ma su mugun kyau , sun yi mugun kama ta ko kamar a jikin ta a ka yi su

ta na zaune ta na latsa laptop din ta cikin konciyar hankali , Safna kuma ta na cikin bedroom din ta ta na barci dan tun safe ta ke jin jikin ta ba dadi
ta na a haka ta ji an bubuga musu kofa a sanyaye
slowly Esra ta dago kai ta kalli saitin kofar , kafin ta rufe laptop din ta , ta ajiye saman table ta mike a hankali ta nufi kofar ,l
ko tsoro babu ta bude kofar
ta na budewa idanun ta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar fuska a marairaice , ya na sanye da kayan shi na safe

idanun shi na sauka saman ta ya ji zuciyar shi ta yi wata muguwar bugawa ya rasa dalili , har wani dan zaro idanu ya yi kadan ya na kallon ta kamar bai san ta ba

ita kuma ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " na zata ba za ka zo ba "
shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na kallon ta babu ko kiftawa

ta na ganin haka ta juya ta na fadin " tun da ba za ka ce komai ba shigo , na shirya maka duk abun da za ka bukata a kitchen "

ba musu ya biyo bayan ta ya shigo gidan kafin ya tura kofar ya rufe
ya na ida shigowa ya gan ta zaune saman sofa ta na rike da laptop din ta
kawai sai ya yi tsaye ya tsare ta da ido babu ko kiftawa

ita kuwa duk hankalin ta na kan aikin ta , ta ma manta da shi
lokaci guda kawai ta ji duk ta tsargu kamar a na kallon ta
wani cool murmushi ta saki kafin ta dago kai ta kalle shi , cikin zolaya ta ce " Ba ni za ka girka ba , ga kitchen din cen , akwai aikin da na ke yanzu idan na ida zan zo na taya ka "

a hankali ya gyada mata kai kafin ya juya ya nufi Kitchen
da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta juya ta ci gaba da aikin ta
Kim kuwa ya na shiga kitchen din ya tsaya ya na kallon ingredients din da ta jera mishi saman counter
a hankali ya juya ya nufi fridge ya bude ya fara bin abun da ke ciki da kallo
cen ya hango fish , Potato , carrot , peas , cikin irin ledodin nan na deep freeze
bai tsaya bata lokaci ba ya kai hannu ya dauki Fish , potato da carrot , ya dawo ya ajiye saman counter , sannan ya juya ya dauki green pepper , da chilli pepper sannan ya rufe fridge din

a hankali ya nufi Oven ya bude ya fiddo tray din ciki ya ajiye saman counter , kafin ya juya ya fara bude closet na sama daya bayan daya da allamun ya na neman wani abu
sai da ya bude closet na biyu sannan ya ga wasu kwalaben spices , hannu ya kai ya dauki thyme , rosemary , garlic powder , onion powder ya juyo ya ajiye geffen tray din oven

sannan juya ya bude closet na gaba ya fiddo Aluminum, ya juya ya ciro ya shinfida saman tray din oven
bayan ya shinfida ya juya ya nufi mixer din da ya hango dayan geffen , ya bude ya fiddo bowl din , ya zuba green pepper , chilli pepper Thyme, rosemary garlic da onion , ya zuba salt da black pepper , ya zuba oil ya koma ya yi mixing din su ya yi marinade

sannan ya fiddo bowl din ya dawo ya wajen counter din ya ajiye
ya kai hannu ya dauki fish da potato da carrot ya Zube su saman tray din oven ya dauki marinade din na ya zuba a sama ya juya ta shiga cikin kowane , sannan ya dauki tray din ya juya ya saka cikin oven din ya riga ya kunna ya yi zafi sannan ya rufe

ya dawo ya tattare ledodin ya zubar a trash ya wanke bowl din mixer din ya mayar
ya na juyowa ya ga Esra tsaye bayan shi ta na sakin wani kyawatencen murmushi

ba karamar razana ya yi ba dan har wani dan baya ya yi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za mu yi yanzu ? "
a hankali ya karaso gaban counter din ya tsaya ya na fadin " oven nawa gare ku ? "
" biyu ne " ta fada ta na karasowa geffen shi ta tsaya
" okay , ki na da puff pastry ? Apple , cinnamon , cane sugar , lemon "
cikin rudu ta ce mishi " me kuma za ka yi da su ? "

sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Apple pie , ko ba ki so ? "
dan zaro idanu ta yi ta na fadin " no , da gaske , shi ne favorite dessert di na "
slowly ya juyo ya kalle ta sai sakin murmushi ta ke , shi kan shi bai san lokacin da ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na ce mata " ni ma haka "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta juya ta nufi fridge ta fiddo mishi duk abubuwan da ya zano mata ta dawo ta ajiye gaban shi ta na fadin " amma fa ban da mold din yi pie "

" no wonder , wadda za mu yi ba ta bukatar mold , it's simple and delicious , cikin 30 minutes za ki iya yin ta "

gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta ce " okay prof , bismillah ina kallon ka "
wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " yawwa student , yanzu kawo min tray din gudan oven din , sannan ki kunna shi saman 180° "

" Yes Chef " ta fada cikin zolaya kafin ta juya ta nufi dayan oven din
maganar ta gaskiya ta ba ta shi dariya har wani murmushi ya ke saki shi kadai
fiddo tray din ta yi ta kunna oven din kafin ta juya ta ajiye mishi gaban shi

ta na ajiye wa ya juya ya nufi gas cooker dama pan din na ajiye a sama , kawai sai ya kunna , ya dawo ya dauki Apples din ya yanka su kana kana sannan ya zuba cikin pan din da ta riga ta yi zafi , ya zuba cane Sugar din da cinnamon da juice din lemon kadan , ya jujuya su , su ka shiga cikin juna har apples din su ka fara yin laushi

ya na ganin hakan ya kashe ya dauko pan din ya juyo da ita ya ajiye saman counter
sannan ya juyo ya kalli Esra ya ce " ina fatan ki na ganin abun da na ke ? "
" ni fa kaina 10000GB ne , duk na yi recording abun da ka ke yi "

wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya juya ya dauki puff pastry din nan , ya shinfida saman tray din oven , sannan ya dauki knife ya raba shi gida 8
da ga haka ya dauki spoon ya fara debo apples din ya zuba saman parts 4 , sannan ya dauko wadancen da bai zuba ba a kai ya rufe su da su , ya dauki fork ya danne bakunan su daya bayan daya dan kar su bude

ya na gamawa ya matsa gefe ya kalli Esra ya ce " za ki iya sakawa a oven "
dan zaro idanu ta yi ta na fadin " ban gane ba , har mun ida ? "
gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba
" mun yi sauri fa " ta fada ta na daukar tray din ta saka a oven ta rufe kafin ta dawo geffen shi ta tsaya ta na fadin " minti nawa zai yi a ciki ? "

" juste 20 minutes " ya fada ya na kai hannu ya dauki spoon ya debo apples ya kawo saitin bakin Esra allamun ta ci

wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta bude baki a hankali ta karba ta na kallon shi
gaskiya ba karamin dadi abun ya yi mata ba har wani dan lumshe idanu ta ke yi
sai da ta gama cinyewa sannan ta kalle shi ta ce " gaskiya ya yi dadi , har na matsu ya gama "

wani cool murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ke ce mutum ta farko da ta ci abun da na girka kuma ya ce ya yi dadi "

" hmmmm , yanzu mintina nawa za mu jira ? "
" just 20 minutes " ya fada a takaice

wani dogon nunfashi ta ja ta na saukewa a hankali kafin ta ce " Yanzu me za mu yi ? "
sai da ya dan jinkirta kafin ya ce mata " Watch cartoon "
dan zaro idanu ta yi a hankali ta na fadin " cartoon ? da wannan shekarun naka ? "
" yeah , har yanzu ni baby ne "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kai hannu ta ja mishi kumatun shi na dama ta na fadin " yeah , you are a big baby "

shi kan shi maganar ta sai da ta ba shi dariya , har sai da wadanan fararen hakwaren nashi su ka fito
a hankali ta janye hannunta ta na kallon face din shi gwanin burgewa tun da ta ke ba ta taba ganin murmushi mai kyau irin nashi ba

wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta na fadin " mu je na saka maka , Big baby kawai "

ba musu ya bi bayanta su ka koma parlourn , su ka zauna sannan ta kunna mishi Tv , ta ba shi remote din sannan ta dauki laptop din ta ta ci gaba da aikin ta

cikin nitsuwa Kim ya fara sauya chanel din har ya samu chanel din da su ka saka cartoon
kamar wani karamin yaro ya tsaya ya na kallo amma ta wutsiyar ido Esra ya ke kallo
ya na a haka kawai ya fara jiyo Muryar ta sama sama kamar ta rero waka

shi ko karatun Qur'ani ne ta , ta na karanto suratul Mariam cike da nitsuwa ga Muryar a sanyaye mai dadin sauraro

duk da bai san abun da ta ke fada ba amma ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi , irin sanyin da bai taba ji ba
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juyo ya kalle ta da kyau ya ce mata " wace waka ce wannan ki ke ? "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login