Showing 15001 words to 18000 words out of 45115 words
bullewa ? ban gane ba "
" ka fi kowa sanin halin yarinyar ka , idan ka ce za ka matsa mata da maganar ba za ta taba amincewa ba , ni ma ina son ta yi aure but ya kamata mu ba ta damar zabar wanda ta ke so ba mu cilas ta mata ba , a cikin 21st century mu ke , an daina wannan hadin auren da a ke "
" ni dama na san ba za ki taba amincewa da wannan maganar ba Aysha , amma in ba haka ba ba za ta taba yarda ta yi aure ba , ki na gani US ta gudu dan kawai kar mu yi mata maganar , amma ina jiran ta dawo auren Yasmina , ba zan bari ta koma ba "
wani dogon nunfashi Aysha ta ja kafin ta ce " ka yi dai tunani mai kyau , ba dan ka na son abotar ku da Wadi ta daukaka za ka hukuntar da yarinyar mu , kuma ba na tunanin za ta amince da auren nan , ni dai zan so ka zauna ka kara tunani , rayuwar ta ce baki daya ka ke shirin yin wassa da ita "
shiru Engineer ya yi bai ce mata komai ba ya na ci gaba da latsa wayar shi , shi dai a wannan maganar ba gudu ba ja da baya duk abun da a ka yi sai ya yi auren Esra da Irfan dan shi ne babban burin shi a rayu
________________________________________
▪US ( NEW YORK CITY )
▪GREENWICH STREET
a hankali ta ke tafiya cike da san'da kamar barauniya , ta na sanye da wata gown white color mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta Purple a kai , ta na rataye da bag din ta kamar kullum
tafiya ta ke ta na waiwaye kar a je akwai gangs din da su ka fito a wannan lokacin
cikin sa'a ko ba ta hadu da kowa ba har ta karaso wajen wannan kangon da Kim ke rama
ta na shigowa ko ta hango shi cen zaune saman wasu box , ya na sanye da wani short white color da shirt Red color babu takalmi a kafafun shi , ya na rike da taba ya na sha cikin konciyar hankali
a hankali ta karaso wajen ta na yi mishi sallama duk da ta san ba zai iya amsa mata ba
ko sannu bai ce mata ba ya ci gaba da shan tabar shi
a sanyaye ta ce mishi " Hi , Good morning "
" Hi ! " ya fada a takaice ya na kai tabar a baki ya kara sha
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " Kim , tun da safe ka na shan taba ? ka yi breakfast ko ? "
a hankali ta saki tabar ya sa kafa ya murje ta , ko zafin wutar bai ji ba , Esra kuwa har wani dan lumshe idanu ta yi ji ta yi kamar ita ta taka wutar
shi kuwa ko ajikin shi kamar ba wuta ba ce ya taka
a sanyaye ya ce mata " wai me ki ke yi a nan ? a sani na chocolate ne ya hada mu , kuma kin ba ni shikenan , why za ki takura min ? "
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ni kai na ban san abun da ya sa na takura maka haka ba "
" to ki rabu da ni mana " ya fada ya na kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo wata sabuwar tabar
da sauri ta kai hannu ta buge tabar ta na fadin " Please , stop , ka san irin illar da abun nan za ta yi maka ba , tun safe ka na sha "
" breakfast ne na ke " ya fada ya na sake kai hannu ya fiddo sabuwar tabar
yanzu ma hannu ta kai ta buge ta na fadin " mu je na saya maka breakfast to "
" da kuma tabar da ki ka buge min " ya fada ya na kai bayan trush ya fiddo wasu sneakers purple ma su kyau , ya saka a kafafun shi kafin ya mike tsaye
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " na yarda , amma bisa sharadi guda "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " wane sharedi kuma ? "
" can i be your friend ? " ta qarashe maganar ta na mika mishi hannu
kallon hannun nata ya yi na dan lokaci kafin ya girgiza mata kai a hankali ya ce " kin taba ganin duhu da Haske sun hadu a waje guda ? ni kamar duhu na ke , ke kuma haske , ba za mu taba kasancewa a tare ba , haka tsarin rayuwa ya ke "
" to ka ba ni dama , na mamaye duhun rayuwar ka da haskena , ka ba ni dama na sauya wannan tsarin , kai ma ka na da izinin samun abokin da zai taya ka kuka , wanda zai taya ka dariya , wanda zai sauya maka rayuwa , ka ba ni damar kasancewa wannan abokin "
sai da ya kare mata kallo da kyau kafin ya ce mata " shikenan , na yarda mu zama abokai just for two weeks , cikin satin nan biyu in har ki ka yi nassarar sauya min rayuwa , abotar mu za ta kasance ta har abada "
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " Eh , na yarda just two weeks , zan sa ka daina shan wine da taba , zan gwada maka colors din rayuwa , idan ban yi nassara ba zan kyale ka har abada "
" All right ! " ya fada ya na riko hannunta su ka yi musbaha
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan , my new friend , mu je na saya maka breakfast , ina da sauran lokaci kafin karfe 8 ta yi ni ma zan samu na yi breakfast "
bai ce mata komai ba ya janye hannun shi ya fara takawa zai bar wajen
da sauri ta bi bayan shi ta na sakin murmushi su ka bar wajen , sai tafiyar shi ya ke cike da nitsuwa , ya na kallon gaban shi
ita dai Esra sai satar kallon shi ta ke ta wutsiyar ido
a haka har su ka karaso restaurant din da Safna ke aiki , cike da mamaki ta shiga restaurant din ta na tunanin yadda a ka yi ya san wajen nan
amma ba ta ce mishi komai ba , su ka shiga restaurant din , su ka zauna saman chair
sai da su ka zauna sannan Esra ta fara bin wajen da kallo , ta ga su kadai ne babu kowa a wajen , sai servers din da ke kula da wajen
a ta mike ta na fadin " bara na yi mana order "
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta fara takawa ta nufi reception
ta na barin wajen ko Adrian ya shigo restaurant din , ya na sanye da wasu suit bakake , hannayanshi rike da wasu paper da laptop , ya na taku cike da nitsuwa
tun da ya shigo Kim ya tsare shi da ido babu ko kiftawa , har ya nufi VIP space ya zauna , ya bude takardun shi ya fara aikin shi
a hankali ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ya kauda kan shi , dai'dai lokacin da Esra ta dawo wajen ta zauna saman chair din ta , ta na fadin " hope ka na shan coffee ? "
" Coffeeeeee ? , na yi miki kama da me shan coffee ? may be ice tea zan iya sha , amma ban da coffee gaskiya " ya kai karshen ya na kauda kai
wata yar karamar dariya ta yi , ta na shirin magana idanun ta su ka sauka saman Adrian da ke zaune bayan Kim , a VIP space
nan take yanayin face din ta ya sauya , ta karewa Adrian kallo da kyau , nan take kalaman Safna su ka dawo mata a kai na wani da ke zuwa ko wace safiyar monday restaurant din
amma ya a ka yi , yau Friday ba monday ba
da sauri ta kai hannu cikin bag din ta ta fiddo wayar ta ta saita Kim akwai ta danna ta yi mishi pic , ga shi ko shi ma ita ya ke kallo pic din sai ya yi kyau gwanin burgewa
wani dan karamin tsaki ta yi ta na fadin " Kim , yi gefe guda please "
ba musu ya yi gefe kafin ya juya ya ga abun da ta ke son gani
a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ga Ta na yi wa Adrian Pic
cikin rudu ya ce mata " celebrity ne ? why ki ke yi mishi pic ? "
ba ta ce mishi komai ba ta sauko wayar ta , ta meda cikin bag din ta , dai'dai lokacin da Server ya iso wajen rike da tray din order da Esra ta yi , ya shirya musu abincin saman table din su sannan ya juya ya bar wajen
ya na barin Wajen Kim ya kai hannu ya dauki Fork ya fara cin toast din da a ka shirya da Eggs ,
ita dai Mug din coffeen kawai ta dauka ta fara sha ta na kallon shi
ya na cin abincin cike da nitsuwa , ga shi ko yadda ya ke aiki fork din sai ka rantse da Allah shi ne jikan Sarauniyar UK Elizabeth
amma ita duk da idanun ta na saman shi , hankalin ta na kan Adrian , shi ko bai ma san abun da ke faruwa ba , sai aikin shi ya ke cikin konciyar hankali
a haka har Kim ya kammala breakfast din , ya sha ruwa ya na yi mata magana amma ba ta ji shi ba
a hankali ya kai hannu ya kyasta mata yatsu saitin face din ta
a razane ta dawo cikin hayacinta ta kalle shi ta na fadin " What ? me ya faru ? "
" za ki yi late wajen aikin ki " ya fada dan ya na son ya dan tsoratar da ita
a razane ko ga dauki bag din ta ta mike ta na fadin " wayyooo ni Esra na shiga uku wajen Sir Kevin , na tafi "
" wait , bari na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye
ina ko sauraron shi ba ta yi ba ta nufi kofar fita , Kim kuma , a hankali ya juya ya kalli Adrian kafin ya juya ya bi bayan Esra su ka bar wajen
su na barin wajen ko Safna ta shigo sanye da uniform din ta
bangaran Esra kuwa , tafiya ta ke da sauri da sauri , Kim na biye da bayanta ya na kiran sunanta
amma ba ta tsaya sai da ta karaso one world trade center sannan ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ta tsaya
a hankali ta juyo ta kalli Kim da ke tsaye bayan ta ta ce mishi " na tafi sai mun hadu an jima "
gyada mata kai kawai ya yi kafin ta juya ta shiga hall din
ta na shiga ko Motar Kevin ta yi parking bakin hall din ya fito sanye da wasu suit purple ma su mugun kyau , ya na sanye da glass a idanun shi
kamar an kira sunan shi kawai ya juya ya kalli saitin da Kim ke tsaye
nan take su ka yi ido hudu , Kim na ganin hakan ya juya cikin nitsuwa ya bar wajen
da kallo Kevin ya raka shi har sai da ya kurewa ganin shi sannan ya juya ya shiga Building din
▪ADRIAN
sai da ya yi wajen good 30 minutes bayan fitar su Esra kafin ya jiyo Muryar Ayden ya na fadin " har yanzu ba ka gama ba mu tafi ? "
wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya dago kai ya kalli Ayden
ya na tsaye gaban table din , ya na sanye da wasu Tracksuit white color ma su mugun kyau , rigar na da hula
ya saka wasu sneakers green kalar gashin kan shi , amma ba ka iya ganin face din shi dan ya saka Face mask , da wasu glass kamar medical glass , amma su na dan duhu kadan ba ka iya ganin idanun shi
" tun dazu kai na ke jira , ya ? a kawo maka coffee ? " Adrian ya fada
girgiza mishi kai Ayden ya yi a hankali ya na fadin " No , idan ka gama tashi mu tafi kawai "
" okay mu tafi " ya fada ya na tattare papers dinshi , waje guda sannan ya mikawa Ayden laptop din shi
ba musu Ayden ya karbi laptop din , su ka fara takawa a tare su ka bar wajen
har su karaso wajen Table din da su Esra su ka zauna kawai sai ya ji ya taka wata paper
cak ya tsaya ya na kallon paper din kassan kafar shi
a hankali ya sunkuya ya dauki paper din ya na kallon ta kafin ya kalli table din da su Esra su ka zauna , har yanzu ba a gyara table din kawai sai ya yi tunanin ko na wanda ya zauna a wajen ne
da sauri ya taro Ayden da ya nufi kofar fita ya na fadin " Ayden wait two minutes please "
a hankali Ayden ya juya , ya gyada mishi kai allamun okay
wani dan karamin murmushi Adrian ya yi kafin ya nufi reception ya na fadin " excuse me , wanda su ka zauna a cen sun manta wannan , da allamun kuma ya na da mahimanci "
wani cool murmushi Safna ta sakin mishi kafin ta ce " okay , na gode , za mu yi kiran su mu mayar musu "
" okay " Adrian ta fada , ya na shirin dago paper din na hannun shi su ka kubce
da sauri ya sunkuyo ya dauki takardun shi kafin ya mikawa Safna paper din da ya tsinta kafin ya juya ya bi bayan Ayden su ka bar wajen
kallon paper din da kyau Safna ta yi , cen kassa a geffen dama ta ga an rubuta ONE WORLD TRADE CENTER , allamun da ga companyn su Esra paper din ha fito
a hankali ta juya ta kalli dayar receptionist , cikin sanyin murya ta ce mata " Please duba min cikin register First client din mu na yau , minene sunan shi "
ba musu ta duba register din gaban ta kafin ta ce " Esra yahaya , around 7h20 su ka shigo wajen nan "
" okay , na gode " Safna ta fada ta na murmushi kafin ta ninke paper din ta saka cikin bag din ta
bangaran Adrian kuwa ya na fitowa ya tardo Ayden zaune cikin wata dankareriar mota fara kal ta ji da gani , irin motar da sai wane jikan wane ke iya shigar ta ba banza bare ba , dan tayoyin ta ma sun isa daukar ido
kai tsaye wajen driver ya nufa ya shiga dan ya San halin abokin nashi , ba ya son tukin mota , idan kuma ya ce zai yi tukin to tabbas mutuwa zai tunkara dan ba karamin gudu ya ke ba kamar zai tashi sama
tada motar Adrian ya yi ya na fadin " ina za mu je ? "
cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " One world trade center , ina son na yi wa kevin magana a kan tafiyar da za mu yi Washington dan ganin sabon building din da mu ke shirin budewa a cen , ina son mu ware Space din restaurant , at least ina son mu yi two type na restaurant a ciki "
wani dan karamin murmushin geffen fuska Adrian ya yi kafin ya ce " wai me ya sa harkar abinci ke burge ka ? ka na fa cikin Top ten din billionaire din United State of America baki daya "
" na sani , kawai restaurant din ne ke burge ni , yau Friday , ina fatan ka sa a shirya abincin da a ke aikawa gidan marayu ? "
" yeah , ban manta ba , ai ko wace Friday abu na farko da ka ke fara tambaya shi ne Adrian ka sa a shirya abincin da za a kai gidan Marayu ? Adrian ka sa an shirya kayan da za a kai gidan marayu ? Adrian ka tura kudin da na ce ka tura gidan marayu ? wadanan tambayoyin kamar a bakin ka a ka yi su , but ina jin dadin hakan gaskiya , kar ka damu na yi duk wani abun da ka ce "
" okay " Ayden ya fada a takaice
da ga haka ba wanda ya sake ce ma wani ufan har su ka karaso wajen wani traffic light
a hankali Adrian ya yi parking din motar , ya na jiran a ba su izinin wucewa
a hankali ya juyo ya kalli Ayden , ya ga ya lumshe idanunshi ya tafi duniyar tunanin shi
wani cool murmushi Adrian ya saki kafin ya juya ya ce " me ka ke ji in ka na tare da ita ? "
kai tsaye Ayden ya ce mishi " peace " a takaice da allamun ba ya cikin hayacin shi
murmushi mai dan sauti Adrian ya yi kafin ya ce " ka yi a hankali , kar plan din ka ya juye maka "
shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba , da allamun ya lula duniyar tunanin shi bai ma san abun da ya ke