Showing 21001 words to 24000 words out of 45115 words
na ke mutuwar son ki , ki na ji tashi ki je ki shirya yau a restaurant za mu yi diner kuma ni zan biya "
dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " la , da gaske ? duk wannan farin ciki saboda paper ? wannan paper ? "
" hmmm , Safna ba za ki gane ba wlh , ba ki san pression din da Sir Kevin ke daura min ba , kamar ni kadai ce ke aiki a wajen " ta kai karshen ta na tattare takardun ta , ta meda cikin bag din ta da laptop din ta
ita kuwa Safna ta tashi ta shiga corridor ta wuce bedroom din ta
da ga nan ta shiga toilet ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata gown red color mai kyau , ta yi Rowling veil din ta white color a kai
ta na fitowa parlour ta tardo Esra zaune saman sofa ta na sanye da kaya tak tak irin nata
wata yar karamar dariya Safna ta yi ta na karasowa cikin parlourn ta na fadin " hmm , my twins ya a ka yi wannan hadin haka ? "
" ke dai zan tambaya " Esra ta fada ta na mikewa tsaye ta dauki yar karamar bag din ta
murmushi kawai Safna ta yi mata ba tare da ta ce komai ba su ka nufi kofar fita su ka fice a tare su ka rufe part din nasu
______________________________________
▪KIM 🕊❤
a hankali ya ke tafiya saman wani kyakyawan titi , ya na rike da wani gwongwanin kamar na maltina amma ba maltina ba ce
kayan nan dai na safe su ne a jikin shi , amma gashin kan shi a tirje ya ke , ya zubo mishi har gaban goshi ya rufe mishi idanu , ya sunkuyar da kai ya tafiya jiki a mace
a haka har ya karaso wani kyawatencen garden cike da ciyayi , babu kowa a ciki sai tsintsaye
a hankali ya nufi wata fountain fara kal , ya tsaya gaban ta ya na kallon kan shi ta cikin ruwan
a hankali ya sa hannu ya janye gashin da ke gaban goshin shi , nan na ga idanun shi sun yi jazir , sun kunbura da allamun kuka ya yi
wani cool murmushi ya sakin wa kan shi kafin ya bude baki a hankali ya ce " shikenan , haka rayuwar ka za ta kare ? , ka ta so a maraye cikin gidan marayu babu uwa ba babu uba , kuma ka mutu a haka ? ko friend babu sai wine da taba ? why Kim ? why za ka lalata rayuwar ka haka ? , na san da ki na nan haka za ki ce min , but now i'm alone , you're not here with me "
ya na gama fadar haka ya saki kuka a hankali ya na fadin " why ? why za ki tafi ki bar ni bayan kin san ke kadai gare ni a duniyar nan , ya ki ke so na yi yanzu ? " ya na gama fadar ya zube saman guyiwowinshi ya na kuka kamar wani karamin yaro
a hankali ya dago drink din shi ya kai a baki ya sha kadan ka fin ya sauko
ya na kallon kan shi cikin ruwan foutain din ya bude baki a hankali ya fara rera waka ya na fadin " SUNDAY MORNINGS WERE YOUR FAVORITE
I USED TO MEET YOU DOWN ONE WOODS CREEK ROAD
YOU DID YOUR HAIR UP , LIKE YOU WERE FAMOUS
EVEN THOUGH IT'S ONLY CHURCH WHERE WE WERE GOING , OHHHHH
NOW SUNDAY MORNINGS I JUST SLEEP IN
IT'S LIKE I'VE BURIED MY FAITH WITH YOU
I'M SCREAMING AT A GOD I DON'T KNOW IF I BELIEVE IN
CAUSE I DON'T KNOW WHAT ELSE I CAN DO , YEAHHHHHH
AND I'M STEEL HOLDING ON TO EVERYTHING THAT'S DEAD AND GONE
NO I DON'T WANNA SAY GOODBYE CAUSE THIS ONE MEANS FOREVER
NOW YOU'RE IN THE STARS AND SIX-FEET'S NEVER FELT SO FAR
AND HERE I AM ALONE BETWEEN THE HEAVENS AND THE EMBERS
OHH IT HURTS SO HARD FOR A MILLION DIFFERENT REASONS
YOU TOOK THE BEST OF MY HEART , AND LEFT THE REST IN PIECES "
sai da kammala sannan ya kai hannu a hankali ya fara goge hawayen da su ka zubo mishi , ya dago drink din shi ya kai baki ya daga kai sama ya shanye ta lokaci guda kafin ya sauko ya tilla gongwanin cen gefe
murya a disashe ya ce " I really missed you " ya na gama fadar haka ya lumshe idanunshi a hankali ya ida sulalewa a wajen ya konta , ya kankame kan shi waje guda ya na ci gaba da kukan shi kassa
( 🤧🤧 WLH HAR YA BAN TAUSAYI )
[19/02 à 10:53] 🪷🩷: *PAID BOOK*
💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
__________________
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH 💋
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{F R E E P A G E 17 & 18 🕊❤}
________________________________________
▪ESRA 💫❤
a hankali su ke tafiya ita da Safna saman titi , su na tafe su na dariya da allamun sun ji dadin fitar da su ka yi
sai da su ka karaso wajen wani traffic light sannan Esra ta tsaya ta na fadin " tsaya mu tsayar da taxi ya meda mu ni gaskiya na gaji "
a hankali Safna ta dawo ta riko hannun ta ta na fadin " please mu tafi , mun ma kusa isowa "
marairaice fuska Esra ta yi kafin ta bi bayan ta su bar wajen ta na fadin " Uhm , Uhm ni kawai ki na son ki gajiyar da ni , to wlh in mu ka koma sai kai yi min tausa "
wata yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta zagayo da hannun ta a wuyan Esra ta na fadin " duk abun da ki ke so , yanzu dai mu tafi , Sarauniyar kyau ba " ta kai karshen ta na bushewa da dariya
wani dan karamin tsaki Esra ta yi ta na fadin " ni wlh ba dan kin tare ni ba da na koma na yi mishi rashin mutuncin da ya dace shege dan iska kawai "
sake bushewa da dariya Safna ta yi ta na fadin " haba Sarauniyar kyau , ke da fan din ki , ai ya ga abun d aya burge shi ne , amma bai san Esra ta fi karfin shi ba , sai dan sarki jikan sarki , ko ba haka ba Sarauniya " ta kai karshen cike da zolaya
wani dan karamin tsaki Esra ta yi ta na kauda kai gefe
Dum ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi , cak ta tsaya waje guda ta kura mishi ido
a rude ita ma Safna ta tsaya ta na fadin " lafiya ki ka tsaya ? "
hannu Esra ta kai ta janye hannun Safna da ke saman wuyan ta ta fara takawa da sauri ta tsallaka titi ta shiga garden din
kai tsaye Kim ta nufa ta na kiran sunan shi
ta na isa ta zube saman guyiwowinta ta talabo kan shi ta na fadin " Kim , wake up , me ka ke yi a nan ? "
shiru ko motsi bai yi ba
ta na a haka ta jiyo Muryar Safna ta na fadin " Esra , wanene wannan ? kin san shi ne ? "
" Eh na san shi , please kama min mu tayar da shi " ta fada ta na sakin shi ta mike tsaye
da sauri Safna ta ce mata " mu kai shi ina ? ki na da lafiya kuwa ? kin ga kyale shi , wuce mu tafi , in ya tashi zai bar wajen "
cikin sanyin murya Esra ta ce mata " haba Safna , ina imanin ki ya yi ? dubi fa halin da ya ke ciki , ki na tunanin a banza zai zo wajen nan ya konta ? da ga gani ya na bukatar taimako , a matsayin ki na musulma ko dan halayan addinin mu ya kamata mu taimaka mishi , in mu ka bar shi a nan wani abu ya zo ya same shi kin san mu ma Allah ba zai kyale mu ba , saboda mu na ganin shi amma mu ka kyale shi har wani abu ya same shi ba mu taimaka mishi ba "
wata nanauyar ajiyar zuciya Safna ta sauke kafin ta karewa Kim kallo da kyau , sam bai yi mata kama da yan shaye shaye ba , kawai sai ta yi tunanin abun da Esra ta fada gaskiya ne , ya na bukatar taimako dan ba ya cikin hayacin shi
" shikenan , yanzu ina za mu kai shi ? ko kin san gidan su ? " Safna ta fada ta na karasowa dayan geffen Kim
a tare su ka hada karfi su ka mikar da shi tsaye , gaskiya Kim ya ji nauyi , da kyair su ka mikar da shi , a haka su ka dinga jan shi har su ka baro garden din da shi
sai da su ka fito sannan Esra ta ce wa Safna " no , ban san gidan su ba , but mu kai shi part din mu , da safe on ya ji sauki sai ya fada mana ina ne gidan su sai mu meda shi "
" Esra , kar ki janyo mana matsala , a ka je dan yankar kai ne ? "
" da ya fara cire naki kan " Esra ta fada cikin ko in kula
wani dan karamin tsaki Safna ta yi ba tare da ta ce komai ba , su ka ci gaba da jan Kim har su ka iso building din su
kai tsaye lift su ka shiga su ka nufi part su
su na shiga su ka kontar da Kim saman doguwar sofa su na nishi kamar wanda su ka kwana su na gudu
a hankali Esra ta zagayo ta cire mishi sneakers din shi ta ajiye a kassa geffen sofar , ita dai Safna tun lokacin da su ka kontar da shi ta juya ta nufi bedroom din ta
a hankali ta zauna bakin sofar , ta dago hannu ta janye mishi gashin shi da ya zubo mishi saman forehead , ta na kallon face din shi da kyau
nan ta lura da yadda idanun shi su ka kunbura kamar wanda ya yi kuka
wani cool murmushi ta saki kafin ta tashi a hankali ta nufi corridor ta shiga bedroom din ta
ta na barin wajen Kim ya bude idanun shi slowly , ya juyo da kan shi ya kalli saitin corridor din kafin ya meda shi ya lumshe su , ashe dama ya na cikin hayacin shi , kawai ya yi shiru ne ya ga in za ta kyale shi ko kuwa za ta taimaka mishi in har da gaske ta na son zama friend din shi
sai ko ya ga ta taimaka mishi , ta kawo shi har cikin gidan su
______________________________________
▪WASHE GARI ⛅💫⛅💫
A hankali ya ware idanunshi ya na kallon ceiling ba tare da ya motsa ba
kamar da ga sama ya jiyo Muryar Esra ta na fadin " sai yanzu ka tashi ? "
wani dan lumshe idanu ya yi ya na bude su a hankali , kafin ya sauko da kafafun shi kassa ya mike zaune bakin sofar
da sauri ya kai hannu ya dafe kan shi , ya datse idanun shi da karfi da allamun kan shi ke yi mishi ciwo
cike da kula Esra ta ce mishi " lafiya ? me ya faru ? "
ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " a ina na ke ? me na ke yi a nan ? "
wani dan karamin murmushi Esra ta saki kafin ta ce " kar ka damu cikin apartment di na ka ke "
" apartment din ki kuma ? me na ke yi a nan ? ta ya na zo ? " ya fada ya na janye hannunshi da ga saman kan shi ya ware idanunshi slowly
ba su sauka ko ina ba sai cikin nata , ta zaune saman sofa ta na kollon shi da murmushi a face din ta
kara fadada murmushin ta ta yi kafin ta ce " ya ka ke jin jikin naka ? "
" Fine " ya fada a takaice kafin ya mike tsaye
da sauri ta ce mishi " ina za ka je ? "
" ban san ya a ka yi na zo nan ba , but ya kamata na tafi yanzu , na gode " ya fada ya na shirin takawa
da sauri ta mike ta na fadin " no , ka tsaya ka yi breakfast kafin ka tafi "
bai ce mata komai ba ya nufi kofar fita ya bude ya fice abun shi
ita ma ba ta yi kokarin tsayar da shi ba , sai da ya fita sannan ta koma ta zauna , ta bude laptop din ta da ke ajiye saman table ta fara aikin ta
_____________________________________________
▪BROOKLYN
▪AYDEN
zaune ya ke saman chair din bakin pool da ga shi shi short , ya mike kafafun shi ya daga kai sama
ya shafa wani abu green a face din shi kamar mask na cream haka , ya lumshe idanunshi lips din shi kawai a ke iya gani pink color da su ma su mugun laushi
ya na a haka Adrian ya iso wajen kamar a na kore da shi , kai tsaye Ayden ya nufa ya na fadin " Ayden , please wake up akwai matsala "
cikin nitsuwa Ayden ya bude baki a sanyaye ya ce mishi " wace irin matsala early haka ? "
" Ayden , ban ga relieve din company ba " Adrian ya fada
cikin ko in kula Ayden ya ce mishi " and ? ba ka na da copy ba a cikin laptop ba ? "
" no Ayden babu copy din ta ....... "
cikin nitsuwa Ayden ya katse shi da cewa " no wonder , ka ban tsoro ni , na ma zata wani abu a ka yi "
" Ayden , in ban ga relieve din nan ba ba za mu san kudin da Kevin ya fitar ba last month , duk investigation din mu zai zama kamar banza "
wani dogon nunfashi Ayden ya ja ya na gyara zaman shi saman chair din ya ce " don't worry , za mu San abun yi , kai dai kawai ka bi tsarin plan di na "
wata yar karamar ajiyar zuciya Adrian ya sauke kafin ya zagayo ya zauna saman chair din geffen ta Ayden kafin ya ce " Bro , tun wuri ya kamata ka san abun yi dangane da Kevin , ko wane month ribar companyn ka kassa ta ke , in a ka ci gaba a haka sai mun yi bankruptcy , hakan na nufin sai ka rufe companyn , na san kuma ba haka ka ke so ba "
shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba amma ya jin abun da ya ke cewa , har cikin ran shi ya na jin zafin satar nan da Kevin ke yi , ya na neman ya kashe mishi company shi kuma ba zai iya jure hakan ba saboda companyn amana ce momyn su ta bar mishi , duk abun da ya samu companyn shi ne mai laifi dan bai tsaya ya kula da ita ba yadda ya dace
ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Adrian ya na fadin " ya kamata ka koma ka ci gaba da kula da companyn ka , please my Bro "
a sanyaye Ayden ya ce mishi " Monday , ka sa a gyara Office di na monday zan koma "
wani kyawatencen murmushi Adrian ya saki ya wata yar karamar dariya ya na fadin " Yes , Yes , Yes , da gaske za ka koma ? i'm really happy , finally tsawan shekaru za ka kama business din ka "
" amma a tare za mu koma "
cike da fara'a Adrian ya ce mishi " no wonder , ni dama a shirye na ke , kai kadai na ke jira , za ka gani yadda business din zai kara habbaka , na san saboda Kevin ba da zuciya daya ya ke kula da shi ba shi ya sa mu ke yin kassa "
shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba da allamun ya tafi duniyar tunanin shi
shi kuwa Adrian sai zuba mishi surutu ya ke bai san da cewa abokin nashi ya yi nisa duniyar tunanin shi ba
sai da ya share