Showing 18001 words to 21000 words out of 45115 words

Chapter 7 - TRUE LOVE by Princess Meerah

14 Jul 2025

3571

ba
a haka har traffic light din ya nuna green , Adrian ya ja motar su ka bar wajen
[17/02 ร  14:02] ๐Ÿชท๐Ÿฉท: ๐Ÿ’ž SOYAYYAR GASKIYA ๐Ÿ’ž
__________________

๐Ÿ’ž๐Ÿ”ฅ TRUE LOVE ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ž






( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH ๐Ÿ’‹







GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY







TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







ุฑุจูŠ ุฃุฒุญ ุงู„ุฃู„ู… ุงู„ุฐูŠ ูŠุนุชุตุฑ ู‚ู„ุจูŠ! ุญุฑุฑ ู„ุณุงู†ูŠ ูˆุฎู„ุตู‡ ู…ู† ูƒู„ ุบู…ูˆุถุŒ ุญุชู‰ ูŠูู‡ู… ุงู„ู†ุงุณ ู…ุง ุฃู‚ูˆู„!





BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM








๏ฝ›P A G E 13 & 14 ๐Ÿ•Šโค๏ฝ








a haka har su ka karaso one world trade center , sai da Adrian ya yi parking din motar a parking space sannan ya tabo Ayden cikin sanyin murya ya ce mishi " ta hanyar sirri yanzu ma za ka shiga ko kuwa ? "

slowly Ayden ya ware idanunshi , ya sa hannu ya bude kofar motar ya na fadin " no , mu je kawai , two minutes sun isa " ya kai karshen ya na sauka ya nufi hanyar shiga building din

cikin nitsuwa Adrian ya kashe motar ya sauko ya bi bayan Ayden



______________________________________



โ–ชESRA ๐Ÿ‘‘


da sauriยฒ ta ke tafiya ko kallon gaban ta ba ta yi , idanun ta cike da ruwa , fuskar ta a marairaice kamar za ta yi kuka , kamar za ta yi kuka ta ke fadin " shikenan ta kare min , in ban samo takardar nan ba wlh mutuwa zan yi "

ta na gama fadar haka kawai ta ji ta bugi kirjin mutun da karfi ,
fuuuuu ta yi baya za ta fadi ta na sakin wata yar karamar kara ta datse idanunta da karfi
cikin zafin nama Ayden ya kai hannu ya damko kugun ta ya taro ta ba ta kai kassa ba
da sauri ta kai hannu ta riko damtsen shi da kyau ta

cak ya tsaya ya na kallon face din ta , ta wani lumshe idanunta ta na cije lips din ta na kassa gwanin burgewa
lokaci guda ta tafi da imanin sa , dan ba karamar fadawa ya yi ba

su na a haka Adrian ya karaso wajen , ya na ganin yanayin da abokin shi ke ciki ya ida isowa da sauri ya na fadin " Ayden , are you okay ? "

a dubu dari Esra ta ware idanunta jin an ce Ayden , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi duk da ya na sanye da glass ba ta iya ganin su
lokaci guda idanun su su ka sarkafe cikin na juna ,
shi kuwa Adrian sai pic ya ke musu dan ba karamin kyau su ka yi ba kamar irin masoyan nan na cikin film

haka ma duk wanda ke cikin hall din cak ya tsaya ya na kallon
su dai ba su ma san abun da ke faruwa a zagaye da su ba
wata boyayyar Ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya mike a hankali ya gyara tsayuwar shi ya tallabo ta ta mike tsaye

su na mikewa tsaye ko Kebin ya iso wajen ya na fadin " Ayden , me ya faru ? " ya kai karshen ya na tsayawa geffen Ayden

ya na ganin Esra ya saki wani dan karamin tsaki ya na fadin " Miss Esra , you again ? what are you doing here ? "

lokaci guda Kuka ya kubce mata , ta bude baki har wata yar kerma ta ke
ta na shirin magana Ayden ya daga mata hannu allamun ta yi shiru
ba musu ta yi shiru ta na sunkuyar da kai hawaye na zubo mata bibiyu

cikin sanyin murya Kevin ya ce " Ayden , Adrian , ku tafi office di na ina zuwa , Miss Esra , koma office din ki "

tun bai rufe bakin shi ba Esra ta raba ta geffen Ayden ta bar wajen da gudu ta na kuka

sai da ta bar wajen sannan Ayden ya juyo ya kalli Kevin ya ce " me ya faru ne ? "
wank dan karamin tsaki Kevin ya yi ya na fadin " nothing , kawai ba ta meda hankali kan aikin ta , shi ne na yi mata magana , mu tafi "

" no , in mun je gida mun yin maganar , akwai inda zan je yanzu , Adrian mu tafi " ya kai karshen ya na fara takawa ya fice wajen Adrian na biye da bayan shi

shi ma Kevin bayan su ya bi ya bar wajen dama fito ya ke son yi
bangaran su Ayden kuwa , ya na isa wajen motar su ya shiga wajen driver , tun kafin Adrian ya iso ya tada motar

da sauri Adrian ya nufe shi ya na fadin " Ayden please sauko zan yi driving , ban shirya mutuwa ba please "

" za ka shiga ko na tafi ? " ya fada cikin wani yanayi kamar ran shi a bace ya ke
da sauri Adrian ya zagayo geffen me zaman banza ya shiga ya zauna

ya na zama Ayden ya tada motar ya bar wajen a 360 kamar zai tashi sama , ga shi kuma ya danne horn , ya ki saki
da sauri motoci ke rabewa gefe su na ba su waje har police din da ke kula da traffic su ka yi kokarin tsayar da shi amma ya ki tsayawa

sai da ya yi ten minutes ya na irin wannan tukin kafin ya ja wani mugun burki sai da kan shi ya bugi steering motar , shi ma Adrian kan shi ya bugu a gaban motar

slowly su ka dago kawunan su a tare , sannan Adrian ya ce " you're mad ? kashe ni ka ke son yi ko kuwa ? "

a sanyaye Ayden ya ce mishi " i'm sorry , idanu na ne su ka rufe "
wani dan karamin tsaki Adrian ya ja kafin ya ce " sauko na mayar da mu gida , ni yunwa ma na ke ji "

cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " mu fara biyawa gidan marayu , kuma gidan ka za mu tafi ba zan koma ya yanzu ba "

" okay , yadda ka ke so haka za a yi " Adrian ya fada ya na bude kofar geffen shi ya sauko
Ayden kuma maimakon ya sauko kawai sai ya matsa ya koma wajen mai zaman banza dan ba ya da ra'ayin saukowa ya shiga yin wani zagaye

shi dai Adrian ba abun da ya ce ya shiga wajen driver ya tada motar ya reversing din ta , ya kama hanyar gidan marayu
cikin abun da bai fi five minutes ba su ka iso
kar ku so ku ga yadda yaran ke farin ciki ganin Ayden da Adrian , sun samu kyakyawan tarba , ga yaran turawa ko da mugun shiga rai ji na yi kamar na sace guda na gudu

haka zalika Ayden ya ji wani mugun sanyi a ranshi ganin yaran nan , duk ya na sanye da face mask amma sai da ya yaran nan su ka gane shi , kenan sun san me kula da su
Ayden kuma bai yi mamakin yadda a ka yi yaran su ka gane shi ba , sai da ya yi musu wassa kamar wani familyn su sannan ya yi musu albishir zai mayar da su makaranta baki daya kuma shi zai dauki nauyin karatun su

ba yaran ba har mai kula da gidan marayu sai da ta yi farin ciki kamar ta yi kuka , ta na yi wa Ayden godiya duk da ba ta san ko wanene ba , ita dai kawai ta san kowace Friday ya na kawowa yaran abincin da kaya wani lokaci har kudi ya ke turawa a kai su shopping , amma ba ta taba sanin wanene Ayden ba

sai da su ka yi wajen one hour a gidan marayu kafin su baro shi , su ka nufi gidan Adrian
na san kuma ku na son ki san dalilin shi na kula da yaran nan kamar yan uwan shi , nan gaba kadan za ku sani amma ba yanzu wajen ba
ku dai ku ci gaba da bibiyar labarin dan yanzu a ka fara

kamar kullum ku na tare da alkalamin MEERAH โœŒ๐Ÿ’•๐Ÿ•Š


[18/02 ร  11:55] ๐Ÿชท๐Ÿฉท: ๐Ÿ’ž๐Ÿ”ฅ TRUE LOVE ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ž






( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH ๐Ÿ’‹






GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





ุฑุจูŠ ุฃุฒุญ ุงู„ุฃู„ู… ุงู„ุฐูŠ ูŠุนุชุตุฑ ู‚ู„ุจูŠ! ุญุฑุฑ ู„ุณุงู†ูŠ ูˆุฎู„ุตู‡ ู…ู† ูƒู„ ุบู…ูˆุถุŒ ุญุชู‰ ูŠูู‡ู… ุงู„ู†ุงุณ ู…ุง ุฃู‚ูˆู„!




BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM




๏ฝ›P A G E 15 & 16 ๐Ÿ•Šโค๏ฝ





______________________________________



โ–ชESRA ๐Ÿ’ซ



ido a rufe ta turo kofar office din ta ta shigo ta na kuka , hawaye na zubo mata bibiyu , kai tsaye chair din ta ta nufa ta zauna , ta kontar da kanta saman desk din ta na kukan ta

a hankali ta fara rage sautin kukanta , lokaci guda abun da ya faru ya dawo mata a kai
a dubu dari ta dago kan ta ta na zaro idanu , ta bude baki a hankali ta furta sunan Ayden , sannan ta ce " wannan shi ne Ayden Brian ? "

da sauri ta mike tsaye za ta bar wajen kawai sai ta tsaya cak ta koma ta zauna ta ja wani dan siririn tsaki kafin ta ci gaba da aikin ta


______________________________________



โ–ชAFTER SOME HOURS



misalin karfe 6 ta sauka da ga aikin ta , kai tsaye hanyar gida ta nufa , ta na tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki

ta na tsaka da tafiyar ta kawai ta jiyo Muryar Kim a bayan ta ya na fadin " Miss Chocolate ! Miss Chocolate ! " ya fada da dan karfi da allamun ita ya ke kira

cak ta tsaya da tafiyar ta har wani dan sanyi ta ji cikin zuciyarta lokaci guda
a hankali ta juya , nan ta gan shi ya na tafiya ya tunkaro ta , bai sauya kayan jikin shi ba
haka ta tsaya ta kura mishi ido har ya karaso gabanta ya tsaya ya na fadin " Miss Chocolate , tun dazu na ke ta kiran ki amma kin share ni "

ba ta ce mishi komai ba ta sunkuyar da kai ta juya ta fara takawa a hankali
a hankali ya fara takawa ya karaso geffen ta su ka jera , ya dan sunkuyar da kai ya na lekon face din ta

cikin sanyin murya ya ce mata " Miss Chocolate , lafiya na ga face din ki ta kunbura haka , ko kuka ki ka yi ? "

kamar dama jira ta ke a yi mata tambayar kawai ta dago kai ta ce mishi " Eh , kuka na yi , ni wlh gidan uwata ma zan koma , na gaji da wannan aikin , Wancen mara imanin mai fuskar shanun ya takurawa rayuwa ta , komai na yi wajen shi ba dai'dai ba ne "

shi dai ya tsaya ya na kallon yadda ta ke magana cike da bacin rai idanunta cike da ruwa

sai da ta gama maganar ta sannan ya ce mata " calm down , me ya faru ne a wajen aikin naki ? "

" wani file ne da za mu tatauna a kai yau na manta dayar paper a gida , shi ne kawai ya rufe ni da fada gaban sauran ma'aikatan , sai da na ce ya bari na koma gida na dauko ta amma ya ki sauraro na "

cikin ko in kula ya ce mata " ni wlh na dauka wani abu a ka yi , wai saboda paper ki ke kuka , paper din da na ke kunna taba da ita , mu je na saya miki wata "

wata yar karamar dariya Esra ta yi ta na fadin " rike abun ka ba na so " ta kai karshen ta na kara saurin tafiyar ta ta yi gaba

ya na ganin haka ya sa hannayan shi cikin aljihu , ya rage tashi tafiyar ya na kallon ta
sai da ta yi mishi nisa sosai sannan ta juyo ta gan shi cen baya ya na tafiya jiki a mace

cak ta tsaya ta na kallon shi har karaso wajen ta ya tsaya su na fuskantar juna
a sanyaye ta ce mishi " lafiya ka ke tafiya a haka ? "

slowly ya bude baki ya ce mata " ba ki saya min sigarin da na ce miki ba "

ta na jin hakan kawai sai ta yi tunanin ko dan ya na son ya sha sigari ne ya ke wannan tafiyar sanyin
tsuke fuska ta yi ta na fadin " ba zan saya ba , wuce mu tafi " ta fada ta na juyawa ta ci gaba da takawa

tsayawa ya yi ya na kallon ta ta na tafiya , da ga ganin yanayin tafiyar ta ka san cikin fushi ta ke
slowly ya juya ya yi hanyar shi ya yi wata kwanar

Esra kuwa ba ta ma sani ba sai tafiyar ta ta ke , sai da ta fara hango building din su sannan ta tsaya ta juyo ta na fadin " ni zan sh...... " kassa kai karshen maganar ta yi saboda ganin bayan nata da ta yi fayam babu kowa

a hankali ta kalli hagu , ta kalli dama ta ga babu Kim babu mai kama da shi
" yanzu yaron nan dan na ki sayar mishi sigari shi ne ya gudu ? za mu hadu gobe ai " ta na gama fadar haka ta juya ta shiga building din

kai tsaye Part din su ta nufa
ko da ta shiga ta ajiye bag din ta saman table , ta wuce bedroom din ta , ta cire kayan jikinta , ta saka bathrobe sannan ta fito ta shiga toilet

wanka ta yi sannan ta dauro da Alwalla kafin ta fito , ta shirya cikin wata gown mata nauyi irin ta zama gida haka
ta saka hijab din ta , ta shinfida sallayar ta ta tada sallat
ko da ta kammala ba ta tashi ba sai da ta zauna ta yi karatun kur'ani , har lokacin sallar isha ya zagayo , ta tashi ta gabatar da ita

bayan ta kammala ta cire hijabin ta ajiye saman bed din ta sannan ta fito
ta dawo parlour ta zauna saman sofa , ta kai hannu ta dauki bag din ta
ta fiddo wasu takardu da laptop din ta daiยฒ lokacin da Safna ta shigo gidan ta na sallama

a sanyaye Esra ta amsa mata sallamar ta , ta na kokarin bude laptop din ta
cikin nitsuwa Safna ta karaso cikin parlourn ta , ta zauna saman sofa ta na murmushi ta ce " ya ? Allah ya sa yau ma kin shirya mana Diner ? "

" hmmm , ba abun da na shirya , ni bar ni da kayan takaici ma " Esra ta fada ta na latsa laptop din ta

" takaici kuma , me ya faru ne ? " Safna ta fada ta na ajiye bag din ta saman table

ba tare da ta dago kai ba Esra ta ce mata " yau akwai wani meeting da Sir Kevin ya shirya mana , wlh akasi a ka samu na yarda daya da ga cikin paper din file di na , mara mutuncin nan kawai ya same ni ya rufe ni da fada wai ba na aiki na yadda ya dace , sa'a ta guda ina da copy din file din a laptop di na , shi ne zan kammala yanzu na tura mishi ta Email "

murmushi mai dan sauti Safna ta yi kafin ta kai hannu ta dauki bag din ta , ta bude ta fiddo paper din nan da Adrian ya ba ta ta mikawa Esra ta na fadin " sa'ar ki guda ki na da friend's din da ke aiki cikin restaurant din da ki ka je cin abinci har ki ka yarda paper din ki "

slowly Esra ta dago kai ta kalli paper din , hakan na nufin a restaurant din da su ka ci abinci ta baro paper din ? ya a ka yi ta fito bayan ita ta san ba ta fiddo paper din ba ? ko dai wani ya fiddo ta ba ta sani ba ?

wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta kai hannu ta karbi paper din ta na fadin " shi ya sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login