Showing 33001 words to 36000 words out of 45115 words

Chapter 12 - TRUE LOVE by Princess Meerah

14 Jul 2025

3578


wani cool murmushi ta saki kafin ta dasa Aya ta dago kai ta kalle shi ta ce " ba waka ba ce "
" to minene ? ni ban taba jin wannan abun ba "

" dama ta ya za a yi ka ji shi , kai da ba musulmi ba kuma babu musulmai a kusa da kai , ka san minene religion ko ? "

" Eh na sani , amma ban taba yarda da su ba saboda duk makaryata ne , sai su yi ta maganar abubuwa da ba gaskiya ba su na karbar kudaden mutane "

" wannan church ne su ke yin hakan , akwai mosque a garin nan zan so ka je ko so guda ne , za ka gane abun da ya ke gaskiya da abun da ya ke karya , amma zan so ka san addini na ba karya ba ne , sai wanda Allah ya so ke samun damar kasancewa musulmi "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " wanene wannan Allah , kenan in bai so mutun ba ba zai iya zama musulmi ba ? , kenan ni ba ya so na ? "

" Allah shi ne ubangijin da mu ke bautawa , shi shi kadai ya ke , babu wani abun bautawa bayan shi , shi ya hallice samai da kassai sannan ya hallice mu dan mu bauta mishi , cikin addini na shan wine haramun ne , shi ya sa na ke son ka daina , bayan hakan babbar illa ce ga rayuwar ka ma "

bai ce mata komai ba ya mike a hankali ya nufi kitchen
Esra kuwa tambayar shi ba karamin dadi su ka yi mata ba tun da har zai iya tambaya wanene Allah hakan na nufin ta fara jan hankalin shi zuwa ga musulumci , in har Kim ya koma musulmi to tabbas abun alfahari ne wajen ta

ta na kallon shi har ya shiga kitchen din ya bude oven kai tsaye kawai ya kai hannu zai dauki tray din
a dubu dari ya janye hannun ya na ja da baya shi duk ya mance da zafi abun gare shi

da sauri Esra ta ajiye laptop din ta ta tasso ta nufe shi ta na fadin " Oh my God , Kim kai ma ina hankalinka za ka sa hannu kai tsaye babu mitten "

" mantawa na yi " ya fada ya na matsowa wajen washbasin ya kunna fanfon ya zuba ma hannun shi ruwan sanyi kafin ya janye

cike da kula Esra ta ce mishi " mu je na shafawa maka pommade kar wajen ya ja ruwa ya zame maka matsala "
potholder ya dauka ba tare da ya ce mata komai ba ya saka , sannan ya fiddo tray din ya ajiye saman counter
ya na ajiye wa wani qamshi mai dadi ya fara tashi a wajen ko ni sai da na hadiye yawu

a hankali ya juya ya nufi gudan oven din ya bude ya fiddo tray din ya ajiye geffen dayan sannan ya fidda gloves din ya ajiye gefe
ita dai Esra ta zama yar kallo a nan ta na hadiyar yawu

shi kuma plates biyu ya dauko , dan madaidaita , ya dauki spoon da fork ya fara dauke Apple pie din nan daya bayan daya ya jera saman dayan plate
sannan ya fara kwassar fish din nan da potato da carrot ya Zube duk saman dayan plate , sannan ya dauki tray din ya kai wajen washbasin ya ajiye




MY BOOK IS ₦500
VIA

8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank




💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
__________________

💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞






( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH 💋






GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!







BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM





{P A G E 25 & 26 🕊❤}





bayan ya ajiye ya dawo ya tsaya geffen ta ya ce " here is , ga shi na kammala "
da murmushi a face din ta ta ce " gaskiya da ga gani zai yi dadi , Yanzu ka iya girki haka ka ke neman bata wa kan ka lokaci wajen yin security a nightclub , why ba za ka nemi aiki ba a wani restaurant ba ? "

" na nema , amma duk restaurant din da na je sai su ce na gwada musu takardun karatu na ko certificate din kwarewa ta a girki , ni kuma ko primary school ban yi ba , shi ya sa na hakura na daina nema "

har cikin zuciyar ta ta rasa dalilin da ya sa ta ke mugun jin tausayin Kim , he look so innocent , amma rayuwar shi ta na neman ta ruguje haka , gaskiya ya kamata ta gyara mishi rayuwa ko da shi ne abu na karshe da za ta yi a ta/ta rayuwar

wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce kai hannu ta dauki plate din Apple pie ta na fadin " okay , let's go and eat " ta kai karshen ta na fara takawa ta nufi parlour

ba musu ya dauki dayan plate din ya bi bayan ta su ka nufi yar dining table din su ta ajiye a sama sannan ta zauna saman chair guda ta na ce mishi ya zauna

ajiye plate din kawai ya yi kafin ya dan ja da baya ya na ce mata " no , lokacin hawa aikina ta kusa , tafiya zan yi "

marairaice fuska ta yi ta na mikewa tsaye har ta bude baki kawai ta ga ya juya ya fara takawa zai fice
da sauri ta ce mishi " Kim , ka tsaya na zuba maka cikin box kar ka tafi da yunwa "

ko juyowa bai yi ba ya sa kafa ya fice ya janyo mata kofar
ita dai da kallo ta raka shi har sai da fita sannan ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta koma zauna ta so ya tsaya su ci abincin tare ko da pie din ce tun da ita ce favorite dessert din shi , amma yanzu ya tafi

a hankali ta kai hannu kai tsaye ko spoon ba ta saka ba ta dauki Apple pie din nan guda ta kai a baki ta na bismillah sannan ta fara ci

a hankali ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya kafin ta lumshe idanunta a hankali , gaskiya taste din da yi mata mugun dadi , ita ba ta ma taba cin Pie din da ta yi mata dadi irin wannan ba , ga shi abun so easy amma taste din duniya ne guda , gaskiya Kim ya iya girki
cikin kankanan lokaci ya shirya wannan abun ina ga an ba shi isashen lokaci abun da zai yi sai ya fi hakan

sai da ta gama cinye sannan ta tashi a hankali ta nufi corridor ta shiga
a hankali ta kai hannu ta tura kofar bedroom din Safna ta na sallama kassa kassa

a konce Safna ta ke saman bed din ta , ta na rufe da duvet
ta na ganin Esra ta dago kai a hankali ta na amsa mata sallamar ta

a hankali Esra ta karaso cikin dakin ta zauna bakin gadon ta na fadin " ya jikin naki ? "
wata yar karamar ajiyar zuciya Safna ta sauke kafin ta ce " da sauki , amma yunwa na ke ji , tun dazu na ke jin wani qamshi na tashi ban san da ga ina ya ke ba , please gyara min wani abu na ci "

wani dan karamin murmushi Esra ta saki kafin ta ce " tashi mu je ki ci , shi ya sa ma na zo na kira mu je mu ci abinci " ta na gama fadar haka ta mike ta nufi kofar fita

a hankali Safna ta janye duvet din jikin ta , ta mike zaune ta sauko da kafafun ta kassa ta mike tsaye ta fara takawa a sanyaye ta fito dakin

ta na fitowa ta isko Esra zaune saman yar dining table din su
dan zaro idanu ta yi ta na kallon abincin da ke sama ta karaso wajen ta janyo dayan chair din ta zauna ta na fadin " Esra , ina ki ka samo wannan abincin ? "

wani dan karamin murmushin geffen fuska Esra ta yi kafin ta ce " kamar ya ? ni na shirya "

a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " fadi gaskiya , na san kin iya girki amma ba ki taba girka irin wannan abincin ba , asali ma ban taba ganin ki gyara fish ba , ko dai sayo wa ki ka yi ? "

wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " kin yi gaskiya , ina saurayin nan da mu ka taimaka a garden ranar nan ? "

a hankali Safna ta gyada mata kai allamun ta gane shi

" To shi ne ya zo ya girka mana , kuma da yay duk karfe 8 zai zo mu yi girki tare "

dan tabe baki Safna ta yi ta na kai fork din da ta debo fish da potato a ciki ta kai baki
sai da ta gama ta hadiye sannan ta kalli Esra ta ce " Yanzu saurayin nan ya yi wannan girkin ? "

gyada mata kai Esra ta yi ta na fadin " ni kaina na yi mamakin yadda a ka yi ya iya girki haka , kuma wlh ko one hour bai yi ba "

" gaskiya ya fi shirmen da ki ke girka mana " ta qarashe maganar ta na wata yar karamar dariya , kamar ba ita ba ce dunkule kamar an aiko mata mutuwa

ita ma Esra wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mata " wannan karan zan yarda da ba ki yi karya ba , amma ai koya min zai yi nan gaba kadan sai na fi shi kwarewa "

ita dai Safna ba ta ce mata komai ba ta na cin abincin kawai ba karamin dadi ya yi mata ba
Esra na ganin ta yi shiru ta gane ta tafi , hakan ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru ta ci gaba da cin abincin

sai da su ka cinye komai har Apple pie din ba su rage ba sannan su ka tashi su ka gyara wajen Safna kuwa har ta dan ji karfin jikin ta
bayan sun gyara table din su ka wanke plates din a tare sannan Esra ta dawo parlour ta zauna
Safna kuma ta koma bedroom din ta , ciki ya cika sai barci


_________________________________________



▪AYDEN 🦋 💙


konce ya ke saman wata doguwar sofa fara kal , ya daura hannun shi guda saman cikin shi , gudan kuma saman idanun shi , wa ya sani ya na farke ko barci ya ke

ya na a haka Adrian ya shigo parlourn da ga shi sai short da singlet fuskar shi da damuwa a kai ya nufi wajen kafafun Ayden ha na zauna
murya a sanyaye ya ce " Ayden , ba ka ce komai ba dangane da paper din nan ba ? "

shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai amma ya na jin shi dan ba barci ya ke ba
a hankali Adrian ya kai hannu ya buge shi a cinya ya na fadin " bro , da kai na ke magana please ka ce wani abu mana "

wata boyayyar ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya ce " Please ka bar ni da abun da ke damu na "

cike da kula Adrian ya ce " Oh my God , damuwa kuma ? wace irin damuwa kuma Ayden ? please tell me , mi ke damun ka ? "

dan jinkirtawa Ayden ya yi kafin ya ce " Adrian , son yarinyar nan ya na neman ya min illa , ban san ya a ka yi na kamu da son ta ba , wai ko na haukace ne ban sani ba ? "

wani kyawatencen murmushi Adrian ya yi kafin ya ce mishi " no , ba ka haukace ba , amma nan gaba za ka haukace in har ka ci gaba da rejecting abun da ke cikin zuciyar ka , ka san minene love at first sight , shi ne kawai ya kama ka , yanzu kuma sai ka yi kokarin ka bawa zuciyar ka abun da ta ke so "
cikin zuciyar shi kuma ya ce " ko da ba ka yi kokarin bawa zuciyar ka abun da ta ke so ba ka tabbata ni sai na mallaka maka ita "

shi dai Ayden bai ce mishi komai ba da allamun ya tafi duniyar tunanin shi

wata yar karamar dariya Adrian ya yi ganin yadda abokin shi ya damu kawai saboda mace , abun da bai taba gani ba
hannu ya kai ya bugi cinyar shi ya na fadin " yanzu tashi ka gyara mana wani abu mu ci dan ni yunwa na ke ji "

wani dan karamin tsaki Ayden ya yi ya na fadin " ba ka san hanyar kitchen ba ? "
" na sani amma ka san ni ban iya girki ba kamar kai , please tashi ka gyara min wani abu , tun safe ban ci komai ba , please bro " ya kai qarshen a sanyaye

wani dogon tsaki Ayden ya ja kafin ya juya ya shige cikin sofar ya na fadin " in dai ni zan girka maka ka mutu da yunwa "

hannu Adrian ya kai ya buge shi a baya kafin ya mike ya bar wajen da gudu kamar wani karamin yaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login