Showing 6001 words to 9000 words out of 45115 words
fara shafawa , sannan ta feshe jikin ta da perfume
sannan ta nufi kofar fita dakin ta fito parlour
ta na fitowa ta nufi doguwar Sofa ta zauna sannan ta janyo table din tsakiya gaban ta , ta dauki Jakar ta , ta fara fido abun da ke ciki daya bayan daya
ta na a haka wata kyakyawar budurwa ta bude kofar gidan ta shigo ta na Sallama
Budurwar kyakyawa ce gaskia , a shekaru za ta kai 22 to 23 years , Skin din ta chocolate ce mai mugun kyau , da ga kan ta ka ga jinin Hausa fulani
ta na sanye da Wando palazzo black color da t-shirt Orange , da wani Veil shi ma orange ta yi Rowling din shi a kai , ta na rataye da wata yar karamar bag a bayan ta , ta karaso cikin parlourn ta na kokarin cire bag din
dago kai Esra ta yi ta na kallon ta , ta amsa mata sallamar ta sannan ta daura da cewa " Safna , yau kuma sai yanzu ki ka dawo "
ajiye bag din ta Safna ta yi saman sofa geffen Esra sannan ta zauna ta na fadin " Kin dai gani wlh duk na gaji jiki na har ciwo ya ke min "
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta juya kan ta , ta ci gaba da fido abun da ke cikin Bag din ta
mikewa tsaye Safna ta yi ta dauki bag din ta , ta na fadin " na shiga wanka " ta fada ta na fara takawa ta nufi corridor
da to kawai Esra ta amsa mata ba tare da ta dago kai ba
ta na tsaka da fido kayan bag din ta , ta fido wani dan karamin abu baki kamar USB stick haka
dago USB din ta yi ta kawo ta saitin fuskar ta , ta na bin ta da kallo
" wannan kuma da ga ina ? " ta fada dan ita a sanin ta ba ta da USB key
sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon USB din nan kafin ta janye ta da ga gaban face din ta , ta dauki bag din ta ta fara meda duk kayan da fido ban da wayar ta , da laptop
sai da ta Kamala meda wa sannan ta dauko laptop din ta , ta daura saman cinyoyin ta , ta kunna ta , sannan ta saka USB key din a ciki ta fara latsawa
ta dauki wajen good Five minutes a haka kafin ta mike tsaye a dubu dari ta na rike da laptop din ta , ta na zaro idanu ta ce " oh my God , ya Allah me na ke shirin gani haka "
ni dai ban san me ta ke kallo ba , wasu rubutu ga su nan irin statistics haka , ita kadai ta san abun da ta ke gani
slowly ta koma ta zauna ta rufe laptop din ta ta zame USB din ta meda cikin bag din ta , sannan ta dauke ta , ta koma bedroom din ta , ta ajiye saman table din office din ta , sannan ta juya ta fito dai'dai lokacin da Safna ta fito da ga cikin toilet ita ma ta na sanye da bathrobe white color
ko sannu ba ta ce mata ta sa kai ta fito corridor din ta koma parlour
Safna kuma ta shiga bedroom din ta
jim kadan ta fito Sanye da kayan barcin ta ita ma amma nata navy blue ne kuma wandon ta iya cinya ne kawai
ta na fitowa ta nufi parlour ita ma ta zauna geffen Esra ta ce mata " wai ba ki gyara komai ba yunwa na ke ji "
dan karamin murmushi Esra ta yi kafin ta ce " kin gan ni nan , ko kitchen din ma ban shiga ba , bare na yi tunanin gyara wani abu , ni na zata za ki biyo mata da take away da ga Restaurant din ku "
dan karamin tsaki Safna ta yi kafin ta kauda kan ta , ta ce " wane restaurant , yau bayan wuya ba abun da na sha , dan jaraba ni su ka bari serving yau , Wlh ba zan yarda ba , ni fa a matsayin Chef na nemi aiki cikin restaurant din , amma wai su ka ba ni receptionist"
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " To tashi mu koma Nigeria mana "
dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " wa ? ni ? ai ni da Nigeria sai dai Ziyara , Ziyarar ma , sai da babban dalili "
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
__________________
💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💋
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
PAGE 5 & 6 💦🔥
Dariya sosai Esra ta yi , wai Ziyarar ma sai da babban dalili kenan sai in parents din ta sun mutu ko kuwa ?
hararrar wassa Safna ta yi mata ta na fadin " matsala ta da ke kenan ba a iya hira da ke "
tsagaita dariyar ta Esra ta yi kafin ta ce " Oya shikenan na daina "
" ko ke fa , amma ba ki tambaye ni abun da ya faru restaurant ba yau "
daga mata gera guda Esra ta yi ta na fadin " Oya fadi ina jin ki ! "
gyara zaman ta Safna ta yi , ta juyo su na fuskantar juna ta ce " Shugaba ku na ONE WORLD TRADE CENTER , ya je sun yi wani meeting da wasu mutane a restaurant din mu , ni da kaina na yi serving din su , sai wajen karfe 4 na yamma su ka tashi "
dan tabe baki Esra ta yi ta na fadin " no really , kenan Saurin da na ga ya na yi da safe cen za shi ? "
daga kafadun ta Safna ta yi ta na cewa " na san ba , amma kin san abun da ya fi ba ni mamaki ? "
girgiza mata kai Esra ta yi allamun a'a
" wani hadaden saurayi ne na gani a tare da su , Esra ina fada miki , duk zaman da na yi a New York , ban taba gani Saurayi hadade irin shi "
katse Esra ta yi ta na tsaki sannan ta ce " Shi ne abun mamakin ? " ta kai karshen ta na kauda kai
cike da zumudi Safna ta ce mata " Ki tsaya ki saurare ni mana "
juyo da kan ta Esra ta yi kafin ta ce " to shikenan ina jin ki "
" yawwa ! ni fa ba haduwar saurayin nan na ke fada miki ba , idan ki ka gan shi ba zai wuce 30 years ba , amma duk mutanan da su ka halarci Meeting din da Boss su ke kiran shi , har shi kan shi shugaban ku , a sani na Kevin Brian shi ne Boss din ku , ko kuma akwai na sama da shi ? "
" haka na ji su na cewa amma wlh ban sani , Fada min ya kamanin shi su ke ? "
yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta ce " Gaskia a jiki dai ya hadu ga tsayi ga fafadan kirji kamar mai dambe , sai dai ya na sanye da face mask ban samu na ga fuskar shi ba , idanun shi kadai na gani , ya na da dara daren sexy eyes , Sai dai kwayar cikin su ban sani ba in blue ce ko green dan da ga nesa na gan shi kuma ya sunkuyar da kan shi , amma dai between Blue or green ce gaskia , ni sai da na ji Muryar shi ma na kara tabbatar wa da shi ne boss din su , kar ki so ki ji Muryar shi kamar a na busa sarewa dan dadi , kuma cikin nitsuwa ya ke magana kamar an yi mishi dole , kai gayen nan duniya ne kawai wannan ina ga shi ne Mister US baki daya ma "
Dariya sosai Esra ta yi har da lumshe idanun ta , ta na fadin " Ni dai na san akwai Miss US , amma ban taba jin Mister US ba sai yau "
hararrar ta da kyau Safna ta yi kafin ta ce " ke wlh dan ba ki gan shi ba ne , amma Allah ya sa su dawo restaurant din sai na dauki pics din shi dan ki gani "
tsagaita dariyar ta Esra ta yi ta na fadin " hum na ji dai malama , yanzu tashi gyara mana wani abu mu Ci yunwa na ke ji "
hararrar wassa Safna ta yi mata kafin ta ce " kin yi sa'a ni ma ina jin yunwa ba dan haka ba sai dai ki sha ruwa " ta kai karshen dai'dai lokacin da ta shiga kitchen din
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta dauki wayar ta saman table
ta na daukar wayar ba abun da ya fado mata a rai sai Kim , kawai sai ta saki wani cool murmushi cikin zuciyar ta ta ce " ko ba komai ya Hadu gaskiya " ta na tuno yadda ta gan shi ya na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali , duk yadda a ka yi wannan akwai wani boyayen Al'amari a tare da shi
ta yi nisa cikin duniyar tunanin ta , ta jiyo Muryar Safna ta na cewa " ke malama tun dazu a na kiran ki a waya ba ki jine ? "
a dan razane ta dawo cikin hayacin ta dago wayar ta ta na kallon screen din
wani cool murmushi ta saki kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na fadin " Amarsu ta ango , lfy a ka kira ni warhaka ? "
wata yar karamar dariya na fara jiyowa kafin na jiyo Muryar wata macen da ga jin ta ta budurwa Ce ta na fadin " Za ki fara ko ? ni yanzu fada min yaushe za ki zo kin san fa jiya a ka kawo lefe amma ko kira na ba ki yi ba " a kai karshen cikin shagwaba
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " Sorry sister na , ya ki ke ya su momy duk da ma mun yi waya da ita da safe "
" Fine ! kowa ya na nan lafya , yanzu fada min yaushe za ki zo ne ? "
" kawai dan ki tambaye ni yaushe zan zo , auren da ko rana ba saka ba " Esra ta fada ta na mikewa tsaye ta fara takawa ta nufi corridor
a daya bangaran kuma a ka ce mata " Hum wa ya fada miki , ai jiya a ka saka rana , Farko ga watan March "
" wow ki ce nan da two months " ta fada dai'dai lokacin da ta ke shiga cikin dakin ta
" eh , nan da kwana 52 bai kai two months ba "
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " to sannu malama har kin kirga ko kwana nawa ne "
" eh mana dole na kirga kwana nawa su ka yi mana saura ni da Habibi kafin mu zama Mr & Mrs Raouf " ta kai karshen ta na yar karamar dariya
dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " ke ki ka san wani Habibi , kin ga sai an jima ni Sallat zan yi , sai da Safe " ta na gama fadar haka ta sauko wayar ta katse kiran
ta nufi closet din ta , ta bude ta dauki wani Hijab White color
ta saka , har kassa sannan ta dauki Sallayar ta shinfida , ta Haye ta tada sallar ta cikin konciyar hankali
___________________________________________
WASHE GARI
▪GREENWICH STREET
a hankali ta ke tafiya saman titin , ta na sanye wando palazzo pink color da Shirt White color , ta yi Rowling veil din ta a kai shi ma White color , ta na rike da bag din ta , ta na tafe ta na juyawa kar a je yau ma akwai baratin nan da su ka tare ta
a haka har ta karaso wannan kwangon da ta ga Kim ya shiga a jiya
ta na shiga ta hango shi cen zaune saman wasu case , ya hada bayan shi da bango ya lumshe idanun shi , ya na sanye cikin wando Crazy jeans black color , da wata T-shirt white color
gaskia wannan bai min kama da dan shaye² ba , dubi yadda ya ke a wanke tsab tsab Masha Allah akwai dai wata a kassa
a hankali ta karaso gaban shi ta na Sallama duk da ta san abu me wuya ne a ce zai amsa mata
ko motsi ma bai yi ba , amma ya san da ita dan tun lokacin da ta yo kwanar ya jiyo qamshin turaren ta
Murya cen kassan makoshi ta ce mishi " Kim ? " ta fada ta na dan lekon Face din shi
ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce mata " What are you doing here ? " ya fada cikin sanyin murya
da sauri ta yi baya kadan , ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta
" Kim , wine ka sha amma ko ? " ta fada dan ta jiyo warin ta cikin breath din shi
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba
" Why ? " ta fada mishi cikin sanyin murya
wani dan karamin murmushi Geffen fuska ya yi kafin ya ce mata " ke ni fa dan iska ne , shan wine karamin abu ne waje na , wai me ya kawo ki nan ma please let me "
cikin Sigar rarrashi ta ce mishi " please ka daina , wlh za ta iya maka illa ba kadan ba "
irin wannan murmushin Takaici ya yi kafin ya ce " please ki daina nuna kin damu da ni , ba ki san ni ba , ba ki san ko wanene ni ba , ki na ganin wajen da na ke zaune , kullum cikin tsangwamar mutane na ke , su na zagi na , Kalle ki , ki kale ni rayuwar mu ba daya ba ce , dan haka ki daina kula ni please ba na bukatar kindness din ki , ki tafi ki kyale ni "
" tabass ban san ka ba , ba ka san ni ba , amma ai ka taimake ni duk da ba ka san ni ba , ka ga ko dan hakan zan iya nuna damuwa gare ka , ni gaskiya ce na fada maka , shan wine babu kyau , ta na iya janyo maka cancer , sannan cikin adinin mu , shan wine Haramun ne " ta fada dan ita sam ta manta da shi ba musulmi ba ne
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Ke ki ka san wani addini , Ni ba ni da wani Aboki duniyar nan kamar Wine , duk lokacin da na sha ta na kan ji damuwa ta ta fi , na kan ji na daina kewar ta , please and please let me ki na damu na "
tsaya wa ta yi ta na kallon shi ba tare da ta ce komai ba
tabass akwai wani boyayen al'amari tare da shi , amma minene wannan abun ? ita ta ma rasa dalilin ya sa ta damu da shi lokaci guda haka , musaman dan ta gan shi yau ta fito tun karfe 7 ga shi kuma ya ce ta kyale shi , ko bude idanu bai yi ba bare ya kale ta
a haka dai jiki a mace ta juya ta fara takawa ta bar wajen
ya na jin ta fara takawa ya bude idanun Slowly
sun yi jazir ko , lalle ya na cikin maye
wani dishi dishi ma ya ke gani , amma a haka ya raka ta da kallo har sai da ta bar wajen , sannan ya meda idanun shi ya lumshe
a hankali ta ke Tafiyar ta duk ta yi nisa duniyar tunanin ta
ba ta fi ten minutes ba ta iso hall din ONE WORLD TRADE CENTER
sai a lokacin ta dawo cikin hayacin ta , ta na shirin shiga ko ta ga Kevin ya fito da ga cikin building din , ya na sanye da Suit sky blue ma su mugun kyau , ya na sanye da bakaken glass a idanun shi , ya na takawa cike da kwarjini
a hankali ta sauke