Showing 33001 words to 36000 words out of 62695 words
shirin ta ya lalace , kuma duk fitar dasuke kullum cikin
cewa Gogal tafita koyan motar dan haka bata samun wata matsala ,...
Ruma sosai tashiga damuwar canzawar da Khalid yayi , dan kullum bata samun wata
kulawa daga garesa , ko waya suke basa minty 5 sai yace mata yana zuwa shikenan bazai
k'ara kiran ta ba sai dai ko ita takirashi , haka zaita shimfid'a mata k'aryar wai kwana biyu aiki
yamasa yawa shiyasa amman tayi hak'uri yakusa dawo wa dai dai , Ruma ta yadda da k'aryar
da yayi mata shiyasa bata kawo komai ba ta amince masa ,....
Ranar da sukayi wata fita sosai Khalid yasamu had'in kan Aysha ta yadda ya tab'a jikin ta ,
murna sosai ya shiga yi a zuciyar sa yana fad'in " da sannu zan kai wajen da nakeso , itama
Aysha a zuciyar ta tace " ka kusa zuwa inda nakeso kazo , lokacin da Khalid yake tab'a kirjin
Aysha a cikin motar yana kai bakin sa a lokacin ta faki idon sa ta shiga yi masa Vedio , bayan
sun rabu dashi tasamu layin ta wanda yake a k'asa ta d'ora ta nemo number Ruma ta whaspp
ta tura mata wannan videon , yana shiga ta cire layin tare da ajiyeshi tana murmushin mugunta
,....
Ruma tuntana yadda da uzirin da Khalid ke bata har tadaina , gashi Daddyn ta yace mata
kwana biyu Khalid baya zama sosai a kasuwa , kullum da wuri yake ficewa daga kasuwar ,
zama tayi tana nazarin can zawar sa da yayi lokaci d'aya , tamkar wacce aka zabura ta mik'e ta
nufi d'akin ta dan d'auko wayar ta , kiran Aysha zatayi dan taje gidan su tabata shawara akan
Khalid dan gaskiya tunanin sa na
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
_NA_
*Zee* *MD*
*WOMEN* *WRITERS* *ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 21
Ruma sai magana takeyi takuma jin shuru , d'agowa tayi a hankali ta tana duban sa
nan taga hankalin sa gaba d'aya baya gunta , duban inda yake kallo tayi taga Aysha rik'e da tire
a hannun ta ta nufo wajen nasu , wani kishi Ruma taji ya rufe ta ta yadda Khalid yake kallon
Aysha , da k'afa ta zunguri Khalid firgigit yadawo hankalinsa , dai dai lokacin Aysha ta k'araso
d'auke da murmushi tana fad'in " kuyi hak'uri na barku shuru ko , duk da nasan kuna nan kuna
hirar ku irin ta masoya , Murmushin yak'e Ruma tayi dan kwata kwata Khalid ya b'ata mata rai ,
zama Aysha tayi tana ajiye lemukan data kawo musu , duban Khalid tayi tace " bisimillah
Angon Ruma ga abin sanyi kasha , Khalid jin maganar Yasake tabbatar wa da kan sa lallai
wannan Aysha ce , dan babu abinda ya ragu a muryar ta sai dai kawai yadda ta goge sosai
tamkar wata 'yar bariki , duban ta yayi yana murmushi yace " muna godiya sosai k'awar mu ,
Ruma dai bata tanka ba dan har yanzu tanajin zafin abinda Khalid d'in yayi , sai yanzu taga
haukar ta na tahowa da saurayin ta gidan su Kawa , duba da irin yadda Ayshar ta had'u komai
yaji ajikin ta babu Namijin da zai ganta batare da yakuma duban ta ba , ganin tayi shuru Aysha
tace " Kawata lafiya kuwa naga kinyi shuru ?
Ruma tayi murmushin yak'e tace " kaina ne yake sarawa yana ciwo , Aysha tace " Ayya
sannu bari nashiga na samo miki magani sai kisha , Ruma tace " kibarshi ma ai yanzu zamu tafi
inyaso naje gida sai nasha , Aysha tace " habadai tun yanzu zaku tafi kuma gashi ko lemon
dana kawo muku baku sha ba , Ruma tace " kiyi hak'uri zanzo miki zuwa na musamman sai
muyi hira amman yanzu kinga kaina ciwo yake , Aysha dayake ta fahimci abinda yasa Ruma
canzawa lokaci d'aya kawai murmushi tayi tace " to shikenan Allah yabaki lafiya sai munyi waya
, Khalid kwata kwata baiso su tafi yanzu ba dan gaskiya yanaso yaita kallon Aysha ko zai ga
abinda yakeso yagani , haka ya mik'e jiki a sab'ule suka tafi.......
Murmushi Aysha tayi bayan fitar su sannan tace " yarinya tabbas zaki wahalar da kanki
akan wannan fasik'in , har yanzu Khalid bai canza hali ba duba da yadda yayi ta kallona ,
amman lokacin canzawar sa yayi dan yanzu wasan nata kanshi zai juyo.......
Tunda Ruma suka baro gidan su Aysha ba wanda yace da wani kanzil , ita tanajin haushin
sa na irin yadda yadunga kallon Aysha shikuma yanajin haushin ta na yadda tak'i bari su dad'e ,
ganin shurun yayi yawa yasa Ruma yin magana "Khalid meyasa muna tare dakai amman
idanunka na wajen da ba muhallinka ba ? Cikin zuciyar sa ya furta indai zanga mace irin
wannan a gabana ai bazan iya duban ki ba Ruma , a fili kuma yace " haba My luv amman
sanake ko labari zaki iya rubutawa akaina ki shedar halina , kinfi kowa sanin waye ni sannan
kinfi kowa sanin irin k'aunar dana ke miki , ko sch d'inku kinsha min k'orafi akan bana sakarwa
k'awayen ki fuska , meyasa yanzu zakimin wani kallo daban ? karki manta abinda yasa nasaki
jiki a gurin wannan k'awartaki saboda yadda naga kin d'aukaketa , amman insha Allah ko
hanyar gidan su bazan k'ara ba tunda har hakan zai fara shiga tsakanin mu , tuni Jikin Ruma
yayi sanyi tafara dana sanin zargin Khalid d'in datayi , cikin siririyar murya tace " kayi hak'uri
Dear idanuwa na sun rufe a kan ka shiyasa , ganin yadda Ruma ta sauko yasa Khalid cigaba
da shigar da ita " bakomai my luv ai nasan kishine akan abinda kike so kikayi amman ki sa
aranki ke kad'ai ce mace tafarko kuma ta k'arshe data samu gurbin zama a zuciya ta , daga ke
kuma bana buk'atar kowacce mace duk kyanta , wani dad'ine ya rufe Ruma tuni tasaki jiki
tashiga zubawa Khalid kalaman soyayya tare da alk'awarur ruka da dama in sunyi aure , Shima
haka yashiga tsara ta da nuna mata bayan ita baya buk'atar kowacce mace a rayuwar sa , cikin
zuciyar sa kuwa Allah Allah yake yakai ta gida yadawo wajen wannan me kama da Ayshar dan
yanaso ya tabbatar da wacece ita , ...
Hameed yau ma ya fito da k'udirin sake duba Aysha , dan kiran da ake masa a k'asar
London yayi yawa so yake yakoma , gashi abun yana neman kaishi ga kwanciya ciwo , dan
kusan kullum baya bacci sai tunanin Aysha wanda yazamar masa jiki , yana k'ok'arin fita daga
get d'in gidan su ita kuma Abida tana k'ok'arin shigowa , karo sukayi kowanne yaja da baya
yana duban d'an uwan sa , Abida cike da so da k'auna ta dubi Hameed tace " Yaya Hameed
ina yini , Hameed batare da ya dube ta ba yace " lafiya sannan yasa kai ya fice batare da
yakuma bi takan ta ba , da idanuwa ta bishi tanajin wani sonshi na k'ara shiga ranta , tabbas
Yaya Hameed ya had'u sosai ga kyau ga kud'i ta ko inah yayi , a hankali ta furta " duk yadda
zanyi nasameka sai nayi Yaya Hameed , dan kaine irin mijin da nakeson kasancewa dashi miji
na nunawa sa'a wanda ko wacce mace zata so samun irinsa.......
Hameed na fita yashiga tsaki yana fad'in " mace ayita kwata kwata bata da aji , samun
waje yayi nesa da gidan su ya zauna yana dube dube tamkar me hango wani abu , gani yake
kamar zaiga Aysha ta b'illo ta wani gidan ...
Koda Aysha ta shiga cikin gida tuni tafara karatun yadda zata fara yak'ara Khalid , tabbas
duk duniya babu wanda ta tsana sama da Khalid , duk wani shirin ta na rayuwa shine ya rusa
mata shi , tabbas zai gane Aysha da da ta yanzu ba d'aya bace , sai ta nuna masa yanzu ita
cikakkiyar *'Yar Hannu* _Ce_ ..........
Kuyi maneji plss
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
_NA_
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page_. 25
Bayan sun kammala cin abincin Aysha ta dubi Ruma tace " 'yar uwa ta inaso in
kuma baki shawara akan ki rage saka damuwa aranki , kici gaba da addu'a komai zaizo da
sauk'i in sha Allah , nan Aysha tashiga bawa Ruma shawar wari tare da nasiha me saka
nutsuwa , sosai Ruma tasamu nutsuwa har tasaki jiki suka shiga hira , sai Bayan sallar Isha'i
sannan Ruma tamik'e tare da yiwa Gogal sallama zata wuce gida , Aysha ta yafo gyale zata
rakata titi suka jero suna hira har suka fito daga gate d'in gidan , suna fitowa waje suka ci karo
da Hameed yana fitowa daga motar sa , kwata kwata Aysha bata ganeshi ba shiyasa ta d'auke
kanta tana bawa Ruma labari , da sauri Hameed ya k'araso yasha gabansu yana fad'in " Barkan
ku da wannan lokacin , tsayawa sukayi turus Aysha tana duban sa , jitayi k'irjin ta ya buga
saboda ganin fuskar Hameed , tabbas bayan Jabir anaci to lallai wannan Hameed d'in shine
na biyu a shugaban 'yan naci , Ruma ce ta amsa masa da fad'in " Barka kadai bawan Allah ,
ya kalli Aysha yana murmushi yace " haba Aysha kin wahalar dani sosai kinsa nafara fita
hayyacina , babu irin neman da banyi miki ba amman sai yanzu Allah yasa zan ganki , Aysha
itama dai murmushin ta d'anyi tana fad'in " kayi hak'uri ina zuwa zan takawa 'yar uwata zuwa
bakin titi , Hameed yayi murmushi yace " muje mana mu taka mata baki d'aya ai nima 'yar
uwata ce , nan ya jera da su yana kusa da Aysha wacce yake jin bayaso tayi masa nisa ko
kad'an , a haka suka k'arasa bakin titin unguwar da babu nisa me napep suka tarar mata
Hameed yabiya kud'in Ruma tamusu sallama ta tafi , ....
Juyowa sukayi tare Hameed sai jan Aysha yake da hira amman tak'i sakin jiki , wayar
hannun tace tashiga ruru kiran Khalid yashigo , har ta yanke bata d'aga ba sake kira yayi akaro
na biyu , Hameed yadube ta yace " wayarki fa ake kira yakamata ki d'aga kiji ko kiran nada
muhimmanci , murmushin yak'e Aysha tayi sannan tace " nasan Gogal ce ke kirana tunda taji
shuru , Hameed bai wani damu da jin hakan ba duk dayasan ba lallai Gogal d'in ce me kiran
nata ba , suna k'arasowa k'ofar gidan Aysha ta kallesa suka had'a idanu dan shima idanun sa
akanta yake , wani abu taji ya ratso ta kanta har jikin ta , batasan meyasa batason had'a
idanuwa da Hameed ba , yana da kwarjini da cikar haiba gashi ingarman namiji , a Hankali ta
furta " ni zan shiga gida dan akwai abinda zanyi , Hameed yadube ta sannan yace " Aysha
wajen ki nazo yakamata ki tsaya ko sau d'aya ne kibani lokacin ki maganar da nazao da ita tana
buk'atar zama , ji tayi bazata iya yi masa gaddama ba samun bakin ta tayi da cewa to kashigo
daga ciki sai muyi maganar , aikuwa Hameed ji yayi tamkar ya taka rawa jin Aysha ta yadda su
shiga daga ciki suyi magana , ada in yazo gidan su tana lek'owa tagansa zata juya abinta ,
amman gashi yau yasamu matsayin da har tace yashigo , suna shiga gidan sai da ya yaba
tsaruwar gidan , amman yana mamakin taya Aysha suka dawo wannan gidan kodama Alhaji Na
Lamma d'an uwan sune ? dan shidai yasan asalin gidan na Alhaji Na Lamma ne tunda suna
gaisawa sosai , dan akwai wata jinya da Alhajin yayi lokacin yana gari shine yake dubashi sosai
har yasamu lafiya , maganar Aysha ce ta katse masa tunani tace " bisimillah ka zauna ina zuwa
, Hameed yaja kujera ya zauna fuskar sa d'auke da murmushi , juyawa Aysha tayi ta nufi cikin
gidan Hameed ya raka ta da lumsassun idanun sa , cikin zuciyar sa yana tasbihi ga ubangijin
da ya halicci kyakkyawar surar Aysha , dan ko ta inah Aysha ta had'u musamman idanuwan ta
da dirin jikin ta , har ta shige ciki idanunsa na kan hanyar data bi tamkar ita yake kuma gani ,
bayan kamar minty 5 saiga Aysha ta fito sanye da hijab d'in ta har k'asa tayi ainahin shigar ta ,
hannun ta rik'e da tire wanda yake d'auke da lemo da ruwa a kai , tana k'arasowa tayi masa
sallama sannan ta ajiye tiren hannun ta kan d'an madai daicin table dake gaban sa , itama
kujerar ta janyo ta zauna sannan ta dube sa tace " Bisimillah ga ruwa kasha , Hameed yayi
murmushi sannnan ya d'auki ruwan yana cewa " nagode sosai da wannan karramawar taki ,
ruwan yasha sannan ya ajiye yana duban ta a hankali ya furta " Aysha inso kibani aron minty
10 in gabatar miki da kaina , tun daga lokacin dana had'u dake zuciyata takamu da sonki sosai
kullum innazo gareki bakya bani lokaci , a haka har na tattara nakaoma k'asar danake aiki wato
London , koda nakoma mai makon in rage tunaninki sai ma k'aruwa da yayi dan kullum dake
nake kwana araina , kwata kwata nadaina samun nutsuwa indai bansamu na keb'e nayi tunanin
ki ba , ahaka har nafara gazawa game da aikina ina samun matsalaloli sosai , kinsan anaso
koda yaushe yakasance likitoci suna samun nutsuwa dan su samu damar kulawa da mara
lafiyar su , tunda na fahimci nima me jinya ne yasani na tattaro nadawo gida nageria , sai dai
wacce nadawo domin ta bata san inayi ba dan ina durowa k'asar nan na nufi gidan ku amman
ina zuwa nasamu gidan a kulle , Aysha naje gidan ku yafi a k'irga amman kullum a rufe yake ,
na tambayi 'yan unguwar ko sun san inda kukaje sai suce suma basu sani ba , nasha zaga gari
Aysha akan nemanki amman Allah bai had'a ni dake ba sai yau d'in nan , duk naganki kwanaki
amman kika nuna bake ceba haka yasa na k'yaleki naci gaba da bibiya har Allah yasa na samu
nasara , zamowa yayi daga kan kujera yad'an matso kusa da ita yana magana a hankali " dan
Allah Aysha ki taimaka ki anshi soyayyata ko zan samu sauk'i daga rad'ad'in da zuciya ta kemin
, ina sonki da gaske kuma inaso kizama matata uwar yayana , Aysha tunda Hameed yafara
magana taji duk kalaman sa suna ratsa jikinta , tabbas tasha ganin maza da yawa kuma tayi
rayuwa dasu amman meyasa shi dayake mata magana takejin ta har cikin jikinta ? kodai shidin
masoyin tane na gaskiya shiyasa takejin hakan ? tabbas badan tayi alkawarin bazatayi aure a
rayuwar taba da babu abinda zai hana ta ansar soyayyar Hameed , sai dai kash bazata tab'a
aure a duniya ba dan har yanzu bata yadda da soyayyar maza ba kawai tana kallon sune
mayaudara wadan da basa son mace dan Allah sai dan wani abu nata , ........
*Kumin hakuri wlh nafita unguwa bansamu yin typing dayawa ba*✍
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
_NA_
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta