Showing 57001 words to 60000 words out of 62695 words

Chapter 20 - YAR HANNU BOOK COMPLETE

Zee Md   

11 Jul 2025

3843

fara shirye shirye ta kowanne b'angare.....
Mummyn Ruma tuni ta tura Amare gida Mrs MD dan ayi musu gyara tare da tsumasu da
magun guna , Aysha kwata kwata bata murna da auran nan dan ita a ganin ta Hameed b son
ta yake ba , kawai dai zai aure tane dan wata manufar tashi daban , ko sau d'aya bai tab'a
zuwa gunta zance ba sannan ace a hakan zasu zauna zaman aure , ba yadda zatayi haka take
zuwa gyaran jiki ita da Ruma , yadda Ahmad ke nan nan da Ruma abin na birgeta amman ita ko
sau d'aya Hameed yaki bata kulawa , bata b'oye wa me gyaran jiki ba aka itafa fa ba cikakkiyar
budurwa bace , nan aka shiga had'a ta da magun gunan matsi masu kyan gaske batare da
Ruma ta gane ba ,.....

Yau saura sati d'aya bikin Aysha da Hameed Ruma da Ahmad , suna hanyar su ta
dawowa daga gidan gyaran jiki sukayi karo da Farouq nan yake gaya mata rasuwar Alhajin sa
da kuma auren da yayi , sosai Aysha taji mutuwar Alhaji Na Lamma tayi masa Addu'ar samun
Rahamar ubangiji , tayiwa Farouq gaisuwa tare da yi masa fatan Al kairi akan auren sa ......

Suna zuwa gidan sukaga ankawo lefen su baki d'aya , Alhaji Ashir gidan Gogal yasa aka
kawo kayan lefe dan shima jin ta yake tamkar Mahaifiya a gurin sa , Ruma ankawo mata
akwatuna takwas ita kuma Aysha Akwatina 12 kaya iya kaya abin ba'a magana , Ruma tafara
yiwa Aysha maganar yadda zasu tsara dinner da party amman Aysha tace bazatayi ko d'aya ba
kawai walima zatayi ,....

A daren ranar Hameed yazo wajen Aysha da maganar tayo masa list d'in duk abinda take
buk'ata , Aysha ta sheda masa bata buk'atar komai duk da haka ya d'auki dubu dari yabata
sannan yatafi ,...
Ana gobe kamu sukaje akayi musu kunshi da gyaran kai , nan ne Aysha taga Jabir yake
sheda mata bayan yazo wajen ta ya tafi yan zuwa gida ya tadda Mahaifin sa ya nema masa
auren wata yarinyar Abokin sa , yanzu haka saura sati bikin sa kuma Baban sa yace mudun ya
bijirewa maganar sa sai ya tsine masa , Aysha tace Allah yasanya Al kairi Ruma tace " itamq
jibi d'aurin auren ta Allah yabata miji na kere sa'a , duk da Jabir yaji rashin dad'i amman yataya
Aysha murna yasan ko ba komai aure shine rufin asirinta ......

Walima kawai sukayi basuyi wata bidi'a ba , Washe gari aka d'aura auren Aysha da
Hameed Ruma da Ahmad , sai muce Allah yabasu zaman lafiya.....

Komai iri d'aya Alhaji Ashir yayi musu babu wani bambanci , Gogal ta had'a musu gyara
sosai itama wacce komai itama kai d'aya tayi musu , dare nayi kowacce aka mik'ata gidan
mijin ta tare da tarin nasihohi daga wajen iyayen su ......

Fad'in had'uwar gidan Aysha b'ata bakine dan gidane na alfarma , kuma Alhaji Ashir ya
zuba musu dukiya sosai kowacce sai san barka , tunda aka kawo Aysha take kuka dan batasan
wace irin rayuwa zatayi da Hameed ba , shigowar sa ce tasa tayi k'asa da murya dan karyaji
sautin kukan nata , ledojin hannun sa ya ajiye tare da shiga toilet yayi wanka , bayan ya fito ya
umarce ta itama akan ta je tayi wanka ta d'auro arwala dan suyi sallah nuna godiy ga
mahaliccin su , Bayan tayi tafito sukayi sallah nan ya yi mata addu'oi tare da addu'ar Allah
yabasu zaman lafiya , .....

Wannan Daren haka Hameed ya rayashi tare da nunawa Aysha zallar k'auna , kwata
kwata sai ya susuce mata tamkar qani k'aramin yaro , ita kanta sai da ta ji ajikin ta dan tabbas
ta yadda da gyara da kayi mata tamkar wata sabuwar budurwa , shi ya taimaka mata ta gyara
jikin ta yana ayyana anya wannan Aysha *'Yar Hannu* ce kuwa ? dan ji yayi tamkar shine yafara
bud'e ya aleda, haka yai tasa mata Albarka ya zage ya rungumi matar sa yana nuna mata zallar
k'auna.......

Satin su biyu sukayi sallama da iyayen su da Abokan Arziki suka d'aga England.......

Acan Aysha taci gaba da karatun ta tana karanta irin aikin mijin ta wato Likita , tare suke
fita kullum suna tare da juna tamkar su cinye junan su sabo da kulawa ....

*Bayan shekara biyu*

Tuni Aysha ta haifi d'iyar ta mace wacce suka saka mata sunan Gogal , wato Aysha kuma
sunan uwara ta suke kiran ta Eesha , lokacin Aysha ta gama karatun ta suka shirya zuwa
Nageria , kafin suzo tuni angyara musu gidan su suna zuwa suka sauka a nan , sai da suka
huta sannan suka je gidan su Hameed , sosai Hajiyar Hameed tayi farin cikin da ganin su tare
da jikar ta , anan suka wuni sai dare suka nufi gidan Gogal , sai dai Aysha tasha mamakin ganin
yadda aka maida gidan Gogal har da saka masa gate , tana shiga taga irin had'uwar da yayi
sosai tasamu Gogal zaune da wata yar matashiyar budurwa suna hira , suna ganin su Gogal
tace " ai bayi fushi wato sai yanzu zaazomin ko , nan Aysha tasa dariya tana fad'in " ko kinyi
fushi dani ai bakyayi da Esha ba , nan Gogal ta anshe ta tanajin k'aunar yarinyar har cikin ranta
, ashe da rabon zataga 'yar gidan Aysha lallai duniya komai mai wucewa ne , Anan suka
kwana sunsha hira sosai anan take gaya mata wannan gyaran gidan Hameed ne yaturo da
kud'i akai musu , sannan ya kaita aikin hajji ita da su Mummyn Ruma da Alhaji , sosai Aysha
tashiga mamaki dan ko sau d'aya Hameed bai nuna mata ba , lallai Hameed gwarzon namiji
ne wanda takewa Allah godiya da samun sa ....
Wannan budurwa da tagani Gogal ta sheda mata ai Matar Habu ce daya auro daga garin
su , shine tace su zauna tare da ita dan batason zaman kad'ai ci , sosai Aysha taji dad'i gashi
ta yaba da hankalin Rabi'a matar Habun , washe gari Hameed yazo ya d'auke ta suka nufi
gidan su Ruma , saida suka jima da Mummy suna hira sannan suka nufi gidan Ruma , murna
sosai Ruma tayi da ganin 'yar uwar tata tare da Esha ita lokacin har tana shirin yaye Abul kairi ,
dayake ta ruga Aysha haihuwa , anan Ruma take bata labarin Khalid ya haikewa 'yar gidan
yayan sa anka masa yanzu haka yana can virson sai ya shekara goma sannan zai fito , Aysha
tace " Allah ya kyauta wato me hali baya canzawa Allah yasa mudace , dare nayi Hameed yazo
ya kwashe su suka nufo gida .....


Aysha tana jikin Hameed a kwance tace " bani da bakin da zanyi maka godiya mijina
akan Alkairan ka gareni , sai dai a koda yaushe ina maka addu'a akan Allah yabiyaka da
mafificin Alkairi , rungumeta yayi sannan yace " Ameen My Baby Esha one inaso kibani had'in
kai a yau musamowa Esha baby k'ani ko k'anwa , dariya tasa tana tura fuskar ta cikin jikinsa ,
anan nafito na barsu dan kar nasa musu ido ......

*Bayan shekara uku*
Tuni Aysha tazama cikakkiyar Dr. Itama tafara aiki a asibitin da Hameed keyin aiki acan k'asar
England , lokacin yaran ta biyu ga Esha ga Daddy wanda yaci sunan Mahaifin Hameed , In
sun samu hutu suna zuwa Nageria dan Gogal ma Aysha tuni ta d'auko ta ta dawo da ita wajen
su , Arzik'i sai Abinda yai gaba , dan yanzu Aysha tazama Babbar Hajiya tare da Mijin ta Alhaji
Dr Hameed , Rayuwa ta sauya musu sai dai suce Alhamdulillah ........ Hameed yazama na
Aysha Aysha tazama ta Hameed , kullum inta tuna irin abubuwan da tayi sai taji tana tarin
nadama tare da kuma yin istigifari dan neman tuban Allah , Allah muntuba Allah kayafemana
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

*Tammat*

*Alhamdulillah Allah yakawomu K'arshen littafin 'Yar Hannu , Abinda nayi ba dai dai ba Allah
ka yafemun , wanda nayi dai dai kuma Allah yasa mu amfana dashi ,*👏🏻👏🏻

_Nagode sosai Masoyana ta yadda kukai ta bibiyar littafina batare da gajiyawa ba , Allah
yabar k'auna Ina muku fatan Alkairi_🙏🏻
*tabbas komai yayi farko akwai k'arshen sa*

*Taku a ko yaushe*
*'Yar Mutan Kanawa*ν ΌνΌΉν Ύν΄ν ΌνΏ»ν Ύν΅°ν Ύν΅°ν Ύν΅°
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *Cigaban 'Yar Hannu*ν Ύν΄’
22

Kiran Aysha zatayi dan taje gidan su ta bata shawara akan Khalid dan gaskiya tunanin sa
yadame ta , gashi ta rasa kan sa kwata kwata dan ko kiran sa tayi kwata kwata baya d'agawa ,
ganin datar ta tayi a bud'e sak'onni na shigowa rufe datar tayi sannan ta shiga neman number
Ayshar kiran ta tayi har takusa katsewa sannan Aysha ta d'aga , lokacin suna tare da Khalid a
manne suna zabga love , ka rantse wasu shahararrun masoyana na gaskiya , amman ina ko
wanne da burin dayake ransa , d'aga wayar tayi tana fad'in " K'awata ya akayi kwana biyu ,
Ruma tace " lafiya lau dan Allah kina gida ? Aysha tace " bana gida amman indai zuwa zakiyi
kibari zuwa anjima sai mu had'u , Ruma tace to shikenan sai kindawo , Aysha ta katse wayar
tana jin tausayin Ruma har cikin ranta , dan tasan tabbas tafi son Khalid akan son dayake mata
, dan yadda ta karance sa kwata kwata ba dan Allah yakeson Ruma ba kawai saboda dukiyar
Mahaifinta yake sonta , kuma da sannu zata rusa masa duk wani shirin sa , zata yi k'ok'arin
raba Zuciyar Ruma da soyayyar sa , sai tasa Ruma ta tsanesa tsana mafi muni , ta kallesa
suka had'a idanu ya wani kashe mata ido , itama murmushi tayi masa a zuciyar ta tana fad'in "
ka kusa yin kuka da idanunka , dan tuni tasamu labarin yadda yasamu aka d'aukesa kasuwa da
k'yar , kuma babu laifi mahaifin Ruma yana masa sallama me tsoka shiyasa yafara shigowa gari
, yanzu lokacin da zata fara rabashi da kud'in jikin sa yayi , dan sotake sai ta rabashi da kud'in
jikin sa sannan ta Rabashi da Ruma da kuma kasuwan cin sa , sai yaji irin ciwon da taji a
zuciyar ta na rabata da Mutuncin ta dayayi.........
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
ν Ύν΄’ν Ύν΄’


_NA_
*Zee* *MD*

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*





_Page._ 23

Aysha ta dubi Khalid tace " kasan da wa mukayi waya ? Khalid ya girgiza kai
yana fad'in " taya zan san da wa kikayi nasan dai mace ce , Murmushi Aysha tayi sannan tace "
Mutuniyar ka wai zatazo yau in ina gida , Khalid ya tab'e baki sannan yace " nasan indai tazo to
sai tayi zan cena , kinsan Allah Baby ni nafison inyi rayuwa da wa yayyiyar mace irin ki ,
inason inga budurwa ta tana bani kulawa kamar yadda kike bani , Ruma babu abinda ta iya
sai k'auyan ci itafa ko romance bata bari muyi , kullum sai ta runga cewa in k'ara hak'uri in
mukayi aure tazama tawa komai sai yadda nayi dashi , ...
Aysha tuni taji wani ciwo a zuciyar ta yataso , tabbas ko wacce mace me mutunci babban
burin ta shine ta tsare mutuncin kanta , amman ita ta k'arfi da yaji aka b'ata mata mutuncin ta ,
ta sanadin haka yanzu gashi ta lalace ,hawaye ne suka cika mata idanun ta tayi saurin maidasu
, dan bata so ko da wasa Khalid yasan damuwar ta , Khalid yaci gaba da magana " kin san
wani Abu Baby ? Aysha ta girgiza kai alamun a'a , yace ko sau d'aya bantab'a son Ruma ba ,
saboda bata d'aya daga cikin Matan da nake da burin aura , kawai ina kulata ne dan kud'in
Baban ta , kuma sannan ina son dukiyar kaf tazama tawa nan gaba bayan babu shi , Aysha ji
tayi wata tsanar Khalid ta nunku a cikin ranta , tabbas Khalid azzalumine kuma sai takawo
k'arshen zaluncin sa nan ba da jimawa ba , Murmushi tayi nasu na asalin 'Yan duniya ta dubesa
tace " to meyasa ka yadda zaka aure ta bayan kuma bata d'aya daga cikin matan da kakeso ka
aura ? Murmushi Khalid yayi sannan yace " Baby ai kinsan a k'ark'ashin Mahaifinta nake kinga
da kunya 'yar sa ta nuna tana sona nak'i amincewa , da zarar komai yadawo hannu na zan iya
rabuwa da Ruma ko kuma na auri wacce rai na keso , Aysha tace " gaskiya kai d'in ka iya buga
game amman karkaje fa ayi maka Babban bugun da ya wuce naka , Dariya yasa yana fad'in "
waye zai bugani alhalin ba wanda yasan meye a zuciya ta indai bake ba dana fad'a miki , kuma
ni nasan ina da tabbacin bazaki fad'awa Ruma komai ba , Aysha tayi murmushi tace " haba
Dear taya zan tona maka asiri , ai in nayi haka tamkar na tonawa kaina asiri ne nima , kadaina
ma fad'in haka dan kasan ni taka ce kai nawa ba ta yadda za'ayi inga wani abu da zai zo ya
kawo maka matsala batare da na kaudashi ba , haka Aysha ta karkace tashiga yiwa Khalid

dad'in baki sosai , nan yayi mata alk'wari komai takeso tafad'a zai siya mata , ...

Aysha tanajin haka ta kashe masa ido tace " account d'inka da zurgi kenan My Dear ?
Khalid cike da shauk'in so yace "2 milloine acikin account d'ina yanzu , sai kinsan dayake ban
dad'e dafara zuwa kasuwar ba , kuma ahakan ma ina had'awa da cuwa cuwa batare da me
wajen ya lura ba , nan Aysha taji sirrin Kud'in da Khalid yake dashi , Murmushi tayi cikin ranta
tace " yanzu zaka fara rabuwa da 1 Million kafin nan da kwana biyu ka rabu da sauran ma ,
cike da kissa Aysha tace " ni yanzu abinda nakeso kawai shine muje kasiyamin zobunan gold
da sark'a dan ina son du sosai , Khalid ganin irin yadda Aysha ta kwanto jikin ta ajikin sa ga Na
shanun ta rabin su duk sun fito yasa shi rud'ewa tare da cewa " muje Baby angama ,......


Jabir tunda suka rabu da Aysha yake ta dakon kiran ta amman shuru , gashi ya gwada
layin ta amman baya tafiya kwata kwata , damuwa ya shiga sosai tare da fad'in " wato wayo
Aysha tayimin batare da nagane ba , meyasa na yadda nabar ta ta tafi batate da nabi bayan ta
ba ? tabbas indai yakuma ido biyu da Aysha bazai barta takuma raina masa hankali ba , kuma
ai yagane number motar ta dakuma kalar motar tabbas zai ci gaba da neman ta tamkar yadda
yayi kwanaki , .......

Yau saura kwana biyu Hameed yabar k'asar Nageria , hankalinsa sosai yatashi ganin har
yakusa tafiya bai samu Aysha ba , yaje sau biyu unguwar su Aysha yana ganin ko Allah zai sa
yayi sa'a sundawo , sai dai ko kad'an basu dawo ba kullum gidan arufe yake , yauma yana
zaune a k'ofar gate d'in gidan su yana chat da wani abokin sa a can k'asar London , kwana
biyu zaman cikin gidan baya masa dad'i saboda Hajiyar sa ta damesa da Maganar Abida ,
shikuma har ga Allah bason maganar yake ba , shifa indai ba Aysha ba haryanzu baiga macen
data yi masa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login