Showing 21001 words to 24000 words out of 62695 words
bud'e gidan da saurin sa yatafi isarwa da Alhaji sak'o.....
Alhaji Na Lamma yana zaune a falor sa yana shan ruwan lipton yaji shigowar me gadi , izini
yamasa yashigo suka gaisa , nan ya sheda masa zuwan Aysha da kalmar datace ya fad'i ,
Alhaji Na Lamma najin ance Me gidace tazo ya mik'e da sauri tamkar zai tuntsira yayo waje ,
Me gadin nasa ma acikin falor yabarshi tsaye baki bud'e , cikin ransa yace " wannan wacce
shu'umar yarinya ce tasa Alhaji wannan rawar jiki haka ? shima biyo bayan sa yayi suka fito
wajen ........
Aysha na tsaye abinta sai k'arewa unguwar kallo take , cikin ranta tashiga yaba tsarin
unguwar na rashin hayaniyar mutane , ga kuma gidaje masu kyan gaske tamkar a turai layin ,
muryar Alhaji ce ta katse ta da yace " sannu da zuwa Hajjaju , Aysha ta bisa da kallo daga shi
sai gajeran wando kana gani kasan baisan ya fito ba , dariya ce taso kama Aysha amman ta
maze cimin ranta tana fad'in " tsohon banza kawai maganin ku ai , dan kuna da kud'i sai
kurunga amfani da hakan kuna lalata yaran mutane , kana da Matanka amman saika had'a da
bibiyar matan waje , a fili kuma ta amsa masa ciki ciki tamkar batason maganar , bud'e mata
k'aramar k'ofar yayi yace " bisimillah mushiga daga ciki ko sai muyi magana , shigewa Aysha
tayi batare da tace dashi uffan ba abinta.......
Sai data shiga falor tasamu guri ta zauna tana kuma k'arewa falor kallo , tabbas gidan
yayi kyau sosai dan yagama burgeta shiyasa takeson gidan , Alhaji Na Lamma shima zama
yayi yana duban ta cike da kulawa , Aysha ta gyara murya tace " anjima nakeso mudawo gidan
nan shine nazo nagayamaka kayi sauri ka kwashe duk wasu abubuwanka masu muhimman ci
daga ciki , sanin kan kane nida Kakata zamu dawo cikin gidan kuma batasan yadda akayi
nasamu gidan ba , Alhaji Na Lamma yace " duk yadd kikeso haka za'ayi yanzu kuwa........
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR* *HANNU*
_NA_
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Alhamdulillah_
*Am* *Back* ✍
_Page._ 16
Aysha sosai ta maida hankalin ta tana kallon Farouq , duk da bawata maganar
arzik'i yake mata ba ba laifi ta fahimci wani abun , kusan awa d'aya suka kwashe yana nuna
mata sannan suka d'auko hanyar dawowa gida......
koda suka zo k'ofar gate d'in gidan ya tsaya batare da ya shiga ba , itama batace masa
uffan ba ya sauka daga cikin motar yayi tafiyar sa , fitowa Aysha tayi taje ta k'wank'wasa k'ofar
gidan , Habu ne ya zo da sauri ya bud'e mata yana fad'in " sannu da zuwa har kundawo kenan
? Aysha tayi murmushi tace " wallahi har mundawo ashe in mutum ya nutsu ma babu wuya
koyan motar , murmushi Habu yayi yana fad'in " Allah yasa anfara a sa'a Aysha tace Ameen......
Komowa tayi ta shiga cikin motar ta zauna sannan ta kunna tashigar da ita ciki , a laifi
sosai Aysha tana da basira , shiyasa ko a makaranta malaman ta suke alfahari da ita .....
Jabir sosai yake zuwa club club wai ko Allah zai sa yaci karo da Aysha , sai dai kwata
kwata bai san zuwa club baya cikin layin Aysha ko kad'an , ganin yajera kwana biyu yana
yawon neman ta yasa yagaji ya hak'ura da zuwa , sai dai sosai Aysha tabashi mamakin yadda a
wannan karon tafishi wayo , tabbas duk inda take a fad'in garin nan sai ya nemo ta , zai nuna
mata shima ba kanwar lasa bane ......
Kwata kwata Aysha ta manta da wani Jabir wanda tayiwa lak'ani da d'an sa'ido ,
Rayuwar su sukeyi ita da Gogal da Habu cikin kwamciyar hankali , gashi kullum sai Farouq
yazo sunfita koyan motar , yanzu haka har ta iya sosai amman tak'i tabarsa ya huta....
Gogal sosai ta murje tayi wani kyau abinta , abinka da farar fata tamkar katab'a ta jini ya
fito , kullum tana cikin ac ga kwana cikin ac ba ruwan ta da sauro , sosai Aysha take kulawa
dasu wajen cin abinci medadi , duk da yanzu hankalin Gogal yana kan Aysha akan yadda taga
tana kashe kud'i , kwata kwata Aysha ta manta da yadda take bida komai a b'oye kar Gogal
tagani , yanzu har wayar ta babba ta bayyana ta tana fito da ita , yauma kamar kullum suna
zaune a falo suna kallo Gogal hankalin ta nakan Aysha wacce ke danna wayar ta tanayin chat
d'auke da murmushi a fuskar ta , ganin kwata kwata ta maida hankalin ta ga waya yasa Gogal
yin gyaran murya tace " wai Sayyada yaushe kika samu wannan Aba haka ? Aysha sai da taji
hanjin cikinta ya ya mutsa kafin tayi ta maza tace " Batawa bace Gogal , ta Asma'u k'awar nan
tawa ce na aro ta , kinsan ina koyan motar to dole sai da irin wayoyin nan zan iya , Gogal
dayake ba sanin kai tayi ba tuni Aysha ta zage tashiga shirya mata k'arya , Gogal duk da ta
yadda da Aysha d'ari bisa d'ari amman sai tasamu zuciyar ta dayin rawa akan Maganar Ayshar ,
haka dai tabar abin aranta batare da takuma cewa Uffan ba.......
Hameed kusan kullum sai yaje Unguwar su Aysha , amman kullum indai yaje zaisamu
gidan yadda yabarshi , yauma yana zuwa hakan ce ta kasance kamar kullum , tsayawa yayi
yana nazari sai ganin wani yaro yayi zai wuce , kiran sa yayi yaron yazo Hameed yace " dan
Allah k'anina ko kasan inda masu gidan nan suka tafi ? yaron yace " wallahi tashi sukayi kuma
bansan inda suka koma ba , Hameed ya maimai ta kalmar tashi sannan yace " kozaka shiga
wancan gidan ka tambayo min inda suka koma , yaron ya kalli gidan sannan ya kalli Hameed
yace " ai gidan mune kuma bamu san inda suka koma ba , nan Hameed ya zaro d'ari biyar
yabawa yaron yana fad'in " ungo to nagode kaji , yaron ya ansa yana godiya shikuma ya juya
yanufi motar sa yatafi ....
Alhaji Na Lamma yana zaune a falon sa na sama yana nazarin wasu takardu , Farouq
ne ya shigo d'auke da sallama abakin sa sannan yasamu waje ya zauna , gaida Mahaifin nasa
yayi cike da girma mawa sanna yace " Daddy ina son yin magana dakai , Alhaji Na Lamma
yadubi d'an nasa wanda yaga ya rame sosai yace " ina saura ranka , Farouq yanisa sosai
sannan yace " Daddy dan Allah meye had'in ka da wannan yarinyar da har take irin wad'an nan
abubuwan ? murmushi Alhaji Na Lamma yayi irin nasu na manya yace " cool down my luvly
son babu abinda ya had'amu da ita kawai dai kabar wannan maganar banason kadamu ,
Farouq sosai yaji rashin dad'in yadda mahaifin nasa yake neman mai dashi k'aramin yaro ,
duban Daddyn nasa yakuma yi sannan yace " a gaskiya Daddy bazan iya hak'ura ina kallon
k'aramar yarinya tana juya ka yadda takeso ba , zan je nasa meta ko wacce za'ayi wallahi sai
dai ayi , mik'ewa Farouq yayi a fusace zai fita Alhaji Na Lamma yayi saurin dakatar dashi da
cewa " Farouq karka kus kura kace zakaje wajen Aysha , ko kamanta laifin da kayi mata kai da
abokan ka ne ? shuru Farouq yayi tare dayin k'asa dakai , cikin zuciyar sa yafara fad'in " lallai
wannan yarinayar ta wuce tunanin sa wato har ta sanar da Daddyn sa abinda suka mata ,
baigama tunani ba yaji Daddyn nasa nacewa " inaso kafita daga sabgar Aysha , tsakanin ka da
ita koya mata motar sai kuma in ta buk'aci kayi mata wani aiken , dan haka ka kiyaye banson
insake jin wani abin ya b'illo , k'asa dakai Farouq yayi sannan ya amsa da to ya fice daga
d'akin......
Da kallo Alhaji Na Lamma ya bi bayan Farouq , cikin ransa yace " laifinka yafi yawa sosai
agun Aysha fiye da nawa laifin , nasan saboda tasan kai d'ana ne tazab'i ta rama abinda kayi
mata ta wannan sigar , tabbas nasan dole wata rana Dole zata gyaru tadaina rayuwar da take ,
Allah yagani inasonta da aure a yanzu inda zata amince min amman nasan baxai yuwuba ma ,
Gashi ta sabamin da jikinta kuma haryanzu banji jiki me dadi irin saba duk irin neman matan
danayi.....
Hameed yau tunda yatashi yake shaawar zama a k'ofar waje dan ya k'arewa unguwar
tasu kallo , kujera ya fito da ita ya zauna tare da lapton d'insa yafara danna wa , dai dai lokacin
Aysha tayi shigar ta ta hijab har k'asa tare da saka Nik'af ta fito wai zataje makaranta , tana
fitowa tafara kalle kalle tamkar me neman wani abin , dai dai lokacin Hameed ya d'ago da
kansa yana duban saitin wajen da Aysha take , da sauri ya mik'e yana kallon inda take sosai ,
cikin zuciyar sa yafara magana " tabbas wannan in ba Aysha bace to 'yar uwar tace , dan irin
yadda Aysha take shigar ta itama wannan d'in haka takeyi , gashi yanayin jikinsu d'aya anya
bazaije yaga fuskar taba ko Ayshar sace ? ......
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
_NA_
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Alhamdulillah Ala Kulli Halin_
_Page._ 15
Aysha tace " wannan me gadin inaso ka sallamesa dan bana buk'atar sa , sannan
kajawa Farouq d'anka kunne lallai karya kus kura ya tako mana cikin gida , Alhaji Na Lamma
tana magana yana kallon ta tamkar ya janyota ya shak'eta ta mutu kowa ya huta , tamkar Aysha
tasan me yake ayyana wa tace " kanajin tamkar ka shak'eni na mutu kowa ya huta ko ? to
kasani ko ka kashe ni dole bazaka tsira ba , dan komai da mukayi k'awata tasani kuma tana da
videon komai a gunta itama , murmushi Alhaji Na Lamma yayi sannan yace " meye ya kawo
maganar kisa kuma Allah ma ya kiyaye ni ko kiyashi ban tab'a kashewa wa bare kuma mutum ,
mik'ewa Aysha tayi tana nuna masa ko ajikin ta maganar sa sannan tace " ni zan tafi sai wani
lokacin in mun sake had'uwa , dan banaso ko sau d'aya naga k'afar ka agidana mutuk'ar na tare
, sannan wannan kujerun karka kwashe su ina son su da kayan kallon nan , Alhaji Na Lamma
yace " duk nabar miki su babu damuwa , ni da shawarar da nakeso muyi itace me zai hana ki
amince kawai muyi aure da irin wannan rayuwar , nayi Alk'awarin yi miki duk abinda kikeso
mutuk'ar kika amince min , Aysha ta dubi Alhaji Na Lamma sosai sai sannan tafara k'are masa
kallo ganin wani k'aton tumbin sa , gashi wani bak'ikk'irin dashi sai wani murmushi yake shi ala
dole ya burgeta , Itama murmushin tayi sannan tace " kayi hak'uri Alhaji ka riga ka makara ,
bazan auri wanda nasan d'an sa kafin nasan saba , da sauri Alhaji Na Lamma ya dube ta
alamar son jin k'arin bayani " ta d'aga kai alamar da gaske take tace " tabbas Farouq yasan ni
shima tunkafin nahad'u dakai , kaga bazan iya aurenka ba kuma koda aure zanyi gaskiya
banajin zan iya auren ka Alhaji , dan haka nabarka lafiya sai wani lokacin , tana gama fad'ar
hakan bata jira cewar saba ta fice daga cikin Falor gaba d'aya......
A ranar su Aysha da Gogal suka tare a gidan Alhaji Na Lamma , da suka tashi tarewa
basu gayawa kowa ba dan Aysha tace basai kowa yasani ba dan kar ayi musu shune tunda
anga sun sami ci gaba , Habu me shagon gidan su harshi suka tare agidan saboda yana da
kirki kuma suna shiri sosai dasu , motar Aysha tasa Alhaji ya tura Farouq ya d'auko ta ya kawo
mata gidan da zummar fara koya mata motar cikin satin .......
Hameed tunda ya sauka a airpot yake jin wani sanyi yana ratsa zuciyar sa , tabbas zaiyi
k'ok'arin shawo kan Aysha wannan lokacin , dan yana sonta sosai bayajin zai barta takuma
kufce masa , a haka direban gidan su yazo ya d'auke sa suka nufi gida ....
Jabir Sai dare ya nufo gidan su Aysha dan jin maganar data ce masa zasuyi , yana zuwa
yasamu gida a rufe da k'aton kwad'o , shima shagon Habu haka yake a rufe da k'aton kwad'on ,
har wajen k'arfe goma yana k'ofar gidan yana jiran yaga ta inda zasu b'illo , ganin sha d'aya har
ta gota yasa yabar k'ofar gidan yatafi......
Washe gari haka yakuma zuwa k'ofar gidan kamar yadda yabarsa haka yagansa , tunani ya
shiga yi akan ina suka tafi haka har suka kwana ? yana tsaye yaga wani yaro zai shiga jikin
gidan yace " zonan kaji , yaro yazo Jabir yace " dan Allah k'anina kasan inda masu gidan nan
suka tafi ? yaron yace " Gogal tashiga gidan mu jiya tace tashi zasuyi zasu koma wani gidan ,
Jabir yace " tashi kuma ? yaron yace Ae , Jabir yace " kasan inda suka koma dan Allah ? Yaron
yace " wlh bamu san ina suka koma ba , dan bawanda yarakasu bare aga gidan , Jabir yace " to
nagode sosai k'anina kaji , Yaron yatafi abinsa yabar Jabir tsaye yana kai komo , cikin ransa
yace "dama tasan tashi zasuyi shiyasa ta tsaya ta saurareni jiya harda cemin wai zamuyi
magana , tabbas duk inda kuka koma saina nemoki Aysha bazan tab'a k'yaleki ba......
Aysha tunda suka koma Gogal keta mamakin girman gidan , Habu kansa yayi mamakin
ace wai a makaran ta Aysha aka bata kyautar gidan , dan shifa dama tuntuni yana zarginta dan
dai bashi da hanyar tuhumar ta , Gogal sosai ta jinjinawa wanda yabawa Aysha kyautar wannan
gida haka , ta dubi Aysha tace " gaskiya kowaye yabaki kyautar gidan nan yana da mugun kud'i
sosai , wannan gida kamar gidan masu kud'i , yakamata ace kin kaini wajen sa nayi masa
godiya dashi da malaman naki , Aysha sosai taji fad'uwar gaba amman sai ta dake tace " dama
sonake sai mun nutsu muje kiyi musu godiya dan kwanan na ma zamu kuma yin wata
musabik'ar , itace wacce in Allah yabani naci to kujerar makka za'abani , wata zabura Gogal tayi
tace " Makka fa Sayyada ? Aysha tace " E mana Gogal , to kowannan gidan da motar ai sunfi
kujerar Makka tsada , Gogal tace " Alhamdullilah Allah yasa kici kinga sainaje a madadin ki in
sauke farali , nan Aysha ta shiga tsara Gogal zancen k'arya da gaskiya ita kuma tana
yadda.......
Yamma nayi Hameed ya shirya cikin shigar sa ta Alfarma , sai zabga k'amshi yake
tamkar wani sabon ango ya nufo gidan su Aysha , yana zuwa yaga gidan rufe da k'aton kwad'o ,
take yaji k'irjin sa ya buga yafara addu'ar Allah yasa ba tashi sukayi daga gidan ba , haka
yagama zama amman ba wanda yazo wucewa ma bare ya tambayesa , haka ya juya ya tafi jiki
a sanyaye yana jin tamkar ya fashe da kuka..........