Showing 60001 words to 62695 words out of 62695 words

Chapter 21 - YAR HANNU BOOK COMPLETE

Zee Md   

11 Jul 2025

3845

, dan acan ma London akwai mata wad'an da suke son sa sosai amman duk
yak'i basu fuska........

Koda su Aysha sukaje wajen saida sark'ok'i , sai da Khalid ya siya mata na Million d'aya
da dubu Hamsin , dan zab'a tayi sai dataji masu kud'i dayawa tace su takeso , Khalid sosai yaji
fitar kud'in amman gudun kar ta gane ya dake tamkar wani Alhajin Birni , da suka taho hanya
tasa shi ya biya da ita wani Shopping Mall tayi siyayyar dubu d'ari nan ma ya biya , Khalid
suna fitowa ya nuna shima yanaso tabashi jikin ta dan haka su biya Hotel yakama musu waje ,
ko kad'an Aysha bata damuba dan dama jiran wannan ranar take , dan tasan daga wannan
ranar bazai k'ara ganin Nonon ta bama bare jikin ta , haka sukaje Hotel Khalid ya kwashi gara
sosai ,kusan sumewa yayi saboda sambatu dan iya jin dad'i yajishi a tare da Aysha , sai yake
ganin ko nawa ya kashe mata bai fad'i ba ganin yadda ta rud'ashi shima , sosai yayi mamakin
yadda Aysha ta k'ware wajen iya wasanni ,ko dayake bazai mamaki ba ganin ta wayayyiyar
Yariya wacce tagaji da had'uwa, haka suka gama d'ebewar su sannan sukayi wanka suka nufo
gida......

Aysha tun a farkon layin su tasa Khalid ya sauke ta , koda zata fita daga motar sai da
Khalid yace " Babyna yaushe zamu kuma had'uwa ne ? dan gaskiya kinjiyar dani wani dad'in

da ban tab'a ji ba sai sau d'aya , Murmushi tayi sannan tace " sau d'aya Dear ashe katab'a yin
sex ? Khalid yace " natab'a kwanciya da wata yarinya duk ba'ason ranta ba mukayi kuma shine
farkon yina nima bana cikin nutsuwa amman haryanzu abin na raina , Aysha wani abune
yataho mata ya tokare k'ahon zuciyar ta , kallon sa tayi cike da tsana tace " Saboda me ya
tsaya maka arai kuma alhalin kace ba'ason ranta kayi ba ? jin yadda tayi maganar yasa ya dube
ta , sai sannan Aysha tayi saurin ankarewa ta sassauta muryar ta tace " sorry Dear tausayin
yarinyar naji ,amman meyasa kayi mata haka Alhalin bataso ? Murmushi yayi sannan yace "
gaskiya sha'awarta tadameni kullum in muna tare to sai kinga abata a mik'e saboda yadda nake
shaawar ta , ban daina jin hakan ba har sai randa na kusan ce ta , tana kuka tana magiya
amman haka idona ya rufe na keta mata mutuncin ta , Aysha jitayi kamar a lokacin Khalid yake
keta mata mutunci , hawaye ne ya cika idon ta wanda ta kasa iya maidasu , tabbas Khalid ya
zalince ta dan shine sanadin komawar ta wannan rayuwar , yanzu waye zai aure ta a irin
wannan rayuwar tata ? Meza tacewa Yaranta dazata haifa nan gaba ? taso ace Mijinta wanda
zai aure ta shine zaifara sanin ta a duniya , amman Khalid ya rusa mata duk wani shirin ta ya
lalata mata rayuwar ta , yasa taci gaba da sab'on mahaliccin ta , duk da tashiryu bayan zubar
da cikin da tayi wanda yayi mata , Farouq shine ya maida ta ruwa shima yasa ta koma *'Yar
Hannu* , tabbas Khalid azzalumine ya cuceta a rayuwar ta , jin tayi shuru yasa Khalid yin
magana yace " meye naji kinyi shuru My Baby ? wani guntun Murmushi tayi sannan tace "
wallahi danaji abunda kayiwa Yarinyar nan sai na tuno da wani Malamina a makaranta nima da
yayimin fyad'e , Khalid yace " ayya sorry Baby kice mugun malami shine yafara yi mana hanya ,
nima kinsan Allah nine nafara yiwa yarinyar nan hanya , daga baya tasamu ciki nikuwa nayi
mata korar kare , dan a ganina taya za'ace daga kwanciya sau d'aya wai ciki yashiga ai tazo da
iskanci , sotake na aure ta ganin bata da wani asali gasu talakawa ba k'aruwa yasa na yi mata
fata fata muka rabu , Aysha jitayi in bata yi saurin fita daga motar Khalid ba to tana gab da
had'a masa jini da majina , shiyasa tayi saurin d'aukar kayan ta tace "muyi waya My dear , bata
jira cewar saba ta fice da sauri abinta , Khalid ko ajikin sa bai kawo komai ba sai ma bin
Mazaunan ta dayayi da kallo yana kuma wassafo dad'in daya sha ajikinta.......


Hameed yana zaune kamar ance masa ya kalli hanya ya hango Aysha ta nufo ta wajen
dayake , da sauri ya mik'e yana murza idanun sa itace dai ba gizo take masa ba , kwata kwata
Aysha bata kula da Hameed ba har tazo ta gifta ta gaban sa , haka yashiga binta batare da yayi
magana ba , sai datazo k'ofar gidan su lokacin Habu na zaune yanajin radio ta wuce shi yana
mata sannu da zuwa , da yauwa ta amsa ta shige ciki abinta shikuma Hameed yaja ya tsaya
gana yiwa Habu sallama.........



*Ina mutukar Son Comment d'inku Masoyana*
_Yin Comment shine ke k'ara mana k'aimin yin Typing_✍✍


*Saina jiku*

*'Yar Mutan Kanawa*
_Ce_
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*




_NA_
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*Bisimillahir Rahamanir Rahim*





_Page._ 34


Aysha firgigit tayi ta mik'e dan batasan sanda tafara baccin ba , duban Hameed
tayi sannan tayi k'asa da kanta dan wani kwarjini yake mata , shuru sukayi kowanne yana sak'e
sak'e aransa , can Hameed ya nisa yace " kishiga Office d'ina sai ki kwanta a ciki in bacci kike ji
, Aysha a hankali tace " ba bacci nakeji ba yanzu ma bansan sanda nafara gyangyad'i ba ,
Hameed ya dube ta sannan yace " amman kinsan dai nan akwai sauro kuma cizon sa zai iya
haifar miki da zazzab'i , Aysha tace " ai zan iya shiga d'akin da Gogal take inyaso danaga ta
farka sai na fito ko , Hameed yace " ai dama ba'a hanaki shiga ba kwata kwata kawai dai a
yanzu tunda tana farkon ciwon dole in ta farko taganki abin zai dawo mata sabo , amman nan
da zuwa safiya ma insha Allah zaki iya shiga ko yaushe kikeso , Aysha ta share hawayen da
ya gangaro mata sannan tace " nagode Dr bari nashiga kafin ta farka sai na fito , bata jira
cewar sa ba ta tura k'ofar d'akin tashige abinta........

Hameed komawa yayi office d'in sa ya had'a ruwan tea yana sha , tunowa yayi ba lallai in

Aysha taci komai ba , da sauri yatashi ya d'auki flast d'in shayi da biscuit ya nufi wajen nata , ..
Yana zuwa ya tura k'ofar d'auke da sallama sai dai ji yayi shuru ba a amsa masa ba ,
gadon da Gogal take ya kallah yaga idanun ta a bud'e alamun ta farka , tuni ya duba ko inah
baiga Aysha ba , hakan ya sheda masa ta fita kenan dataga Gogal d'in ta farka , to ina ta shiga
tunda bai ganta a waje ba kafin ya shigo ? gadon ya nufa d'auke da murmushi yana fad'in "
sannu da jiki Mama dafatan yanzu babu abinda ke miki ciwo ko ? Gogal ta d'aga kai batare da
tayi magana ba , Hameed yace " bari na had'a miki ruwan tea kisha sai inbaki magungunan ki
kisha ko , da sauri ya had'awa Gogal ruwan shayi sannan ya tashe ta ya jingina jikin filo,
hawowa yayi kan gadon da kofin tea yashiga bata a hankali yana lallab'a ta , aikuwa babu laifi
sosai Gogal tasha ruwan shayin wanda yaji kayan k'amshi , ..

Duk abinda akeyi Aysha na hangen su ta cikin toilet d'in d'akin , tunda taga Gogal tafara
motsi tayi saurin shigewa toilet d'in tare da addu'ar Allah yakawo Dr.Hameed d'in , Allah kuwa
ya amshi addu'ar ta saigashi yazo har da Shayin sa a hannu , dama tunani take me za'abawa
Gogal d'in taci gashi dare yayi , yadda Hameed ke bawa Gogal tea cike da nuna kulawa ba
k'aramin birgeta yayi ba , take taji wata k'aunar sa na ratsa duk ilahirin jikinta tabbas Hameed
shine irin mazan da mata ke muradin samu , da ace lokacin da take Sayyadar tace da babu
abinda zai hana ta amincewa da auren Hameed , dayake toilet d'in a tsaftace yake shiyasa
Aysha bata damu da zaman ta a ciki ba,....

Hameed ya kammala bawa Gogal magungunan ta , duban sa tayi kamar zatayi magana sai
kuma ta fasa , Hameed yayi murmushi yace " ki kwantar da hankalin ki karkisa damuwa aranki
yanzu ki kwanta ki huta zuwa safiya , Gogal itama murmushin ta maida masa batare da tace
komai ba ta kwanta a hankali da taimakon Hameed.....
Hameed zama yayi a gefen Gogal yana ta danna wayar sa , ba'afi minty 10 ba Gogal ta
koma bacci abinta , rufe mata jiki Hameed yayi tare da rage mata gudun fanka sannan ya mik'e
zai fita daga d'akin , gani yayi ana k'ok'arin bud'e toilet dan haka ya tsaya dan ganin waye ,
Aysha ce ta fito tana sunkuyar da kanta k'asa , Hameed cikin ransa yace " dama tana cikin toilet
duk wannan dadewar ? A fili kuma ya kalleta yace " Dama kina cikin toilet ? Aysha ta d'aga
masa kai batare da tayi magana ba , d'an tab'e baki yayi sannan yace mata "ga tea can a flast
ki tsiyaya kisha sannan ya mik'a mata biskit yace "ki had'a da wannan dan nasan ba lallai
inkinci wani abun ba , yana gama bata tasa sannu biyu ta ansa tare da yi masa godiya ya shige
ya fice daga cikin d'akin.......


Washe gari tun asuba Aysha ta farka dama ba wani bacci tayi me tsayi ba , shiga toilet
tayi ta d'auro arwala sannan ta fito ta shimfid'a d'an kwalin ta ta tada sallah , bayan ta idar ta
zauna tana lazimi da yatsun hannun ta , abinda Aysha bata lura ba shine tun fitowar ta daga
toilet Gogal ta farka ta zuba mata idanuwa , wani kallo Gogal takewa Aysha wanda yake nuni
da tanajin harda sakacin ta a lalacewar da yarinyar tayi , kuma a yanzu tadaina ganin laifin
Ayshar dan duk acikin abinda yafaru da ita ta had'u da yaudarar 'Yaya maza ne , Abinda yafi
d'aga mata hankali shine jin wai har ciki Aysha tayi kuma taje ta zubar batare da ita ta fahimci

hakan ba , tabbas tayi sakaci sosai kuma nadama tashige ta na yadda tayi sakaci da rayuwar
Marainiyar Allah , hawayene suka shiga zubowa ta idanuwan Gogal tanajin tausayin kansu ,
yanzu wane namijin arziki ne zaiso Ayshar har ya aure ta ? tabbas wannan abu zaiyi wuya
tunda ta riga tazama uwar mata , Aysha d'aga hannu tayi tana addu'a akan Allah ya bawa
Gogal lafiya tare da neman gafarar ubangiji akan laifikan ta data aikata , hawaye na zuba tana
fad'in " Astagafurullah Allah natuba kayafemin bazan sake aikata zina ba , duk addu'ar da
takeyi Gogal najin ta tana kuma amsawa da Ameen , sai da ta shafa addu'ar sai taji Muryar
Gogal nacewa Sayyada zo ki kaini band'aki in kama ruwa nima nayi sallah , Aysha da sauri ta
waiwayo dan batasan sanda Gogal d'in ta tashi ba , wani sanyi taji a ranta hakan na nufin Gogal
ta rage fushi da ita kenan , da sauri ta nufi wajen gadon tana kamo ta tashigar da ita band'aki ,
bayan ta gama kama ruwa tayi arwala sannan Aysha tazo ta fito da ita daga cikin toilet d'in ,.....

Bayan ta idar da Sallah Aysha ta dube cike da jin wata iriyar kunyar ta tace " ina kwana ya
sauk'in jiki ? Gogal ta amsa da lafiya lau jiki Alhmd babu inda kemin ciwo , shuru ce ta biyo
baya kafin Gogal tayi gyaran murya tace " Aysha inaso kibani aron hankalin ki , tabbas kinyi
wauta da tun farkon da Khalid ya kusan ceki baki gayamin ba , da tun a lokacin zan d'auki
mataki akan hakan , amman saboda kina tsoron kar nashiga damuwa yasa kika cuci kanki har
abin ya girmama , duk da nima nataka rawa a komawar ki haka ta b'angaren sakaci da rashin
saka idanu akan ki , duk irin yadda kike kashe mana kud'i bantab'a kawo wa ba a makaran ta
kike samu ba , tabbas nima nayi kuskure babba kuma ina neman yafiyarki a akan hakan ,
Aysha da take kuka tunda Gogal tafara magana da sauri tace " baki da laifin komai Gogal , nice
na zalinceki da halayena masu kyau taya zaki yadda zan aikata wani halin makamancin
wannan , ban daina shigar mutunci ba ban kuma daina janyo aya ba duk lokacin damu ke tare
dake , nice na yaudareki da fuska biyu wacce na zama saboda dalilin d'aukar fansa , tunda ga
lokacin da Khalid ya yaudareni kuma yazo ya gujeni tare da gayamin maganganu mara sa dad'i
nafara shirin d'aukar fansa araina , kwata kwata banyi basirar cewa cutar da kaina zanyi garin
d'aukar fansar ba , idanuwa na sun rufe wutar d'aukar fansa na ruruwa a cikin zuciyata , na
d'auki fansa Kamar yadda na k'udurta amman ina meyin tarin nadama da abinda na aikata wa
rayuwata , wallahi natuba Gogal bazan k'ara aikata zina ba har nakoma ga mahaliccina , jikin
Gogal ta kwanto tana kuka me tsuma zuciya tare da tarin yin nadama game da son zuciyar ta
data bi..........






_Ina farin cikin sanar da Mata 'Yan k'walisa da Amare masu shirin shiga daga ciki , ga dama
ta samu maza ku garzayo dan gyara jiki tare da mallakar tsumi gangariya ,_

*Akwai maganin gyaran nono ga macen da take shirin yaye yaron ta , ga turarukan gyaran jiki
dana turara d'aki da na wanka tare da Humrah me ratsa zuciyar megida , akwai kulacca da man
shafawa me kamshi ,*

_Uwargida Amarya maza ku garzayo dan mallakar naku , gyara shine mace Mata kutashi
ku gyara dan kwato mazajenmu daga wajen matan banza _

*Dan samun kayanmu ku tuntubi wannan number 07046107812*
Sai najiku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login