Showing 27001 words to 30000 words out of 31090 words

Chapter 10 - DEPRESSION (damuwa)BOOK ONE TAKUN FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO

31 Oct 2025

1383

yadda kake min, sannan ka nuna masa kauna kamar yadda ka nuna min" daga Haka Abjeed ya fita daga cikin gidan Baki daya Yana goge hawayen Dake Shirin gangaro Masa.




"Adeena maza ki..."karka cemin komai abbanmu " Adeena ta dakatar da shi da sauri "abbanmu meyasa zakayi Mana haha, duk da Ni yarinyace karama ,za a iyacewa bansan menene so ba Amma nasan komai, nasan da cewa baka son uncle sannan Kuma baka kulashi, to meyasa ,abbanmu banason jin komai amsa kawai nake son ji, abbanmu bakasan zafin da zuciyata take min ba ko, to ciwo nakeji a duk lokacin da naji ka batawa uncle Rai ,inajin zafi da daci acikin zuciyata , yau nima naji sha,akwai son sanin asalin labarin A.K FADAMA ?"



"Nikam nashiga uku dan Allah abar wannan zancen daga baya ayi ,abba kazo mukamashi musa a mota muje asbiti kada su mutu" Ammi ta fada tana share hawayen.




"Mu kadai baza mu iya daukan Abeed Musa shi a mota ba, Adeena Maza jeki kirawo malan mai gadi ya taimaka Mana " batare da Adeena Tace komai ba ta karasa inda Mai gadi yake, ta kirawo shi, a tare suka taho zuwa inda Abba yake, durkusa wa Mai gadi yayi yace "subahanallahi alhaji Mai yake faruwa Haka , Naga alhaji karami a kasa ,lafiay?" "Lafiya ba lafiya ba yanzu dai ka taimaka mana musa shi a mota" ah Tom shikkenan " mai gadi ya fad'a tare da mikewa ya daga Abeed Abba ma ya Kama kafarsa ita ma momy ta tallafo shi ,Adeena ta bude kofar motar, suka sakashi a mota, yau dai abin da abba Bai taba yiba shi yayi ,wato tuki da kansa, batare da Bata lokaci ba Abba ya Soma Jan motar Mai gadi ya bude gate suka fita,










Gudu Abba yake sharara wa akan titin Yana tuki gumi Yana faman karyo Masa, idanun Nan nasa kuwa, sun kada sunyi jajur, Haka ya daure ya cigaba da tukin har ya karasa wani babban asbiti dake garin faransa , hon yayi wa Mai gadin ya bude, sanan ya danna hancin motar ciki, Yana shiga yayi parking a parking space din asbitin ,Ammi ce ta fito da gudu ta shiga cikin asbitin, tun daga bakin kofa take kwalla musu Kira, doctor's din fitowa sukai da sauri hankali q tashe suke kallonta, "lafiya ?,lafiya kuwa Baiwar Allah" "inafa lafiya Dan Allah ku tai maka Mana kada su mutu " " hajiya Ina yaran suke?" "Suna mota" Ammi ta fita suka bita a baya Har harabar asbitin, ba bu wani Bata lokaci Aka fito da bed aka dorasu a Kai sanan aka turasu zuwa ciki, ammi da Abba kuwa sun kasa zaune sun kasa tsaye sukai su dawo sukai sukoma Haka suka dinga Yi ,kowa yakasa zaune ya kasa tsaye.








Shi kuwa Abjeed tun da ya fita daga cikin gidan su Babu inda ya nufa sai , adama wa, ma,ana A.K FADAMA EXCITED , Yana karasawa ya bude kofar d'akin da ya shiga, Nan take abubuwa da dama' suka Shiga dawo Masa a wanan lokacin, take ya Soma tuna abubuwan da suka faru lokacin da suna zaune a cikin gidan, anan ne rayuwar da sukayi da abin da ya faru ya Soma dawo Masa sabo fill, bakin gadonsa ya samu ya zauna tare da dafa Kai , ya lumshe Ido ya furzar da iska daga bakinsa yace "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Innalillahi wa'inna ilaihirraju un !!wanan masifar da mai tayi kama, yaya Abeed Kana cikin jarabawar rayuwa" Yana tsaka da surutai shi kadai ya ga wayarsa tana ruri bugu biyu ya daga, abbane ,"hello Abjeed kana Ina Dan Allah ka dawo" "a,a abbana wallahi bazan dawo ba indai har gidan kane bazan sake dawowa ba," "haba Abjeed maiyasa zakace Haka indai Akan abin da nakewa Abeed ne na daina Ni dai BURINA kawai ka dawo" "allah abba bazan dawo ba shikuma yaya Abeed ka cigaba da masa abin da kakeso indai nine na hakura da gidan ka ,kaje Kai da allah abba ko Mai kakeyi Allah Yana ganinka indai abin da kayi dai dai ne Tun aduniya zaka ganu, kafin na kashe wayar Nan Ina son Abba na Dada tunatar maka da wata magana da ka manta, ba Kana cewa Yaya Abeed shine Mai kefi ba ,to kaima kana da laifi idan ka manta Ni Zan tuna maka, duk abin da Yaya Abeed yayi Kaine musabbabin komai Kar ka manta da wannan ,mommy azeema itace wadda zata baka wannan amsar , Ina fata yanzu ka gane inda na dosa" "na sani Abjeed ban manta ba wannan dalilin ne yasa nake son ganin zarah a rayΓ© bana son ta mutu dan Allah ka dawo karka ta fi ka barni kamar yadda Dan uwanka yazeed ya tafi ya barni abaya" "wallahi abba komai zakai bazan dawo ba ni danasan inda yaya yazeed yake a yanzu ma binsa zanyi" Yana Gama fadar Haka ya katse wΓ yar batare da ya sake cewa komai ba .

Abba kuwa zaman durshen ya sakeyi a gurin tare da kallon ammi yace "shikkenan shima yatafi" "nashiga uku Wai shima Abjeed din ya tafi ya barmu kenan?" Innalillahi wa'inna ilaihirraju un! " Ta sulake a gurin a sume.


πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 15*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 15*











Acan adamawa kuwa ummace keta faman Kiran numbar doctor ak fadama Amma Ina Bata shiga, Nan d'anan hankalin ta ya tashi ta sake kallon sumayya, itama sumayya kallon ta tayi Tace "Wai umma yauma babu sa a shikkenan inaga yadaina Kira ,to ko ya mutu ne?" "N'a ci uwarki a gurinnan ubanwa ya kasheshi insha Allahu ma yanan araye Bai mutu ba ,sokike kifada abakin mala iku narasa Wanda zai bani kudade, itama shegiyar yarinyar Nan ciremata kayannan tun da Bai daga ba, Kuma wallahi akanta Zan huce, Ni za asa asarar kudi, kigani fa Har naira dubu biyu na cire n'a sayawa yarinyar nan Kaya d'uk dan ya gani ya ji dadi ya turamin wasu kudin Amma yaki kunna wayar sa" umma ta fada lokacin da take damko Amnaa tana janta har ta cire mata Kayan, sannan ta SHIGA dala Mata duka kamar ita ce ta Hana Abeed din daga wayar, Allah sarki Amnaa ta dage sai zunduma ihu take, ",shegiyar yarinya Gama kukanki Babu Mai ceton ki wallahi uban nakima saura kiriss n'a hallakashi Har lahira" "innalillahi a,a umma sokike kimai damu marayu Dan Allah karki Soma indai akan wannan yarinyar ne gwara ita ta mutu" dallacan shashasha wazaki rainawa wayo mai uban naki ya tsinana Miki ,harda zakice min ke kar ya mutu ,to saina kasheshi din saime" umma tayi tsaki ta tashi tare da sakin amnaa a kasa, jikuke kwalla ta bugu da bango take tasake chanyarewa da kuka kanta ya kumbura.


*Faransa*


Tun da Abba ya sake zubewa a jikin bangon Bai motsa ba Haka ma momy tana zaune tana faman aikin kuka, Gaba ki daya ma ta manta da Zaid a cikin gida Yana baxcy Sabi da tsananin tashin hankali.


Doctor ne ya Soma Takoma in da suke bayan awa biyu da kawo su fu ad, Abba dai ganin yadda likitan yake tun Karo in da suke yasa ya tabbatar da cewa su Abeed ko sun mutune ko sun ta shi, Dan Haka da sauri ya nufi in da yake yace "doctor! Doctor!! Ya jikin nasu sun farka ko, Dan Allah kada ka fadamin mummunan labari sonake n'a san suna raye, kada kacemin sun mutu"


"Amm ka kwantar da hankalin ka alhaji indai yaran Kane cikin ikon allah yatashi kafadin su ,saΓ― dai muce alhamdulillah allah ta Kara mana lafiya baki daya, amma saΓ― dai alhaji akwai wata matsala guda daya, "matsala kuma tame?" Abba ya fad'a Yana zaro manya manyan idanuwan sa waje, "no ka kwantar da hankalin ka yar karamar matsala ce a yanzu, nan gabane nake tunanin zata iya zama babbar matsala" "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Doctor matsalar me?"

"Yaran ka duk da bansan mai yake daminsu ba ,Amma dai babban ya Dade Yana fama da damuwa a zuciyarsa Kuma muddum ba a daina yimasa abin da zai sashi a depression ba zuciyar sa tana gab da bugawa ,Dan ayanzu ma sai dai kuyi hakuri ya kamu da ciwan zuciyar" baya abba yayi tare da dafe kirji ya saki kuka Mai ban tausayi Yana girgiza Kai yana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Shikkenan wallahi duk laifi nane, duk abin da ya faru da shi nine silah"


Cikin kulawa da nuna dumuwa akai doctor yashiga lallaba Abba Yana Dan bashi Baki da llabawa Yana cewa "kayi hakuri alhaji ,komai kagani jarrabawa ce daga allah , to ka kaddara ma wanan ciwo da ta samu danka jarabawa ce daga allah kayi hakuri ka fawwala wa allah ,ciwan zuciya da ya Kama Abeed hakan baya n'a nufin cewa mutuwa zaiyi ba, a,a bazai mutu ba saΓ― lokacin sa yayi " "innalillahi wa'inna ilaihirraju un doctor bazaka gane ba, bazaka gane abin da nake nufi ba, Ni kadai nasan abin da nake ji game da abin da yasamu yaranna wallahi nasan komai ne akaso dari n'a wanan abin kaso 99 nine Sana di , doctor kada ka cemin shima fu ad din ya kamu da ciwan zuciya ,Dan Allah ka fadamin wani abin da zaisa zuciyata bazata sakΓ© karaya ba" abba ta ciga ba da kuka har da majina.


Shiru doctor ya danyi kamin daga bisani yace "tabbas ba irin wanan maganar Zan fadamaka ba ,sai dai shima fu ad shigen irin abin da na fad'a akan Abeed Zan sanar maka, domin ayan Zu idan tausayin ka ya hanani fad'a maka ,to fa na cuce ka domin ciwan zai coga ba ne da addabar zuciyar yaronka shiyasa gwara n'a sauke hakkina n'a sanar maka ,ko Babu komai zaka dauki mataki akai "

Shiru Abba yayi ya tsaya da kukan da yake ,can Kuma sai yace "shikkenan doctor Ina sauraron ka ,ko Babu komai nayar da da Allah shine Mai tsara komai ,Kuma shine Mai dorawa bawa duk kan abin da kaga ta sameshi domin ya jarraba shi yaga yadda zai dauki jarabawar".




"Haka ne alhaji ,wanan kwarin guywata dana gani a tattare dakai ba karamin burgeni yayi ba, irin ku akeso acikin duniyar nan masu karbar kaddara hannu bibbiyu mai kyau ko Mara kyau, yau wa yanzu bayan na fad'a maka sai ka biyoni kaga jikin nasu KO?"


"Oh Tom shikkenan Babu damuwa muje Amma Dan Allah doctor kada ka Bari mai dakina taji wanan batun, nasan idan taji hankalin ta bazai taba kwanci yaba kataimaka"

"Shikkenan alhaji insha allah bazan Bari ta sani ba ,muje ki!"


Tafiya suka Soma yi zuwa dakin Abeed dake farko kafin su karasa abba ta kalli likitan yace "yauwa yanzu kam n'a dan dawo hayyaci n'a ,fadamin shi Fu ad din Mai yake damunsa?"

"Uhm"

Doctor ya danyi murmushi n karfin hali kafin daga bisani yace "ba komai bane kusan irin ciwan su daya da yayan sa Abeed ,saΓ― dai shi baikai na Abeed ba, ban bancin anan shine Abeed ko ayaushe zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu tun da shi ciwan zuciya ya kamashi, shikuma Fu ad ciwan Bai kamashi ba ,sai dai Yana bara zanar kamasa sabi da damuwar da ya sa azuciyar sa, so ya kamata a ce kun kiyaye damuwar sa da duk wani abu da zai Bata Masa Rai" Jin wannan kashai din na doctor da yayi Masa yasa Abba yaji zuciyar sa ta Soma bugu ,tunanin rugimar fu, ad yake Yi yasan muddum idan Fu ad ya tashi dolene sai ya nemi wannan littafin domin ya karasa Karan tawa, zuciyar Abba cike da farga ba yace "nashiga uku wallahi tun da fu, ad ya San akwai abin da ake boye Masa nasan Babu mahalukin da zai Hana shi karasa karanta littafinnan, Kash maiyasa ma na nuna Masa inda book din yake, Gaba kidaya n'a sha,AFA namanta da duk wani abu da ya faru ,nayi tunanin Abeed kawai Zan batawa Rai Sabi da girman abin da nayi Masa, ashe Nima har Dani aceki innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Ta furta tare da bude kofar d'akin ya shiga,



πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 16*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 16*







Jiki Babu kwari Abba ya hango Abeed kwance idanunsa a lumshe sai zub da hawaye yake, da kamar ya fita, sai Kuma yayi karfin hali ya karasa ,kujera ya janyo zai zauna ya tsinkayo muryar Abeed Yana cewa "kada ka zauna abbanmu , bai ka mata ace ka zauna a gurin mutumin da baka so ba," jin maganar Abba yayi kamar saukar aradu bakinsa har rawa yake wajen cewa "Babana haba Abeed Ni nace maka bana sonka Taya za ai uba yace baya son dansa " "uhm abbanmu kenan ,lokacin yin wanan maganar ta wuce kama ta yayi ace iyanzu Kana gida Kana farincikin yanko likkafanin bonne mu, burinka ya cika Abba kayi sanadiyyar sa zuciyata kamu wa da ciwo, kasa rayuwa ta acikin masifa ,akullum laifina kawai kake gani baka ganin laifin zarah baka ganin laifin ka Ni kawai ka tsana idan Zara 'yar kace ta sunna nima d'an Kane abbanmu komai ya faru Abba Kaine ka fara lalalta komai shiyasa Allah ya nuna maka ishara akan Hakan mu" "no Babana kadai na fadan Haka indai wanan matsalar ce kasa aranka n'a hakura Kuma zamu dawo kamar da ,Zan kula da rayuwar ka" " uhm abbanmu kenan Babu lokaci, lokaci ya ruga da ya wuce ,karike kulawarka bana bukata ,lokaci ya wuce Kuma kasan Abba ance lokaci baya jira, albishir daya zanmaka shine ,idan Fu ad ya tashi Zan bashi Wanan littafin ya karanta iya karfin sa Har lokacin da zai Gane abin da kuke boye Masa" "nashiga uku Abeed kada Kai Haka, Dan Allah bana son rasa Fu ad ,wanan littafin zai iya sanadiyyar sa zuciyar sa ta buga ya mutu ya bar duniya, Dan Allah ka taimaka kaji" "abba walalhi Babu abin da zai Hana na bashi littafin Nan ya karanta , da bakason ya San komai ka dauki book din ka bashi ,daman nasani Haka zata faru, kuma ga ranar tazo ,abbanmu kayi hakuri kaddarace ga kudi ga mulki da sarauta Babu abin da baka hada ba, komai Allah ya baka , Amma ya dauke maka kwanciyar hankali da nutsuwa, depression babbar matsalace ga Dan Adam, Kuma ba kowa bane asalin damuwa sai Kai Abba Ni kawai dorawa nayi" kuka Abba ya fashe dashi gami da mikewa jiki Babu kwari ya fita.



Abba Yana fita Abeed ya runtse ido tare da furzar da iska daga bakinsa, ya lumshe Ido, Yana zub da hawaye yace "uhm abbanmu kenan ,Allah ya fitar da mu daga wanan jarrabawar Ni ayanzu nasan tawa tarugata kare " daga Haka Kuma ya Kara sakin murmushin karfin hali ya daga idonsa sama Yana kallon silif.


Abba kuwa bayan ya fita gurin doctor ya koma yace "doctor ka kaini dakin da Fu ad take" Babu musu doctor ya shige Gaba Abba ya bishi a baya Har zuwa d'akin da Fu ad yake, tura kofar yayi ya Shiga shikuma doctor ya dawo office dinsa, kaitsaye Abba Shiga yayi ,a zaune ya samu fu ad ya hada Kai da gywa idanun Nan nasa sun kada sunyi jajur, jiki a sanyaye Abba ya karasa bakin gadon ya zauna, shiru ya danyi baice komai ba ,Haka shima fu ad Bai d'ago ba Kuma Bai Masa magana ba, har tsawan yan dak'iku ,can Kuma sai Abba ya dauki hannunsa ya Dora akan hanun Fu ad kana ya d'ago sa, yanayin yanda yq ganshi ne yasa Abba ya tsorata ,zuciyar sa ta SHIGA bugu bakinsa ya kasa furta komai ,ya bude Baki zaiyi magana Fu ad ya daga Masa hannu Ade da cewa "abbanmu Kar ka cemin komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login