Showing 3001 words to 6000 words out of 31090 words

Chapter 2 - DEPRESSION (damuwa)BOOK ONE TAKUN FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO

31 Oct 2025

1375

"malan lafiya Naga jikinta duk ciwo ?" "Uhm kedai Bari wallahi fadowa tayi mikomin madarar na Bata" Mika Masa tayi ,har ya dakko kofin zai fara Bata da chokali sai Kuma yaga sai tiriri take "a,a haba zainab Yana ga madarar Kuma tana da zafi wanan ai sai ta kona Mata Baki" "ah haba malan idan baka gode mun ba ai bazaka tsinemin ba duk kokarin danari wajan hada madarar nan abin da zaka sakamin da shi Kanan nufinka Zan iya cutar da ita kenan" ta fashe da kuka har da majina "kawai dai kace min Dan bani na haifi yarinyar Nan ba nakeso na kasheta, Haka kakeso kace ko Sabi da bani na haifeta ba shine zakace nayine domin na Kona Mata Baki haba malan " "kinga Dan Allah ya Isa karki dameni ki karamin wani damuwar kiyi hakuri ba abin da nake nufi ba kenan yanzu dai dauki ki firfita ya Sha iska" "uhm shikkenan Amma malan shikkenan dai.." "shikkenan me Ke barshi ma nasan yadda zanyi" Afusace ya dauki madarar ya kurba ya jujjyata a bakinsa sann ya durkusa fuskar yarinyar daidai bakinta ya Dora nashi bakin yashiga zuba mata madarar a hankula tana shanyewa idanunta a bude cikin idon mahaifin na ta sai faman kallonsa take kamar Mai Shirin Gane wani abin, "nashiga uku ikon ALLAH malan mai zan gani tsabar soyayyar ce yasa saΓ― ta Haka zaka Bata madara tasha?" "Banza yayi mata ta cigaba da diban madarar ya na zubawa a bakinsa Yana Bata har ta koshi, bayan ya kammala ya kalli zainab sake zaune a gefe ta saki Baki yace "bani zani" "malan mai kuma zakayi da zanin?" "Ina ruwanki ki bani zani nace" "Tom" Tace sanan ta Mike ta d'akko Masa zani ta Mika Masa sanan ta tsaya tana kallon abin da zaiyi da zanin, abin mamaki taga ya Dora jaririyar a bayansa ya saka zanin ya daureta Yana faman jijjigata batare da yace uffan ba ,haushi da bakin ciki ne ya kama zainab Dan Haka Tace" Amma malan yanzu duk matan dake cikin gidanan gani ga sumayya ga munira duk bamu Isa mu Goya taba sai Kai haba malan wanan ai duk salon ka janyo mana zagi ne" still Bai kula taba ya cigaba da kaiwa da komowa a cikin falon Yana jijjiga ta har tasamu tayi bacci "Dan Allah malan ka sakko ta n'a goyata yanzu idan wasu suka shigofa saΓ― su zagemu Akan Haka" "Babu wan da zai zageki Akan Haka da ce 'yarki ce shine za a zageki akai amma wanan ana gani ansan mahaifiyar ta itace ta rasu yau kuma Bata da Wanda zai goyata saΓ― ni d'in kingane" ya karasa fadin Haka tare da ficewa daga dakin ya nufi dakinsa, "kutumar uba"zainab ta kurma wata uwar ashariya Tace "wallahi da sake tur'kashi lallai kam yanzu aka fara wasan.




πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 3*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 3*




"Umma Dan Allah ki daina da mun kanki akan wannan Dan abin mene Dan ya goyata" "dallacan shashasha rufemin Baki ke da bakisan ciwan kanki ba ,ko da Kuna yara Babu wadda yata'ba goyawa acikin ku sai yanzu zai wani Fara goyata Ni fa aduniya bana kaunar jinin fateema ya sarara a duniyar Nan, wallahi duk yadda za ai saina tarwa tsa rayuwar yaran Nan" " uhm umma kenan ance duk abin da babba ya hango yaro ko ya hau dala da gwaran dutse bazai hango ba to Ni yanzu na hango Miki wani abu da zai faru a Nan gaba" "to sumayya Mai kika hango?" "Ba so kike ki kashe jaririyar Nan ba karta girma?" "Eh hakane Amma yanzu Ina tunanin Babu wata hanya da Zan iya kasheta tun da mahaifinta kullum Yana makale da ita sai dai in ta girma na ci ubanta" "umma kenan to idan ta girman ma bazaki iya kasheta ba" "mai?" Nashiga uku mai yasa kikace Haka 'yarnan ?" "Abin da yasa nace Miki Haka lokacin da zata girma zaidu ya tasa yazama saurayi ya mallaki hankalin kansa ,Kinga kuwa Baki da damar taba kanwarsa a gabansa idan kika fiya takura Matama zai iya daukan kanwarsa su bar gidan Nan" "tabbas kuwa hakane Amma sumayya kina da basira Taya akai kika gano Haka ni ban sani ba?" "Uhm umma nifa 'yar yauce nasan komai n'a rayuwa kuma kullum idona dada budewa yake yanzu abin da zakiyi shine Dole zamuyi yadda zamu fitar da zaidu daga gidannan tun kafin ya girma ya mallaki hankalin kansa" "hakane 'yar albarkar 'yata" "to Amma umma hanyar da zamu fitar da shine bani da ita inason ya bar gidan Nan na har a bada yadda Abba ma zai tsaneshi ya koreshi da kansa" "hhhhh yarinya kina da uwa shu,Uma Taya zamu rasa hanya kedai kawai ki zuba Ido ki Sha kallo zai du a satinan mahaifin sa Zai koreshi da kansa" "to umma ko fadamin Mana Taya kenan kinsan yadda Abba take son zaidu kuwa shi kadaine fa namiji acikin mu?" " An jima da daddare Zan turoshi d'akin ku ki kasance cikin shiri ai kin dai Gane abin da nake nufi ko?" "Kan bala'i wallahi na gane ai kuwa Babu makawa mukayi Shirin Nan sai Abba ya koreshi Kinga sai musamu damar cin uwar yarinyar Nan " "ai dolema na hallaka jaririyar Nan ko Dan Sabi da akwatin gold dinnan" "akwatin gold Kuna ta me?" " Bakisan komai ba 'yanan Zan Baki labari Nan gaba kadan" "Tom shikkenan umma Bari n'a je n'a fara shiri".


*After one week*

Bayan sati d'aya da haihuwar yarinyar Abban su ya Yi sadaka wan da yayi daidai da kwanan mahaifiyar yarinyar a makabarta yau tacika bakwai Kuma yau ne suna Dan Haka ba ayi wani taro ba kawai ya yanka ragone na suna kamar yadda kowacce yarinya ko yaro idan yazo duniya ake yanka Masa, Haka itama aka yanka Mata katon rago sannan mahaifinta ya rada mata suna Mai dadi da ma,ana *FATIMA* wato sunan mahaifiyar ta ya mayar Mata Amma ana Kiran ta da *AMNAA* Masha Allah Allah ya Raya bisa sunnar annabi Muhammad (s.a.w)


Acan gida kuwa lokacin da zainab ta samu labarin sunan da Aka mayar wa da jaririyar saΓ― taji aduniya ta kara tsanar yarinyar domin gani take kamar fateema ce ta dawo "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Wannan Wace iriyar masifa ce ya tabbata dai sainayi kishi da wannan yarinyar to wallahi ba a isaba " "haba umma ki kwantar da hankalin ki Mana sokike Abba yagane kina bakinciki da zuwan amnaa duniya ,Allah idan kika cigaba da wannan mitar sai kin batamana shirinmu Gaba daya dan Allah kiyi shiru ki daina wannan abin, mai akai akai wata jaririya amnaa yarinyar da ko sati biyu batai ba bamuma da tabbacin zata Kai gobe dan Allah ki kwantar da hankalin ki mu fara gamawa da Wan da muke tsammanin zai iya rayuwa yazama wani a duniya" "ke dallacan rufemun baki shashasha kawai ,yau n'a tabbatar da baki da hankali uban wa yasan Zan Kai gobe ,ke kanki yanzu kina surutun nan Zaki iya mutuwa bama amnaa ba ,dan kina ganinta 'yar karama shine kike tunanin bazata rayuwa to kema daga Haka n'a haifeki kika girma Haka, saΓ― kiga zaidu ya mutu amnaa Bata mutu ba shashasha kawai " "to umma hakane abin da ma tab kenan kinsan da Haka kike cewa Kuma Zaki kasheta ba kya tsoron kema ki mutu?" ",Ke kinga dan n'a fada Miki Haka bashine zaisa kice Zan mutu yanzu ba ,ajikina na kejin bayanzu Zan mutu ba ,ke meyasa jahilace ne nakaiki islamiya dankiyi ilimi amma bakisan komai ba kin ki zama saΓ― kita zama da jahilcin ki ai ni fita ki bani guri ,ku ki shirya ayau sai zaidu ya bar gidannan" batare da sumayya ta ce komai ba ta futa ta bar dakin . Tana fita munira ta shigo idanuwan ta cike fal da hawaye ta tsaya tana kallon mahaifiyar tasu, "ke dalla lafiya kikazo kika sani agaba Haka zakiyi kuka bana son shashanci fa" "umma yanzu abin da kuke shiryawa kenan naji komai dan Allah umma Kar kuyi Haka zaidu Bai San komai ba sai maraici bashi da wayan da zai iya zama shikadai yayi rayuwwa Dan Allah kar kusa Abba ya koreshi" "to uwata ah nace sannu uwarmu ko nace sannu sahabiya uwar tausayi to Bari kiji idan har naji zancenan agun wani kema sainaci ubanki wallahi sai kin gwammace bani ce mahaifiyar kiba,ki fice ki bani guri tun kafin naci ubanki a gidannan muna fukar banza muna fukar hofi ke ala dole mai imani" sum sum munira ta fuce daga d'akin tana goge kwalla.


*Tom misalin karfe 12 na dare kowa yayi bacci a gidan ba kyajin ihun komai sai na tsuntsaye ,zainab ce tsugune a gaban zaidu tana bugunsa da hannu ,shikuwa zaidu cikin baccinsa yaji ana tashin sa dan Haka ya fara bude Ido Yana kallon ta dishi_dishi can Kuma sai ya fara ganinta tarau ,cikin voice dinsa Mai ban wahala yasoma kinkina Yana cewa ummmmmm um umm umma! "Kai da dalla rufemin baki banason ka 'batamin lokaci da wannan maganar taka haba sai muyi minti 5 kafin kace umma Ni tashi ka biyoni" Babu musu zaidu ya tashi ya biyo bayanta batare da sanin cutar da shi zatai ba, sai da suka zo daidai d'akin su sumayya sannan ta tsayar da shi cikin rada Tace "kana jina ko Maza kaje aunty sumayya tana kiranka Kuma duk abin da tacemaka kayi idan bakayi ba wallahi saina yankaka kajini?" "Sauri zaro Ido waje yayi ya Kura Mata Ido "au tsareni Kai da kallo bakaji abin da na ce makaba" "saurin d'aga Kai yayi ya bude baki zai ce to ,ta dakatar dashi da sauri "Kai Ni bana son jin amsarka sokake ka batamin lokaci Maza SHIGA" Babu musu zaidu ya shiga d'akin Yana dube dube Dan ya kunna kwai sai Kuma yaji an rufe kofar d'akin an saka sakata, sannan an kurma ihu "wayyo taimako umma ! Umma ki taimaka min wayyo abba! Abba!! Kuna Ina Wayyo " Abba wan da ke kwance a kan gadonsa amnaa n'a kan kirjinsa ya ajiyeta a kan gadon ya sakko da sauri yafito Yana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Sumayya lafiya" ganin zainab da yayi a bakin kofar itama yasoma tambayar ta Yana cewa "lafiya?" "Ina fa lafiya nima bansan mai yake faruwa ba Ina kwance najiyo ihunta , malan kayi wani abu akai" .





πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 4*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 4*



Munira da ke kwance ko runtsawa batayi ba Sabi da a gaban idonta sumayya tagama shirya komai sannan akan idonta zaidu ya shigo gashi Bata da yadda zata iya taimaka Masa, Dan Haka ta Kara kudin dunewa tacigaba da kukan ta ,har sai da taji muryar Abban su Yana cewa "Wai babu wan da zai iya bude kofar ne?" SaΓ― lokacin ta Mike ta karaso gaban kofar ta zare sakatar, da sauri abba ya shigo ya kunna kwai yadda yaga sumayya be yasa ya runtse ido "subahanallahi "sumayya Ina rigarki Mai yasameki Haka? Zainab ce tayi saurin karasawa ta d'akko Zani ta rufeta ,sannan abba ya bude idonsa karaf akan zaidu Wanda ke zaune a gefan shimfidar su ya takure guri daya sai muzurai yake, "Kai zaidu maiya kawoka Nan taso maza zonan, abba ya Kamo hannunsa, "abba wallahi bazan Yar daba Dan uwar yaronan Ni da,ar sace daman Ashe yaje an koya masa iskanci ban sani ba, akanme ina bacci zaina shafani " "zafaki kuma wannan dan yaron sumayya kiji tsoron Allah "zainab ta fada kamar batasan komai ba, "n'a rantse da Allah umma da gaske nake kinsan kaf gidan Nan Babu wan da ya kaini son zaidu bazan taba iya yimasa sharriba Amma abin da zai sakamin dashi kenan Allah na tsani yaronan , indai Abba Bai dauki mataki ba yau d'inan Zan varmuku gidan Nan.


"Tsaya waini ban fahimci abin da kuke nufi ba Maine ya faru?"

"Ah lallai malan yanzu baka ga abin da ya faruba ya tabbata fateema ta maka asiri shiyasa baka ganin laifin yaranta ko kadan?"

"Ke zainab ki san abin da bakin ki zai dinga fadi Akan ta idan ban da rashin hankali baiwar allahn ko wata daya batayi da rasuwa ba kudin ga fadin irin wannan magan ganun akanta ,Ina Miki kallon Mai hankali Ashe Babu hankalin ki barni nayi magana da yarana bana so na sake jin bakin ki akai" ya fad'a Yana huci.

"Iyye ah Dole wato n'a barka kayi magana da yaranka Tun da Ni an Dada maka atishawa nayi na haifosu ,wallahi in dai Akan su sumayya ne baka da ikon da zaka hanani magana sannan baka da ikon dazaka hanani Kare hakkin yarana, shi dai zaidun naji shi ba 'dana bane tun da Haka kakeson na ce To kaje shi bazan sake magana akan shiba Amma wallahi muddum zancen Nan ya tabbata gaskiya sai dai ka za'ba ko zaidu ko mu"

Juyawa tayi ta kalli munira wadda hawaye yabi ya wankemata fuska tsabar tsananin tausayin zaidu da ya cika Mata zuciya tana ji tana gani ga gaskiya Amma Babu damar fad'a,. "Ke kukan uban me kike ke kuma ko kema ya shafa kine shashasha kawai" "uuhm Babu komai umma kawai Ina hango rayuwarnan yadda ta zama abin ban Al,ajabi" "to Dan uwarki da Baki hango abin Al,ajabin ba sai da wannan abin ya faru ko da bakisan duniyar ta lalace ba sai da kika kalli fuskata?" "Uhm umma wallahi tausayin ku nakeji" "tausayin mu ?" Tausayin mu to kima daina ji huce ki bani guri tunkan na har Baki"


"Kinga zainab ya Isa Haka sumayya! Zonan"


Kara sowa sumayya tayi ta zauna idonta ya kumbura suntum hanci duk majina sai shashshekar kukan karya take.

Abbane ya kalle ta ya ce "sumayya ! Sumayya!! Sumayya!!! Nakira sunanki sau uku sumayya kiji tsoron Allah kitina Zaki mutu ki tadda allah kuma kisa azuciyarki a yanzu idan mutuwa tazo Miki Zaki iya mutuwa ina da tabbacin cewa kin San alkalami ya hau kanki a yanzu ,idan har kikayiwa yaronnan kazafi Allah saiya hukunta ki Kuma hukunci Mai tsanani Dan Haka kiji tsoron Allah ki fadamin gaskiya sumayya".

Jikin sumayya Gaba ki daya yayi sanyi saΓ― taji kamar ta ce karya takeyi ,to Amma idan tau Haka ta zubar da mutuncin ta dana mahaifiyar ta ,sabi da Haka yasa sumayya tayi karfin halin cewa "abba hakika ban taba tunanin irin wannan halin daga zaidu ba saka makon irin kekkewar tarbiyyar da kabamu duk da kasan cewar sa yaro karami ya ayka ta min abin da bazan iya yare Masa ba da farko nayi tunanin babban mutum ne dana bude Ido Naga zaidu ban Yar da shi bane sai da na sake murza idona Dan tabbatar wa ,wallahi Abba idan har nayiwa zaidu sharri Allah ya saka Masa cikin gaggawa, haba Abba kayi tunani Akan Haka Mai zaisa nayi Masa sharri ko Babu komai d'an ,uwanane kuma nasan idan nayi masa sharri Dole Zan mutu na tadda Allah ga shinan ka tam bayeshi".

"Ban gane atam Baye shi ba wannan Mai zai iya cewa ban da a 'batawa mutane lokaci yanzu kafin ya Fadi kalma daya sai gari ya waye gwara kawai amasa hukunci tun da dai anzan baza kiyi Masa sharri ba" cewar umma Dake zaune a gyfe tana kallon yadda sumayya ta dage tana fadin karya kamar gaske.


" A,a har yanzu bakisan Mata ba zainab bana tunanin wannan d'an karamin yaron zai iya aikata abin da kukace amma Bari naji ta ba kinsa" "zaid! Zaid !! d'ago ka kalleni kaji ko" dagowa zai du yayi ya kurawa mahaifin nasa ido cikin farga ba da rashin sanin abin da zaice.

Cikin nutsuwa ya Soma yimasa magana Yana cewa "zaid shin da gaske ne ka Shiga dakin yayarka sumayya kuka abin da Tace kayi mata kay?" ,"Haba malan wannan ai ba adalci bane yaza ai kadinga Masa irin wannan tambayar Kai ma kasan gaskiya sai karinga takewa" "Kinga zainab ya isheki Haka kibari kamar yadda namata magana a nutse shima nayi Masa"

"Zaidu kabani amsa hakane?" "Ah ahh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login