Showing 30001 words to 31090 words out of 31090 words

Chapter 11 - DEPRESSION (damuwa)BOOK ONE TAKUN FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO

31 Oct 2025

1385

,banason n'a kara magana da Kai Har sai ka bani labarin abin da ya faru abaya, yanayin yadda Naga kuna boyemin Abu ya tabbatar min da cewa akwai abin da yafaru wan da ba kwasan nasani, Abba na rokeka Dan Allah ka dakko min wanna littafin kada ka Bari zuciya ta ta buga bansan komai Akan Haka ba, Allah aba kaba namutu Sana din damuwa Akan Haka, bazan taba ya femuku ba koma menene ake boyemin" saurin dagowa abba yayi arazabe yace "ta sallam fu ad Mai yayi zafi Haka ? Dan Allah kada ka fadi Haka ,sanan n'a rokeka ka hakura da sanin wanan labarin ,rashin sanin labarin shine alkairi a gareka" "wallahi Abba maganar Nan da ka fada Takara samin kaunar karanta wanan littafin KO abani littafin kokuma n'a kashe kaina " turo kofar sukaji anyi tare da cewa "ba saï ka kashe kanka ba fu ad ka kwantar da hankalin ka indai har Akan wanan littafin ne zaka karanta shi" Abeed ya fad'a lokacin da take karasowa gabansu, sanan ya zuya ya kalli abbansu yace "abbbanmu Kaine wan da ka fara buga wasan ,Kaine wan da ka fara Toni wanan sirrin da ace baka bashi littafin Nan haryanzu hankalin ku a kwance ,meyasa ba zaka bar wanan gabar iya Ni ba ? Dolene Ni saika kunta tamin, ai aikin Gama yariga da ya Gama dolene Fu ad ya San komai Babu yadda ka iya da kaddara, Fu ad ka shirya karanta littafin nan yanzu ?" Abeed ya fad'a ya na kuka, gyd'a Kai fu ad yayi Yana kallon sa, "Tom shikkenan hakan ya tabbatar min kanason cigaba da karantawa ,kataso mutafi gida nabaka littafin" murmushi Fu ad yayi yace " dagaske Yaya zaka bani?" "Dagaske nake Fu ad taso mutafi" yafada tare da juyawa shima fu ad ya Mike daker ya bi bayansa, abbama tashi yayi jiki Babu kwari ya bi bayansu har suka karasa inda momy take a zaune tana kukan zuci, mamaki ne ta kamata ganin yadda su Fu ad suka fito ,Abba ta kalla Tace "abbanmu Yana ga sun fito Kuma?" "Uhm taso mutafi gida ammi nakara maganar acan" daga Haka suka fita zuwa parking space ko sallama basuyiwa doctor ba suka tafi gida.



BAYAN sun koma gida Abeed ne ta Shiga dakinsa ya dakko wanan littafin , juyowar da zaiyi yaga Abbansu ya marairaice kamar zaiyi kuka ,ga idonan nasa ya kada yayi jajur, Allah sarki tsabar tashin hankalin da yake ciki fuskarsa har ta fad'a,

Muryarsa ya tausasa yace "Babana kada Kai Haka Dan Allah, masu sunan ka akwaisu da jin magana kuma kaima nasan Kana jin maganata sosai ban San maiyasa zuwa yanzu zuciyarka ta kekashe kake tsallake magana ta, Abeeddeen ka taimaka rokarka nake amatsayina na mahaifinka kada kace zaka aikata Haka , wallahi tashin hankalin Gaba saiyafi nayanzu zafi da kunci, fu ad Bai San yayanku yasid ba baisan maiya fitar da shi daga gidanan ba, Haka zalika baisan maiyasa tsawan lokaci da Kai da abdulmajeed bakwa gida ba, yanzu gashi Abjeed ya sake tafiya ga zarah tatafi kaima so kake narasa ku?" "Uhm abbanmu ai bansan Rashi kariga da kayi shi karasa Yaya yasid ma ballan tana Fu ad, ai karka damu nine wan da zanfi Jin Babu dadi idan nasashi, to Kuma Nima din saura kadan abba kasa zuciyata ta buga" Yana gama fadar Haka ya ratsa ta kusa da Abba ya huce batare da ya jira abin da abbansu zaice ba.


K'asa ya sakko dauke da littafin a hannunsa Yana zuwa ya samu Adeena a zaune da Zaid sai ammi ta zabga tagumi ,gefe Kuma Fu ad ne zaune Yana aikin da ta Saba wato tunanin Mai zaifaru dashi Nan Gaba, mikewa yayi ganin Abeed ya dakko littafin ,Yana tsaye har ya karaso ya Mika Masa, jikin Fu ad da hannunsa na rawa ya amsa Yana kallon cikin idon Abeed din, tabbas ya hango tsoro da fargaba da tsananin tashin hankali acikin idanun yayan nasa, Abeed Bai ce komai ba ya juya sama, ammi kuwa zarw Ido tayi tana kallon littafin dake hannun Fu ad, da sauri ta hau sama ,d'akin Abeed ta nufa, Bata sameshi ba, sai dai Abba dake zaune kamar macacce, sai ka kula sosai sannan zaka fahimci idon sa a bude yake, ganin Haka yasa ammi ta zube a gurin sharaf tana kallon mijin nata cike da tausayawa, hannun ta takai kan kafadar abba Yana rawa ta bude Baki zatayi magana sai ta kasa, kawai itama ta saki kuka Mai ban tausayi, suna zaune a gurin na tsawan lokaci suna kuka, har Abeed ya zo shigowa d'akin ya kasa Sabi da kukan da yaji sunayi, gani yake kamar idan ya shigo zuciyarsa zata karye ya amso littafin Nan, Babu yadda ya iya Haka yaja kafarsa daga kofar dakin ya bar gurin.



Ammi ce ta d'ago ta kalli abba Tace "abbanmu komai ya faru Kaine kaja ,yanzu ga shinan wagari ya waya, Ni wallahi har tsoron fadawa duniya irin wannan babbar kazantar da ta faru nake, yanzu mezaka fad'a musu eh, sai da na fad'a maka akwai lokaci komai Daren dadewa sai abin da muke biyewa ya bayyana ko da ace Fu ad Bai tono ba Dole Adeena sai ta tono komai , innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Munshiga uku" "uhm Ammi kidaina cewa kin SHIGA uku Baki shiga ukuba nine Wanda nashiga uku " "uhm ba Kai kadai ba Abeeddeen ma Yana ciki da ace yasid ya nanan komai zaifi saituwa Amma Kash ya tafi ya barmu bamusan duniyar da ya shiga ba ,Haka itama Zara,u ,yanzu kenan yazamuyu?" "Babu abin da zamuyi da ya wuce mu fawwwalawa Allah muga abin da zai faru Nan Gaba".




Fu ad kuwa daki ya shiga ya turo kofa , ya cire rigarsa, ko wanka Bai ba Sabi da cin gudu yake yaga abin da yake ciki, shiyasa ma Bai bu ta kan abinci ba ya hau kan gado tare da bude shafin da ya tsaya yaci Gaba da karatu kamar Haka.......




ALHAMDULILLAH

DUKA DUKA ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN DEPRESSION BOOK 1 SAI MUN HADU A BOOK 2 IDAN ALLAH YA BANI TSAWAN RAI DA NISAN KWANA BOOK 2 AND 3 NERA 700# BABU TSADA GADUK WAN DA YAYI SHIRIN BIYA YAMIN MAGANA.


BOOK 2 AND 3 700# ONLY NO 09166764540

HAFSAT UMAR DANGORO


Duk Wanda ya karanta batare da ya biyani hakkina ba ALLAH YA ISA BAN YAFE BA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login