Showing 42001 words to 45000 words out of 140150 words

Chapter 15 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

223

muryarsu ya Zarah ma a falon k'asa". Tana fad'ar haka juya tabar d'akin.huyaam ta juya ta k'arasa parking gashin.


A falon k'asa kuwa gabad'aya su Ammie da ya Zarah suna tsaye suna zaman jiran shigowar Afeef Huyaam ce kawai Bata nan.ya haidar ne ya fara shigowa falon sai Afeef Dake biye dashi a Baya Hannunsa cikin na muneeb suka shigo bakinsu d'auke da sallama.har suka k'arasa shigowa falon. da gudu muneefa taje ta rumgume shi tana murmushi cikin murna tace .

"Well come back Yaya".ta fad'a tana k'ank'ame shi .hannu yasa ya d'agota yana sakin fuskarsa yace.


"Thank you so much muneefa" gabad'ayansu suna tsaye suna kallansa fuskarsu da murmushi kafin kowa ya shiga yi masa Barka da zuwa kallansu yayi D'aya bayan D'aya Yana ansa musu.Ammie na murmushi tace.

"Sannu da zuwa Afeef".ya k'arasa gaban Ammie da murmushi a fuskarsa ya cire face mask d'in fuskarsa ya zare hular kansa sannan ya D'an duk'ar da kansa kad'an agaban Ammie.hakan da yay Ammie ta Gane Mai yake nufi,Ta K'ara fad'ad'a murmushinta . kafin ya furta .

"Lafiya lau Alhamdulillah Ammie nasameku lafiya". Ammie na murmushi tana kai hannunta ta shafa kansa tace. "lafiya lau Alhamdulillah! sannu da zuwa ka k'arasa ciki ka huta". ya dago da kansa yana kallanta yace cikin deep voice d'insa.

"Alwala Zanyi naji ana K'iran sallahn magrib ne". Ammie ta Jin jina kai tace.

"Eh hakane ka k'arasa cikin to saika fito". ya Jin jina mata kai Daga haka Afeef ya haura sama zuwa b'angarensa . Bayan tafiyarsa Ammie ta sauke numfashi tana kallansu Huda tace.

"A'a! ina huyaam ya bangan taba?..." Ta fad'a tana waige waige a falon ko zata ga inda ta mak'ale.Huda tace.

"tana d'aki Bata gama bane". Ammie tace.

"Ok shikenan to ku wuce kuma kuje kuyi alwalan sai kuyi sallahn".Babu musu duk suka juya suka haura sama Dan zuwa suyi sallahn ya haidar kuma da muneeb suka fita daga falon suka tafi masallacin palace d'in.....



____________?&


Tunda Afeef ya Fita sallahn magrib Bai dawo ba Har Sai da akai har sai da akai sallahn isha'i sannan suka dawo b'angaren nasu shida ya haidar sai muneeb .da sallama suka shigo babu kowa a falon sai k'arar AC data fan da suke tashi.bayan sun k'arasa shigowa falon ganin Babu kowa suma su Ammien Basu Sau ko ba yasa ya Afeef ya Haura sama zuwa d'akinsa Dan ya watsa ruwa,shi Kuma ya haidar ya samu waje anan falon ya zauna kan D'aya daga cikin kujerun falon. muneeb kuma ya wuce ya haura sama zuwa d'akin Ammie...Da shigar Afeef falonsa Wani daddad'an k'amshi ne ya Doki hancinsa ya lumshe ido at the same time Yana bud'ewa Dan d'azu Daya shigo da yake ko zama Bai yiba yasa Bai k'arewa falon d'akin kallo ba.karasawa k'ofar bedroom d'insa yayi ya Murd'a k'ofar a Hankali ya tura ya shiga ciki .nan ma Wani daddad'an k'amshin ne ya sake ziyartar hancinsa tsayawa yayi ya Shiga k'arewa d'akin kallo yayi neat kamar Wanda ba tafiya yay ya Barshi a haka ba, sai dai wannan an gyara shi an can za zanin gadon da kayan Dake kan mirror Wanda duk yawancinsu ma kayan shafa shafa ne kamar su lotion sai turaruka na maza kala kala d'akin dai yayi masa sosai yadda yake buk'atar ganin sa Dan sai kace dakin wata amarya yasan Kuma wannan ba aikin kowa bane saina Ammie.sauke numfashi yayi ya k'arasawa gaban makekem gadonsa ya fara rage kayan jikinsa Yana gamawa ya shige toilet d'in nanma dai Wani k'amshin ya tadda a toilet d'in, shima kansa banda k'amshi Babu abinda ke tashi acikinsa babu Bat'a lokaci ya cire towel d'in jikinsa sannan ya had'a ruwan wanka ya shiga bath tube d'in....


A falo kuwa su Huyaam suna yin sallahn isha'i kowa ya fito Suka zazzau na a nan falon saman kujeru ,Huyaam da Huda na zaune waje D'aya suna hira k'asa k'asa ya Zarah kuwa wayarta ta d'auka ta kunna data,Ammie ce k'arshen fitowa bayan ta zauna kan kujera tana kallan ya haidar tace .

"Ina Afeef d'in yake?.." ya haidar ya d'ago da kansa daga kan wayar sa Yana kallan Ammie yace.

"Bai fitoba Yana d'akinsa".Ammie ta Jin jina kai tana kallansu Huyaam tace.

"Ku taso ayi dinner kafin ya fito ko?..Babu musu suka mik'e suka k'arasa dining d'in....fitowarsa daga wanka kenan duk jikinsa Yana d'igar ruwa ya k'arasa tsakiyar d'akin ya yatsa hannunsa rik'e da k'aramin towel ya fara goge ruwan jikinsa dashi tun daga kansa har gadon Bayansa bayan ya gama ya k'arasa gaban mirror ya fara shafa lotion d'insa bayan ya gama ya K'arasa wardrobe ya d'auki k'ana nun kaya zai sa yasa ya ya d'au tarare ya feshe duka jikinsa dasu sannan yasa hannunsa ya d'auki comp ya fara gyara gashin kansa bayan ya gama ya k'arasa kan gadon ya d'auki wayoyinsa sannan ya fito daga d'akin bayan ya kullo k'ofar.tun kafin ya gama saukowa downstairs k'amshin turaransa ya fara isar musu da zuwansa,take duk suka zubawa stairs d'in ido har ya k'arasa sauko gabad'aya Yana rik'e da wayoyinsa ahannunsa.yana d'ago da kansa idanuwansa akan Huyaam suka fara sauka wacce itama ta zuba masa nata Idon tana kallansa,kafin ta D'an Bud'e ido kad'an alamar Mamakin ganinsa da tai tana kallansa tare D'an murmushi sai Kuma ta rufe Bakinta har lokacin murmushi take Wanda ya kasance na murnar one and only yayan nasu tasowa tai daga dining d'in ta k'araso cikin falon har inda taga yaja ya tsaya ya rungume hannunsa Yana kallanta ganin ta nufoshi d'aukar sa yanzun ma rungume shi zatai ya hanata. Aikuwa dai sai yaga rungume shin zatai take yay mata Wani kallo jiki a Sanyaye Huyaam taja ta Tsaya a inda take ganin Irin kallon da yake Mata ta sunkuyar da kanta k'asa kafin ta d'ago tai masa murmushi kan kyakkyawar fuskarta da k'yar ta iya cewa.

"Well come back Yaya".ta fad'a tana langwab'ar da kanta tana kallonsa. janye idonsa yayi Daga nata Yana wuceta yace.

"Thank you". HUYAAM ta juya tana kallonsa ganin yadda ya ansa mata ta sai Kuma tura Baki gaba tana k'unk'uni tabi bayan sa sudai su Huda kallansu kawai suke suna Murmushi ganin har yanzu dai yayan nasu Yana nan da tsare gidan da yake musu bai sauyaba..da A falo zai zauna Hakan yasa Ammie tace .

"A'a k'araso ka zauna abinci zaka anan ci anan ko su tashi ne?..." Ta fad'a tana kallansa.girgiza mata kai yay Batare da yace komai ba harya k'araso dining d'in Huda tai saurin tashi ta ja masa kujera kallanta yay sai kuma ya zauna.yana furta thanks a saman lab'b'ansa.huda tai murmushi ta koma itama ta zauna ido suka had'a da Huyaam Hakan yasa ta sauke nata ta k'araso dining d'in itama dama a kujerar Dake kusa da Huda take zaune Dan haka tana zuwa taja ta zauna har lokacin bata daina tura Bakin gaba da take Yi ba shiko Afeef Bai K'ara kallantaba har ta zauna kan kujerar sai ya zamto sunyi passing juna ita da Afeef .ya Zarah ce tai serving kowa Ammie kuma tai serving ya Afeef tai selecting Irin abincin da tasan yake so Kuma yay missing ta ajiye anan gabansa. yana kallan Ammie da murmushi yace.


"Thank you mother". Ammie tai murmushi ta zauna nan suka fara cin abincin.tunda ya fara cin abincin nan Bai d'ago da kansa ba Huyaam dai tana ci tana Satan kallansa magana take son Yi Amma Kuma tana tsoro haka nan dai ta maida hankali kan Abincinta itama..shine ya fara mik'ewa bayan ya yasha ruwa ya d'auki tissue ya goge bakinsa dashi ya fita daga dining d'in ya koma falor ya zauna duk suka bishi da kallo Amma babu Wanda yay magana har Ammien ma... D'aya bayan D'aya suma suka dinga tashi bayan kowa ya k'oshi duk suka koma falon suka zauna .Huyaam ta mik'e bayan ta gama ta koma falon ta zauna kan kujerar da ya Afeef yake kai Dama akan two seater yake tana kallan sa tana murmushi.Afeef ya juyo Yana kallanta tai k'asa da murya tace.


"Good evening Yaya". ta fad'a tana Wani narke masa .ya Motsa bakinsa kad'an yace.

"Evening HUYAAM ya kike".ya fad'a Yana kallanta tana murmushi tace.

"Lafiya lau Yaya,ya hanya ya gajiya".yana d'auke kansa daga kallanta yace.

"Alhamdulillah". Ammie ce ta sauko k'asa tana kallan Afeef tace.

"Mai martaba ya shigo Yana falonsa ta k'ofar Bata yabi". Afeef yace.

"Ok".mik'ewa yayi ya haye stairs Dan zuwa falon Mai martaba huyaam ta d'aga murya tace .

"we are waiting for you Yaya saika dawo". ta fad'a cikin D'aga murya,Bai juyo ba harya gama hayewa stairs d'in.sai kuma ta mik'e da sauri ta koma kusa da Huda suka zauna tana mata magana k'asa k'asa gefe D'aya Kuma suna zaman jiransa...



# # # #


07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =???)__*



*Bismillahirrahmanirrahim*



PAGE 1?? 9??


___________?&


Da sallama a bakin Afeef ya k'arasa shiga falon Mai martaba.ya sameshi zaune ya kishin gid'a jikin tuntun sarautan dake babban falon nasa,Mai martaba ya d'ago Jin sallama Yana kallan Afeef harya k'araso ya Zauna a k'asan carpet d'in idonsa na kan Afeef.duk'ar da kansa Afeef yayi cikin girmamawa yace .


"Barka da dare rankai Dad'e na sameku lafiya".ya fad'a har lokacin kansa Yana k'asa Bai d'ago ba.mai martaba ya gyara zamansa Yana kallan Afeef da kyau yace da kulawa.

"Lafiya lau Alhamdulillah Muhammad ya ingiland d'in fatan kadawo lafiya?...". Afeef yace cikin girmamawa.


"Alhamdulillah rankai Dad'e"Mai martaba ya Jin Jina kai yace.

"Masha Allah! ya company Kuma? kodan ina kallan komai ma ta system kuna k'ok'ari sosai..."sai a sannan Afeef ya d'ago Yana kallan Mai martaba da kyawawan idanuwansa Wanda suka kasance kamar ruwa saboda yadda suke garai dasu yace cikin nutsuwarsa a Koda yaushe.


"Lafiya lau Alhamdulillah Abba".Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Masha Allah!, sai Kuma ya cigaba Yace. "Kun gaisa da Babanka turaki kuwa? wambai dai nasan baya nan?..."Afeef yace. "Eh! mungaisa d'azu a masallaci rankai Dad'e".Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Masha Allah Hakan yayi kyau Allah yay muku albarka". Afeef ya ansa da Ameen,sai Kuma yace.

"Allah ya tai makeka ka duba budget d'inmu na new year Dana tura Maka ta email kuwa?Ina so ne tunda na dawo muyi komai a gida kawai...."Mai martaba yace. "na gani komai yayi Muhammad amma tunda yanzu kana gida zamu sake zama in Sha Allah in yaso sai a sake wasu tsare tsaren, sannan company kullum samun cigaba yake Allah yayi albarka yasa afi haka". Afeef ya ansa masa da Ameen.basu Dad'e ba Sosai suna magana ba Mai martaba yace yaje ya huta shida ya dawo daga tafiya yana buk'atar ya huta, Babu musu Afeef yaywa Mai martaba sallama sannan ya fito daga falon gabad'aya.su huyaam suna Zauna har lokacin Basu bar falon ba Ido Huyaam ta zuba masa har ya k'arasa saukowa downstairs d'in gabad'aya Batare da ya Kallesu ba tun kallan farko da Yay musu .ganin zai nufi b'angaren sa Bai musu magana ba yasa Huyaam tai saurin cewa.

"Yaya ka dawo kuma shine zaka tafi?ta fad'a cikin shagwab'a..." Kamar bazai tanka tab'a sai Kuma ya juyo yana kallonta yace cikin yanayin muryarsa. "Eh". atak'aice .Huyaam tai saurin cewa "To Yaya Ina tsarabarmu take?...."yace. "Saida safe".tai murmushi tace.

"Tom Allah ya kaimu".nan ko Batasan tun dawowarsa aka shige da kayan d'akin Ammie ba, Bai ansa ba ya juya Yana kallan Ammie da take masa magana tace.


"Ya kamata kaje kan ka huta Afeef tafiya daga ingiland zuwa Nigeria ba nan bace..." Ya Mutsa bakinsa kad'an yace.

"In Sha Allah! good night". Ammie tace.

"Okay good night,Allah ya tashe mu lafiya".ya ansa da Ameen su Huyaam duk sukai masa saida safe sannan ya juya ya haye stairs d'in b'angaren su Yana ansa musu,dama tuni ya haidar ya bar wajen tun lokacin da sukai dinner, su muneefa ma tun bayan da Afeef ya shiga b'angaren Mai martaba sukai shige D'aki sukai bacci.. bayan tafiyar Afeef Ammie na kallan su Huyaam ganin k'arfe shad'aya ta wuce yasa tace musu .

"To Kuma tashi Haka nan kuje ku kwanta ko?...". gabad'ayansu suka mik'e sukai mata sallama kowa ya shige D'aki Dan kwanciya. Bayan tafiyarsu itama Ammie barin falon tai bayan ta kashe kayan wutar falon gabad'aya sannan ta tafi kitchen ta had'awa Mai martaba black tea bayan ta gama ta juye a cup ta D'ora a plate ta wuce Falonsa da shi......



*Washe gari*


Tun kafin Afeef ya tashi daga baccin Daya koma bayan sallahn ASuba su Huyaam suka tafi ismaliya tahfeez bayan sun gama tambayar Ammie yayan nasu tace Yana bacci sai dai idan ya tashi ,haka nan suka tafi islamiya suna Mai kewar ganinsa.... k'arfe 11 da mintuna na safe Afeef ya sauka downstairs tashinsa kenan daga bacci wanka kawai yayi ya shirya cikin kayan sarauta Wanda sukai masa bala'in kyau Kamar ki sace sa ki gudu Dan kyau ya fito Yana gyara hannun rigarsa harya k'arasa saukowa downstairs d'in.mai aikin Ammie Dake goge goge a falon ta tsugunna har k'asa ganin fitowar Afeef d'in ta Shiga gaidashi cikin Ladabi .Batare da ya kalleta taba ya ansa mata ya K'araso tsakiyar falon.baba magajiya data fito daga dining hannunta rik'e da wata cooler zata k'arasa kitchen d'in ganin afeef yasa itama ta tsugunna ta har k'asa tace.

"Barka da safiya rankai Dad'e fatan mun tashi lafiya". Afeef ya D'an Kalleta ta gefen ido yace.

"Lafiya lau Alhamdulillah".tace .fatan ka dawo Lafiya rankai Dad'e jiya bansamu nazo mun gaisa ba."ta fad'a tana murmushi.Afeef yace. "Lafiya lau Alhamdulillah".baba magajiya tace.

"Masha Allah! nace "rankai Dad'e ko akwai abinda kake buk'ata ne ". Afeef ya D'auke kansa daga kallanta yace.

"Babu komai". Baba magajiya tace.

"To! to!! Shikenan,Amma Naga kamar yanzu ka fito zaka karya Dama an gama gyara tebirin abincin ne ko zaka k'arasa kaci ne?..."Afeef yace.

"Okay" atak'aice.baba magajiya ta mik'e ta bar wajen Bayan tai masa sallama.. Afeef ya k'arasa dining d'in ya ja kujera ya zauna,bayan ya gama yin breakfast d'in Wanda bama na kirki yayi ba ya goge bakinsa da tissue sannan ya d'auki wayoyinsa ya wuce b'angaren Ammie... Ammie na zaune Bakin gado tana ware Tsaraban da Afeef yayo musu zata aikawa da mutanan gidan kowacce nata dana yaransu akai knocking d'in k'ofar.ta juya tana kallon k'ofar sai Kuma tace.

"Waye?.."muryar Afeef taji Hakan yasa tace ya shigo .da sallama abakinsa ya turo k'ofar d'akin ya shigo kansa a k'asa sai Wani baza k'amshi yakeyi har ya k'arasa cikin d'akin ya zauna kan kujerar Dake d'akin.ya Kalli Ammie yace cikin cool voice dinsa.

"Barka da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wannan lokaci". Ammie ta kalleshi tace.

"Barka ka tashi Kenan ya gajiya".yace.

"Lafiya lau Alhamdulillah". Ammie tace.

"Masha Allah! Sai Kuma tace.

"Yanzu Ina zaka?..."yace.

"Zance fadane wajen Mai martaba yace naje na sameshi acan a kwai inda zamu anjima da kad'an". Ammie ta Jin jina kai tace.

"To idan Kun dawo Koda da daddare ne ka k'arasa kaje ka gaida matan gidan karsu fara yad'a mun da magana"ta fad'a tana kallansa . kallan Ammie Afeef yayi azuciyarsa yace wai maiyasa Ammie take gudun maganar matan masarautar nan ne indai magana ce sun jima basuyi ba, kamar zaiyi magana sai Kuma ya fasa yana kallanta yace.

"In Sha Allah! Zanje".Ammie tace.

"To Shikenan Allah yay Maka albarka sai Kun dawo d'in". Tana fad'ar haka Afeef ya mik'e yay wa Ammie sallama sannan ya fita daga d'akin bayan ya kullo mata k'ofar.Ammie ta Sauke numfashi ta d'auke idonta daga kallan k'ofar ta cigaba da abinda takeyi.....



____________?&


K'arfe biyar Saura na yamman Ranar Hajiya Lubabatu ce Zaune a d'akin da suka Saba zama ita da fulani Salamatu.. Hajiya Lubabatu tai k'asa da murya tace.

"Oh!! wai kina nufin kema Daya dawo tun jiyan Amma baizo ya gaida keba?..."ta fad'a cikin alhini.. Fulani Salamatu tace Cikin fushi da b'acin Rai.

"hmmm! Lubabatu kenan Ina zaizo ai yanzu wuyansa ya isa yankan da Yana ganin yakai Wani matsayi,ai yanzu Bai d'auke ni amatsayin matar ubansa ba sai dai amatsayin abokiyar kishinsa,kamar yadda uwarsa ta d'auke ni". ta fad'a tana Wani Irin hucin b'acin rai .Hajiya Lubabatu tace.

"Uhmm Tab' >?? d'ijan Amma wallahi fulani Maryam bata kyauta ba ai ko shi Afeef d'in baizo Dan kansa ba, ita ai ta sashi yazo ya gaida ke ko Dan kina a matsayin matar ubansa ma? Abarshi ma mu ba dolensa bane yazo ya gaida mu tunda mu a amatsayin matan k'annin Mai martaba muke Amma ke dai dolensa ce tunda mahaifinsa Mai martaba kike AURE. bama iya wannan ba Karya manta kece fa hasken idaniyar masarautar kano".... ta fad'a cikin zuga.Fulani Salamatu tace.


"Hmm! ina zan zama dolensa tunda Yana da uwa aini ba dolensa bace ba Lubabatu kima daina fad'ar haka ,da ace iyayensa sun nuna masa Ina da mutunci a idonsa da tuni yazo ya gaida ni kina fa ganin Mai martaba dayazo d'azu koya tambayeni Yace min Afeef d'in yazo gaidani Bai fad'a haka ba, Kinga ko Shima Ina zai ganni da mutunci tunda ba'a nuna masa Ina da mutunci ba?...". Hajiya Lubabatu ta rik'e baki tace.

"Tab' d'ijan Amma lallai fulani Maryam ta cika marar mutunci". fulani Salamatu tace. "Hmmm ". Amma batace komai ba ranta na cigaba da tafar fasa.... Hajiya Lubabatu ta sauke numfashi tace. "Allah ya kyauta". Kamar wacce ta tuno da Abu tace.

"Yauwa! Kinga abinda nakeson fad'a mikin ma tun d'azu sai yanzu yazo min,nace ba,D'azu dai sai ga hadiman fulani Maryam su biyu ta Aiko su kawowa su ikleema kayan Tsaraba mu Kuma gold da less guda biyu kema an kawo mikin koh?..."ta fad'a da sigar tambaya. fulani Salamatu tab'e Baki tace.


"Nima Ankawo min d'azu , wallahi da har zance da wacce ta kawo d'in ta Maida mata sai kuma kawai na Karb'a kar ta k'ara had'ani da Mai martaba yazo Yana min k'ana nun maganganu ,sai Kuma Wani tunanin ma ya K'ara zuwamin nace nida dukiyar 'ya'yana anje an sakar masa ita yana can ya mamaye mana Yana facaka da kud'i yadda ransa yakeso ai dole ya iyo wannan uwar siyayyar ta kaya masu bala'in tsadar gaske Dan wallahi iya kayan da aka kawowa su Aziza yafi million biyar bare kuma namu".


Hajiya Lubabatu ta gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login