Showing 6001 words to 9000 words out of 140150 words

Chapter 3 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

178

su kullum cikin kwantar mata da hankali da nasiha suka mata kuma har lokacin Daada Bata dawo k'asar ba bare ta sani .ahaka dai har gimbiya Aysha ta fitar da Rai Daga samun baby Zainab Amma fa ciwon nan Yana nan Acikin zuciyarta Bai warke ba Bata kuma tunanin akwai ranar da zai warke tunda har ta rasa 'yarta a haka ta cigaba da safgoginta Amma fa abun Yana nan a ranta .



A wannan lokacin kuwa shakundum Wani Irin farin ciki take ciki tareda walwala ganin yadda gimbiya Aysha ke cikin k'unci wannan shine babban burinta a rayuwa kullum taga gimbiya Aysha cikin k'unci gefe D'aya Kuma tana nan tana shirin yadda zata K'ara Sako sultan agaba dasa masa ciwuwuka iri iri ahaka har ya mutu shima shikenan idan tai haka burin ta ya gama cika sannan Bata da wata sauran far gaba.wannan kenan.




*Tofa masu karatu meke shirin furuwa ne haka>??? Wannan Karan Kuma ga inda Alk'alamin
'? MRS SARAKIES =??? ya kawo mu ,shin Ina baby Zainab take Shin tana raye ko Bata raye?idan tana raye tana Ina?su waye suka d'auketa?kudai ku kasance Dani Dan jin yadda labarin zai kasance dan war ware muku shi bit by bit Dan wannan tafiyar ta banbanta da sauran*




?& Present ?&


4 April,2025



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD






*


(The love e&? story)





*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*___(MRS SARAKIES =???)=?1?___*




*Bismillahirrahmanirrahim*




Page4??


__________?&


*Present*

4 April,2025


*Emir palace kano state*



Wajen k'arfe shida dai dai na yamman Ranar, Wata k'atuwar mota ce nagani ta tunkaro Wani babban gate Irin na gidan sarauta motar k'irar family car ce sabuwa dal da ita . tun kafin motar ta k'araso naga wasu dogaraye Wanda suke Zaune abakin gate d'in gidan daga waje Wanda ak'allah zasu kai kusan su shida sai police guda hud'u Wanda da dukan alamu sune suke tsaron gate d'in.mutane biyu daga cikinsu naga sun mik'e cikin sauri suka wangale k'aton gate d'in gidan, adai dai lokacin motar ta iso bakin gate d'in gidan direct ta kutsa kai ta shiga har cikin gidan yayin da fadawan nan suka cika wad'anda ke cikin motar da kirari tare da saukowar su lafiya.


A babban compound d'in gidan motar tai parking .Wani dogari na gani ya fito daga gaban motar cikin sauri inda yay saurin zuwa ya Bud'e bayan motar Wanda naga yaran gidan ne gabad'ayansu sanye da uniform na islamiya a jikinsu Wanda da dukan alamu daga islamiyar aka d'aukosu.


yara mazan ne wad'anda ke seat d'in farko suka fara fitowa daga cikin motar cikin shigar uniform na islamiya kusan su hud'u Wanda a shekaru a k'alla zasuyi 12 years haka,sai da suka gama fitowa sannan naga Yara matan suma sun fara fitowa , Wad'anda sune k'ana nun cikinsu,su su hud'u ne suma Wanda a shekaru a k'alla zasuyi 8 years haka D'aya ce kawai take 12 years Acikinsu.bayan sun gama fitowa sai yayunsu 'yan mata Suma su hud'u Wanda duk Sa'an nun juna a shekaru zasuyi 17 years haka , bayan sun gama fitowa sai yayansu suma su hud'u biyune manyan cikinsu wadda suka fisu dan sune manya Wanda a shekaru zasuyi 24 haka sai sauran biyun Wanda su Kuma ashekaru zasu 22 haka , gabad'ayansu sun gama fitowa wasu sun cikin gajiya Dan naga sai Wani ya Mutsa fuska suke alamar gajiyawa atare dasu .bayan sun gama firfitowa kowa ya nufi part d'insu dayake gidan Irin K'aton gidan nan ne Mai d'auke da sashe daban daban Wanda a k'alla zasuyi guda biyar agidan, sashe biyu suna b'angaren dama sai sauran sashe ukun Dake nan b'angaren hagu.


Wanda ke b'angaren Daman part na farko naga wasu daga cikinsu sun nufa su_su biyar suka nufi part d'in Wanda su Hud'un mata ne sai namiji guda D'aya,yaran sune agaba macen da namijin kenan, namijin Yana rik'e da Hannun k'anwar tasu Mai suna muneefa wacce itace autar su sai shi Mai suna muneeb.


Daga bayansu kuma yayar suce Wadda itace Babbar cikinsu Mai suna zarah sai K'annanta Wanda suke bi mata suna bayanta D'aya na rik'e da D'aya ajikinta da dukan alamu d'ayar Babu lafiya ne Wanda Sa'an nun juna ne .


Ta juya Ganin da tana bayansu,ganin basa sauri yasa tai gaba.ta tsaya tana kallan wacce ke rik'e da d'ayar tace cikin fad'uwar gaba .


"Huda! meya samu HUYAAM d'in naga kin rik'ota?...."ta fad'a tana kallan HUYAAM wacce idonta ke lumshe.


Wacce aka k'ira da Huda ta d'ogo tana kallan wacce tai maganar tace cikin Damuwa.


"Wallahi ya Zarah tun muna class tace min kanta na ciwo,to sai yanzu Kuma da muka dawo gida muna sauka sai naga tana k'ok'arin fad'uwa shiyasa na rik'ota".ta fad'a cikin damuwa.


Wacce aka k'ira da Ya zarah ta k'araso da sauri cikin fad'uwar gaba Dan tana tsoron ace ciwon k'anwar tasu ne zai tashi ta Mik'awa Huda Jakar Hannunta tace.


" rik'e min bari na kamata". ta fad'a tana k'ok'arin rik'o HUYAAM daga jikin Huda..Babu musu Huda ta karb'a ta had'a ta rik'e musu jakan kunan duka ukun.ya Zarah tai gaba tana rik'e da HUYAAM Huda Kuma tana binsu abaya.


Da suka shiga falon babu kowa sai k'arar AC data fan sai k'arar TV dake tashi da sautin karatun Al'qur'ani Mai girma daga bakin Wani babban malami a k'asar nan.direct sama Huda ta haura zuwa d'akinsu rik'e da bags d'in nasu Dan ta ajiye musu .ita Kuma ya Zarah d'akin Dake nan downstairs Wanda shima yake a mazaunin nasu Duk da Basu fiye zama acikinsa ba sai lokaci zuwa lokaci yasa ta nufi Dan takai HUYAAM tunda tasan ba lallai ta iya haurawa sama A wannan yanayin da take ba.tana shiga d'akin ta k'arasa har gaban gadon ta zaunar da HUYAAM akai wacce idonta har sun kad'a sun koma JAA daga farin da suke ada. ya Zarah ta kalleta ganin kwanciya take son Yi tai k'asa da murya tace cikin Damuwa da lallashi.


"Sannu HUYAAM! bari na Baki magani in yaso sai ki kwanta d'in".ta fad'a tana kallanta da tausayawa.


Huyaam ta k'ara lumshe idonta Amma Batai magana ba.hakan yasa ya Zarah ta fita daga d'akin ta tafi kitchen Dan d'auko mata ruwa. Tana fita Huda ta shigo d'akin ta k'arasa har saman gadon wajen HUYAAM Dake kwance ganin kamar bacci take yasa ta juya ta tashiga toilet d'in d'akin Dan d'auro alwala tunda K'iran sallahn magrib akeyi .Babu dad'ewa ya Zarah ta dawo d'akin da gorar ruwa a hannunta ta tafi gaban lockan Dake gaban mirror ta jawo na tsakiyar ta d'auko Wani k'aramin box ta Bud'e ta d'auko park d'in PCM ta b'alli guda biyu sannan ta Maida ta rufe ta dawo gaban gadon inda har Huyaam ta kwanta ta zauna tana k'ok'arin d'ago Huyaam zuwa jikinta tace .


"Tashi Huyaam kisha maganin".ta fad'a tana kallan Huyaam bayan ta d'ago da ita.da k'yar Huyaam ta yadda tasha maganin nan . Saida Zarah ta tabbatar da ya maganin ya D'an tsirga mata sannan ta taimaka mata ta kwanta. tana k'ok'arin Tashi Daga saman gadon kenan aka Bud'e k'ofar toilet d'in d'akin Huda ce ta fito daga cikin toilet d'in tana d'igar ruwa alamar ta d'auro alwala ya Zarah tana kallanta tace .


"Yauwa Huda ki zauna da ita bari naje Nima nai alwalan" ta fad'a tana kallan Huda.


Huda data d'auko darduma a inda suke anyiwa tana k'ok'arin shimfid'a darduma Dan yin sallahn tace.


"To ya Zarah!, da sauk'i ai jikin nata ko?.ta fad'a tana kallan HUYAAM wacce ke sauke numfashi.


Ya zarah juya itama tana kallon Huyaam d'in kafin tace .


"Eh nadai Bata maganin Tasha"Huda ta gyad'a kai daga haka ya Zarah tabar d'akin.



Ya zarah tana yin sallahn magrib ta dawo d'akin Dan K'ara duba jikin Huyaam d'in ta Tarar da Huda ta fito daga toilet rik'e da HUYAAM wacce da dukan alamu ta tai maka matane tayo alwala itama, Huda ta zaunar kan daddumar dake shimemfid'e nan tsakiyar d'akin.


Ya zarah ta k'araso cikin d'akin tana kallan Huyaam tace .


"Sannu HUYAAM jikin da sauki kenan",sai kuma ta Kalli Huda tace." sallah zatayi ne?..."Huda tana k'ok'arin sakawa HUYAAM hijab Ajikinta tace.


"Gatanan dai cewa tai nakaita toilet zatai alwala"ta fad'a tana matsawa daga gaban HUYAAM bayan tasa mata hijab d'in Dan Bata dama tai sallahn.


Ya zarah ta sauke ajiyar kafin tace.


"Allah ya sawake tunda kina tare da ita bari naje".Huda tace.


" Shikenan".daga haka ya Zarah tabar d'akin.


Bayan sallahn isha'i gabad'ayansu suna zaune a dining gabad'ayansu tun daga kan ya haidar har zuwa kan muneefa suna dining suna yin dinner muneefa Dake kusa da Ammie ta Kalli ya Zarah tace .


"Ya zarah Inasu ya HUYAAM naga bangansuba?..."ta fad'a tana kallan ya Zarah . Ammie itama kallab ya Zarah tai tana jiran ansar da zata bawa muneefa Dan itama Ammien tambayar Dake ranta kenan tun d'azu muneefa ta rigata,ganin Bataga yaran nata ba bayan kuma ba haka suka sababa indai suka dawo daga islamiya ko boko tofa sai sunje har Inda take sunce sun dawo bayama HUYAAM itakan tana da k'ok'arin wannan .


Ya zarah Dake juya abincin gabanta Wanda Bata kai ga ciba tace cikin Damuwa .


"Suna nan,HUYAAM ce Bata da lafiya kanta ke mata ciwo Shiyasa Basu fito ba". ta fad'a tana k'in kallan Ammie wacce ta zuba mata ido.


Take gaban Ammie ya Fad'i Jin abinda Zarah ta fad'a sai kuma ta Dake tace.


"Amma shine babu Wanda yazo ya fad'amin acikinku?,bayan kunsan cewa bana wasa da duka jinyanku musamman ma HUYAAM kinsan Bata da lafiyar Amma shine kika kasa fad'a min Zarah"ta fad'a cikin b'acin Rai.


Ya zarah ta marai raice tana kallan Ammie tace."ai Ammie na Bata magani fa"ta fad'a tana kallan Ammie.

Ammi tace.

"Rufe min Baki babbar kawai kinsan Bata da lafiyar Amma kika kasa fad'a min".ya Zarah tai shiru ta sunkuyar da kanta k'asa .
Muryar Ammie taji tace.


"Tun yaushe ne kan nata ya fara ciwon?...."sai a sannan ya Zarah ta d'ago tace.


"Huda tace tun suna aji har muka dawo". Ammie tace.


"Yanzu tana Ina?.."


Ya zarah tace.


" Suna nan d'akin downstairs tare da Huda"tun kafin takai k'arshe Ammie ta mik'e ta nufi hanyar d'akin jikinta a Sanyaye gabad'aya sai Suma suka Mik'e suka bi bayan Ammie.


Ammie tana tura k'ofar d'akin ta Tarar da Huda suna kokawa ita da HUYAAM a Saman gadon bil hakk'i da gaskiya sun Zubo da pillows d'in Dake saman gadon k'asa gabad'aya sun jik'e sharkaf da zufa sai kace Wanda sukai gudun tsere fuskar Huda tayi jaga jaga da hawaye da sauri Ammie ta k'araso ta rik'o HUYAAM wacce gashin kanta ya bar baje saman kanta ta kamota kamar wata mahaukaciya tana cewa .


"Subhanallah Meya faru Huda?..."ta fad'a tana k'ok'arin rik'o HUYAAM Dake San k'wacewa daga rik'on da tai mata. Huda tace tana huci.


"Ammie wai dole saita fita kuma fa Bata da lafiya"ta fad'a kamar zatai kuka.


Ammie ta kalli HUYAAM wacce har lokacin idonta Yana rufe tana k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da Ammie tai mata tace cikin sanyin murya.


"HUYAAM! Ina zaki?..

HUYAAM tai shiru batai magana ba Kuma Bata fasa k'ok'arin k'wace kanta daga rik'on da Ammie tai mata ba.Nan Ammie ta Gane ba ita bace ba, take ta fara Yi mata addu'o'i HUYAAM ta k'ank'ame Ammie tana cewa.


"Ammie kaina , Ammie kaina ki rik'emin zai fashe , Ammie zan Mutu"ta fad'a tana rusa da Wani Irin ihu.


Take Ammie tai Saurin rufe mata Baki tana K'ara mannata da jikinta tace Cikin damuwa.


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Baza ki mutuba HUYAAM in Sha Allah sannu" ,ta fad'a tana tufa mata addu'o'i har lokacin.itadai Huyaam sai jujjuya kanta take tana kuka ganin haka yasa Ammie ta dubi Huda tace cikin Damuwa .


"jeki d'akina ki Bud'e drower ki d'auko min maganinta yanzu sannan ki taho min da wayata akan mirror".ta fad'a tana tana rik'o HUYAAM.babu Bat'a lokaci Huda ta fita daga d'akin cikin sauri tai d'akin Ammie. babu dad'ewa ta dawo Hannunta rik'e da wata gora wacce ke d'auke da Wani magani aciki.ta Mik'awa Ammie gorar maganin da wayar. Ammie ta karb'a ta ajiye wayar nan gefenta ta Bud'e gorar ta tsiyaya a hannunta sannan ta shafa a fuskar HUYAAM wacce ta jik'e da gumi,ta K'ara d'iban Wani ta shafa mata a fuskarta .take HUYAAM taja wani dogon numfashi tana sakin jikinta a jikin Ammie.ganin haka yasa Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana kallan Huyaam. ta juya bayanta Jin sautin Kukan muneefa ta kalli haidar tace.


"Wayece ku shigo da ita?maza kamata ku fita da ita"Babu musu haidar ya kama hannun muneefa yana kallan Huyaam yace .


"Allah ya K'ara lafiya".ya Zarah ta ansa da Ameen. daga haka ya fita daga d'akin rik'e da muneefa muneeb ma yabi bayansu.bayan Wani lokaci HUYAAM ta fara Bud'e idanuwanta ahankali a hankali ahaka har ta gama Bud'esu gabad'aya.ta tsaida su akan Ammie kafin ta juya Tana kallan sauran saikuma ta fara k'ok'arin mik'ewa zaune Ammie ta rik'eta tana cewa.

"Me zakiyi haka ?..
HUYAAM tana yamutsa fuska tace.

"Ammie meya faru?.."Ammie tai mata murmushi tace.

"Kankine ke ciwo shine na Baki magani"ta fad'a tana kallan yadda HUYAAM take rarraba ido.

Sai Kuma tace.

"Kan ya daina ciwon yanzu ?..."ta fad'a tana k'ok'arin parking gashin HUYAAM.


HUYAAM ta gyad'a mata kai sai kuma tace

"Ammie Ina Abba?..."Ammie tace .


"Yana masallaci Bai shigo ba "Huda ta kalli HUYAAM tace.


"Sannu HUYAAM". HUYAAM ta gyad'a mata kai ya Zarah ma tai mata sannu ta ansa mata sai Kuma ta fara zame jikinta Daga na Ammie tace .

"bacci nakeji". Ta fad'a tana juya bayanta.Ammie tace .


"A'a tashi Muje kici Abinci". Huyaam tace Batare da ta juyo ba.

"A'a sai anjima".daga haka ta K'ara gyara kwanciyar ta.


Ammie batace komai ba ta d'auki wayarta ta kunna Karatun Al'qur'ani ta mik'e ta ajiye nan saman mirror Dake d'akin ta barwa Huyaam tana kallan su ya Zarah tace .


"To muje mu barta ta huta anjima Huda sauki had'o mata abinci Dan kada ta kwana da yunwa"Huda tace.

"To Ammie".daga haka suka fita daga d'akin Ammie ta jawo k'ofar ta rufe.


Wajen k'arfe 9 na dare Mai martaba ya shigo part d'in Ammie Yana zaune a falonsa Dake nan part d'in bayan duk yaran sunzo sun gaida shi sannan suka fito daga falon.

Muneefa tana mak'ale da mai marataba Da take bashi labarin HUYAAM Babu lafiya.Ammie ce ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Hannunta rik'e da D'an k'aramin plate Wanda ta d'orowa Mai martaba black tea akai ta k'araso har falon cikin ta risina ta ajiye nan gaban Mai martaba.tana kallan muneefa tace.


"Wato Baki tafi kin kwanta ba ko?..."Mai martaba yace cikin nutsuwarsa.


"Fulani! wai jikin Huyaam ne ya K'ara tashi?..."ya fad'a Yana kallan Ammie.


Ammie ta d'ago ta kalleshi sai Kuma ta Kalli muneefa wacce ke k'ifta ido tace.

"Wato ke uwar surutu kece kika fad'a masa koh?..."muneefa ta sunkuyar da kanta k'asa. Ammie ta sauke numfashi tana Maida dubanta kan Mai martaba tace cikin Damuwa.


"Shine rankai Dad'e Amma na Bata sauran maganin Daya rage Wanda da muka kaita Egypt muka karb'o Ina shafa mata nan da nan ta dawo hayyacinta".


Tunda ta fara magana Mai martaba yake kallanta yay Jimm alamar tunani kafin ya sauke numfashi yace.


"Allah ya Bata lafiya"Ammie tace .

"Ameen ya Rabbi".

Mai martaba yace .

"Yaushe ne zaku koma?..."


Ammie tace." nan da wata uku ne in Sha Allah.


Mai martaba ya Jin Jina kai . Amma baice komai ba.Ammie ta kalli muneefa wacce ta fara gyangyad'i ta d'auke ta ta fita da ita daga d'akin Dan zuwa ta kwantar da ita .tana kwantar da ita ta shiga wanka ta fito ta kimtsa cikin kayan bacci bayan ta gama ta feshe jikinta da turaruka masu bala'in kamshi da tsada ta d'auki dogon hijab d'inta tabi tanan corridor Dake gefen d'akinta tai part d'in Mai martaba Dan yau kwanan tane.





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*

(The love e&? story)



*Paid book =???*


*Free pages*





*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*




*___(MRS SARAKIES =???)=?1?___*



*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 5??



__________?&


Washe gari haka HUYAAM ta tashi kamar Bata tab'a wata jinya ba.baccin tama tasha babu Wanda ya tasheta sun bari ne ta tashi da kanta .Sai wajen k'arfe 11:30am ta tashi ,sannu a hankali ta sauko daga saman gadon daga ita sai rigar bacci ajikinta ta mik'e tsaya tana Mik'a kafin ta tafi ta d'auko towel ta d'aura ajikinta bayan ta cire rigar baccin tai hanyar toilet Dan yin Wanka . Babu dad'ewa ta fito d'aure da towel ajikinta kanta sai d'igar ruwa yake ta k'arasa wajen hanga Dake d'akin ta d'auko Wani k'aramin towel ta fara tsane gashinta kanta dashi, bayan ta gama ta d'auki hand dryer ta busar da gashinta bayan ta gama ta Maida ta ajiye a inda yake sannan ta koma gaban mirron ta d'auko lotion d'inta masu dadin kamshi da tsada ta fara shafawa saman lallausar fatarta. bayan ta gama ta k'arasa gaban wardrobe d'inta ta d'auko wata cotton d'in doguwar riga marar nauyi wacce Bata kama taba Sosai sannan ta D'ora hula akai kalar rigar sannan ta fito daga d'akin zuwa main falorn gidan.


Iya Huda da muneefa ta tarar a falon zaune suna kallo ta k'araso cikin falon bakinta d'auke da sallama. Huda ta juya tana kallonta kafin ta ansa mata sannan ta Maida kanta kan tv tana cigaba da kallonta .muneefa kuma ta tafi da gudu ta rumgume Huyaam tace.


"oyoyo ya Huyaam tun d'azu nake lek'aki Baki tashi ba sai Yanzu".ta fad'a Tana murmushi . Huyaam ta ja mata kumatu tana murmushi tace.


"Gani yanzu na fito ai, Ina Ammie take?..."ta fad'a tana duba falon kamar zataga Ammien . muneefa tace.


"tana D'aki tanana shirya ya muneeb zazu tafi masallaci". HUYAAM ta Jin jina kai ta rik'o hannun muneefa suka k'arasa shigowa falon tare.


Huda ta juyo tana kallon HUYAAM tace.

"Ya jikin?...."

HUYAAM tai murmushi tace.


"Alhamdulillah shine wato ko ki tasheni koh?..."ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.Huda ta harareta kafin ta d'auke kai tana cewa.


"Hmm borin kunya kawai kikeyi ,ked'in ce zakiso na katse miki baccinki idan kinayi keda kamar kasa haka kike indai kina bacci ai ko tashin ki nai bazaki tashi ba..." HUYAAM ta harareta kafin tace.


"Me kike nufi wato nice ma kasa ko?....

Kafin Huda ta Bata ansa Ammie ta K'araso cikin falon tana kallan Huyaam tace .


"Daughtern Ammie ya jiki?..."Huyaam na murmushi tace.


"Naji sauk'i Ammie?..."Ammie tace .


"To Allah ya K'ara lafiya hope

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login