Showing 111001 words to 114000 words out of 140150 words

Chapter 38 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

171

sauka Maza Kuma acan b'angaren Bak'i Dake cikin palace d'in anan Suma aka sauke su.. Amare Kuma suna can b'angaren Antyn su ikleema wata k'anwar su Mai martaba mai suna Hajiya Amma ita ta ce su tattaro kayansu su dawo b'angaren Antyn su ikleema su sameta ita zata shirya su, Babu musu kuwa suka dawo tun a ranar da tazo ta...yanzu haka k'arfe sha biyu da Rabi ne na Rana,Hajiya Amma ce ta turo k'ofar bedroom d'in da Amaren ke ciki bayan tayi sallama.d'aga kai ya zulaihat tai dake zaune kan stool tana shafa lotion tana kallon Ammah.hajiya Ammah ta rufe k'ofar bayan ta shigo tana kallan ya zulaihat ta ce "wai zulaihat tun d'azu da nace kuyi wankan bakuyi ba sai yanzu ko ya_ya?" ya zalaihat ta sunkuyar da kanta k'asa ta ce cikin sanyin murya "Ammah d'azun ummi ce ta k'irani shiyasa ni banyi ba sai yanzu" Hajiya Ammah ta ce "Ina ita Bahijjan take?" Zulaihat ta kalli k'ofar toilet d'in ta ce "tana ciki wanka takeyi" Hajiya Amma ta sauke numfashi ta ce "to ke kiyi Maza ki fito ga Mai kwalliyar nan tana falon Antynku tana k'iranku kunga dai Yanzu saura one hour and some mintutes a d'aura auren, To gara ke ki fito a fara miki kwalliyar lokaci na tafiya" gyad'a mata kai ya zulaihat tai" daga haka Hajiya Ammah ta fita daga d'akin ta koma falon Antynsu ikleema Inda Mai kwalliyar take jiransu....


b'angaren Ammie Shima dai cike yake da Bak'in har cousin sisters d'inta Dake AURE anan kano da yaransu Suma duk sunzo wasu duk sunyi wanka sun shirya suna zaune a falo wasu Kuma suna cikin d'akunan suna wanka tunda yanzu k'arfe D'aya da mintuna.hadiman gidan kuwa sai kai da komowa suke acikin falon kowa Yana aikinsa. su Huyaam Kuma ana can d'aki anai musu make up.... Afeef ne ya saukowa daga stairs zuwa downstairs cikin shigar manyan kaya, yasha milk color d'in shadda da hula zanna bukar wacce ta dace da kayan jikinsa,sai takalmin Daya sa black kalar agogon hannunsa kayan sun masa kyau ba kad'an,Dan ya fito sak a babban mutum sai Wani tashin k'amshi yakeyi fuskar sa tayi Wani Irin fresh kamar Wani sabon ango sai dai fuskar dai babu yabo babu fallasa kamar ko yaushe Amma dai ya kame kansa kamar Wanda baya so akawo masa raini.tunda ya sauko mutanan Dake zaune falon suke kallansa shiko kallo D'aya yay musu Ya d'auke kansa harya k'arasa saukowa falon.da har zai nufi k'ofar falon ya fita Batare da yayiwa kowa magana ba sai Kuma ya fasa ganin akwai manya acikinsu gaishe su yayi cikin deep voice d'insa kamar Wanda baya son maganar.suko suka ansa masa da fara'a har suna tambayar sa kwana biyu shi ba'a Ganin sa wata da take a matsayin kanwar Ammie ce ta fad'a,D'an sakin fuskar tasa yayi Yana sosa kansa Amma baiyi magana ba har ya cigaba da tafiya zai fita daga falon Ammie ta sauko downstairs d'in tana kallan sa juyo wa yayi Jin muryar Ammie ya gaisheta ya ce "zan tafi masallacin Ammie" Ammie ta ce "Allah ya kiyaye" ansa mata yayi Yana fita daga falon gabad'aya....


K'arfe biyu da Rabi dai dai aka shaida d'aurin AUREN su ya zulaihat,Wanda ya samu halartar manyan mutane Wanda duk yawancinsu mutanan Mai martaba ne saboda shi duk suka zo ciki kuwa harda governor kano Dan mai martaba yayi gayya Babu laifi shima.bayan angama anyi reception wasu Bak'in duk suka fara tafiya. alokacin ne Kuma angwaye da Dan dazon abokan su suka shigo cikin palace d'in yin gaisuwar iyaye kowa ya nufi b'angarensa surukansa shida rakiyar abokansa....wata k'anwar hajiya Aysha ce ta ce mutanen Dake falon kowa ya kimtsa ga angon zulaihat nan ya shigo da abokan sa, kimtsawa kowa ya farayi har suka shigo bayan an Basu Iznin shiga sukai gaisuwa bayan sun gama akace za'a Rakasu b'angaren matan sarki su Gaida da su,nan suka fito suka nufi b'angaren Ammie kafin na Fulani Salamatu tunda Ammie ita ce a farko... Ammie na zaune a main falor tareda su Anty khadija da sauran Bak'in Dake b'angaren angwaye suka shigo cikin ladabi suka duk'a har k'asa suka shiga gaishe da Ammie da Sauran mutanan wajen cikin girmamawa. Nan kowa ya ansa musu da kulawa.basu jima ba sukai wa Ammie sallama suka fita sukai b'angaren Fulani Salamatu....


K'arfe 8 dai dai akace za'ayi rakiyar Amare.dan ko wacce a yau za'a kaita gidan ta,tare da key d'in motocin da Mai martaba ya bawa ko Wacce acikin su d'ai d'ai Kuma acikinta Za'a kaita .ita dama ya Bahijja anan kano zasu zauna ya zulaihat ce dai zasuyi two weeks Anan Kano kafin nan da two weeks tabi mijinta zuwa turai inda nan ne yake business d'in sa, Amma Kuma jere da komai duk anan gidan mijin Dake nan kano anan aka Mata jeran.Tun k'arfe bakwai da mintuna Arba'in motocin d'aukar Amaren suka iso kad'an ne suka iya shigowa cikin palace d'in sauran da akazo d'aukar Amaren dasu duk an barsu a nan bakin gate d'in palace d'in ne saboda yawan motacin Dake harabar gidan wanda duk aka fito dasu saboda hidimar bikin ne yasa ba'a Maida suba ma'ajiyar suba, duk suna Parke a nan compound d'in gidan shiyasa harabar palace d'in ta cika ba damar ashigo da wasu motocin duka....


K'arfe takwas da mintuna aka shigo da ya zulaihat b'angaren Ammie Dan itama tai mata Fad'a tareda da Dan dazon wad'an da zasuyi Mata rakiya zuwa gidan ta.kuka kawai ya zulaihat take tana sauraran Ammie Dake mata fad'a cikin sigar lallashi,har Ammie ta gama mata.ya zulaihat ta mik'e da k'yar ta rumgume Ammei tana kuka kamar me.Ammie na murmushi tana shafa bayanta kafin ta d'ago ta ta ce "Allah ya Baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba zulaihat".da k'yar dai ta saki Ammie nan aka kamata aka fitar da ita daga falon akai compound da ita zuwa wajen motar ta... Ammie na kallan su Huyaam da suke k'ok'arin bin bayan masu rakiyar ta ce "Ina zaku?" A tare suka juyo suna kallanta Suka ce rakiyar Amaren zamuyi" Ammie ta ce "A'a ku hak'ura ku dawo karkuje" Huyaam ta Bat'a Rai ta ce "harda su safnah fa zamu Ammie" Ammie ta ce "A'a nifa bana son ku fita da daddaren nan ku dawo kuyi zaman Ku a gida" wata k'awar Ammie Dake zaune a kusa da ita ta ce "ranki Dad'e da a k'yalesu Mana suje tunda naga ai ba iya su kad'ai zasu ba Ina harda sauran yaran gidan" Ammie ta ce "waye zai kaikun Dan gara Nasan Wanda zai kaisun"ta fad'a tana kallan matar.matar ta ce "eh wannan kan gaskiya ne"Huyaam tai saurin cewa "ya Aziz ne ya ce zai kaimu" ta fad'a tana Jin Kamar ta fad'i wani Abun zunubin,Dan in ba acikin shida lamid'o ta ce Wani ne zai kaisun ba tasan ba lallai Ammie ta yarda ba, Kuma tun d'azu ma Aziz d'in yay ta damunta da rok'onta akan idan har zasu kai Amarya Dan Allah zai kaisu,abinda yasa yanzun ma ta cewa Ammie shi zai kai su dan Ammien ta barsu ne yasa ta fad'i hakan.Ammie ta ce "tunda Aziz ne zai kaiku da sauk'i Amma Karku Dad'e Kuna zuwa kuce Aziz d'in ya dawo daku" ansamu mata Sukai suna fita daga falon gabad'aya....


Kallan HUYAAM siyama tai bayan sun fita daga b'angaren Ammie ta ce da sigar tsokana " ah lallai ne Huyaam wato mutumin da ake cewa ba'a so yau shi aka ce zai kaimu Kai Amarya? Ah lallai ya Aziz ya iya sace zuciya" ta fad'a Tana kallan Huyaam wacce ta kalleta a firgice lokaci D'aya nan siyama ta fashe da dariya" Huyaam ta harareta ta ce "waye ya iya sace zuciyar? Aini Banga Wanda ya isa ya sacemin zuciya ba kema kinsani Kuma shaida ce, tunda nace banasan sa to bana son nashin har abada Yanzum ma dan kada Ammie ta hanamu zuwa ne shiyasa kikaga nace mata shi zai kai mun Amma badan haka ba kema kinsan ko mutuwa ake ana dawowa bazan tab'a yadda na shiga motar Saba,Kuma Yanzun ma na fasa zuwa tunda har kika ce haka kuje ku nemi Wanda zai kaikun" ta fad'a tana makawa siyama harara tareda juyawa kamar zata koma b'angaren nasu.siyama tasa dariya tai saurin rik'o HUYAAM tana cewa sorry wallahi da wasa nake miki Dan Allah kiyi hak'uri" banza Huyaam tai mata tana k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da siyama tai mata" Saida Huda tasa baki tana Bata hak'urin sannan Huyaam ta hak'ura da k'yar suna nan tsaye saiga su ikleema sun iso wurin itada safna adai lokacin da wayar Huyaam tai ringing dubawa tai tana juyar da kanta gefe,sai taji Wani Iri ganin Aziz d'in ne ke k'ira kamar bazata tai picking sai kuma dai ta dai dai ta kanta ta saki ranta ganin yadda duk suka Zubo mata ido suna kallan ta, Dan kada ma su zargi Wani Abun a tsakaninta da Aziz d'in yasa ta ce "Hello! eh gamu nan mun fito kai muke jira" kashe wayar tai tana kallan su ta ce "ya ce gashi can muje" daga haka tai gaba Suka bi bayan ta suka nufi inda Aziz d'in ya ce musu Yana wurin...Huda ce ta shiga front seat d'in bayan sun k'arasa, Dan Huyaam k'in shiga tai_tai maza ta shige bayan Motar wurin su siyama Dan kad'a ma Siyaman ta ce mata ta Shiga. ta-da motar Aziz yay bayan sun shiga suka fice daga cikin palace d'in. Akan idon Afeef da shigowarsa gidan kenan Yana Jin gine jikin motar sa Yana answering call duk da darene Amma Kuma ya ganesu tunda ga hasken wutar lantarkin nan ko ta Ina Daya haske ko Ina na gidan Babu Wanda baza ka iya Gani ba a wannan daren saboda yadda haske ya bayyana a ko Wani angle dake gidan. kallan su kawai yake Dan tun da ya shigo gidan ya hangesu Babu wacce Bai Gane ba Acikinsu ,Yana kallan lokacin da suka nufi wajen motar Aziz har suka shiga,kallan motar kawai yake har suka fice daga cikin palace d'in gabad'aya ya sauke numfashi ya rufe motar ya nufi b'angarensu.....


_____________?&


A wajen palace d'in aziz ya tsaya da motarsa Yana jiran motocin dake gaban sa su wuce shima yabi bayansu.Huyaam dai Dake zaune bayan motar tana kallan yadda sauran motocin Amaren ke tafiya a hankali Kallan Huda Aziz yayi ya ce "wa zaku raka ne acikin su?" ikleema Dake Zaune a bayan motar tai saurin cewa ya zulaihat zamu fara rakawa saboda ita tafi nisa idan muka dawo sai mu biya gidan ya Bahijja" gyad'a kai Aziz yayi ya ja motar ganin motar da za'a kai ya zulaihat d'in tayi gaba tareda sauran motacin Dake gabansu haka nan dai ya bi bayansu.Saida motocin d'aukar ya zulaihat kaf suka fara wucewa sannan masu rakiyar Bahijja suka bi bayansu....Sun shiga har cikin gidan ya zulaihat Wanda ya gaji da tsaruwa da had'uwa basu Dad'e ba suka fito Dan Basu manta da gargad'in Ammie ba,daga nan Kuma gidan ya Bahijja suka nufa,itama gidan ta ya had'u sosai nan ma dai basu dad'eba suka fito daga cikin gidan gabad'aya suka shiga mota Suka koma gida...basu suka dawo gidan nan ba sai wajen k'arfe 10 da mintuna na dare lokacin har 'yan rakiyar Amaren wasu sun daddadawo.Aziz Yana yin parking duk suka fito kowa ya gaji Dan haka sukai sallama da junansu kowa ya wuce b'angaren su.binsu HUYAAM Aziz yayi da kallo yana son yayiwa Huyaam magana amma tak'i bashi fuskar Hakan tun a Hanya yake tai Mata message akan idan sun dawo gida ta daure ta tsaya ta Saura reshi Amma tak'i,Dan ko reply batai masa ba Kuma Yana da Tabbacin ta Gani kawai k'yaleshi tai.ganin su ikleema duk sun kusan shiga b'angaren su yasa yay saurin b'alle murfin motar ya fito yabi bayan su HUYAAM Yana K'iran sunan ta ganin suna gab da shiga b'angaren su. juyowa Siyama tai Ganin ana K'iran sunan HUYAAM haka ma Huda ita ko Huyaam tsaf ta Gane muryar sa yasa tai Banza ta k'yaleshi saima ta K'ara saurin tafiyar ta_ta. ganin Aziz ne yasa Huda ta ce "HUYAAM ki tsaya mana ya Aziz ne fa me K'iran ki?" Huyaam tai banza ta k'yalesu saima ta K'ara saurin tafiyar ta .siyama ma ta ce "Dan Allah Huyaam ki tsaya Kinga Babu Dad'i fa" juyowa Huyaam tai a fusace ta ce"wai Baku San Yaya Yana nan bane da zakuce na tsaya?idan ya fito ya sameni dashi fa Mai zance masa?be side ni bazan iya tsayawa ma dashi ba saboda Banda ra'ayin Hakan.Siyama ta ce "ai Kuma Yaya ma bazai tab'a kawowa Wani Abu ba tunda yasan ya Aziz ne ba Wani ba" Huyaam ta girgiza kai ta ce "dan Allah ku rabu Dani Huda wallahi bazan iya ba" Huda ta dafa ta ganin Aziz na Isowa gab da su ta ce "na rik'oki sis ki saurare shi Babu kyau walak'anta mutum, sannan mutum Irin ya Aziz ma ai Bai kamata ace Yana miki magana Kin rabu dashi ba, ki tuna Alkhairinsa garemu, please badan niba Dan Allah Huyaam ki tsaya ki Saura reshi kona 2 minutes ne Dan Allah" daga haka taja hannun siyama suka Shiga b'angaren nasu, Huyaam ta bisu da kallo sai Kuma ta juyo ta sunkuyar da kanta k'asa ganin Aziz d'in ya k'araso....
_
Aziz yay sallama Yana gyara tsayuwar sa lokaci D'aya Yana kallanta ita dai bata yadda ta d'ago da_ kanta ba, yay k'asa da murya ya ce "barka da wannan lokaci sweet" ya fad'a da Wani Irin shaukin Santa ganin yadda ta k'ara masa kyau ba kad'an ba" Banza tai dashi ta K'ara tsuke fuska ta Aziz yay murmushi ya cigaba ya ce "please sweet kimin magana ko zanji Dad'i mana?" ya fad'a Yana Wani kashe murya.kamar Huyaam baza ta ce komai ba sai Kuma can ta ce Batare da ta kalleshi ba "Dan Allah ka Fad'i abinda zaka fad'a na tafi kar yaya yazo ya same ni" ta fad'a cikin tsoro. Aziz ya K'ara sakin Wani murmushin Yana shafa sajensa ya ce "in Sha Allah bazai ma ganki ba Kuma idan ya gankima nasan Babu Abinda zai miki tunda ai yasan nine" Huyaam ta K'ara Kau da kanta gefe ta ce "nidai kaga na tafi" ta fad'a tana k'ok'arin juyawa zata bar Wajen Aziz yay saurin cewa" Noo! Please ,haba sweet dan Allah karki tafi" ya fad'a da Wani Irin sauti, Huyaam Bata saurareshi ba ta juya gabad'aya da nufin Shiga b'angaren su sukai ido hud'u da Afeef dayake D'an nesa dasu .Wani Irin rass gaban ta ya Bada sauti take zufa ya keto mata Wani Irin tsoro da firgici suka shige ta lokaci D'aya. Shiko Aziz baima Kula da Afeef saboda Baya ya bashi Kuma idonsa ya makance a akon San Huyaam ta saurare shi ya ce"okay thank you for your time and good night sweet love".ya fad'a da d'an k'arfi Yana juyawa yabar wajen ganin tak'i sauraransa.sauke idonta k'asa Huyaam tai tana kasa kallan Afeef saboda irin kallon da yake mata .shidai Afeef kallanta Kawai yake sama da k'asa Dan Fitowar sa daga b'angaren nasu Kenan zaije ya d'auko a Abu a mota tun daga nesa yake kallansun yana mamakin Mai ya tsaida Huyaam da Wani Kuma ganin Aziz ne yasa mamakinsa linkuwa har yaga ya juya ya bar wajen bai daina kallansa ba, Yana mamakin Maiya tsaida su su biyun.da k'yar Huyaam ta iya d'aga k'afarta tai saurin shigawa b'angaren nasu da sauri tana dafe k'irjinta Dake bugawa da k'arfi har tana had'awa da gudu a haka har ta shige cikin falon nasu batare da ta tsaya ba tana toshe bakinta da Kuka keson kufce mata ai da gudu ta haura stairs bayan ta shiga Falon ta shige d'akinta ta rufo k'ofar har tana murza key sannan ta jingina da k'ofar ta saki Kukan da take ta rik'ewa tana cewa ta shiga uku shikenan yayansu zai kasheta su Huda sun ja za mata bala'i dama Saida tace yayansu zai gansu Amma suka ce ba haka ba gashi Yanzu ya gansu ai, da k'yar da Jan k'afa ta k'arasa cikin d'akin ta fad'a Saman gadon tana cigaba da Kukan ta kamar Wanda aka Mata wani abun,tana cikin kukan taji ana knocking k'ofar,ai da Wani Irin expression ta d'ago da kanta tana kallan k'ofar tana yarfe Hannu k'irjinta na bugawa da k'arfi tana cewa ta shiga uku ta lalace gashi yanzu Afeef ya biyota har d'akinta zai kashe ta tana ji Aka K'ara knocking d'in for the second time Amma ta kasa tashi bare ta iya Bud'e wa.sai ma Wani marayan ihun kuka data saki tana yarfe hannuwanta.....



Saura 2 page mu gama Free pages saboda haka ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =?G?

Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =?G?

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =?G?
07066508376



*Yan Niger 07066508376


# # # # #


*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Assalamualaikum warahmatullah.*

*Ina kuke manyan mata masu capacity =???=???? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >??? da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=???=??? wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire
*To idan yau kuka tab'a ji????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login