Showing 108001 words to 111000 words out of 140150 words

Chapter 37 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

217

mata kai Huyaam tai tana kallon Mai kwalliyar ta ce "angama ne? Gyad'a mata kai Mai kwalliyar tai tana cewa "eh angama" tafad'a tana murmushi.mik'ewa Huyaam tai ta nufi k'ofar fi????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ta ganin har Huda ta fita daga d'akin Mai kwalliyar ta bita da kallo tana Yaba kyawunta bama ita kad'ai ba kusan dukansu ma kyau ne dasu Jin jina kai tai nan ta cigaba da har had'a kayanta...


A can Wani k'aton fili dake tsakiyar b'angaren su Ammie da Kuma b'angaren su ikleema yazamto wurin yana tsakiyar b'angaren su Ammie kenan, to anan za'ayi cocktail partyn. anyiwa wajen decorations na musamman ga table da aka jejjera Wanda ko wanne ke d'auke da kujeru Suma duk an musu decorations wajen dai ya tsaru yayi kyau ba kad'an ba. K'arfe biyar da mintuna wurin ya fara cika da Dan dazon mutane 'yan uwa da abokan arzik'i Wanda duk yawancinsu 'yan mata ne tunda wannan partyn na iya Amarene da k'awayensu sai k'ananun su Irin su Huyaam kenan,k'awayen Amaren sun zo duk sun Sha anko anci kwalliya ba kad'an ba.su Huyaam ma sun k'araso wajen su biyar abinsu har siyama da Huda da safna sai ikleema banda Aziza wacce ta ware kanta tak'i shiga cikin su, saima ta samu wasu 'yan uwansu Sa'an ninta ta shige cikinsu. Wuri ya cika mak'il Amare kawai ake jira su Huyaam suna zaune a wurin zamansu da aka tana dar musu.suna nan Zaune babu Dad'ewa Amare suka k'araso wajen partyn take waje ya d'auki Sowa masu pictures suna yi ta ko Ina masu busa sarewa da tamburan sarauta nayi a haka har suka k'arasa wajen zamansu da aka tana da domin su tareda rakiyar k'awayensu .angwaye dai Basu zoba sai gobe idan za'a Yi dinner. Bayan sun zauna nan aka shiga fara gudanar da shagalin partyn cikin nutsuwa Babu Wani Baragada bare hayaniya Abu dai akayi na masu class saboda kowa kika gani a wurin iyayensu suna da kud'i dan kuwa dukansu 'ya'yan manya mutane ne. K'arfe takwas da mintuna aka tashi daga Taron masu tafiya gida kowa ya kama Hanya, wad'an da kuma ba'a garin suke ba sunzo ne har a gama bikin duk sun Wuce masaukinsu. Agajiye Huyaam suka koma part d'insu,cikin sauri ta cire kayan jikinta bayan ta shiga d'akinta ta d'aura towel ta Shige toilet d'in Dake d'akin . fuskarta ta fara wankewa da sabulu Saida ta wanke ta tas sannan tai wanka bayan ta gama ta d'auro alwala ta fito shaf shaf ta Saka wata doguwar riga marar nauyi ta d'auki gogoggen hijab d'inta tasaka ta k'arasa ta d'auko darduma ta shimfid'a nan tsakiyar d'akin ta fara rama sallolin da suke kanta both magrib and isha'i....da daddare wajen k'arfe 10 na dare har Huyaam ta kwanta bacci Dan yau da wuri ta kwanta saboda gajiyar shiga da ficen da Sukayi, ta baro su siyama da Huda dai afalo Dan sunce su ba yanzu zasu kwanta ba,K'ara gyara kwanciyar ta tai nan taji wayarta na ringing,jawo wayar tai tana duba Mai K'iran,tsuke fuska tai lokaci D'aya Ganin Abdallah shattima ne ke K'iranta take ta jaa D'an k'aramin tsaki tai rejecting call d'in ko ajiye wayar bata kai ga Yi ba saiga K'iran Aziz chiroma nan ya shigo wayar tata dafe kanta tai tana jin Wani Irin k'ululun Bak'in ciki Daya to kare mata k'irji lokaci d'aya taji wata zufa na keto Mata ita kan ta shiga uku yanzu ace haka zata tafiyar da rayuwar ta kullum acikin tsoro da fad'uwar gaba akan abinda zai je ya dawo akan masu K'iran nan nata duk ranar da wani ya gani tsakanin yayansu da Ammie.lokaci d'aya wasu zafafan hawayen tausayin kanta suka shiga ziraro mata a fuskarta.nan ta kifa kanta acikin filo tana rare kuka a hankali tana jin wayar nata ringing Amma Bata iya yin picking ba daga k'arshe ma ganin baza'a tab'a hak'ura da K'iran ba yasa ta kashe wayar gabad'aya a fusace ta jefar nan saman gadon ta juya baya ta kwanta tana rera kuka k'asa k'asa a haka har bacci ya d'auketa....


Washe gari da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi ana ta shirye shiryen tafiya dinner.kowa ya ci kwalliya daga iyaye har yaran Babu Wanda aka barshi a Baya, bak'i ma da suka zo na kusa Dana nesa both 'yan uwan Hajiya Lubabatu da Hajiya Aysha sai 'yan uwansu baba turaki da Baba wambai Wanda dama su duk family D'aya ne tunda 'yan uwansu ne na jini.anyi general anko na musamman na dinner Wanda aka ware just for iya 'yan uwa da abokan arzik'i ne akayi shi,less ne kowa ya D'inka Mai bala'in tsada.sai ankon dinner Wanda aka ware na musamman na iya Yaran cikin palace d'in daga kan su ya Zarah zuwa su Huyaam iri D'aya akai musu sai sauran Yara kamar su muneefa Suma kalar nasu daban sunyi kyau ba kad'an.nikan an Kon dinner nasu na yau ne ya K'ara d'aukar hankali na Dan kuwa Wani rantsatstsan less material akai musu gabad'ayansu iri D'aya dukan su tun daga yaran har su 'Yan matan irinsu ya Zarah da Salima Dan kuwa komai iri D'aya akai musu kalar ce kawai ta banbanta. Su nasu Huyaam maroon color ne sai nasu muneefa Wanda ya kasance pitch color ne nasun,kayan sunyi musu kyau ba kad'an ba,Dan yau ma dai Mai kwalliyar ta k'ara tsantsara musu dukan su ukun har siyama,dama kwalliyar ta kwana uku Ammie ta ce zatai musu.....


Motoci ne kawai ta ko Ina a Cikin harabar palace d'in nan, wasu na shiga wasu na fita,Dan yau ba'a Cikin palace d'in za'ayi dinner ba acan Wani k'aton hole ne Dake cikin government house acan za'a Yi dinner. Duk motar da kika ga dama ita zaki shiga, Dan kuwa motocine wali ishi a harabar palace d'in wasu ma Sabi ne dal aka fito dasu ba'a tab'a hawan suba sai a ranar a Kuma ciki Za'a debi mutane akai su wurin dinner Dan kuwa saboda bikin kawai aka fito dasu.motar Amare kuwa suma duka Sabi dal aka fito dasu aciki za'a kaisu.ana ta wannan had'a hadar Amma Banga su Huyaam ba Dan kuwa naga har an fara d'iban mutane ana tafiya dasu.sai da na d'aga kaina can na hango su suna tsaye daga gefe suna kallan yadda ake ta d'aukar mutane a cikin motocin sai tafiya suke Amma su sunja gefe sun tsaya siyama data gaji da tsayuwar ta Kallesu ta ce "wai mu a wacce motar zamu tafi ne da muka ja muka tsaya anan ne? Ta fad'a tana kallan su Safna ta ce "nima abinda nake tunani kenan, Amma yanzu kuzo muje mu shiga waccen Motar naga kamar Babu kowa aciki" Huda ta ce "to muje" har sun fara tafiya wayar Safna tai k'asa alamar shigowar k'ira.picking tai Ganin Mai K'iran ta ce "hello Yaya" daga D'aya bangaren akai mata magana ta ce "okay Tom muna jiranka" daga haka ta sauke wayar Bayan taji abinda aka fad'a matan tana kallan su Huyaam Wanda suma kallan nata suke tace "Ya lamid'o ne yace mu jira shi zai fito yanzu ya kaimu" ai Huyaam na Jin haka taji gabanta ya Wani Irin Fad'uwa Dan kuwa haka kawai taji Bata son ace lamid'o ne zai kaisu kwata kwata, duk da kuwa rabon da su sake had'uwa dashi tun ranar daya kaisu wurin tailor nan.suko su Huda ko ajikinsu saima murna da suke tayi Jin Lamid'o ne zai kaisu.Sauke numfashi tai Ganin siyama ta dafa ta ta ce "what happened naga mood d'inki ya sauya?" Murmushin yak'e Huyaam tai mata tace "nothing" adai dai lokacin da mota tai parking a inda suke tsaye ya sauke glass Yana kallansu idan su ya sark'e cikin na juna da Huyaam Amma sai tai saurin d'auke kanta tana mayar wa gefe gaban ta na fad'uwa.Huda tai murmushi ta Kallesu ta ce "shine kuzo mu shiga" ta fad'a tana yin gaba bin Bayan ta sukai siyama na rik'e da Hannun HUYAAM wacce jikinta yake a Sanyaye har suka k'araso wajen motar suka Shiga back seat, wannan Karan Huda ce a front seat.bayan sun shiga lamid'o Yaja Motar suka fita daga cikin palace d'in gabad'aya suka d'au titi sai government house. akan idon Aziz Dake tsaye daga can gefe a harabar gidan komai ya faru ya furzar da huci Mai zafi Yana Jin zuciyar Wani iri shida yake da niyar ya kaisu Amma Kuma sai yaga sun shiga wata motar sauke numfashi yayi nan ya juya koma b'angaren su Dan Hajiya lababatu tace shi zai kaisu........


_____________?&


Har suka isa government house lamid'o Yay parking a dai dai k'ofar babban hole d'in inda anan ne za'a Yi dinner Huyaam a takure take, Dan kuwa yauma dai lamid'o da Wani irin k'urullan kallo kawai yake binta dashi tunda suka taho Kuma data d'ago da kanta saita ga idonsa Yana kanta.ta ras a ya zatayi. sauke numfashin salama tai Ganin har sun iso hole d'in,ai Yana yin parking da sauri ta b'alle murfin motar ta fita taja gefe ta juya baya ta tsaya tana jiransu Dan dama itace a farko. Godiya sukai masa bayan sun fito daga cikin motar gabad'ayansu ,ansa musu yay da ka kafin ya ce "idan antashi daga dinner sumai magana shi zai Maida su, ansa masa sukai tare da k'ara Yi masa godiya daga haka suka shige cikin hole d'in gabad'aya .suna shiga nan suka tadda wurin acike mak'il da Dan dazon mutane ta ko Ina ga kid'a na tashi gefe guda kuma masu busa sarewa da tamburan sarauta nayi suna tai wa mutane da Ka'nnen amaren kirari.nan suka k'arasa suka nemi wurin zaman suka zauna. Babu dad'ewa saiga su Ammie Suma sun Shigo wurin itada Hajiya Aysha maman amarya da Anty khadija cikin shiga ta Alfarma Ammie tasha alkyabba sai Wani walwali take Yi fuskarta cike da annuri ga hadimarta Mai rik'e mata jaka tana biye da ita a abayanta gabad'aya mutanan wurin mik'ewa sukai alamar girmamawa ganin shigowar matar sarki sai kallonsu suke suna furta masha Allah,masu busa sarewa da tamburan sarauta kuwa sai suka K'ara himma wajen Yi,sai masu kirari Wanda sukai tai wa Ammie da uwar Amarya har suka k'arasa wurin da aka tanadar musu na musamman saboda su, sai sauran k'awayensu Dake biye dasu abayansu da Suma suka samu wuri kusa dana su Ammie suka Zauna.daga bayansu kuma Hajiya Lubabatu da Fulani Salamatu ne Suma suka shigo cikin shiga ta Alfarma Suma sunyi kyau ba kad'an ba nan ma dai kirarin akai tai musu har suka k'arasa wurin zamansu inda yake opposite da na su Ammie suka zauna.babu dad'ewa Amare suka k'araso tareda da angwayensu, Masha Allah haka na furta araina Dan kuwa sunyi kyau ba kad'an ba idan ka kallesu dole ka sake kallansu saboda had'uwar da Sukayi.kirari a kai Tai musu har suka isa wurin zamansu inda aka tanadar musu.nan da nan aka shiga gunadar da shagali dinner anan akai bud'ar kai kowa yazo ya Zuba kud'insa Kuma kudi ba k'ana nan kud'ad'e ba mak'u dai Ammie ma ta zuba nata million uku uku ta zuba wa duka amaren ,ganin Haka yasa da akazo kan Fulani Salamatu itama tasa 4_4 million ita adole saita fi Ammie,oho itakan Ammie Bata ma san tanayi ba domin ita zuciyar ta D'aya tasa kud'in nan. Haka har aka gama taro aka watse aka maida kowa gida kamar yadda aka kawo su, wannan Karan ma dai lamid'o ne ya Maida su Huyaam kamar yadda ya fad'a.aikuwa Yana yin parking a compound Huyaam tai saurin ficewa daga cikin motar ta shige b'angaren su da sauri Batare da ta jira kowa ba,Bata kula ma su siyama ba Dake ta K'iran sunan taba.....


Tana shiga b'angaren su falon ta Bud'e ta shiga Babu kowa aciki Hakanan yasa ta K'arasa shiga ciki harta nufi stairs zata haura sama kenan kawai taga Afeef Yana zaune a dining Yana sipping drinks zaro ido tai tare da k'walla wata iriyar K'ara.Afeef da tunda yaji an Bud'e k'ofar falon ya d'aga kansa Yana kallan k'ofar har aka shigo dayaga itace ya zuba mata ido Yana kallanta baya ko kiftawa.daka matsa tsawa yayi ganin tana masa ihu Kuma yaji shi har tsakiyar kansa,Bata saurare Shiba ta cigaba da ihunta ganin yadda take ihu bilhakki da gaskiya zata juya da gudu ta fita daga falon yasa Afeef yay saurin mik'ewa tsaye ya fito daga dining d'in gabad'aya cikin few seconds ya isa gareta ya rik'o ta yana cewa "miye Hakan? kuka kawai Huyaam take tana kallan sa Dan a gaskiya bata yadda Afeef bane tunda babu Wanda ya fad'a mata cewa zai dawo ko Yana hanya Dan ko Ammie bata fad'a musu ba bare su San zai dawo d'in ,Dan ita duk d'aukarta aljanine yayi siffarsa ya bayyana a agareta bashi ba. Ganin Bata daina ihun ba yasa Afeef ya fara kalle kalle a falon Dan baya son Wani daga cikin hadiman gidan su jiyo ihun Huyaam Hakan yasa ya toshe mata Baki ta tafukan Hannunsa ya jata zuwa d'akin su Dake nan downstairs stairs ya rufe k'ofar adai dai lokacin da su Huda suka shigo falon..Yana kallan Huyaam Ganin yadda take zaro ido waje ya K'ara rufe mata Bakin ta yadda Babu damar tai ihun ya K'ara tsuke fuska tana kallan ta yay k'asa da murya yace cikin deep voice d'insa "ihun me kikeyi haka? Girgiza masa kai Huyaam tai har lokacin gaban ta Bai daina fad'uwa ba,Dan ba Bak'ara min tsoro taji ganin sa ba,yana kallan har sannan ya ce "tsoro kika ji Dan kin ganni? Gyad'a masa kai tai da sauri ya ce "relax nine ba Wani ba d'azu na dawo okay" nan ma gyad'a masa kan tai tana kallan sa ya ce "tunda yanzu kinji nine karki sake ki k'ara yimin ihu kinji na fad'a miki" ya fad'a cikin fad'a.daga haka ya sake ta zamewa tai ta zauna a k'asa dab'as shi Kuma Afeef ya Bud'e k'ofar fito daga d'akin gabad'aya bayan ya kullo K'ofar.yana zuwa falon bai Tadda kowa ba Yana dai Jin hayaniyar su Huda da siyama a saman. k'arasawa dining d'in yayi ya d'auki wayoyinsa ya bar wajen ya haura stairs zuwa b'angarensu....sai Da Huyaam tai kusan 20 minutes a inda take zaune bata iya tashi ba saboda shock d'in da ta shiga lokaci D'aya, Dan Bata tab'a tunanin yayansu na hanya ba ko kad'an, mik'ewa tsaye tai a hankali ta fita daga d'akin gabad'aya bayan ta kullo k'ofar. Falon ta fito ganin babu kowa Shi d'in ma baya nan yasa ta haura sama da sauri tana waige waige......



# # # # #


Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =?G?

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =?G?
07066508376



*Yan Niger 07066508376


*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity =???=???? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >??? da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=???=??? wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire
*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire
*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*

*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*



My channel link =?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y


*Bismillahirrahmanirrahim*



PAGE 4?? 0??


___________?&


Washe gari da safe Kuma da shirye shiryen d'aurin AUREN aka Tashi,tun daga k'arfe 11am na safe Bak'i suka fara sauka a cikin palace d'in,manyan Bak'i wad'an ba ba'a kusa suke ba daga nesa zasu taso zuzo Irin su sarakuna da da governor ni da Manyan 'yan kasuwanni wad'an da suke abokan Mai martaba tun kafin k'arfe Sha biyu suka iso, suna can an sauke su a masauki Mai kyau cikin palace a fadar mai martaba.suna can suna hutawa Kafin lokacin d'aurin AUREN yayi,Dan k'arfe 2:00pm dai dai bayan anyi sallahn juma'a za'a d'aura auren. Ga DSS da police na governor's d'in da suka zo Wanda Suke a matsayin guard d'insu sai shawagi suke a harabar masarutar Kano Dan bawa ubayen gidan nasu TSARO na musamman ke kyace Wani abun ne ya faru marar kyau...Acikin gida kuwa nan ma dam yake da mutane 'yan uwa da abokan arzik'i both b'angagarorin Dake gidan har na Ammie da fulani Salamatu duk akwai mutane aciki saboda gabad'aya familyn su Mai martaba duk sun zo bikin,matan da suka zo Kuma a part d'in matan gidan suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login